Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 126

27K to 30K   out of 377.2K words

yin™ura da ™yar ta tashi, ta Waukko bargonta a saman wardrobe, ta nufe shi."

"""Ka tashi ga bargo ka rufa"""

"A hankali ya buWe idonsa, ya kalle ta, kawai ya mayar ya lumshe. Ba ta ha™ura ba ta sake cewa ga shi ka"

"rufa tun da sanyi ka ke ji. Ta yi maganar tana ajiye masa bargon. HankaWe bargon ya yi gefe a zuciye,"

yana ™o™arin gyara kwanciyarsa.

"""Me ya sa zaka jefar mini da abu, idan ba ka so sai ka jefar mini, haka Wazu ma ka jefa mini bedsheet a"

"kaina, ni ka daina yi mini haka. Kawai ya tashi zaune. Me Nana za ta gani, kamaninsa sun koma na tsohon"

nan da take gani a tare da shi. Ihu ta kurma da ™arfi ta suma a gurin.

*

"Sanye take da doguwar rigar bacci shara-shara blue black, ta yi mata kyau sosai, ga tsohon cikinta, tana"

gefen gado tana shan abu a cikin kofi.

"Da sallama ya shigo Wakin, ta amsa masa, ya zauna a kusa da ita. Ta ce ""Ya yi baccin?"""

"Ya ce ""Ya yi da kyar, ban da labarin Anty Nana, babu abin da yake yi mini, yana ta biya mini abin da take"

"koya masa. Babu yadda za a yi ta dawo gidan nan ne ta ci gaba da kula da shi?"""

"Ta kwaSe baki ta ce ""Ta ina? Na gaya maka an yi mata aure da buzayen da suke gadin gidanmu"""

"Ya ce ""Ikon Allah, to dama buzaye na auren wasu wanda ba irin su ba ne?"""

"Shukura ta ce ""Waye ya san musu ma? Abin ne dai ga shi nan"""

"""Allah ya kyauta, ni dai Haidar nake ji, da alama sun sha™u, wai me ki ke sha a cikin kofin nan ne?"" Ya yi"

magana yana karSar kofin.

"Magani ya gani a ciki, ya tsuke fuska ya ce ""Wai me yasa ba kya ji ne? Na hana ki shan wannan"

"abubuwan, ya za a yi ki na da tsohon ciki ki din ga shan wannan abubuwan? Sai kin yi wa kan ki illa?"""

"Shukura ta Sata fuska ta ce ""Ba fa da yawa na sha ba, kuma ai duk dan kai nake yi"""

"""Kuma ni na ce miki ina bukatar wannan abin? Fruit bai ishe ki ba me ki ke nema kuma? Kawai sai kin"

"illata mini yaro? Wallahi na kuma ganin kina shan wannan abubuwan sai ranki ya Saci"" ya tashi ya fice ya bar mata Wakin."

"Haushi ne ya ishe ta, kawai ta nemi guri ta kwanta."

"Girma da nauyin cikin jikinta, bai hanata yin gudun ceton ranta ba, tana gudun tana waiwaye, ga"

"numfashinta na neman barin huhunta, saboda tsananin gajiya."

"Karo ta yi da wani mutum sanye da farar riga, mi™a masa hannu take yi, tana faWin ""Dan Allah ka taimake"

"ni"""

Ayshacool

"Lokaci Waya abin da yake cikinta, ya yi wani irin dun™ulewa, ya na danno ta. Cikin gigita ta tsaya tare da"

"dur™usawa a kan gwiwoyinta, tana jin nishi."

"Mutumin da yake bin ta ya ™araso gabanta, ya saka hannu ya cire abin da ya rufe fuskarsa da shi."

