HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   36 / 53

105K to 108K   out of 158.4K words

taje ta tsaya tana kallonshi yana magana da duka ma'aikatan gidan sama da mintuna biyar kan ya shiga mota wanda ba ma dashi suka fita ba ya ja ya fice daga gidan, sa?on Shigowar message taji ta janyo wayanta sai ta ga kati ne mai yawa aka saka mata ta kama baki ta ri?e mamaki na so ya kasheta da ranta data ta kunna sai taga hoton da Jannah ta Wauke su ne ta turo mata sossai hoton ya mata kyau har bata san ta saki kyakyawar murmushi ba tana shafa fuskar wayan...



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*44*

*Laamu Fombina  Daular Gabas*

A yankin kudu maso gabashin ?asar Arewa da bafulatani kai tsaye ke ?ira da Fombina bature kuma ya ce Southland, an yi wata Daula mai kafaffen tarihi da kuma mulki wacce ta samo asali tun daga jahadin ?anfodiyo ta hannun Walibinsa Muhammadu (Modibbo Adama) tsakanin shekarar 1809-1847.

Mafi akasarin mutanen wannan yanki FulSe ne ko kuma a ce musu Fula suna daga cikin manyan ?abilun Africa musamman a yammacin nahiyar. Asalin su yana da matu?ar zurfi, masana tarihi sun taSa jayayya kan inda suka fito amma dai an fi karkata kan manyan ra'ayoyi guda uku.

Ra'ayin Africa ta yamma, Yawancin masana sun ce Fulani 'yan asalin yankin
Senegal ne da Mauritania, daga nan suka bazu zuwa Nijar, Mali, Najeriya da sauran kasashe.

Ra'ayin Arewa(Africa ta Arewa), Wasu sun danganta asalin su da yankin Masar ko Sudan, suna ganin sun shigo cikin Sahara tun
zamanin da.

Ra'ayin haWe da larabawa, wasu sun danganta asalin su da haWewar 'ya'ya tsakanin mutanen Africa da Larabawa, musamman saboda musulunci da kuma tsananin tsarkin jini da suke ri?ewa.

Gaskiya kusan duka Fulani Musulmai ne, tun da musulunci ya shiga Afirka ta Yamma ta hanyar su.
Sun taka rawar gani wajen yaWa addinin Musulunci musamman Shehu Usman dan Fodiyo wanda ya kafa Daular Sakkwato a karni na 19.

Fulani suna da Wabi'u da al'adu na musamman da suka bambanta su:
1. Rayuwar Makiyaya (Nomadic / Pastoral
Fulani)
Mafi shahara a duniya saboda kiwon shanu.
Suna yawo daga wuri zuwa wuri suna neman ciyawa da ruwa. Wannan ya sa ake kiran su Bororo'en.

2. Fulani Masu Zaune (Settled Fulani)
Su ne suke zaune a birane da kauyuka, suna noma, kasuwanci da neman ilimi tare da yaWa ta. Su ake kira Fulbe Na'i ko Fulbe Gidda.

3. Mutunci da Tsarkin Jini (Pulaaku)
Pulaaku shine tsarin dabi'a da falsafar
Fulani. Kuma suna da ababen sha'awa da suka kunsa wanda sun haWa da:

" Munyal (hakuri)
" Semteende (kunya da ladabi)
" Hakkilo (hikima)
" Ngorgu (jarumtaka).

A ?ar?ashin wannan yanki da mutanenta suka kasance rabi da kwata Fulani (Pulaaku) aka kafa Masarautar fombina, masarautar tana ?ar?ashin Lamidon farko ta ?asar Modibbo har wa yau da jininshi ne ke mulkarta, ya kasance daga ragowar daulolin Fulani da suka wanzu tun daga Usmanu ?anfodiyo.
?atuwar masarauta ce da idan na tsaya misalta muku girmanta da kyawunta zamu kwana muna abu daya bamu gama ba. Cikin Masarautar gari ne guda da ke Wauke da Sangarurruka daban-daban kama daga kan Fada, Sangaren sarki da
iyalinsa, Galadima, madaki, wambai, Turaki, Makama sarkin faWa, Sarkin yaki da ma kowani mukami mai matsayi da ?ima a sarauta, inda kowa sashinsa ke tareda nasa iyalin daidai matsayin kowa.

