HAIHUWA DA HANJI COMPLETE HAUSA NOVELS Fatima Muhammad Gurin.doc

Author :  Fatima Muhammad Gurin Category :  Romance

Chapter   13 / 53

36K to 39K   out of 158.4K words

ta shiga gaisheta tana yi mata godiya, Albarka Ummar tayi ta sanya mata kan suka yi sallama ta mi?a mishi wayar tana Wan tura baki na fushin yadda ya saka ta jin kunya, murmushi yayi
"Kar ki sa na narke fah Afeefah"
Tayi murmushi
Ya mi?a mata wani leda mai girma da farko kin karSa tayi sai dai da ya matsa ta karSa Win tare da godiya suka yi sallama ta nufo ciki.

Da hanzari Saleem ya Wauko wayanshi ba ta ko kai ga shiga Wakinta ba ta ga sa?on shi

"Menene ke tsakani ki da Sulaiman?"

Mu?ut haka ta haWiye wani miyau kaman yana gabanta, da sauri ta shige Wakin ta ajiye ledar tare da zame mayafinta ta jefa kan katifa ta fara safa da marwa cikin tunanin amsar da za ta bashi, sam bata so yayi fushi da ita da kyar ta iya rubuta mishi
"Babu kawai kyautatawa ce da suke min shi da ahalinshi"
Shiru ba reply, ta san ba wai ya yarda bane kuma kila shirun nan da ya yi fushi yayi, ta kasa zaune ta kasa tsaye haka ta yi ta sa?e-sa?e ita kaWai, ?iran Magrib ne ya katse ta jiki a sanyaye ta shiga bayi tayo alwala ta zo ta gabatar da sallah ta zauna nan tana karatu.

Sulaiman kasa zuwa office yayi haka kawai yake sake tariyo kallon da saleem ke yiwa Afeefah, ji yayi ko ya je office ba zai taSuka komai ba yana bu?atar shawara da mahaifiyarshi don tamkar ?awarshi haka take.

"Wash Allah na!"
Ya faWa yana kwantar da kanshi a kan kafafunta, ta sa hannu ta shafa sumanshi
"Ya dai likita?"
"kawai gajiya ne umma"
"faWamin gaskiya ko dai kai da surkar tawa ne?"
Ya Wan yi shiru kan ya ce
"Ina tunanin umma saleem na son Afeefah, ko dai ita bata sani ba ko kuma ta sani tana min wasa da hankali ne"

"Saleem shi ne Wan masu gidan da take aiki?"
Kai ya gyaWa mata
"Kuma Baaba ta tabbatar min kaman yarinyar tana shan wahalan gidan aiki haka ne?"
Nan ma ya gyaWa kai fuskar shi babu walwala
"Kaman saleem Win ne kawai yake taimaka mata, kuma kaman ba ta da kowa don dole ne kawai take zaune gidan"
"Ka kwantar da hankalinka Sulaiman, kila ba soyayyar ba ce tsakaninsu sai kyautatawa don ya na tausayinta, kila kuma yana son ta Win amma yana tsoron bayyana mata don iyayenshi, zai ma iya yiwuwa ya sanar mata Win amma ta ?i bashi haWin kai don babu macen da za ta yi kuskuren jefa kanta inda ta san ba'a ?aunarta ko kuma inda za ta sha wahala"

Numfashi ya sau?e
"Umma haka kawai nake jin kaman ba zan sameta ba"
"Ka cigaba da kyautata mata domin zuciya tana son mai kyautata mata, idan har matarka ce za ka aureta, ni ma zan so ka sameta don na tabbatar wacce ta iya mallake zuciyar My Son ba ?aramar nagartaccciyar mace ba ce"
Ya mi?e zaune yana murmushi
"Umma za ki fara taya autocinki zolaya ta ko?"
"Ai gaskiya ne sabon shiga, duk ka bar komai obvious sai gano ka muke yi dubi duk yadda ka ruWe daga sanin tana da wani saurayin"
Ta ?arasa da dariya.
"Duk ba za ku gane bane umma ni dai na yi nan"
Yana ji tana cewa
"Toh zo ka ganar da mu mana"
Yayi murmushi kawai. Allah ya gani shi karan kanshi ba zai ce ga sadda ya fara jin son Afeefah a ranshi ba, kawai dai ya san ta yi mishi kyau ranar da ya fara ganinta, sanyin muryarta idan tayi magana sai yake jin tamkar ?an?ara ake zuba mishi. Ko da ta bar asibitin bai wani sa hope Win sake ganinta ba amma daga ranar da ya je ya isketa cikin fitar hayyaci sai ya ji tamkar an soki zuciyarshi da mashi barin ma da ya gama fahimtar tana shan wahalar rayuwa a gidan, sannan ya san babban burin ta a rayuwa shi ne ta yi karatu ta zama wata public figure da za'a yi alfahari da ita, kaman tana da wani ciwo ne da take jin ba zai taSa warkewa ba har sai ta yi nasara a duniyar ta, ba ya jin zai iya bar wa saleem ita za su buga wasa ne duk wanda ya iya allonsa ya wanke.