"Cikin tashin hankali ta ce ""Daddy"""

"""Ki yi ha™uri Shukura, ni za ki taimaka, ki sadaukar mini da abin da yake cikin ki"""

"Jan jikinta ta fara yi, tana girgiza kanta, cikin kuka da azabar na™uda take faWin ""A'a Daddy, dan Allah ka"

"bar mini jaririna, na baka tawa rayuwar amma ka bar mini jaririna dan Allah"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Ba na bu™atar rayuwar ki Shukura, yaron nan kawai nake bu™ata"""

"Mutumin nan mai farar riga, ya buWe fuskarsa, sai ta ga doctor Sharif ne. Cikin kuka take ce masa ""Dan"

"Allah Doctor ka taimake ni, ka ba shi ha™uri""."

"Bai saurare ta ba, ya dur™usa ya yi mata wata allura, take ta yi wani irin nishi, jaririn ya faWo."

"Ya Wauke shi har mabiyiyar, ya mi™a wa Alhaji Zailani."

"Alhaji Zailani ya ciro wata 'yar wu™a, ya Waga jaririn kansa a ™asa, ™afafuwan sa a sama."

"Ihu take iya ™arfin ta, tana yi masa magiya, amma ya Waga wu™ar nan zai caka wa jaririn, bai kai ga caka"

"masa ba, ta ji an kira sunanta. Tana Waga kai ta ga Nana."

"Nana ta jefa mata wata sharSeSiyar wu™a, a rikice Alhaj Zailani ya yi kan Shukura, cikin sa'a ta caka masa"

wu™ar da Nana ta jefo mata.

"""Shukura lafiya? Me ya same ki? Me ya samu jaririn naki?"" Ta buWe idonta a hankali ta kalli fuskar mijinta"

da ke Wauke da matsananciyar damuwa.

"""Meya faru?"" Ya sake tambayarta."

"Jikinta ne kawai yake karkarwa, tana zare ido cike da matsanancin tsoro da tashin hankali."

"Ba ta iya yi masa magana ba, sai godiya da ta din ga yi wa Allah a zuciyarta, da ya zamana mafarki ne ba"

gaskiya ba.

*

"Da safe Nana na ta karkaWe Waki tana gyarawa, ko gaishe shi ba ta yi ba, dama ba amsawa yake yi ba idan"

"ta gaishe shi. Sai dai fes take tuna abin da ya faru jiya da daddare, yadda fuskarsa ta canza baki Waya. Sai"

"dai haryanzu tana ji a ranta, sharrin ˜aisar ne ya sanya take ganin wannan abubuwan a tattare da shi."

"""Zan yi wanka"" ta ji muryarsa tana tsaka da gyara Wakin."

"Ta kalle shi ta ce ""To banWakin zan biyo ka ko ya za a yi?"" Ta yi maganar cikin tsiwa."

"Bakinta ya bi da kallo, rasa me zai ce mata ya yi, a wannan karon ma, ba ta gane abin da yake nufi ba,"

kawai ya wuce banWakin. Yana shiga ta dira mitar abin da yake yi mata.

"""Wai zai yi wanka, ko bin sa zan yi na yi masa wankan, ni ban gane ba"""

"Ta ci gaba da aikinta, yana fitowa bai tsaya wata-wata ba, ya sake yaye bedsheet Win da ta gama"

shimfiWawa ya rufa yana rawar sanyi.

"A hanzarce ta Wago a ™ule ta ce ""Lafiya, meye haka wai?"" Ta yi maganar kamar ta fashe da kuka, saboda"

a lokacin ta gama sanya zanin gadon.

"Jin ta tsaya masa a ka, saboda ya Wauki bedsheet ya sanya ya mi™e, ya watsar mata da shi a gurin."

"Ya Wauki kayan da zai saka ya shiga toilet ya canza, ya fito ya bar mata Wakin. Cikin hantsi ya fita ya zauna"

"ya takure jikinsa, Wumin ranar yana taSa shi."

Nana ta ci gaba da mita tana ™ara gyarawa.

