Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 126

72K to 75K   out of 377.2K words

kirana fa ki ka yi"""

Ya yi maganar yana haWa bakinsa da nata.

"Bayan ya cika ta, ta sunkuyar da kanta tana jin kunya. Ji ta yi jikinta ya fara sanyi, ™irjinta yana bugawa,"

"ta kalle shi ta ga fara'ar fuskarsa ta kau, ya haWe rai. A tsorace ta Wan ja jikinta, tana tunanin me ta yi masa. Tana kallon mudubin ta ga duhu ya gauraye Wakin sai iya wannan tsohon ta iya gani a cikin"

"mudubin a tsaye, sai dai a wannan karon ci yake yi da wuta."

"Tattara nutsuwarta ta yi, ta fara Addu'a a cikin zuciyarta, ta waiwayo ta kalle shi."

Ta ga fuskar sa Wauke da murmushi.

"Ya mi™o hannunsa zai taSa ta, ta ri™e hannunsa, ta yi yin™urin kallon idonsa amma ta kasa, ta ji tamkar"

zuciyarta za ta buWe.

"""Waye kai?"""

"Ya amsa da ""Mijinki mana"""

"Ta yi murmushi ta ce ""Ba Sayyid ba ne? Ai na riga na ganka. Me yasa ka zaSi muzgunawa rayuwata ne?"

"Da ina zargin ko ˜aisar ne, amma na fara fahimtar kai daban shi daban. Mece ce manufarka a kaina? Me ka ke bu™ata?"""

AYSHERCOOL

08081012143

Ayshacool

"Wata irin dariya ya saki, ya ce ""Har kin yi ™warin da ki ka daina razana da ganina kenan. Haka nake so"

"fansa zan Wauka, yanzu ne lokacin da ya dace na Wauki fansata"""

"""Wani laifi na aikata maka da ka ke i™rarin Waukar fansa a kaina"""

"Ba tare da tsammani ba, ya sha™e ta, ya Waga ta ya yi jifa da ita, ta bugu da jikin wardrobe ta faWi."

"Šakin ya gauraye da matsanancin duhu, ta ri™e wuyanta tana numfarfashi cikin yanayi mai kama da"

Wimuwa da kuma suma.

Ta daWe a haka kan ta ji kamar daga sama muryar Sayyid.

"""Rayuwata bacci kuma daf da magariba a ™asa? Ga abincinki ya fara ™onewa"""

"Nana ta Waga kai ta kalle shi suka haWa ido, amma ba ta ji komai ba. Ta tashi da ™yar ta ji mararta ta ™ulle,"

"ga hannunta da ta bugu. Amma ta daure ta kashe gas din, ta shiga yin alwala."

"Abubuwa da dama su ka zo zuciyarta, tabbas wannan sabon ™alubale ne a gare ta. Muddin zai cigaba da"

"fita daga hayyacinsa yana yi mata haka, to tana tsoron wataran ya yi mata illa."

"Haka kurum yake jin sa cikin farin ciki, sai dai lokaci Waya ya lura ita ba ta cikin walwala."

"Su na cin abinci, ya Wan shafa cinyarta. Ta farga ta kalle shi."

"Ya ce ""Ba kya cin abinci mene ne?"""

"Ta yi murmushi ta ce ""Lafiya ™alau, Abincin ne ba na so"""

"Cikin damuwa ya ce ""Na sayo miki buredi za ki ci? Ko ™os"""

"""A'a zan ci wannan Win"" da ™yar ta tilasta kanta, ta ci."

"Yanayin yadda yake ta bin ta da ido, ya sanya ta san akwai abin da yake so, sai dai a Wan tsorace take."

Haka ta ci gaba da addu'oi da neman Waukin Ubangiji.

"Duk da haryanzu tana jin nauyin sa, amma ta shirya cikin kayan baccinta na gwanjo, da Ummi ta ba ta ta"

shafa turare. Sai dai zuciyarta gaba Waya a tsinke take.