A daren da misalin ?arfe tara ya ?ira layinta, ta gama wanke-wanken dare kenan da yau yayi yawa sossai saboda abincin da aka yi kalolin daban-daban, sai duba wayan take ko za ta ga sa?on saleem don gabaWaya ranta babu walwala, ko da suka haWu ko kallonta bai yi ba kuma ta sake mishi sa?o babu reply.

"Assalamu Alaikum warahmatullah"
A natse ya amsa
"Wa'alaikissalam gimbiyar mata"
Tayi ignoring sunan da ya ?iratan
"Ka koma gida lafiya?"
"Da an damu da ni ai da an neme ni, ni da ya zama dole na ba gashi na kira ba. Ya kike?"
Har za tayi magana ya katse ta
"Wait!! Kina lafiya ko? Ya na ji muryarki duk cike da damuwa da rashin Walwala ba yadda na bar ki ba?"
Ta Wan ja numfashi tana tafiya kwance daga zaunen da take jingine da gini.
"Kaina ke Wan ciwo"
"Eyyaa so sorry, kina da ORS?"
Ta girgiza kai tana amsawa da
"A'a"
"Ki sha pcm da safe zan zo in auna jinin ki sai in taho miki da ORS Win, ciwon kai bashi da daaWi musamman ga ke da jininki sau?a yake kuma kin san ya fi high BP hatsari"

Idanu kawai ta runtse bata san me zata ce ba tunda ta riga ta yi suSutar baki ta ce kanta na ciwo zuwa kam sai ya zo to kuma saleem da har yanzu bai sauko daga fushin Wazu ba fa?

"Kina ji na kuwa Afeefah?"
"Eh ina ji, na ce da ma ka barshi in na yi bacci zai daina"
"hmmm ke dai kawai in na zo Win zan ?ira ki, kwanta ki huta Allah ya baki lafiya"
Yana kai nan ya katse wayan ba ya so ta hana shi zuwa haka tayi ta juye-juye har bacci ya sure ta.

Washegari tana gama goge-goge ko Waki bata koma ba sai ga ?iran shi, gate kawai ta wuce don ta karSa da sauri kan saleem ya tashi ya ganta
"Sannu da zuwa"
"kin tashi lafiya?"
Yayi tambayar yana ?are mata kallo, ita kam ko me ta saka kyau take mishi
"Alhamdulillah ya su umma?"
"Umma na gaishe ki da jiki ta ce in miki sannu"
"Na gode sossai"
Leda ya fitar ta zare ido, ko kayan jiya bata buWe ba saboda damuwar fushin saleem da ita yanzu kuma ya sake ciko leda? Shi kam ba ya gajiya ne?

"Hidimarka na yawa a gareni Dr. Na kan rasa kalaman godiya a gareka, wani lokacin sai in ji tamkar ba na kyauta maka don ka fara ?aunata tun ba ka san wacece ni ba! Ban san ya za ka karSeni ba a duk ranar da wani ya tare ka ya ce maka Afeefah annoba ce!"

Kallon bana fahimtar zantukan ki yake mata daidai sa?o ya shigo wayar ta sanin saleem ne ya sa dole ta buWe tana ta ?o?arin haWiye kukan dake zuwar mata
"Ki sallame shi za mu yi magana"
Ta Wago ta kalli Sulaiman da har lokacin idanunshi ke kanta.
"Zan shiga ciki za mu yi magana"
"Saleem Win ne ya ce ki sallameni?"
Ya faWa cikin wata murya yana ?ara tsare ta da idanu.

