HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   30 / 53

87K to 90K   out of 158.4K words

ya haukace tsoro ya rufe su, bindiga ya zaro
"Ko ku faWa min me nayi muku da kuka zalunceni ko kuma dukkanku in kashe ku... Me na muku???"
Da wani irin tsawa yayi maganan duk suna zube a ?asa a gigice don yadda yaken nan tsaff sai ya harbe su, a darare Yaya ya fara cewa

"Kayi ha?uri Don Allah ka yi ha?uri.."
Gini ya harba karar bindigar ya saka Yaya fitsari Sabrina da Gaje suka tafi a sume, ruwa ya kwaso ya zo ya kwarara musu yana nuna gini
"Kun ga yadda ginin nan ya fashe ko? Toh billahi ko ku faWa min ko in fashe kawunanku haka"

"ka saurareni ka yi hakuri zan faWa wlh zan fada maka..! Mahaifiyarka da ni mun kasance 'yan uba tun da muka tashi iyayenmu mata ke nuna mana ba Waya muke ba, hakan yasa muka tashi da wani irin ?in juna a zuciya, sai kuma Allah ya daukaka Hussaina hakan ya ?ara mini hassada da ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kyashinta barin ma da muka rasa iyaye bata daukeni dan uwa kuma abokin shawarar ta ba, bata kula ni ko 'ya'yana sai in bukatarta ne ya kawo ta wurin mu, ta daukeni tamkar Wan gidanta bata girmamani babu ruwanta da kyautata mini tana nuna min itama wahalar ta ya sama mata in tashi in nema anan na ?udiri aniyar mayar da dukiyar ta nawa, mun yi shige shige dayawa a baya kasancewar kana yawan zuwa duk ruwan da za mu baka akwai wani asiri ciki sai dai duk basa kama ka saboda kana neman kariya kuma kana Adu'a, har ma mun fitar da ran samunka muke tura yarinyar mu nema mana kuWi da surarta don muna so itama ta auri mai kuWi mu kerewa Hussaina(Mommy) sai kwatsam ta dawo da son zuciyarta garemu... Mun yi amfani da hakan Allah kuma ya bamu dama saboda ba don Allah ta neme mu ba muka juye ka ka zama sai abin da Sabrina ta ce..."

Hawaye ne ke sauka mishi a haukace yace
"Ni na zama kwallonku kenan?? Ni ne da nake tausaya muku nake taimakonku daidai gwargwado kuka zaSi salwantarwa da tura ni cikin fushin ubangiji??"
"Kayi hakuri don Allah! Ka yi hakuri..."
"Ku tashi ku fita a gidan nan har abada kar ku bari fuskata ta kalli naku... Duk ranar da hakan ta kasance sai na sa bindigata na harbe ku ku fita nace!!!"

A gigice suka mi?e suna ji suna gani suka fita da kayan jikinsu kawai don ko cokali ya hana su Wauka duk tatsarshi da suka dinga yi na kuWi suna boyewa duk yana cikin gidan, ko takalmi babu kafafunsu haka suka fita rike da Sabrina da ta sauya kamanni tana ta kuka barin ma da ya furta ya sake ta saki biyu ta je ta ?arata..
(?arshen alewa ?asa!)

Su mommy suna zaune suna kallon sunna Tv da ake hasko wa'azin likitan zuciya wato sheikh tijjani Ahmad yusuf guruntum kawai suka ga an turo kofa an shigo, a razane suka mi?e tsaye sai ganin Saleem suka yi yana tahowa yana haWa hanya a rikice mommy ta nufe shi
"Saleem..! Saleem...!! Kai ne? Kai ne da gaske.."
Taro shi tayi ganin zai faWi yana furta
"Mo..myy"
Sai ya sume musu..