"Kwanciyarta babu jimawa, ya zo ya kwanta shi ma."

"""Rayuwata duk kin rage walwala"""

"Ta Wan ja numfashi ta ce ""'yan kwanakin nan, baki ya buWe, Ubangiji Allah ya Worar da lafiya"""

"""Amin ma vie. Ina jin daWin haka sosai"""

"""Saura kuma, Ubangiji Allah ya sanya ka tuna waye kai. Hankalina zai fi kwanciya"""

"Ya Wan yi shiru ya ce ""Ina wannan ™o™arin, ji nake kamar abin ya fi ™arfina. Amma ko da nan gaba, idan"

"ban tuna waye ni ba, ki nuna wa Wa na su Habu a matsayin dangina, tun da ku kaWai na sani"" Ya yi maganar muryarsa na rawa."

"""Shikenan mu bar wannan maganar."" Ya yi shiru bai kuma magana ba."

"""Sayyid fushi ka yi ne?"""

"""A'a ban yi fushi ba"""

"Ta din ga shafa kansa zuwa bayansa, sai dai daga ™o™arin rarrashin sa, ya fara ™o™arin zarcewa."

"A hankali ta fara jin wannan ™amshin turaren, yana ratsa kafofin hancinta."

"""Sayyid ba ka jin wani ™amshin turare?"""

"""Ina ji a jikinki"""

"""A'a ji nake kamar ba a Wakinmu muke ba"""

"Ya yi dariya, ya cika ta ya ce ""Ba sai kin yi mini wayo ba, na ™yale ki"" Ya Wan ja jikisa ya koma gefe, yana"

"ajiyar zuciya. Ta Wora hannunta a kan nasa ta ce ""Ba wayo zan yi maka ba, ai ka san ba na gudun ka."""

"""Kar ki damu, ki yi bacci"" ya Wora kanta a ™irjinsa yana shafa bayanta."

*

"Shukura ji take yi, tamkar za ta haukace, sai kokawa take da sashe daban-daban na ™wa™walwarta,"

domin samawa kanta nutsuwa.

"Gari ya tsit amma ita sai kaiwa take yi tana komowa a cikin Waki, tamkar mai jiran sa™on wani abun."

Ta zauna ta haWa kai da gwiwa ta yi tagumi.

"Ta sake tashi tsaye, ta tafi bakin taga ta tsaya tana kallon waje. Ta ™udurce a ranta, sai ta tuntuSi doctor"

Sharif ta ji mene ne ya kashe mata Wa? Haryanzu ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

"Alhaji Fatuhu kuwa, ™arfin hali kawai yake yi, ji yake tamkar an daddane rayuwarsa da jikinaa gaba Waya."

"Babu abin da yake yi masa daWi, ya daina jin daWin komai, tamkar ya fasa ihu ko zai ji sanyi a ransa."

"˜arfin hali ya yi gurin sanya Fadila farin ciki, har ya samu ta yi bacci, tun da ta yi bacci ya raba ta da"

"jikinsa a hankali, ya tashi zaune ya rafka tagumi ya din ga jin tamkar ana buga masa abu mai nauyi a kansa."

"Ya shiga banWaki ya yi wanka, ya yi alwala ya zo ya tayar da salla, amma tunani da wasi-wasi ya mamaye"

"shi, ya kasa nutsuwa a cikin salla. Ya din rafkanuwa. Ya din ga sallamewa yana sake tayarwa har ya gaji ya nemi guri ya zauna."

Ayshacool

"Tunanin yadda kayansa za su iso, a sallami mutane ya ™ara mamaye kansa, ya rasa bakin zaren matsalar"

"baki Waya, haka ya zauna har aka yi kiran sallar asuba."

****

"Tari ne ya sar™e Nana, ta tashi ta ji kamar wadda ta ™ware tana numfashi sama-sama. Ta shafa ta ji"

"Sayyid ba ya gurin, ta ji an kama hannunta an bata kofi, ta karSa ta shanye ruwan, ta ajiye kofin saboda yadda wani irin nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita."

