Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   114 / 126

339K to 342K   out of 377.2K words

taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faWa kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila.

Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba Waya, komai sai an yi mata. ˜arshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya.



*****



Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga.

Sultan ya ™i kallon inda Zahradeen yake, zai Wauki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taSa shi.



Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse.

Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi.

"Ranka ya daWe, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun Wazu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon.

Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taSa shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?"



"Fita ki bani guri"



Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?"



"Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko ™aunar ganinki, ki fita kafin na Wauki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin Sacin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?.

*****

Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a Wakin nan da suke, ta samu nutsuwa.

Da kyar ta samu ta iya yin salla.

Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buWe ™ofar Wakin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaWan. Ta mi™e tsaye ya ™araso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya Wago ya kwantar da kansa a jikinta.

Nana ta ™ara janyo shi jikinta, ta ™an™ame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta.

"Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana ™ara shigewa jikinta.

"Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma ™an™ame shi.

"Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini"

"Ba komai Sayyid"

"To idan dai kina so na sosai, Wan bani sanyin mana" Yayi maganar yana Wan shafa jikinta yana murmushi.

Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya Wago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu ™wari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?"

"A'a"

"Mene ne?"

"Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi ha™uri ka yafe mata"

Ya yi murmushi mai ciwo, ya ce "Me Asal Win ta yi?"

"Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata"

Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta"

Nana ta ce "Wata™ila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi ha™uri ka yafe mata"

Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta ™ara ™an™ame shi, cikin matsanancin tausayawa.



*****



Sultan na kashingiWe, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a Wauka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta.

Sultan ya Wago ya numfasa cikin ™asaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da ™a'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya.

Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a ™asar Agadez. Ba™a™en buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata ™abila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karSe ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya Wan da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria.



97

1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic

08081012143



Gaba Waya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan.



Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da ™o™arin bawa Wanka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata"



"Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin Sarna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin Wan uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya Waga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata"



Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari"



Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya bu™atar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne.

Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na ™asar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin ™asar Niger, domin kowane Wan Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran Wan ™asa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a ™asar nan.

Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daWi ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad Wana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buWe tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da ba™o a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso"

Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira.

Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a WaWWaure da igiya tamau kamar Sarawo.

Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi ™uri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya Wuri ruwa.

Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya ™ara sanyawa duk aka zuba masa ido.



Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani"



Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai"



Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez"



Sarkin baka ya ce "Kuma me?"



"Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki"



"Mene ne dalilinka na yin hakan?"



Ya numfasa ya saci kallon Sultan ya ce "Na haka ne, saboda huce takaicin yadda ake bautar da mu tun daga kan kakana, wannan dalilin ya sanya lokacin boka Riyan, na koyi harkar bokanci a gurinsa"



Sultan ya ce "Ina fatan kun ga Waya daga cikin illolin wannan al'adun da muke yi, marasa tsuhe balle makama? Mu na jinka ci gaba"



Sarkin baka ya ce "Ba ka ji ka ci gaba mana"



"An bani wasu ayyuka, duk da ba kowa ya san ina bokanci ba, sai dai akwai wani babba a masarautar nan da shi ya ™arfafe ni na koyi harkar bokanci.

Ni aka saka na yi wa Imam Hammad Asiri, da aljanin da ya sanya ya bar ™asar nan, ya manta komai da ya shafe shi, ciki hadda tuna waye shi.

Sannan aka bani aikin yi masa asiri da wani tsohon aljani a cikin gidan tarihin, da yake sanya masa wannan zafin jikin da yake gigita shi".

Sarkin baka ya sake cewa "Yaya ka ke yi?"



"Da fari na ha™a rami a cikin tsohuwar kurkuku, ana kawo mini itace cikin dare, ina tona tsofaffin kabarurruka na cikin gidan, na Wauki ™warangwal Win, na saka shi a cikin wuta, da hatimai daban-daban da sunan Imam Hammad, duk lokacin da na babbaka wannan wutar yadda ™warangwal Win nan yake ™onewa haka yake jin zafin a jikinsa. Idan ™warangwal Win ya murmushe saboda zafin wuta, sai na kuma tono wani. Daga baya kuma aka koma kawo mini sababbin gawarwaki na koma yin aikin da su, idan na saka musu wutar nan, haka yake jin wannan zafin a jikinsa"

Gurin ya yi tsit, aka rasa wanda zai yi magana. Jikin Matawalle yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma suwaye haka?"