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*37*

Bayan ta tashi daga baccin da ya dau?eta tun bayan Sallar asuba wanka tayi ta shirya cikin wata doguwar riga mai hannun roba purple da ya amsheta ta Waura dankwalin a kanta sai ta nufi sashen mammi don gaisheta, da sallama ta sanya kanta ciki ta ga mammin kwance a kan sallayar da tayi sallah ta Wora kanta saman pillow tasbihi take a hankali tana ta maimaita

"Allahumma inni As'aluka husnal khatima, Allahummar ruzu?nee taubatan nasuha qablal maut, Allahumma ya musalibbal quluub thabbit qalby ala dinika, ya musarrafar quluub sarraf quluubina ala Wa'atik..!"
Abin da ta lura kusan kullum a kwanakin ya zama tasbihin Mammi kenan, a ganganta ta zauna

"Mammi...kina lafiya?"
Tayi tambayar hankalinta na kan mammin gabaWaya ganin yanayinta kaman marar lafiya lumshe idanu mammin tayi ta buWe kan ta ce a hankali
"Afeefah je ki buWe bedside za ki ga wani kwali ki Wauko"
Mi?ewa tayi taje ta buWe ta Wauko ta dawo tana zama ri?e dashi
"Mammi gashinan!"
Mammin bata motsa daga kwancen ba don bata jin zata iya tashi tace a hankali
"Afeefah ki buWe ki gani menene ciki?"

BuWewa tayi sai ta ga set ne na dankunne sarka da abin hannu da kuma zobe, daga gani ka san ba ?arami bane don ma bata san gold ba da sai ta ce wannan Win gold ne babba ma don yadda yayi wani irin kyau ga Waukar ido.
"Set na sarka ne Mammi"
"Masha Allah, sadakinki kenan da na yi amfani dashi na saya miki wannan kadarar, ki ri?e a wurin ki naki ne halak malak ban baki tsabar kudin bane don na san ba zai ajiyu ba amma wannan ko shekara nawa zai yi a zaune babu abin da zai yi sai ma darajar shi ya ninku"

Rasa bakin godiya Afeefah tayi sai hawaye ya shiga ziraro mata
"Mammi kin yi min komai a wannan duniyar ba ni da abin da zan saka miki face Adu'ar Allah ubangiji ya baki lafiya, Allah ya yaye miki wannan ciwo ya kawo mana karshensa mu ga kema kin warke kaman kowa, Allah ya sa kaffara kika yi"
"Ai lafiyar ta zo ma Afeefah"
Ta faWa tana rufe idanu jin yadda take jin ciwo mai tsanani a ciki da ma jikinta gabaWaya.

"Mammi...!"
Sai ta ga wani irin zufa na karyo mata numfashinta na fita da kyar da kyar har chasbin hannunta na zamewa da kanshi, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ta da gudu ta mi?e ta fito sai tayi side Winsu kaman za ta kifa haka ta tura kofan ta same shi tsaye gaban madubi, ba zata ce ga yadda ta riske shi ba ita dai ta san ta isa gabanshi tare da ri?e hannunshi

"Mammi...! Mammi.."
"Me ya sameta?"
Ya faWa hankalinshi na tashi lokaci Waya, ganin duk ta ruWe yace
"Je ina zuwa"
Fita tayi da sauri shi kuwa ya Wauki boxers kawai ya saka da jallabiya tare da zaran keyn mota kafafunshi ma silifas ce ta wanka ya fice da hanzari, yanayin da ya sameta sai da ya ?ara Waga masa hankali haka ya Wauketa Afeefah na ta kuka suka nufi Asibiti duk ma'aikatan hankalinsu ya tashi da sauri aka karSeta sai oxygen aka sanya mata sun yi iya kokarinsu har numfashinta ya Wan daidaitu, Rayyan dai ya kasa aikata komai don ba karamin girgiza yayi ba duk tashin ciwonta bai taSa ganin kaman wannan ba, bai zaci za su iso asibitin da ranta ba jikinshi rawa kawai yake yana tsaye daga gefe yana kallonsu a sadda zuciyarshi ke cigaba da bugawa kaman zai fashe, idanunshi sun rine sai adu'a yake yana ro?on Allah akan ya bata sau?i a ranshi.

Ganin ta dawo daidai oxygen Win na tafiya a hankali ba kaman daga farko ba da in ta ja kaman ba zata sau?e ba ya isa gangarta ya ri?e hannunta kawai ya zauna, a jikin gadon ya Waura kanshi yana danne abinda yake ji na taso mishi, ina ma da zai iya kuka da yayi ko don samun sassaucin abinda yake ji a ranshi da ma kwakwalwanshi!