"˜aisar ta gani a tsaye yana kallonta, jikinsa duk a ™one, bai yi mata magana ba, ya dan™i wuyanta ya zuba"

mata wani abu mai kama da haya™i a cikin bakinta.

"A take ta ji cikinta ya hautsuna, mararta ta ™ulle, ta kalle shi a razane ta ce ""˜aisar me ka yi mini?""."

"""Cikin jikinki ba shi da amfani, dole ya bar jikin ki"""

"""Saboda me, ina ruwanka da cikina?"""

"""Saboda ba zan ™arar da rayuwata a matsayin bawa ga zuriyar ku ba, ki na wahalar da ni."""

"Kafin ta yi magana, ta ji tamkar ana fizgar naman cikin mararta, ta yin™ura ta tashi a gigice."

"""Subhnallah, Sayyid, Sayyid"" ta kira sunansa a wahale."

"Daga banWaki ya fito a tsorace, ya nufo ta. Ta mi™a masa hannu, ya ri™e ta."

"""Kai ni banWaki"" ta faWa tana rintse idanunta."

"Ya kamata ta mi™e, jini ya fara biyo ™afafuwanta, ya kai ta banWaki. Su na shiga ta dur™usa a kan"

"gwiwoyinta, ta saka hannu Waya ta rirri™e ™afarsa tana girgiza kanta cikin matsanancin ciwo. Da ta ja numfashi da ™arfi, sai ta ji jinin yana zuba da yawa."

"Ya rasa yadda zai yi, ga baki ya rufe ya kasa magana."

"Can ta yi wani irin nishi, ta ™ara rirri™e ™afarsa da ™arfi, sai ga gudan jini ya faWo. A hankali ta din ga"

"samun releif, ta jinginar da kanta a jikin ™afarsa ta kasa motsi. Jin yadda ™arnin jinin ya ishe ta, ya sanya ta motsa a hankali, ta yin™ura ya kama ta, ta tashi tsaye."

"""Ka canza kaya ka yi sallar, bari na wanke jikina"""

"Ya motsa baki, amma magana ta gagara, ya dage yana ™o™arin yi, amma gumi ya fara tsatstsafo masa."

"""Ya lafa mini, ka yi salla kar ka makara, zan wanke jikina"" da ™yar ya fita, ta rufe banWakin ta wanke"

"jikinta, duk da tana jin sauran ciwon kaWan kaWan."

"Ta fito yana salla, ta Waura zani, kan ya idar ta goge gurin da ta Sata, ya idar ya ™araso gefen katifar da ta"

"zauna, idanunta har sun faWa saboda wahala."

"Ya zauna ya saka ta a gaba, ga magana amma abu ya gagara, ta kwanta a kan cinyarta, ga ciwon buguwar"

"jiya, ga rashin lafiya da ba ta gama warkewa ba, ga kuma wannan matsalar da ta tashi da ita."

"A hankali yake shafa jikinta, yana Wan matsa mata, ta ji daWin hakan sosai da sosai."

"Wajen ™arfe bakwai, ta kira Ummi, Ummi ta Waga ta ce ""Lafiya, kira da sassafe?"""

"""Kira ni kuWina ba su da yawa"""

"Ummi ta kira ta, ta ce ""Lafiya na ji muryarki a haka?"""

"""Ba na jin daWi ne Ummi, dan Allah tambayar ki zan yi, idan mutum yana da ciki yana period ne?"""

"""Wane irin period kuma? Dama ciki ne da ke? Haba ni fa in ce ranar da ki ka zo na ga alama wallahi."

"Meyafaru?"""

"""An ce akwai, kuma yau na tashi da ciwon mara ina zubar da jini"""

"""Kai, subhnallah bari na sallami yara, gani nan zuwa gidan naki"""

"Duk da jikinta babu ™wari, ta tashi ta saka kaya, ta kunna turaren wuta, Saboda a hancinta ba ta daina jin"

™arnin jinin nan ba.