Kuyangu, bayi da Fadawa ma nasu gashin kan suke ci a Sashukansu na musamman inda suke gudanar da rayuwarsu bayan sun taso daga wurin ayyukansu na yau da kullum. Kitchen kuwa fankacece suke dashi inda ake general abinci a kai wa kowani Sangare nasu dukda kuwa kowani Sangare akwai kitc?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? hens ciki. Akwai asibiti mai zaman kanshi cikin wannan masarauta da ma'aikata ?wararraru akwai kuma Makaranta da aka yi musamman sabida ma'aikatan masarautar da iyalansu dake amfanuwa.
Kodayaushe kashigo Masarautar za ka samu ko wani Sangare ana hada-hada ana kai kawo. Fadawa na fada, kuyangu da bayi na wuraren ayyukansu, Dogaraye na aikin ba wa Masarautar tsaro dare da rana ayayinda Masu Masarautar daukansu ke aiki ka'in da na'in wurin ganin sun kawo cigaba a Masarautar da al'umman gari baki daya.

A zamanin nan da Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a wasu yankunan, abu ne da kan tada hankali kuma matsala ce ga kowani zamantakewa da tsaro, babu ?abila ko yare, babu namiji ko mace, babu babba bare yaro haka ta shigo cikin wannan Daula ta Fulani ta kutsa kai har cikin masarautar saboda an wayi gari da tashin hankalin garkuwa da ?a Waya tilo da LaamiWo Muhammadu Modibbo ya mallaka a wannan duniyar.

Wannan matsala ta saka LaamiWo girgiza har ta kai yana tuna wani al'amari da ya faru a chan baya da ya haddasa ciwon da yake fama da shi a tsaitsaye shekara da shekaru tashi, kasancewar shi nagartaccen sarki, LaamiWo Mutum ne wanda ya gina al'umma mai gwaSi, mutum ne da kowa ke rububin ganinshi don agajinshi, Mutum ne da kowa ke son haWa ala?a dashi don Arzikinsa. Kyawawan halayensa ya sa ya zamana kowa ya shiga jimami a tare dashi hakan kuma ya ba da gudummawar Gomnati na tura manyan ?wararrarun sojoji don aiki akan wannan lamari.

Ko da Shigowarsu cikin masarautar a Motocinsu saboda an fara isar da su fada ne domin su huta su kuma fara bincike daga tushe, Rayyan ne ya zama na ?arshe wanda ya buWe murfin motar sanye yake da full khaki na sojoji fuskar nan kaman ko yaushe a matu?ar haWe Dukda ma idanunshi masu Waukar hankali da kuma karan hancinshi ne ya bayyana kasancewar akwai facemask ma?ale a fuskar tashi, yana ajiye ?afa kan daSen ?asan masarautar Wani irin guguwa mai ?arfin gaske da ?ura ya fara tashi a take wani kalar sautin kuka marar daaWin ji ya karaWe kunnuwan ahalin masarautar har ya kai ga gigita su.

"BO?EJO!"
Kusan shine sunan da bayi, dogarai da kuyangi ke ta ambata a ruWe, BO?EJO wata macijiyace na gado wacce take da shekaru sama da Wari tana kuma rayuwa a cikin wannan masarauta kaman la?ani ce na wannan masarauta kuma BO?JO bata kuka babu dalili ta kan yi sau Waya idan yayi tsanani sau biyu a kowani bayan lokaci mai tsawo. Kasancewarta Jajazir a jiki da idanu masu firgici da banda sarki ko magajin sarki babu mai iya arba da ita ya wanye lafiya ya sa aka saka mata suna BO?EJO dake nufin kalar JA.

Wasu da ba ma su taSa jin irin wannan kukan mai firgici da tayar da hankali haWe da ?ura mai tsananin duhu ba duk sun ruWe, a take manyan fada suka ba da umurni mai girma na rufe kowacce kofofin masarautar kar kowa ya fita akwai matsala, abin mamaki BO?EJO na yin shiru sansanin bai kai ga watsewa ba wani irin kiWan Serewo (Algaita), Tambin (Ganguna) Da Hoddu (kalangu da sarewa) masu mafisar ?arfi da daaWi suka shiga tashi cike da sautin da idan ka ji ka san wannan ba dai mutum ke yi da baki ba, sojojin duk da yau ne karon su na farko a irin wannan yanayin sun yi tunanin ma sumame ne ko wani abu don kukan BO?EJO babu biladaman da ba zai kaWawa ?ar hanji ba.