Ba Ta yi magana ba ta mayar da kanta ?asa kawai.
"Ya za ki saka ni a duhu kuma ki tafi ki bar ni ciki? Me kike nufi a tare ni a ce ke annoba ce? Mutum ya taSa zama annoba ne Afeefah?"
Muryar ta na rawa tace
"Kwarai Dr. Sulaiman da za ka iya da ka yi tattaki zuwa Dutsen-wai ka tambayi wacece Afeefah kamal ina da tabbacin bayan nan ko mai sunana aka ?ira maka za ka gudu! Umma ta karSe ni ne domin itama bata san w???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?acece ni ba don babu uwar da za ta karSeni matsayin surka muddin tana ?aunar Wan ta"
Ranta zafi yake mata, tana maganar ne tana tuna mahaifiyar saleem da kyamatarsu gareta ta wani Sangaren kuma bata ga laifinsu ba don ba laifi bane mutum ya kare abin da yake so.

"Ka yi ha?uri ka tafi Dr. bana so sai ka zurfafa kasan ni wacece in karya maka zuciya, na tafi ciki"

Tana kai nan ta nufi ciki ta bar shi tsaye, hawaye take zubarwa ba wai duk cikinsu babu mai nagartar aurenta bane sai dai tana ji babu inda za'a karSeta matu?ar an san wacece ita!
TaSon nan da bata san mafari ba ba zai taSa goguwa a tarihin ta ba, tabo ne mai raWaWi da har Abada za ta cigaba da rayuwa cikin gangar jikin da ruhi mai tarin buruka suka mutu... Da saleem ta ci karo a sadda ta shawo kwanar Wakinta ido kawai ya zuba mata ko da ta zo bata tsaya ba kawai ta wuce shi yayi saurin shan gabanta.

"Afeefah saboda Sulaiman kike Sata rai da ni?"
Hawaye take yi wadda ta kasa sarrafa su cikin rabuwar murya tace
"Ba saboda shi bane yaya saleem"
Ta sake yunkurin wucewa ya sake tare ta
"Ban gane ba bayan ga idanunki nan suna zubar da kwallah Afeeefa?"
Cikin Muryar kuka ta shiga cewa
"Ina kuka ne saboda na gaji da yaudara ta da zuciyata ke yi na cewar zan samu farin ciki, ina zubar da hawayene saboda na farka daga mafarkin da bashi da tabbas"
Shesheka ta ja tana kallon cikin idanunshi
"Ka gaya min Yaya saleem a cikin ku biyu da waye zan dogara? Da Kai da mahaifiyarka ta yi Allah ya isa muddin ka yi min maganar da ta wuce ta minti Waya ko da Dr. Sulaiman da bai san wacece Afeefah ba?"

Wuce shi kawai ta yi don ta san ba zai amsa ba saboda minti Wayan ya riga ya wuce hakan ya kara rura wutar zuciyarta ?arfin kukan ya ?aru, jakar hannunshi ya bi ta har cikin Wakin ya ajiye ya tsaya ya zuba mata idanu yana jin kukanta na sukan zuciyarshi, idanunshi suka sauya sossai tausayinta da ?aunarta suka ninku a cikin ranshi.

Samha da ke tsaye jikin pampo ta sake hanci da baki tana kallon su ta kwasa da gudun tsiya ta kamo hannun mommy
"Mommy zo zo zo ki ganewa idanunki wallahi Ya Saleem ne Wakin Mayyar chan..."
Mommy har tana tripping garin sauri suka nufi bayan a lokacin suka hangi bayanshi ya fito ya nufi hanyar waje, duk su huWu suka nufi Wakin kowa da bala'in da ke cin shi a rai...





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*017*

18hours Earlier

Kanta a ?asa tun da Sulaiman ya fita daga gidan tana tsaye ne jikin taga tana kallonsu tun Shigowarshi da ma isowar su saleem da tafiyanshi bayan ya ba Afeefar Abu a leda, bata taSa sanin haka so yake ba sai da ta faWa komar Sulaiman zuciyarta yayi mata wani irin nauyi, tsananin haushin Afeefah take ji kaman ta samu bindiga ta harbeta kowa ya huta, a yanzu ma bata san hawaye na zuba mata ba sai da ta ji an dafa ta.

