Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   95 / 126

282K to 285K   out of 377.2K words

Abincin da sauri na ba shi"



Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara"



Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banWakin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta ™ara goge gurin da ya Sata da aman.



Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?"



Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin"



Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri Waya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana ™o™arin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba Waya".



Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun Waure mini kai sosai da sosai fa"



Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai Waure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema"



*****



Mama ce take kallon Jamila cike da ba™in ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaSi mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya ri™a mu je a cire shi kin ™i, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa.



Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki ™yale ni kawai"



"Jamila ni ki ke cewa na ™yale ki? Kin gwammaci ki dur™usa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?"



Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. Wata™ila haifar Wan nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki ™yale ni"



Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar Wan sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa"



Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wata™ila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata"



Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta yi shahada"



Jamila ta ce "Mama ba ki san tarin zunuban da suke kaina ba, tuban da na yi sai Allah ya karSi shahadata." Takaici ya sanya Mama fara rafka wa Jamila maficin hannunta ta ko ina. Jamila ta tashi da sauri, amma ta bi bayanta tana ci gaba da raWa mata.

Baba ya kawo kai cikin Waga murya ya ce "Rabi, wannan wane irin rashin imani ne haka? Yaya yarinya ba ta da cikakkiyar lafiya za ki biyo ta kina duka, me ta yi miki?" Mama ta tsaya tana mayar da numfashi cike da ba™in ciki da takaici.

Suwaiba kuwa da take gefe, ta din ga tuntsura wata irin dariya mara daWin ji, wadda ke bayyanar da rashin cikakken hankali ga mai yin ta.

Mama ta rasa ihu za ta zunduma ta ji daWi, ko kuma me yakamata yi ta ji sanyi. Hutu da fatan arzikin da take da shi a kan 'ya'yanta duk ba ta samu ba, ga mahaukaciya ga karuwa Nasiru shi ma ya fara 'yan Wauke-Wauke, dan sau biyu 'yan vigilant na kama shi, da laifin satar tukwanen mutane da kayan ™arafa ya sayar da sunan gwangwan. Dan tun da Jamila ta cire tallafin da take ba su, ta daina zuwa gurin Hajiya Sa'a, suka koma ruwa.

Baba ya ci gaba da yi mata faWa a kan dukan da ta yi wa Jamila, ba tare da ya tsaya ya ji cikakken abin da Jamilar ta yi ba. Ji ta yi tamkar ta kama shi shima ta jibge shi, ko ta huce. Dan duk wannan masifar shi ne sila da ya tsaya ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da wata™ila ba su shiga wannan halin ba.

Babban abin da ya ™ara Sata mata rai, shi ne rashin zuwan Hajiya Sa'a ta duba Jamila, duk da taga kwana biyu ba ta zuwa maimakon ta neme su ta ji ko lafiya amma ba ta yi hakan ba. Ga Maman Khairat ta tashi daga unguwar da ta so zuwa a rakata gidan Hajiya Sa'a ta ji ko wani laifin Jamila ta yi wa Hajiya Sa'a haka?.



Hajiya Sa'a kuwa tana can tana fama da kanta, dan tun mutuwar Abba ta shiga wani mawuyacin hali, duk lokacin da ta zauna babu abin da take yi sai tunanin ko yaya Abba ya ji da dodon ™ungiya ya zu™i jininsa har ya mutu? Ta daina bibiyar duk wani abu da ya shafi kungiyar. Kasuwancin ma ta tattara ta ajiye a gefe ta koma guri Waya kawai. Daga kuka sai kwanciya da dana sani. Ga shi da ta fara tunanin wani irin mummunan ciwon kai yake yi mata dirar mikiya, har sai ta daina gani sosai. Wasu lokutan haka zata kulle kanta a Waki ta wuni, sai dai mai aikinta ta yi ta sabgoginta itakaWai. Ta ce ko mutanenta sun zo, kar a bar kowa ya shiga inda take, kaWaici kawai take so.



****



Mahmoudu ya dawo, ya kai wa Nana shayi da kayan marmarin da ta ce . Sai kuma kayansu da Al™ur'ani. Ya haWu da Sultan a hanyar da suke bi su shiga gurin. Domin wani sashi ne a can cikin sashensa da ba kowa ma ya san da shi ba. Hatta iyalansa sai da izninsa suke zuwa gurin. Wasu lokutan ya kan sanar da ya yi tafiya, ya tafi cikin gurin ya kulle kansa ya samu hutu da nutsuwa.