Shi kam baya ya koma ya jingina da motar tare da lumshe ido kunnuwanshi na jiye mishi irin rububin da ake da umurnin da sarkin gida ke bayarwa na a binciko duk wani ba?o da ya shigo masarautar a yau ana son ganinshi a faWa matukar namiji ne da gaggawa umurnin LaamiWo ne, a take fadar ta zama babu shiga babu fita.

Wambai ne ya tuna da su don kusan aikin wambai kenan karbar ba?i da kulawa da al'amuran masarauta da sauri ya taho wurin shugabar tafiyar wanda General ne kuma abokin aiki ne ga Rayyan ba wai shugabanshi ba, hannu ya bashi suka gaisa yana bashi hakurin abin da ya faru da yadda aka manta dasu, General Win yace

"Ranka shi dade ai mu ba ?aramin tsorata muka yi ba da wannan al'amari mun zaci sumame ne ake shirin kawowa hanyar sanarwar taku kenan!"
Wambai na murmushi mai nauyi da ma'ana mai tarin yawa yace

"Wannan kuka da kuka ji na macijiyar gadon wannan masarauta ce ta kan yi kukan nan a duk ranar da aka haifi Ciroma wato magajin sarki, haka ma wannan kiWan kalangun kayan kida ne da suke zaune sama da shekara da shekaru da kansu suke buga kansu a duk ranar da aka haifi ciroman wannan masarauta."
Yana musu iso suka fara takawa zuwa ciki tunda ?urar ya lafa sossai General Win yace
"Toh Masha Allah, an samu ?aruwa kenan?"

"Ko kuma nesan da muka jima cikin tsumayi ta matso kusa ba, bismillah ku zauna za'a kawo muku ruwa"
Zama suka yi bai ba General din damar sake magana ba ya fice.

LaamiWo dake tsaye har yanzu tun fara kukan BO?EJO ne jiri ya kwashe shi ya tafi zai faWi a sadda Sarkin ?ofa ya zo ya tabbatar da ba ba?in da suka shigo masarautar a wannan lokacin Galadima yayi saurin tare shi.
"Allah rene (Allah ya baka kariya) bi a hankali, Sannu!"

"Galadima ka fa ji kukan BO?EJO ka ji kalangu taya za su yi motsi a banza tsawon shekaru talatin da Waya kenan basu yi kuka ba, dole ku je ku nema min Ciroma wlh shi ne!"
Dukda a hankali yake maganan kusan kowa a fadan na ji don sun yi tsittt ne, sun san ba lafiya ya cika ba a kwanakin sannan rabon da yayi dogon magana haka tun da aka sanar da shi Satan Gimbiya Aissatou(Aisha, na yi pronouncing yadda Fulani suke pronouncing ne).

Turaki ne da aikinshi ya zama ba sarki shawara yace
"Allah sene (Allah ya yalwataka da farin ciki) ko za'a bincika cikin ba?in sojoji da suka taho wannan ?asa tamu? Don da alama ba?in cikinmu ne ke gab da yayewa."

Tsam ya mi?e a take dogaran da suke tsaye gefen hagu da damanshi suka fara jefa kirarin
"Gyaaaaraaa kintsi da kyau..! Taka lafiya mai talakawa"
"wambai kaini wurinsu"

"Allah ya baka yawan rai ba za'a yi ?ir...!"
Hannu kawai ya Waga mishi, a take manyan fada da duk suke tsaye suka rufa musu baya don tuni wambai ya shiga gaba.

Yalwataccen parlor ne mai cike da kayan alatu na sarautar zamani, an cika gabansu da tarin kayan itacuwa da ma ababen alfarma har da su Siradam Wanyen tatsa, sun yi nisa da ci amma shi kam yana zaune ne kawai idanunshi zube a wuri guda, fuskarnan tayi ja idan ka zuba mishi idanu za ka fahimci baya cikin natsuwarshi don karfin hali ne ya ajiye shi wurin.