Ba zai ce ga adadin lokutan da ya Wauka zaune a wurin cikin wannan yanayi ba chan dai ya ji kaman ana shafa suman kanshi da Wan hanzari ya Wago sai suka haWa idanu tana ta kallonshi, gyara zama yayi yana kirkiro murmushi mai nauyi ya ce
"Mammi na! Kin farka? Ya jikin?"
Ta sake yin murmushi a hankali ta nuna mishi oxygen na hancinta sai ya cire yana jin yadda take sauke numfashi a kai akai
"Mammi ki yi saving energy Winki kar ki yi magana kin ji?"
Ta sake yin murmushi
"Ina so na ji abin da ke bakin ka! Ka ba ni labari...tun jiya na lura kana son min magana amma kana ri?e wa menene?"
Shiru ya Wan yi
"Speak up Saraki, yanzu ne kake da lokacin magana da ni anjima kaWan kila sai dai matarka ko 'yan uwanka"
Da sauri ya Wan kalleta tana ta murmushi, kanshi ya du?ar a hankali ya fara furta

"Mammi ki daina irin wannan maganan don Allah"
"Toh na daina Saraki!"
Ta faWa tana lumshe ido, hannunshi dake cikin nata ne ya ?ara yin sanyi she can feel the nervousness a cikin tafin hannunshi zata iya cewa yana cikin yanayi ne marar fasaltuwa sai dai da yake namiji ne kuma jarumi yana iya shanye damuwarshi kaman babu komai.

Idan Mammi ta tafi ba tare da ya sanar da ita menene a ?asan Ranshi ba tabbas zai yi nadama mai girma, tunaninsa ya dinga rarrabuwa har yana jin kaman zai zauce idan ya cigaba da zurfafa a cikin muguwar tafiyar rayuwarshi...iya tunanin kaWai kan karya duk wani guntun karsashinsa.

*****

A hankali yake buWe idanunshi har ya ware su akan Mommy da su Sadiqa dake zaune a Wakin jugum jugum.
"Saleem! Ka farka? Sannu ko mu je asibiti ne?"
Girgiza kai yayi yana Mi?ewa zaune jikin gadon ya kalli mommy da ita ma take kallonshi a hankali yace
"Mommy na tuba! Mommy ki yafe min wallahi...."
"Shhhh Saleem na sani, na san ba da saninka ka aikata hakan ba na san baka cikin hankalinka a lokacin da komai ke faruwa, laifina ne wlh laifina ne ka yafe min Saleem son zuciya Sacinta, hakika na yi amfani da son zuciyata wurin WaiWaita maka rayuwa don Allah ka gafarceni"
Ta roka yafiyarshi tana kuka su ma duk su sadika suka shiga bashi hakuri, anan ya zauna yana jin yadda komai ya kasance... Hakika mommy ta yi kuskure Afeefah ce ta faWo mishi a rai ko tana cikin wani hali yanzu? Ko ya rayuwa yayi da ita? Allah masani


******

"Mammi..!"
Ya sake ?ira a karo na biyu ba tare da ta buWe ido ba tace
"Uhmm"
"Zan faWa miki ne, zan faWa miki wanene ni..."
Da sauri ta buWe ido ta kalleshi cikin yanayin jin jiki ta zura mishi idanun a hankali ya cigaba da cewa
"Ban manta komai ba, na ?i faWa ne saboda wacce daraja da ?imarta suka zama ?ololuwa a gare ni ta yi fatali da hakan ta Wauke ni ta yasar tamkar tsumma a cikin al'ummar da ba ni da masaniyar yaya suke bare ya rayuwarsu take, ya al'adarsu take ko ya imaninsu yake, ba tare da ta damu da zan ci ko bazan ci ba, shin rayuwata za ta inganta ko za ta yi lalacewa marar iyaka? kafin na haWu da ke na zaci uwa masifa ce ga 'ya'yanta ta kan nesanta su da farin ciki ta saya musu wahala, ta kan zama tamkar ginin ?asa da muddin Wa ya jingina da ita sai ya faWi, a maimakon ta kasance garkuwata sai ta zama ita ce a farkon cutar da rayuwata, na kasance a koyaushe bana rufe idanu na buWe ba tare da na ga sadda take cire hannayenta daga cikin nawa ba tare da tura ni cikin dattin juji...ta tafi! Ta tafi da rayuwata da dukkan farin cikin da ya taSa wanzuwa cikinsa ta tafi da rai da ruhi na..."