"Muryar Habu ta jiyo, ta le™a ta taga, ta gan su tare a zaune. Yadda Habu ya yi shiru ya nutsu ne, ya sanya"

"ta gane mijinta magana yake yi, amma muryarsa ™asa-™asa, ba a jin tasa sai dai ta Habu ake iya ji."

"Ta saki labulen ta nemi guri ta zauna, Habu ya yi sallama a ™ofar Wakin. Ta amsa masa. Ya ce ""Na shigo?"""

"""Eh bismillah"" sai ta ga ya shigo shikaWai."

"Nana ta ce ""Ina kwana?"""

"""Lafiya ™alau Alhamdilillah. Ya rayuwar?"""

"Nana ta yi murmushi, haryanzu hausar su wasu lokutan sai a hankali, ta ce ""Lafiya ™alau"""

"""Ga wannan"" ya yi maganar yana ba ta leda."

"Jiki a sanyaye ta ce ""Malam Habu, abin da ya faru Allah ne ya ™addara, wannan Wawainiyar ta isa haka,"

"kullum sai kun kawo mana Abinci, ga Wawainiya da ku ke ta yi. Zan fara girki in sha Allah"""

"Ya yi murmushi ya ce ""Kar ki damu, ai dolen mu ne mu kula da ke. Kayan miya ne a ciki da sauran kayan"

"amfani. Duk abin da babu, akwai lambata a rubuce a gurin mijin naki, sai ku kira ni"" Nana ta jinjina masa kai."

Ayshacool

"Sai kuma Habu ya yi murmushi ya ce ""Amm amarya, mutumin fa ya kawo mini ™arar ki, ya ce ki na yi"

"masa rashin kunya, ki na Waga masa murya. Dan Allah kamar yadda na gaya miki ki yi ha™uri da shi dan"

"Allah. A hankali za ki fuskanci yadda za ki zauna da shi, na san abin zai yi miki wahala amma dan Allah ki"

"yi ha™uri hakan tamkar jihadi ne, ke ma Allah ya kawo ki mu yi tare"""

"Nana ta haWiye maganganu da tambayoyi da ta so yi wa Habu, ta daure ta ce ""Hmm ™ara ta ma ya kawo"

"ko? To shikenan na daina"""

"""Ki yi ha™uri amma, yanayin ciwon nasa ne ba ya son hayaniya, shi yasa"""

"Nana ta ce ""Babu damuwa in sha Allah, ina son ma na yi maka wasu tambayoyi, amma sai ka kuma"

"dawowa"""

"Gyaran muryar sa su ka ji, Habu ya mi™e. Buzu ya juya yare ya yi masa magana, Habu ya jinjina kai."

"Ya zo ya wuce ya buWe wardrobe, ya Webo kayansa masu datti, da ya nannaWe ya bawa Habu."

"Habu ya karSa, ya yi musu sallama, ya tafi."

"Nana ta din ga kallonsa, bakinta fal magana, amma ya ™i kallonta."

"""Shi ne ka ce ina yi maka rashin kunya ko? To me na yi maka na rashin kunya? Dama ashe ka na magana"

"ni ce ba ka kulawa ko?"" Ya lumshe idanunsa yana kaWa ™afar sa."

"""Idan ba ka yi mini magana, ba zan san na yi maka laifi ba, ko na san abin da ka ke so ba, da wanda ba ka"

"so"" ta gama surutunta, ganin ba shi da niyyar tanka mata ya sanya ta kama wani abin."

"Kayan miyar da Habu ya kawo, ta zauna ta gyara tsaf, ta yi greating Win su. Ta Wora a kan gas. Tana jin"

"yadda yake tari, saboda zafin attaruhu. Ta dafa taliya da miya."

"Ya din ga bin ta da ido, har ta gama."

"Ta zuba masa ta ajiye masa komai, ta tashi ta je ta yi alwala, ta dawo ta tayar da sallar azahar."