Wajen tara da rabi sai ga Ummi.

"Ummi ta gaishe shi, ya Waga mata hannu tare risunar da kansa, ranar farko da Ummi ta gan shi babu"

"rawani, ya sha kitso a kansa jelar ta sauka a kafaWarsa."

"Ta ™arasa inda Nana take cikin kulawa ta ce ""Sannu Nana ya jikin?"""

"""Alhamdilillah"""

"""Gaskiya ki zo mu je a yi scanic, mu tafi Asibiti"""

"Nana ta girgiza kai ta ce 'A'a ba sai mun je ba, ni ba na son mu je, a yi ta huda ni"""

"""To Nana lafiyarki ba ta fi komai ba, tashi mu je"""

"Nana ta kalle shi, yadda ya tsare su da ido, ta ce ""Sayyid za ta raka ni Asibiti, ka zauna kar su zo yau ma a"

"neme ka, baka nan ya zama abin magana."""

"Ta kalli fuskarsa ta ce ""Na gane, ba sai ka yi magana ba"""

"Ya tashi ya buWe wardrobe Win sa, ya Waukko kuWi, ya mi™a wa Nana."

"""Ka bari da kuWi a gurina, wanda Imrana ya bani"""

"Tsuke fuska ya yi, dole ta saka hannu ta karSa, ya Wauki mayafin yin rawaninsa ya yafa a kansa, ya biyo su"

"har bakin gate, yana kallon Nana."

Ayshacool

"Ta Waga masa hannu tare da yin murmushi, shi ma ya Waga mata."

"Su na fita Ummi ta dasa mita, ta ce ""Jaraba, wannan kallon da yake yi miki, sai da na ji kamar na bar"

"masa ke na yi tafiyata, Nana sai ka ce auren Soyayya bawan Allah duk a rikice yake. Kuma dan Allah yana magana, anya na taSa jin maganarsa kuwa?"""

"Nana ta yi murmushi ta ce ""Yana yi mana"""

"""To ai ban taSa ji ya yi ba. Kai tubarkallah Nana Allah ya baki kyakyawan miji, sai ki yi ta kaffa-kaffa"

"saboda 'yan mata. Kodayake yadda yake yi Win nan ma wace za ta ce tana so?."""

Nana ta yi murmushi.

"Ummi ta sake cewa ""Na ji daWin ganin yadda ya nuna damuwarsa a kan ki, Ubangiji Allah ya sanya ya"

"Wore. Nana idan hankalin mace a kwance yake a gidan mijinta, komai mai sau™i ne"""

"Da haka suka ™arasa Asibiti, su na zuwa aka tura su scanic, da suka yi suka koma, aka tabattar da cikin ya"

fita. Aka ba wa Nana magunguna suka dawo gida.

"Yana ganin dawowar su, ya tashi. Nana ta yi masa murmushi suka wuce Waki."

"Nana ta cewa Ummi""Kar ki gaya masa, zan gaya masa da kaina"""

"Ummi ta ce ""To shikenan"" ta wanke wa Nana kayan da ta Sata, ta ™ara gyara mata Wakin, ta yi mata girki."

"Duk yana waje ya kasa shigowa. Sai da Ummi ta gama ta yi wa Nana sallama, ta fito za ta tafi, sannan ya taso."

"Da ™yar ya iya cewa ""Na gode"" shi ma sai da ya ji tamkar numfashinsa zai Wauke."

"Ummi ta ce ""Ba komai Allah ya ™ara lafiya""."

"Ya shiga Wakin da sauri, ya tarar da Nana a zaune a gefen katifa, ya zauna a kusa da ita, ya kamo"

"hannunta, tare da tsare ta da ido. Yana jiran ta yi magana."

"Ta numfasa ta ce ""Sayyid, Sari na yi"""

Yanayin fuskarsa ya sanya ta fahimci bai gane me take nufi ba.

"""Cikin babu, ya fita, jinin da na zubar cikin ne ya zube"""

"Ji ta yi tamkar hannunsa da ya ri™e ta da shi, ya yi mata shocking, saboda wani irin zirr da ta ji."