"Gyaaara kintsi da kyau..!"
Da ke ta ?arato su ne yasa suka fahimci kaman mai martaban ne da karan kanshi ya taho hakan ya sa duk suka mi?e tsaye, General Win ne ya taSa Rayyan hakan ya sa shima ya mi?e ya mayar da kanshi ?asa yana jin yadda zuciyarshi ke tseren gudu, LaamiWo ya shigo parlorn tuni kwarjini da girman matsayinshi ya saka su sake natsuwa, tsabar yadda yake jin a lokacin zai iya mutuwa idan bai yi ido huWu da cikar Muradin shi ba binsu ya fara yi Waya bayan Waya yana kallon fuskokin su, jikinshi har rawa yake idanunshi sun cika tafff da kwallar marari da bege.

A lokacin da ya iso kan Rayyan ya tsaya kawai yana kallon irin tsawon Fulani da yake dashi, bambancin ya gina jikinshi hakan ya Wan rage mishi tsawon kaWan amma Dukda haka ya ma kere Lamidon da kaWan.

"Babana!"
LaamiWo Ya faWa cikin wani karyayyen murya yana kai hannunshi ya dafa kafaWar Rayyan da ya saka shi dolen Wago idanunshi da suka cika da kwallah masu zafi suka haWa idanu.

Jiri ne ya kwashi LaamiWo ya tafi kaman zai faWi tsabar wani abu da ya dake shi sai Rayyan yayi saurin sa hannu ya tare shi yana Waga idanunshi sama don hana hawayen shi zuba amma inaaa sun riga sun taho, LaamiWo ya fusge facemask din dake fuskarshi cikin harshen fulatanci yake cewa

"Babana kaine? Da gaske kai ne a gabana? Sameeer..."
Za ka iya fahimtar ruWu, farin ciki da tarin damuwa duka a cikin Muryar tashi.
A hankali Rayyan ya ce
"Abeey!"
Sai LaamiWon ya rungumeshi shi kuwa ya Wora kanshi a kan kafaWar shi yana barin hawayen shi zuba cikin wani irin yanayi marar fasaltuwa, tuni jama'ar parlorn suka fara fita sai da aka watse tas aka bar su su biyu kachal rungume da juna, kan kace kobo kunnuwan masarauta sun fara aiki inda sashe sashe, bayi bayi, kuyangi kuyangi ake ta zancen dawowar Ciroma Sameer Muhammad Modibbo cikin masarautar bayan shekaru ashirin da shidda da Sacewar shi.

Babbar macece mai cike da wani irin izza da ?asaita da kana kallonta sai gabanka ya faWi, bata da fara'a ko na miskala zarratin haka komanta tana yi ne cikin isa da wani irin mulki da ta saba shimfiWawa cikin masarautar shekaru da dama, Fulani Adama kenan uwargida ga LaamiWo kuma uwar Wakin duk wata mace da zata shigo gidan ko a mata ko a kwarkwara tana da irin izza da har kan ba mutane tsoro, ga kafaffen zuciya da salo salo wurin shimfida mulkin son rai da samun duniya a tafin hannu.

Jeka-ka-dawo take a tsararren falon nata, sanye cikin shigan alfarma da kamshi na musamman tun kukan BO?EJO na farko taji kaman an tsire mata zuciya ne hakan yasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk wani abinda zai hana Fulani Adama natsuwa ba ?arami bane, Shigowar Amintacciyarta da gudu yasa tayi hanzarin Juyowa tana zuba mata firgitattun idanunta masu kaWa 'yar hanji.

"Allah ya ja kwanan Fulanin LaamiWo, farin ciki masarauta, Uwargida kuma hasken zuciyar LaamiWo uwar yarima da yardar..."
"Bana son Sata lokaci Menene ya faru? An yi ba?i ne? Me ke shirin faruwa ne Balki?"

"Gobara daga kogi ranki shi dade..."
Baya baya tayi ta kai zaune cikin tsadaddun kujerunta hannayenta duk biyu dafe da Goshi.

A chan wani tsararren sashe cikin wasu kujerun alfarma Fulani FaWimatu ce zaune fuskarta Jajazir idanunta har sun jirkice Dukda tsaf take cikin shiga ta alfarma da ?awa kallo Waya za ka yi mata ka san cewa ba ta cikin natsuwar ta kukan BO?EJO kaman ?ara mata damuwa cikin damuwarta yayi don ta gigice ta kasa zaune ta kasa tsaye a sadda Kuyangarta ta shigo ta zube ?asa
"Allah ya kara miki lafiya da yawan rai, Allah ya kare gabanki da bayanki"

"Menene kande? Me ke faruwa?"

"GIZO BA YA HANA RUWA GUDU...! Zakarar da Allah ya nufa da chara..."