Shiru yayi yana cije lip Win shi na ?asa da har su ma rawa suke yi.
"Ke ce kika ba ni hope na rayuwa, a kan ki na yarda uwayen ma suna suka tara Mammi kin zame min gata a sadda na kasance cikin wahala, kin ba ni duk wani kulawa da gata ba tare da tsammanin lada ba kin bani kaunar da bata taSa yankewa ba, kin zame min rayuwa, rahama da kyautatawa da bata da iyaka. Mammi Sunana Sameer..."
Lumshe ido tayi a hankali hawaye na sauka mata ya sa hannu ya share mata.

A hankali ya cigaba da bata labarin da kafin ya gama jijiyoyin kanshi sun yi raWa-raWa, idanunshi tamkar garwashi muryarshi har yankewa yake amma Dukda haka jarumtarshi ta ?i barin ruwan hawaye ko guda ya diga bisa fuskar shi ko zai samu salama cikin rai da ruhinshi, ba zata iya Mi?ewa ba da zata iya da ta rungumeshi ta rarrasheshi da ta nuna mishi komai na duniya mai wucewa ne, da ta tuna mishi da irin girma da darajar da Allah ya ba uwa don kalamanshi sun yi tsauri sossai a kanta, bata san dalilin ta na yin hakan ba amma ta san babu uwar da zata so tagayyarar Wan ta, Wan ma mai tarin gata, daraja da martaba irin Rayyan.

"Ka zama mai ha?uri da rayuwa! Ka zama mai afuwa Saraki ha?i?a an cuce ka an kuma Wauki alhakinka mai yawan gaske amma ina ro?on ka da ka bari komai ya wuce kaman ba'a yi ba, ka yi uzuri ga mahaifiyarka ka waiwayi gida..."
Shiru tayi sai ta Wan yunkura kaman zata tashi ta koma ta kwanta tana sha?uwa.
"Ka min al?awari Rayyan!"
Girgiza kai yayi yana Wago rinannun idanunshi gareta sai ya ji tana ambaton Allah da salati Wauke a Bakinta a kan idanunshi, hannunta na a cikin nashi Mammi ta ja numfashinta na ?arshe da ya tafi da duk wani ?warin gwiwanshi, ya tafi da duk wani haske da yake tunanin da shi yake amfani wurin haskaka tarin duhun dake mamaye da shi, gigice wa ya nemi yi sai ya manta da cewa shi Win ma likita ne, ya kasa yanke hukuncin cewa ta tafi ya kasa yardar wa kanshi cewa da gaske ta tafi ta bar shi...
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Shine kalaman da ya fito da kyar ya ratsa harshenshi har ya fita sarari.

Ya fi mintuna ashirin a zaune a haka baya iya ko da kifta idanun kirki, kila mafarki yake, kila bacci tayi za ta buWe idanu kila zai iya ganin kirjinta ya motsa ya cigaba da bugawa kila za ta ja numfashi ta ce mishi wasa take... Shigowar wani likitan ne ya tabbatar mishi da cewa da gaske ya rasa Mammi rasawa ta har abada ha?i?a Waci da raWaWin mutuwa ba za su faWu ba ba kuma za su misaltu ba.

A chan reception kuwa Su jannah da Afeefah ne zaune cikin damuwa mai yawa don tunda suka shigo Afeefah bata daina zubar da kwallah ba, ta san mutuwa kuma ta ga mutuwa daban daban bata fata ya kasance a kan Mammi nan kusa Dukda ta san da cewa mutuwar dole ce ga dukkan mai rai, su uncle Musa da iyalan shi da Abeeha ta ?ira ta sanar musu jikin Mammi babu daaWi duk suna cikin asibitin a lokacin da wannan likita ya fito ya sanar musu da rasuwar gigice wa suka yi suka fice daga hayyacinsu, Jannah ce ta yanke jiki ta faWi sai jini ya fara fita mata Abeeha kam rasa ma ya zata yi tayi sai da uncle Sanusi ya ri?o ta yana ta maimaita salati ta kankanmeshi ta fara kuka mai tsuma zuciya shikenan sun zama marayu babu uwa babu uba, Mammi ta tafi lallai dukkan mai rai mamaci ne.