"Ta idar ta yi azkar, ta ninke dadduma, ta gan shi ya haWa gumi, yana cakalar abincin, fuskarsa ta yi jawur,"

sai gumi ne yake tsatstsafo masa.

"""Lafiya ya na ga ka na gumi, abincin babu daWi ne?"" Ya ja numfashi ya kalle ta, hannunsa ri™e da cokali"

mai yatsu.

"Babu irin tambayar da ba ta yi masa ba, amma bai ba ta amsa ba, har ta gaji ta rabu da shi. A haka ya"

cinye abincin.

Nana ta rasa abin da ya sanya shi haWa wannan uban gumin. Idonta ne ya sauka a kan wayarta. A take

tunanin mahaifiyarta ya ™ara faWo mata. Jiki a sanyaye ta ™arasa ta Wauki wayar tana kallon screen Win.

"Jiki a sanyaye ta buWe wayar, ta shiga gurin kira, ta shigar da lambobin kamar yadda ta haddace su, cike"

da fatan Allah ya sa wayar ta shiga.

"Babu zato babu tsammani, ta ji wayar ta shiga. Gyara zamanta ta yi tana fatan Allah ya sa ta ji abin da"

"take tsammanni. Sai dai akasin haka ta ji muryar namiji, muryar mutumin da ta tsana a rayuwarta."

"Cikin dakiya ta ce ""Baba ina wuni?"""

"""Lafiya kalau wace ce?"""

"Cikin sanyin murya ta ce ""Dan Allah me wayar nake nema"""

"Ya ce ""To wace ce ke Win?"""

"Ta yi ajiyar zuciya ta ce ""Baba Nana ce, mamana nake nema"" ta yi maganar cikin rawar murya, idanunta"

na cika da hawaye.

"""Ai dama na sani, wallahi na sani, na san ba ta fasa bibiyar tsohon mijinta ba, wallahi zan gauraya da ita"""

"A ruWe Nana ta ce ""Dan Allah Baba ka tsaya ka ji, wallahi ba sa waya da Babanmu, lamba ta ce, dan Allah"

"ka haWa ni da ita ko muryarta na ji, dan Allah.. ™it ya kashe wayar ba tare da ta gama faWar abin da za ta faWa ba."

"Wata irin tafasa zuciyarta ta din ga yi, cike da Sacin rai da tashin hankali. Wasu irin hawaye masu raWaWi"

suka fara biyo fuskar ta.

"Ta Wauki wayar ta yi jifa da ita, caraf ya cafke wayar."

Ya kalli yadda hawaye yake fita daga idanunta.

"Kawai ya ga ta taso za ta fita daga Wakin, jikinta yana rawa."

"Har za ta gota shi, ya dan™o hannunta ya yo baya da ita, yana ™arewa ˜aisar kallo da ya bayyana a"

gefenta yana huci!.

Ayshercool

08081012143

Ayshacool

Page 31

"Bai kula ˜aisar ba, ya ja Nana zuwa kan katifa, ya zaunar da ita, idanunta a lumshe, har a lokacin kuma"

"fitar da hawaye suke yi, babu ™a™™autawa. Ya taSa tafukan hannayenta, ya ji sanyi ™alau kamar an ciro ta daga ™an™ara."

"Ya ™ura mata ido yana nazarin ta, a take ya tuno ranar da ta shiga Wakinsu, tana kiran Haidar, su na haWa"

ido ta ja da baya ta ™wala ihu ta faWi.

"Haka jikinta ya ™andare, ta din ga karkarwa, ya ga wani narkeken ba™in muzuru ya bayyana a Wakin, yana"

ta zagaye ta.

"Ya sauke numfashi, ya sanya yatsunsa biyu, ya danna bayan kunnenta. Ya mi™e ya bar kusa da ita. A"

"hankali jikinta ya daina rawar, ta buWe idonta, sai dai tun da ta buWe idon, ba ta tashi daga gurin ba balle ta ci abinci."