Mahmoudu ya ™arasa gabansa cikin girmamawa.



Ya ce "Abincin ka kawo musu?"



"Eh ranka ya daWe"



Sultan ya numfasa ya ce "Shikenan, amma ina fatan babu wata matsala barinsa tare da yarinyar nan, duk da na fuskanci tana da hankali akwai abubuwan da take Soyewa. Ni kaina ba komai nake son kowa ya sani ba"



"In sha Allah Sultan, kare martaba, mutunci da kuma sirrikan Imam Hammad abu ne da ya zama wajibi a gare mu. Kuma tabbaci nake da shi ba ya™ini nake da shi, ba za ta taSa aikata wani abu da zai cutar da shi ba"



Ya jinjina kai ya ce "Na ga alamun haka, duk da na ga wasu abubuwa na ban mamaki a tattare da ita. Dama Hammad ya gaya mini sai mun neme ta, amma ban Wauki zancen nasa da wani muhimmanci ba. Akwai wasu abubuwa da ya gaya mini da ban gama gane ma'anarsu ba, amma bari mu jira mu gani ya samu sau™i"



Mahmoudu ya risuna ya ce "Godiya muke ranka ya daWe, Allah ya ™ara maka lafiya da tsawon kwana" Ya Waga wa Mahmoudu hannu.



Nana na ganin Mahmoudu ta yi ajiyar zuciya, domin shi take ta jira ya kawo abin da za ta ba wa Hammad ya saka a cikinsa. Yana kwance a kan cinyarta tana shafa gashin kansa.



Ya ajijiye mata kayan, Nana ta ce "Sannu da ™o™ari, Ubangiji Allah ya biya ku da kai da mahaifiyarka, na fuskanci kirki da karamci a jininku yake, gado ka yi Nene akwai kirki"



Ya ce "Allah ya taimake ki, ai kin ™wace mini ita" Nana ita abin dariya yake bata, idan ta ji su na girmamata.



Ta ce "Sayyid, ga abinci an kawo tashi ka ci" Mahmoudu ya taimaka mata, ta zaunar da shi. Ta zuba shayin a kofi, ta fara ba shi a hankali da cokali.

Duk da wata irin yunwa da yake ji, tamkar ya haWa da Nanan ya cinye, amma haka ya daure ya din ga karSa a hankali.



Ta ce wa Mahmoudu "Ka je ka samu ka huta, amma dan Allah ka zo da wuri, ka san ni da kai na saba, kuma kai kaWai nake jin zan iya sakin jiki da kai. Sannan dan Allah abincinsa kar a bari ya biyo ta hannun kowa, ta gurinka kawai"



Ya ce "In sha Allah, zan yi yadda ki ka ce, sai da safe"



Sosai ya din ga cin kayan marmarin nan, yana sake shan shayin girfae da Habu ya kawo. Sai da Nana ta lura jikinsa ya daina rawa. Ya Wan huta sannan ta tashi tsaye ta ce masa "Sayyid yin™ura a hankali ka tashi mu gani"



Ya dafa gadon, ya tashi a hankali amma ya ji kamar kayan cikinsa zai zubo. Ta ri™e hannunsa yana dur™ushe yana tafiya a hankali.



˜ofar banWakin suka je, ta tsaya ta kalle shi ta ce "Mun yi wanka a Nigeria, yau za mu yi a Agadez ko?"



Murmushi ya yi mata sai da ha™oransa suka bayyana. Suka shiga banWakin. Sai dai wata irin kunyarsa da ba ta san daga ina ba, ta bujiro mata. Za ta iya cewa yau ji™a-ji™a kawai ta yi masa, saboda yadda ya ™ara yi mata kwarjini take ganin kamar wani aka canza mata. Babban abin da ya ™ara takura ta, shi ne kallon da yake ta bin ta da shi, kamar zai lashe ta. Da kanta ta yi masa brush, hakan ya din ga tuna mata da rayuwarsu ta Nigeria.

Ta saka ya yi alwala, suka dawo Wakin ta saka masa doguwar rigar jallabiya. Ta ce "To an ce kwananka takwas baka hayyacinka, yanzu zaka lissafa sallolin da suke kanka. Ka yi wanda zaka iya yanzu sauran sai ka ci gaba ko gobe in Allah ya kaimu ne"



Ya jinjina kai, ya kalli gabas daga zauna ya tayar da salla, saboda ba zai iya tsayuwa ba. Nana ta din ga tunani ko ta ro™i alfarmar su nuna mata Wanta ta gan shi, tun da nasu Wan ya farfaWo, amma wata zuciyar ta hana ta hakan, duk da tarin kewar Muhsin da take yi. Ta shiga banWakin ita ma, ta yi wanka ta gama ta sako hijjabinta ta fito.