Afeefah kam ba zata ce ga yanayin da take ciki ba, Dukda ta kaWu iya kaWuwa sai dai ko motsi ta kasa yi daga inda take hawayen idanunta ma kafewa suka yi, wata cousin Win su Abeehar ce ta ri?e mata hannu sai ta firgita tana kallonta idanunta duk a waje...
"Wai cewa suke Mammi ta rasu? Ko kunnuwana ne basu ji da kyau ba?"
"Sai ha?uri Afeefah, sai ha?uri..."
Wasu irin hawaye ne suka shiga zubo mata masu zafi da raWaWi, da kyar take iya maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun....

A lokacin Rayyan ya fito hannunshi na tura gadon da mammin take kai a hankali yana tafiya ne ba tare da ya san inda yake jefa kafafunshi ba, Uncle Sanusi ne da matarshi suka taho da sauri suka saka mishi hannu don kaman zai kifa, idanunshi sun zama wani iri jikinshi na rawa zuciyarshi a bushe haka suka fice yana gaban motar da Mammi ke ciki wacce amblance ce aka dauko ta a baya har cikin gida, a Wakinta aka sanyata babu wani jinkiri Matar uncle Musa dattijuwar malama da taimakon wasu malamai mata aka yi mata wanka aka yi mata sutura, kan kace mene gidan ya dinke da mutane masu kuka na yi masu yabon kyaun halinta na yi, Jannah dai tana asibiti don Sari tayi ba tare da ta sani ba.

Abeeha da Afeefah banda kuka da du'a babu abinda suke yayinda Rayyan na a parlorn shi a zaune wane mutum-mutumi tasbihi yake yi amma ba zai iya cewa ga abin da yake cewa a ciki ba, Saleem ne ya shigo Dukda ba ?arfin jiki ya samu ba sai dai labarin mutuwar ya dugunzuma hankalinshi.
"Rayyan!"
Ya kira sunan.
Jajayen idanunshi ya buWe ya zura mishi ba tare da yayi magana ba
"Sannu! Allah ya gafartawa Mammi Allah ya haskaka makwancinta ya sadata da annabin rahama"
Da kyar ya iya furta
"Ameen"
Idanunshi na kan hawayen da Saleem Win ke yi ina ma zai iya? Ina ma ya san ta yadda zai nemo hawayen? Ina ma zai iya cire zuciyarshi ya yasar? Da yayi hakan ko zai huta raWaWin da ke gasata wane wuta.

"An gama shirya ta ayi alwala a fita gabatar da sallah don samu a kaita makwancinta!"
Wannan kalma ta Uncle Mansur ya zama kaman zuban wuta a jikinshi, shikenan fa yanzu ko? Shikenan zai rabu da Mammi rabuwa ta har abada? Saleem ne ya ja hannunshi har zuwa bayi yayi alwala suka fito a tare zuwa Wakin Mammi aka Wago makarar aka nufi fita da ita haraba inda kuka ke tashi, kowa idanunshi na kan Rayyan ne da yake ta focusing akan hanyar da yake takawa kar ya faWi ri?e da gawar Mammi da yayi mata sallama na ?arshe da qulhuwallahu ahad!

A tare da shi aka yi mata Sallah aka kaita makwancinta na gaskiya, shine ya ba da ghdumuwa wurin sakata a rami kuma shi ne ya fara zuba mata ?asa kan yayi baya baya zai faWi aka tare shi su Uncle Mansur ne da Saleem, Wagowa yayi yana kallonsu kila su basa jin abinda yake ji tunda gashi suna hawaye! Har aka gama binne Mammi aka kamo Rayyan zuwa mota baya

30 / 53