"Ya din ga satar kallonta, amma ba ta tashi daga in da take ba, balle ta ci abinci. Yana son ya yi magana"

amma ya rasa me zai ce mata.

"Ta tashi zaune da ™yar, ta haWa kai da gwiwa, ta yi kuka mai isar ta. Sai da aka kira la'asar sannan ta tashi"

"ta yi alwala, ta tayar da salla."

"Bayan ta idar tana zaune ta yi shiru, ya dawo Wakin, ya duba gurin da ta gama girkin, babu alamar ta ci"

abinci.

"""Ba za a ci abinci ba?"" Ta ji maganar sa babu tsammani."

"Ta Waga kai ta kalle shi, kamar mai jiran ™iris, kawai ta sake fashewa da kuka. Ya yi zuru da ido yana bin ta"

"da kallo, bai ce ta yi shiru ba, har ta yi mai isar ta yi shiru."

"Duk ya damu ganin ba ta ci abinci ba, ya rasa me zai ce mata, ga shi yanayinta ya fahimci rigimammiya ce."

"Jin motsi a waje ana taSa gate, ya sanya ya tashi ya rufe fuskar sa, ya fita ya duba waye."

"Tsayawa ya yi yana kallon su, mata ne su uku, da ™anan yara sai wani Wan matashin saurayi."

"""Sannu malam, ko kai ne mijin Nanan?"" Ya tsaya tsuru yana kallon su."

"""Gurin Nana mu ka zo tana nan?"" ya nuna musu Wakin su."

"Suka wuce, Ummi tana cewa ""Na yi ™o™ari fa da na iya kawo mu gidan nan"""

"Bayan Jamila ya bi da kallo, jikinsa na ba shi wani abu a game da ita."

"Wata irin zabura Nana ta yi ta rungume Ummi, ba ta taSa tsammanin ganin su ba. Ta rungume Jamila"

"cikin farin ciki ta ce ""Dama za ku zo ba ku gaya mini ba?"""

"Ummi ta ce ""Mu ki bamu guri mu zauna"""

"Nasiru ya ce ""Hajiya Anty Nana amarya"" da™uwa ta yi masa ta ce ""Gidanku"""

"Ya yi dariya ya ce ""Na yi missing Win ki sosai"""

"Take ta manta da damuwar da take ciki, ta ware suka hau hira. Ta juye musu sauran abincin da ba ta ci"

"ba, ta ce za ta Wora musu wani."

"Ummi ta ce ""Ke a ™oshe muke, ga shi wannan miya ce na Wan yi miki, tun bayan kawo ki da kwana biyu,"

"na so yi miki, bana jin daWi ne. Ga Wan cin-cin da dubulan na yi miki. Ga kuma turarukan wuta da wata"

"ma™wanciyar ku, ta bayar a kawo miki ga humra ma. Sai kuma kaya da na Wan ™ara sayo miki"""

"Nana ta ce ""Allah sarki, na gode sosai da sosai Anty Ummi, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Jamcy ya"

"garin ne?"""

"Jamila ta ce ""Uhumm mamaki nake yi, kamar ba ke ce ki ka gama uban kuka ba, an aura miki buzu,"

"amma kalli yadda ki ka ware yanzu"""

"Nana ta yi murmushi ta ce ""To ba dole na ware ba, lafiyayyen Waki, ga wardrobe, ga katifata ga"

"banWakina nikaWai ba takura ga wuta 2hrs ba yankewa"""

"Suwaiba ta ce ""Katifa ko abin da ake yi a kan katifar?"""

"Nana ta ce ""Duka Wan sunna ai ba zai ™i sunna ba Jamila, tun da dan haka ake auren"""

"Ummi ta ce ""Dan uban ku da yara a gurin ku ke yi mana batsa"""

"Nana ta yi murmushi ta ce ""Ya Baba, ina mama su ba za su zo ba?"""