Dafe zuciyarta tayi tana fashewa da rikitaccen kuka mai tsuma rai.



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*45*

"Babana...Sameer ka gane ni?"
LaamiWo ya faWa har lokacin gani yake kaman mafarkin da ya saba ne yana motsawa zai iya ganin Rayyan ya Sace, rauninshi ne ke sake bayyana a gaban dattijon wanda dama tun yaranta shi ne mutum Waya jal dake ganin hawayen shi sai Baba Maudo wanda ke matsayin Galadima kuma Wan uwa na jini ga mahaifiyarshi.

Hannun Abeey ya ri?e ya zaunar da shi tare da yunkurawa ya kai ?asa kan gwiwowinshi gabanshi kanshi a ?asa a hankali ya furta
"A gafarceni ta?awa"
Ri?o hannunshi Abeey yayi ya Wago shi ya zaunar dashi gefenshi yana jefar da duk wani formalities na sarki don a yanzu uba yake.

"Da gaske ne kenan..! Kai ne da gaske nake gani Sameer? Ina ka shiga ka manta da asali? Me ya fitar da kai daga cikinmu ya nesanta ka? Wani irin rayuwa kayi a wani wurin da babu mu har zuwa wannan lokaci Sameer? Na yi nema! Na yi nema har yau ban fidda ran ganinka ba ashe da rabon sake ganinka kafin in bar duniya!"
Yana maganan yana ta duba jikinshi ko zai ga wani alamun wahalar rayuwa amma ya ganshi fes kuma fresh don ko daga tafin hannunshi da ya ri?e ya fahimci yana cikin hutu da jin daaWi Dukda haka sai da ya tambaya zamanshi Uba mai cike da yunwar ganin Wan shi namiji Waya tilo da ya mallaka a duniya.

"Abeey ka kwantar da hankalinka don Allah, ni ne! Sameer ne a idanunka ba zan jefar da sunan da ka yi min yanka ba sai dai Rayyan ne a idanun duniya wanda shi ne sunan da hasken rayuwata kuma wacce ba ni da kamarta a wannan duniya ta bani... Abeey Aisha tana chan hannun azzalumai shine abin da ya kawo mu duk wannan za mu yi daga baya na tabbatar Abokan aikina suna chan suna jira na"

Kallonshi kawai Abeey ke yi yadda yake jera maganan da rashin cikakken fara'a mai tsanani da ya kamata ya gani a fuskarshi.
"Aisha na da muhimmanci kwarai kasancewarta mace cikin miyagu amma kai ma kana da muhimmanci Ciroma... Mahaifiyark.."
Da sauri ya katse shi
"Abeey...!"
Sai yayi shiru don bai saba katse maganan mai martaba ba, duk jimawanshi wani wurin an haife shi ne cikin masarautar kuma ya tashi da horo mai tsanani da kuma jarumta na asalin 'ya'yan sarki waenda ake musu mafarkin sarauta a gaba don haka yana sane da komai bai manta ba.

"Abeeyy ka yi ha?uri ka gafarceni ka bar maganarta for a while ina cikin farin cikin ganinka cikin koshin lafiya, adu'ar da nake ta yi kenan duk ranar da zan riskeka in riskeka cikin lafiya da kuzari in ga wannan farin cikin dake shimfide bisa kamilallayar fuskarka, ka haske ni da annurinka, ka cika ni da kwarjininka ka min hirar tarihin Fulani masarautunsu da ma al'adunsu..."
Muryarshi ne ke rawa ya mayar da kanshi ?asa yana datse harshe don kuka ne ke zuwa mishi mai ciwo, shi kaWai ya san irin raWaWin kewar mahaifinshi da yayi a wannan duniyar, shi kadai ya san irin halin da ya shiga na rashin shi kusa dashi ba tare da ya bari damuwar shi ya fita fili ba don ya san shi aka fi cuta, an cutar mishi da mahaifi ainun da baya tunanin zai iya yafe wa.

Mai martaba ma hawaye yake zubarwa, amma fahimtar wani abu da yayi ya sa bai iya sake magana ba suka yi shiru. Chan da Wan jimawa ya ce
"Aisha! Ta ya ta Sace Abeey?"
"Makaranta suka tafi da 'yar uwarta Zara'u akan suna da jarabawa dake ?aratowa za su kai

36 / 53