Jakar kayanta ta buWe, tana duddubawa, ta ga magungunan da Nene take bata na sha da wanka a ciki.

Kawai ta yi murmushi ta shafa mayukanta, ta duba kaya masu sau™in nauyi dan ta saka, dan duk da ba shi da lafiya ba za ta kwana shimfiWa Waya da shi ba, da haryanzu ba ta san matsayinta ba, da matsayin kawo ta gurinsa ba, duk da da aka zo ita ta nema. Ga uwa uba rashin tabbacin da gaske tana da juna biyu ko kuwa?.



Ta sakankance da salla yake yi, saboda a bayansa take zaune tana ™o™arin canza kaya. Kawai ta ji ya faWo jikinta, suka faWi ™asa a gurin, hasken wutar Wakin ya Wauke baki Waya duhu ya mamaye Wakin.



Ayshercool



85



LITTAFIN KUŠI NE, KI BIYA KUŠIN KARATU KAFIN KI KARANTA. VIA 0069685771

AISHA ADAM STANBIC BANK

08081012143





Nana ta razana ta ce "Sayyid lafiya kuwa?" Ya rirri™eta jikinsa na rawa.



Nana ta yi shiru cike da damuwa, ga shi yanzu ta fara wahala da ri™on da yake yi mata, dan ya ninka wanda yake yi mata su na Nigeria. Haka ta ha™ura ™yale shi.

Can bayan wani lokaci, hasken Wakin ya dawo, a lokacin ya samu bacci, Nana ta yi shiru tana tunani daban-daban a kansa. Tabba! Tana da tarin tambayoyi da take bu™atar samun amsarsu, daga gare shi, dan akwai tarin abubuwan da suke faruwa, da suke Waure mata kai.



Ta ture shi da kyar, ta tashi ta saka kayanta, ta kwanta a bayansa, tana jin yadda jikinta ya ™ara tsami da ciwo.

Sai dai bayan bacci ya Wauke ta, ta din ga munanan mafarkai marasa kyau da ban tsoro a cikin baccin. Abubuwan da ta din ga gani a gidan, sun tsorata ta. Har da ya™e-ya™en da aka din ga yi, kafin kafuwar masarautar, da irin azabar da bayi suka sha haka ta din ga gani. Ban da miyagun Aljanu masu Wauke da siffofi daban-daban na ban tsoro a cikin baccin.

Juyi ta din ga yi tana haWa wani irin gumi, tana sauke numfashi saboda tsoro. Ga shi a baccin da fari a gefe take tana kallon abin da yake faruwa, kafin daga bisani ta ganta tsamo-tsamo a cikin rikicin da ake yi, daga bisani ma miyagun abubuwan suka din ga nufo ta. Cike da tashin hankali ta farka tana waige-waige. Amma ta yi ido huWu da Hammad a zaune yana kallon ta, da alama ma sallolinsa ya yi.

Mamaki ya kama ta, yaushe ya tashi har ya yi alawala ya zo yana rama sallolin. "Sannu ya jikin naka?" Ya jinjina kai yana kallonta.



Ta sake cewa "Ka gama rama sallolin ne?"



Ya girgiza mata kai, ta ce "To shikenan, bari na ™ara maka kayan marmarin, zuwa da safe sai ka fara gwada cin abinci" ya jinjina kai ta din ga Sare masa ayaba yana ci, tana ba shi ruwa yana sha. Sai da ya yi mata nuni da ya ™oshi.

Ta tashi ta tafi banWaki domin ta yi alwala ta ji mararta ta ™ulle. Ta tsuguna ta yi fitsari kawai ta ga fitsarin haWe da jini. Ta shi ta yi cikin tsoro, ta gyara jikinta sai dai ta kasa gane jinin Al'ada ne, ko kuma na Sari? Tun da dai ya ce mata tana da ciki. Ta kintsa jikinta ta fito, tun da ta fito idonsa a kanta, ta ™araso tana cewa "Sayyid, ka ce ina da ciki, yanzu kuma na ga jini ya zo mini, period ne ko Sari?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido, cike da son tabbatar da abin da take zargi.