?ago kai tayi ta kalli Samha sai ta du?ar da kan again tana share hawayen fuskarta
"Sameera me ke damun ki haka? Menene ya sameki kike kuka?"
"Babu Samha"
"A'a Sameerah ina fa lura da ke kwana biyun nan duk kin chanza kaman ba ke ba, kullum kina cikin damuwa 'yar faWan nan da kike biye ni muyi tayi duk yanzu bakya yi walwala ta kau daga fuskanki har mommy Wazu maganan take yi, in baki faWa min ba wa za ki faWawa Sis?"
Kuka kawai ta sakarwa samhar, sai da tayi mai isarta kan ta Wago ta kalleta
"Samha ko na faWa ma ba ku da maganin damuwata"
"Ko Adu'a muka taya ki ai mun taimakeki bare kila akwai shawarar da zan iya baki, idan ba kya son kowa ya sani ne ma i promise ba zan faWawa kowa ba".

"Samha na kamu da Soyayyar Dr. Sulaiman"
Tsayuwa tayi tana tunanin waye Drn Sulaiman sai da yayi clicking a brain Winta kan ta yi saurin cewa
"Wannan likitan dake zuwa duba Mayyar chan?"
Kai ta gyaWa a sanyaye
"Samha kaman soyayya suke da ita"
"Amma Sulaiman Win bai santa bane ba ko? Ina nufin bai san wacece ita ba rufe shi take kokarin yi ta nuna mishi ita 'yar gidan nan ce?"
Samhar ta fada har yanzu tana mamaki, Afeefah ta kai Sulaiman ya ce yana so?
"Da alama kam"
"Toh me kika yanke?"
Ta Wago jajayen idanunta tace
"Dole su rabu idan na cigaba da kallonsu tare zuciyata zai iya bindiga Samha, dole ko in sakata ta rabu da shi ko kuma in san hanyar da zan bi gidansu su san wacece ita! Ko yana sonta ai ba shi zai aurar da kanshi ba ko?"
Kai Samha ke gyaWa wa
"Wannan haka yake, shawarar nan yayi kuma ki sameta ki ja mata warning mai girma ta tsaya matsayin ta"

A hakan suka yanke don har ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi da Afeefah da safe kuma tana tashi bacci wanka kawai tayi ta fito kaman an ce ta le?a waje ta hanjeshi tsaye da ita, ko abinci bata ci ba ta zauna parlor tana jiran Afeefar ta dawo don ta lura abin nasu gaba yake, bata gama tunanin ba sai ga Samha da gudu ta ?ira su suka nufi Wakin Afeefar...

***

Tana zaune kanta haWe da ?afafunta tana aikin zub da hawaye kawai ta ji an banko ?ofan Wakin, suka tsaya suna ?arewa Wakin kallo kan Sadiqa ta nufi wayanta da ke zaune gefenta
"Kutt! Yaushe kika yi waya? Na dai tabbatar ba da ita kika zo gidannan ba"

Kayakinta Samha take dagawa tana cewa
"Mommy yau dai kam Yaya da kike yabo ya watsa miki ?asa a idanu duk wa zai saya mata su bargo har da su heather in ba Yaya ba? Dubi ?walamar dake Wakin nan? Mommy anya ba asirce shi tayi ba?"

Ita dai tana tsaye tana kallonsu duk da zuciyarta da ke dukan sakwara ta kame bata firgice ba, Sameera ta je ta fusgo ledojin da Sulaiman ya kawo mata tana zazzage kayakin ciki idanunta cike da kwallah.

"Shikenan wallahi tambaWe mana take shirin yi a gida, wani namijin ne zai na kashewa mace kuWi haka ba tare da ta bashi komai ba?"
Sadiqa ce tayi maganan tana ganin turaruka da dogayen riguna masu tsada da mahaifiyar Sulaiman ta bata.