"Ummi ta ce ""Za su zo ne, Baba babu lafiya ™afarsa ce take ciwo"""

"Nana ta ce ""Ciwon ™afa kuma?"""

"""Wallahi kuwa, ba za ki kira mijin naki mu gaisa ba"""

"Nana ta Wan kwaSe baki ta ce ""Ba kula ku zai yi ba, Nasiru ya makaranta"" ta karkatar da zancen ga"

"Nasiru. ""Makaranta lafiya ™alau Alhamdilillah"""

"A ™ofar Wakin ya yi gyaran murya ya tsaya, Nana ta yin™ura ta tashi, ta Waga labulen. Babu hijjabi a jikinta,"

sai doguwar rigar atamfa.

"Ya mi™o mata leda, ta saka hannu biyu ta karSa, bai ce mata komai ba, ya juya ya koma bakin gate."

"Fura da Nono ne kaya guda, abin sai da ya bawa Nana mamaki, ba ta san a ina ya samo su ba. Ta ajiye"

"musu suka dama, suka sha."

Ayshacool

"Jamila ta mi™a wa Nana Wan ™aramin flask ta ce ""Nana ga mutuniyar ki na yi miki wainar fulawa"" Nana ta"

"haWiyi yawu cikin murna ta din ga yi wa Jamila godiya. Ta ce ""Wannan sai dare zan dafa shayi na ci da ita"""

"Suwaiba ta ce ""Ashe fa buzu ki ke aure, ba za a gaya miki shayi ba yanzu"""

"Nana ta ce ""Kamar kin sani, ni yanzu shayi ai sai dai na koya wasu, kwana muke mu wuni shan shayi"

"babu ™a™™autawa"" suka yi dariya."

"Har magariba su na gidan, sai da suka yi sallar magariba, Nana ta fito har bakin gate ta rako su, sai dai"

baya nan.

"Ummi ta ce ""Kin ga har zamu tafi, bamu haWu mun gaisa ba"""

"Nana ta ce ""Ina ga yana masallaci"""

"Suka yi sallama, suka tafi Nana ta koma Waki. Har cikin ranta ta ji daWin zuwan su."

"Ta yi wanke-wanke ta gyara Wakin fes. Ta Waukko flask Win wainar fulawar, ta saka a gaba ta fara ci. Ba ta"

"ci da yawa ba, Haula ta yi sallama."

"Nana ta amsa cikin sakin fuska, duk da ta yi mamakin ganinta a daidai wannan lokacin."

"""Anty Haula ba ki yi fushi ba? Haryanzu ban fara fita ba, shi yasa ban shigo miki ba"""

"Haula ta ce ""Allah sarki, kar ki damu wallahi, ashe ba™i ki ka yi?"""

"Ba tare da Nana ta yi tunanin komai ba, ta ce ""Eh, 'yan gidanmu ne su ka zo, bismillah matso mu ci"

"abinci"" Aikuwa Haula ta gyara zama ta zura hannu a kwano, ta fara cin abincin. Kafin Nana ta yi loma"

"Waya ta yi huWu da rabi, kafin wani lokaci Nana sai filin kwanon ta gani, Haula na ta suWar baki saboda yajin wainar."

"Sai da ran Nana ya sosu, dan kuwa ta so cin wainar nan ta ™oshi."

"Labulen Wakin kawai ya Waga ya shigo, Haula ta tashi zumbur. Ta kalli Nana ta ce ""Na gode sosai sai"

"anjima"" sai da Haula ta fice sannan ya shigo Wakin."

"Ya zauna a gurin da ya saba zama, Nana ta Waukko ta sa furar da ta ajiye masa, da cin-cin da dubulan a"

"plate, ta nufe shi."

"""Sannu da zuwa"" ya jinjina mata kai."

""" 'yan gidanmu ne fa suka zo"" ta yi maganar fuskarta na bayyanar da annashuwa. Ya gyaWa mata kai."

"""Na

10 / 126