"A take fuskarsa ta yi jawur, ya ji tafukan hannayensa sun Wauki zafi, jijiyoyin kansa sun mimmi™e. Ya ci"

"gaba da motsa bakinsa zai yi magana, amma ya kasa."

"""Sayyid lafiya kuwa? Ko wani laifin na yi maka?"""

"Ya din ga murza tafukan hannayenta da Wan ™arfi, yana sauke numfashi."

"""Sayyid mene ne?"""

"Bai yi magana ba, jin ya kasa maganar ya sanya, ya saki hannunta, ya nemi guri ya kwanta yana haki"

sama-sama.

"Abun duk sai ya Waure wa Nana kai, to mene ne ma'anar hakan? Me ya sanya shi canzawa haka lokaci"

"guda? Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga ya lumshe idanunsa. Ta Wan matsa kusa da shi, ta taSa jikinsa ya ji ya fara Waukar wannan zafin. Kafin ta yi wani yin™uri tuni ya fara wannan jijjigar, jikinsa yana kakkafewa."

"Kawai ta zuba wa sarautar Allah ido, tare da rashin sanin cikakken abin yi."

Ayshercool

08081012143

Ayshacool

"Ganin abun ba na ™are ba ne, ya sanya Nana yin™urawa da ™yar, jikinta babu ™wari, ga sanyi tana ji."

"Ta Wauki hularta, ta zubo ruwa a kwano, ta zo ta ajiye a gefensa, ta zauna da niyyar karanta abin da ya"

"sauwwa™a a Al™ur'ani, ta busa a ruwan ta shafa masa. Amma ta ji komai ya Wauke daga kanta, ta kaWa ta raya amma ta kasa tuna komai."

"Ta janyo wayarta, ta fara laluben folder karatun Alkur'ani, amma wayar ta fara haske tana Waukewa"

"tamkar ta ci screen, abin fa ba taSa yi ba sai yau."

"Ta ajiye wayar jikinta yana rawa, ta rasa abin yi, ga shi yana kwance sai tsuma yake yi. Tashi ta yi ta nufi"

"wardrobe, ta buWe watso kayanta ™asa. Jakar gurin sarkin baka, ce ta faWo daga cikin kayan. Nana ta"

"dur™usa ta Wauka, ta nufi gurin da yake kwance. Ta Wora masa a ™irjinsa. Kamar ta Wora masa wuta, haka ya zabura, ya juya a hankali ya gyara kwanciyar sa, ya daina wannan tsumar ya hau bacci."

"Ta saka hannu ta Wauki jakar, tana ™are mata kallo. Sam ba ta ga wani abu na musamman a tattare da"

"jakar ba. Ta ajiye ta, ta kwanta a gefe tana jin yadda jikinta yake yi mata ciwo."

"Bayan wani Wan lokaci ya yi juyi a hankali, ya kalli agogon Wakin, ya kalle ta ya yin™ura ya tashi, ya yi"

"alawala ya yi sallar la'asar. Ya zauna a kan sallayar ya yi shiru, fuskarsa na bayyanar da damuwa."

"Nana ta tashi daga gurin da take. Ta ja ta zauna sosai ta gyara zamanta. Ta ce ""Sayyid na kasa fahimtar"

"abin da yake faruwa, ban sani ba ko na yi wani abun da na Sata maka rai ba."""

"Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, na wani Wan lokaci, ba tare da ta yi tsammani ba ya yi magana."

"""Duk na yi ™o™arin Soye matsanancin farin cikin da na shiga, da na ji za ki haihu. Na kasa Soye damuwar"

"da na shiga, da na ji na rasa abin da yake cikinki"

"Ban san dalili ba kawai na ji ina matsanancin son, abin da ban taSa gani ba, kuma yanzu na rasa shi, ba"

"tare da na yi tsammanin hakan ba""."

"Jiki a sanyaye Nana ta ce ""Sayyid idan kai ka ce haka, ni na ce me?"""