Sameera ta katse ta
"Ko dai asiri ta yi musu ba yaya sadiqa in tambaWe wa ne kenan har da Yayanmu kalli wayan nan kalar text messages dake ciki na tsantsar soyayya don tsabar rashin kunya da nuna cewa ta isa dashi ma kin ga sunan shi gatsau tayi saving saleemullahi"
A fili ta fara karantowa mommy wasu inda yake tabbatar mata da zai iya jurar komai a kanta kuma zai jajirce har sai ya ga sun samu cikar burin su na kasancewa karkashin inuwa daya.

"Ya isa haka sadiqa"
Mommy ta faWa jiri na kwasarta ta samu wuri ta zauna, har Dishi Dishi take gani saboda yadda kanta ya sara ashe salim zai iya tsallake maganar ta? Yanzu idan da basu lura da wuri ba tayi amfani da wannan dama ta kashe mata shi fa? Da gaske maita na tafiya da aljanu? Ai kuma duk inda Aljanu suke akwai asiri kenan dai tun farko ma asiri ta mishi ta sa ya kawo ta matsuguninsu?

"Lallai saleem! Ni yaron nan zai nunawa Wan yau ne shi? A kan mace? Macen ma Mayya marar galihu da tushe haWe da asali mai kyau? Allah ya isa na a banza ya Wauke shi? Ni saleem...?"
Sai ta kama hawaye, hankalin Afeefah ne ya tashi ganin mommyn na mishi hawaye bata son masifar hawayenta ya taSa shi ko ta wani Sangare da sauri ta isa gaban mommyn ta zube a kan gwiwowinta

"Don Allah Hajiya ki yi ha?uri kar ki mishi kuka, wallahi yana jin maganarki yana kuma tsoron fushinki, Ni ce mai kuskure ni ce na nemi ya sayamin kar ki yi fushi da shi domin fushinki bala'i ne a tare da shi..."

Tauuuu sadiqa ta Wauke ta da mari
"Kin san hakan amma kike hure masa kunne ya saSa mata? Kin san abin da Sacin rai daga gareshi zai iya ja mata?"

Samha da ta janyo jakar da saleem Win ya shigo ya ajiye mata ta zazzage komai na ciki tana cewa
"Wallahi yarinyar nan so take ta raba mu da Wan uwanmu Mommy, kalli uwar tsarabar da ya kawo mata a Soye ko ke bai kawo miki irin hakan ba bare mu... Farraku take shirin yi mana daga karshe ta sa ya kora mu daga gidan nan"

"?ira min saleem sadiqa"
Da wayan Afeefar ta ?ira shi, ringing Waya ya Waga a hankali ya kira sunanta sai ta du?ar da kai hawaye na gangaro mata jin muryarshi.

"Yaya Salim Sadiqa ce Mommy ke son ganinka"

Runtse ido yayi da ?arfi gabanshi na faWuwa, bai shirya ba! Bai shirya tashin hankali a yanzu ba ba yanzu ba da yake jin son Afeefah yayi mishi yawa a zuciya.
Da sauri ya juyo kan motar dama bai yi nisa ba ya dawo wani irin parking yayi ya sau?a ya nufi sashen Boys quaters Win yana Adu'ar Allah ya sa kar mommy tayi mata wani abu, sai kace-nace ya same su suke yi ana ta maida magana, Afeefar na tsugune kaman mai neman gafara tana kuka.

Gaban mommyn ya je kusa da Afeefar shima ya du?a kawai ba tare da ya furta kalma ko guda ba.

"Saleem"
Ta ?ira sunanshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba
"?ago saleem ka kalleni, ka Wago ka tabbatar min da kai ke tura duk wani sa?o da na gani wayar yarinyar nan, da gaske kai ne kake son wannan marar cikakken asalin?"

Ya runtse ido wani irin nauyin Afeefah yake ji kaman yayi yaya, baya so baya kaunar ta ke jin furucin Satanci daga ahalinshi zuwa gareta musamman mahaifiyarshi.

"Mommy ni ne, Son ta nake kuma aurenta nake Son y...."
Wani irin mari ta Wauke shi da shi, karo na farko kenan da ta kai hannunta jikinshi don shi yaro ne mai tsananin biyayya a gareta.
"Maimaita!"
Ta daka mishi tsawa ya sake cewa
"Mommy ina ?aunarta, kuma aurenta nake buri"
Wani marin ta sake dauke shi da shi, ba shi kaWai ba har su sadiqa

13 / 53