Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   107 / 126

318K to 321K   out of 377.2K words

fita. Kowanne a cikin su yana ta sa™e-sa™e a cikin zuciyarsa.

Sai dai bayan an yi hawan ra™uman, da Hammad ya faWo tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana le™en mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta Wauke da damuwa.



A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba.



Ayshercool

08081012143



93

93

LITTAFIN KUŠI NE, KI BIYA KUŠIN KARATU KAFIN KI KARANTA.

08081012143



Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani.

Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daWi, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faWo daga kan Taguwa.

Wajen ™arfe sha Waya, da ya ji sau™i, ya lallaSa ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faWo. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa.



Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa.

Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son ™as™antar da ita ko ta halin ™a™a.

Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki ha™ura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka Waukko ni na yi miki"



"Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuWi zan iya bayarwa na saye ki"



"Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu.  Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta ™arasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haWiye maganganun da ta yi niyyar caSawa Nana.



"Cherié, ba zai yiwu ki Waukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya."



Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya Wora yatsansa a kan laSSansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haWa su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa Wimaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan".



"Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na ™asa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin ™arfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya ™arasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo ™amshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaWa hancinsa.



Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba.

Ya kira wayar Hammad, amma bai Wauka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haWu da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar.

"Anya yaron na ba Wan Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai Waga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu.



"Tun jiya nake kiran ka ka ™i Waga wayata"



Hammad ya ce "Ban jin daWi ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?"



Mahmoudu ya ce "A ina zamu haWu, ina da magana da kai"



Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba"



"Idan ya sallame ka, mu haWu a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu"



Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?"



Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haWu"



Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar.



Da yamma suka haWu a sahara, lokacin rana ta yi sanyi.

Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?"



Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare."



Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta.

Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa.

Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?"



"Ina tunanin yarinyar nan ne"



"Wacce?"



"Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita"

Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taSa ganinta ba ko a wani guri?" Ya Wan yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taSa ganinta"

"Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo.

Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne"



Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na MaraWi ta Waukko ta a gurin su Al-Husssain"



Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya mi™a masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah"

Hammd ya sanya hannu ya karSa, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya Wago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?"



"Samo shi na yi kawai na nuna maka"



Ya dam™e wayar da ™arfi, ™irjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba Wana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine"

"Ka na da wata matar ne da zata haifa maka Wa? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ko Waya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faWin ™asar nan"



"Me za ka yi musu?"



"Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da ala™a da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan"



Mahmoudu ya karSi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba Waya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo.

Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai Wago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai.



˜aisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaWan. Giyaz ya Waga kai ya kalle shi, ya ce "Šan samari ya dai?"



"Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?"



Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?"



"Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga Wa a tsakaninsu ko iya yanzu ka Wauki fansar ai, ka ™yale ta ta huta haka?"



"Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ™ona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na Wagawa ™afa ma sassauta mata?"

"Ba na son ala™ata da kai ta ™ara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" ˜aisar ya yi maganar cikin ™unar rai.

Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi"



Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taSa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba.

Gefe guda ya so haWuwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki.

Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ™amshin da take yi, har wani ™ara nutsuwa ya yi yana kallonta.

"Tuba nake ranka ya daWe" Sayyid Win da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa.

Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya Waurin Wan kwali, ta yi kyau.

Ya ce "Amm Asma'u ko?"

Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa.

"Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na MaraWi ta Waukko ki ko?"

"Eh Sayyid"

"Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?"

Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya Sata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria"

Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba.

A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga Wakin.

˜ara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaWan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buWe idanunsa, ya ji yadda ta ™an™ame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faWin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ™an™ame shi tana ci gaba da kuka. Gaba Waya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani sa™on take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yin™uri ba, ya ji tana magana da ˜aisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe.

Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu.

Sai gefin Asuba da ta bar Wakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raWaWi a tsakiyar kansa, zuwa ™irjinsa gaba Waya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ™wa™walwarsa na nema ta hargitse.

Garau ya mi™e bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana.

Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani Waurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba.

Ko da ya dawo, har ya wuce Wakinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla.

Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi Wakin Nana. Sai dai da ya je Wakin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye.

Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya Wauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen Win wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen Win wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ™arfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar Wakin.



AREWABOOKS



Ko da Nana ta shigo Wakin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki.

Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma  kasancewar sa Namiji Wan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta ha™i™anin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta.

Tun da ya bar Wakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a Wakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taSa ganin Nana ba, amma meye haWinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne ala™arta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faWar wannan maganganun da suke nuna da ala™a a tsakaninsu.

Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaWi bai yi ba.

Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar Wakinta, ya koma ya nufi Wakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ™ofar. Ya buWe ™ofar Wakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, ˜aisar ne ya ™ara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanWa Hammad ya Wauki wayar ya yi waje.

Bai ko sake nufar Wakinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi.

Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?"



"Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?"



Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen Win da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu.

"Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala.



Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka"

Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faWi Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali.

Ya Wauki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?"



"Eh ya kira ni, ya yi mini maganar"



"To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?"



Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuSe su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na Wauke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare"

Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka ™arasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna"

Sanin ala™ar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to.

Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da ™ara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaSa ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faWin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil"

Mahmoudu ya dur™usa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa.

"Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa.

"Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali.



"Na'am Imam"



"Mene ne ala™ata da yarinyar nan?"



"Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna"



"Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?"



"Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna"

Sai zuwa yamma Hammad ya Wan samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi.

Da daddare Asal ta Wauki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai Waukar ido take yi. Yana ta ™o™arin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa.

Sai dai bai iya taSuka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa.

Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana Sullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama

107 / 126