"Ya Wan girgiza kai ya ce ""Ba za ki gane ba"" ya tashi ya naWa rawaninsa, ya fice daga Wakin."

"Nana duk ta gaji da kwanciyar, ta yin™ura ta fara mayar da kayan wardrobe Win da ta watso."

"Ta Waga labulen window, dan iska ta ™ara wadatar Wakin, kawai ta hango Siyama ta fito, sanye da"

"doguwar riga da Wan ™aramin mayafi, ™onuwar hannunta, ko gama warkewa ba ta yi ba."

Sai dai Nana ta ga Sayyid take tunkara.

"Ganin tana tunkaro shi, ya sanya ya sunkuyar da kansa, daga kallon gurin da take tahowa. Sai dai tana"

"™arasowa inda yake ta tsaya tare da yin murmushi ta ce ""Sannu da ™o™ari"" ya jinjina mata kai, ba tare da"

ya kalli inda take ba.

"""Amm dan Allah magana nake son mu yi"""

Ya Waga kai ya kalle ta cikin mamaki.

"Ta Wan sunkuyar da kanta ta yi murmushi, ta ce ""Dan Allah a abubuwan da suka Wan faru, na rashin"

"kyautawa da na yi maka, nake son ka yafe mini na san na yi kuskure, ka yi ha™uri"""

"Ya Waga idanunsa ya kalle ta, ya mayar da kansa ya sunkuyar."

"""Ka yi magana mana"" ta yi maganar cikin iyayi."

"Jinjina kai ya yi, yana ™ara kawar da kansa gefe."

"Ta sake cewa ""To ai ba zan gane ba, idan ka ha™ura, ka yi magana"""

"""Ya wuce"""

"Ta saki murmushi ta ce ""Na gode sosai"" ta juya ta koma cikin gida tana murmushi. Tabbas Buzun nan, irin"

"mutanen da idan ka Wora kana relationship da su, za a ga ka haye, ya haWu ta kowane Sangare. Ta yi maganar a zuciyarta."

"Nana rasa abin yi ta yi gaba Waya, ta ji ™irjinta tamkar ta haWiyi kibiya, wani abu ya tsaya a tsakanin"

ma™ogwaronta da ™irjinta.

"Ta zauna ta yi shiru, kawai ta ji sallamar Siyama. Nana ta Waga kai ta kalle ta, sai dai ta kasa magana."

"Siyama ta zauna a kusa da ita ta ce ""˜awata kwana biyu ba ki zo ba"""

"Nana ta kalle ta ta ce ""Kina lafiya?"""

"""Ashe kuma ba ki da lafiya? Ya jikin naki?"""

"Nana ta kalli Yusra ta ce ""Ya aka yi ki ka san ba ni da lafiya? Waye ya gaya miki?"""

"""Sai an gaya mini, ina ganin komai ai. Ko kin manta gidanmu ne nima? Allah ya baku wani."""

"Nana ta ce ""Ina cikin damuwa, dan Allah kar ki dame ni"""

"Yusra ta yi murmushi ta ce ""Na sani, amma kin san faWa ya kaure a tsakanin ˜aisar da dattijo? Kuma duk"

"a kan ki?"""

"Nana ta ce ""Waye dattijo?"""

Ayshacool

"""Wanda ya ke kawo muku ziyara, da ke da mijinki, idan ba ki yi wasa ba, abu mara daWi zai iya faruwa."

"Kodayake kar na yi shishshigi, gurin shiga hurumin da ba nawa ba. Amma abubuwa na daf da rikicewa. Me ma ya faru kafin ki yi Sarin cikin jikinki?"""

"Nana ta Wan yi shiru tana son ta yi tunani, amma ba ta iya tuna komai ba, tana Wagowa ta nemi Yusra ta"

rasa.

"Damuwa da rashin sanin abin yi, ga takaicin abin da ta gani ya haWu ya sanya, ta tashi ta sake watso"

kayan

25 / 126