Kawai ta ga yana murmushi. Cikin rashin fahimta ta ce "To ka yi mini bayani ko da hannu ne, zan gane. Dan Allah cikin ne da ni da gaske Sari na yi? Ko kuma ba ni da komai dama?"

Ya ci gaba da murmushi yana ™an™ance idanunsa yana kallonta, kamar ba mara lafiya ba.

Ji suka yi ana bubbuga ™ofa, ya tsuke fuska kamar ba shi ne yake murmushi ba. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Mamaki ya kama Nana yadda ya iya zuwa da duku-dukun nan.



Ya ™araso suka gaisa da Nana, ya kalli Hammad ya ce "Wai ya na ga daga jiya zuwa yau kamar ba kai ba. Ko dama rashin lafiyar ta ta ce?"

Hammad ya Wauki fulon hannunsa zai kai masa duka, amma ya kauce yana dariya. Sai mamaki ya kama Nana, dama yana wasa da Mahmoudu haka? Kodayake ko da suna Nigeria, su na hira amma ba sosai ba, a nan ma tun da ta fara ganinsu tare, duk maganar da zai yi masa cikin girmamawa yake yi masa. Amma kuma yanzu ta ga yana zolayarsa.



Mahmoudu ya ce "Gimbiya ya jikin nasa, duk da daga haka ma Alhamdillah na ga alamun sau™i a tattare da shi"



Nana ta Wan Sata fuska ta ce "Dan Allah ka daina ce mini gimbiyar nan."



"Wallahi dole a ce da mijin Iya Baba Nana, babu wadda ta dace da wannan sunan a kaf Agadez idan ba ke ba. Ya jikin naka?" Ya ™arasa maganar yana kallon Imam Hammad.



A sanyaye Nana ta ce "Ai maganar ba ta dawo ba tukuna sai a hankali"



"Ikon Allah, kenan dai da gaske bayan tafiyata ya ci gaba da irin wannan ciwon, ni fa na zata tun da muka tafi bai sake yi ba. Amma Nana yaya abubuwa suka kasance ne bayan tafiyata, na san akwai tarin abubuwa marasa daWi. Na san zuciyar musulunci ce ta sanya ki ke saurarenmu a yanzu ma, amma ki yi ha™uri. Har Nigeria aka je aka kama mu tare da su Sule. Sannan aka zo aka matsa ni da azabtarwa sai da na faWi inda yake. Aka je gidan da ku ke gadi, ba kwa nan. Na raka su gidanku ina tsoron ya san yana da mata saboda gudun kar a cutar da ke. ˜aninki ne ya gaya mini inda ku ke. Lokacin da aka je da ni shikaWai muka tarar a gidan ba kya nan. Wallahi har aka Waukko shi sunanki kawai yake kira, yana ba zai tafi ya bar ki ba. Babu halin na faWi cewa ya yi aure saboda na san hukuncin hakan a masarautar nan. Ga shi aka rufe ni a kurkuku da zargin ni ne na sace shi na kai shi Nigeria saboda ra'ayin kaina. Amma duk abubuwan da suka faru Nana ba su faru dan ni da Imam mu zalunce ki ba, dan Allah ki yi ha™uri"

Tamkar ya sosowa Nana abin da yake yi mata ™ai™ayi, da dannewa kawai take yi, ta fara hawaye.

Ba Mahmoudu da ya Waukko maganar ba, shi kansa Imam Hammad sai ya rikice gaba Waya.



Mahmoudu ya ce "Dan girman Allah ki yi ha™uri, da na san maganar nan, za ta Sata miki rai da ban Waukko ta ba, ki yi ha™uri"

Ta jinjina kai kawai, dan ita kanta ba ta san cikakken dalilin kukan ba, ta san dai tana bu™atar yin kukan ne ta samu afuwa a zuciyarta.



Yau Sultan ne kaWai ya zo duba Imam, sai dai ya ji daWin yadda ya gan shi. Ya tarar har ya ci abinci ya yi wanka ya canza kaya, sai dai ba magana.

Ya kalli Nana, ™asan zuciyarsa yana yaba wa ™o™arinta da ™arfin halinta. Ya ce "Kuma zai yi magana, na ga haryanzu bai ce komai ba"



Nana ta sunkuyar da kai ta ce "Zai yi in sha Allah, sai dai wasu lokutan ya kan jima bai ce komai ba, kafin maganar ta dawo"



Sultan ya jinjina kai cike da gamsuwa, ya ce "Muna godiya sosai da sosai. Ko akwai wani abu da ku ke bu™ata?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.



"To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini.

95 / 126