Sultan ya ce "Ba sai an faWe su ba, amma sun san kansu, kuma duk wanda yake da ja a kan maganar, yana iya zuwa gidan tarihin da kansa ya tabattar. Dan haka a yau na kawo ™arshen zaman yau, dan haka zan zo da sauran bayani da abubuwan da zamu caccanza".

Nan aka ci gaba da salallami, aka rasa mai sake cewa komai.



Nana tana kwance tare da Hammad, kamar zai shige cikinta, sai shafa gashin sa take yi sannu a hankali.

Ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru.

Yadda bokan nan ya din ga yi musu bayanin, Imam Omar da mahaifinsa Sardauna, suke zuwa da yadda suka yi masa asirin nan na zafin jiki. Kuma da sanin Tafawa, kowa fafutukarsa Wansa ya samu mulki. Haka zalika Asal ta yi soyayya da Omar, ita take ajiye wa Hammad takardun nan. Ko da auren Hammad sun yi soyayya tare, kafin daga bisani da ta ga babu amfani soyayyar tasu, ta fara son Hammad ta daina biye masa.

Sai dai ya ci gaba da yi mata barazanar sai ya tona mata asiri, irin hirarrakin da suke yi. Sai dai babu wani abu na saSon Allah da ya taSa shiga tsakaninsu, sai dai duk wasu zantuttuka na banza har da wanda bai kamata ba, suna yi. Babu abin da bai sani ba a game da aurenta, da abubuwan da yake faruwa tsakaninta da Hammad ba.

Hatta sirrin shimfiWar aurensu, babu abin da Omar bai sani ba. Shi ya din ga ziga ta, tun daga lokacin da aka ce za a yi aurenta da Hammad, shi ya din ga ziga ta har bayan auren.

Ya ci gaba da zuwa gurin bokan nan, yana karSar wannan takardar, yana bawa Asal, wanda da ya yi tozali da takardar yake sake ruWewa, jikinsa ya rikice ya yi ta jin ihun da alajanin nan yake yi a jikin ™warangwal Win nan, duk ya fita hayyacinsa.

Babu yadda Omar bai yi da Bokan nan, ya yi masa abin da Asal za ta yarda shi, amma ya ce ba zai yi wannan cin amanar ba saboda Hammad yana yi masa alheri ta wasu Sangarorin. Gaba Waya bokan ya gaya musu labarin, da abin da yake tsakanin Omar da Asal a baya.

Babban abin da ya Waga wa Nana hankali, bai wuce yadda bokan ya ce, ko za su kashe shi, zai iya lalata sihirin da ya yi da aljanin jikin ™warangwal Win da yake amfani da shi, amma ba zai iya raba Hammad da Giyaz ba, saboda Giyaz baya saSa al™awari, kuma ga Nana tana tare da Hammad, yana ganin Wansa a jikinta, idan ba kashe Giyaz za a yi har lahira ba, ba zai rabu da shi ba.

Da ta zo nan a tunaninta, ta lumshe idanunta hawaye na zirarowa a hankali.

Hammad ya yin™ura ya tashi zaune, ta maze ta goge hawayenta. Ya ™are mata kallo ya yi wani irin tattausan murmushi, ya shafa gashin kansa ya ce "Ba ™aramin kyau ki ka yi mini ba ma vie, ina kewa, Wan yi mini wa™ar mana abar ™auna" Yayi maganar yana sumbatar hannunta, tare da matsawa kusa da ita.

Ta Wan matsa kaWan ta ce "Ana ta kai ka na ta kaya"



"To ni kayan ne suka fi damuna, fiye da kayan ai. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zan yi miki, kuma ina ro™on Allah kar ya kama ki da laifin guduna da ki ke yi, saboda kin fi ni gaskiya ta kowace fuska.

Amma har abada ni mai ™aunar ki ne, kuma ba zan taSa yarda a raba ni da rayuwata ba in sha Allah" Ya yi maganar yana sake rungume ta, wani abu mai sanya nutsuwa na fizagarsa game da ita.

"Ka daina yi mini wannan kallon mana" Ta yi maganar tana hararasa cikin wasa.

"Idan ban kalle ki ba wa zam kalla, kina nan a yadda ki ke ma vie, kamar baki haifi Muhsin ba"

Ta Wan Sata fuska ta ce "Da na canza daina sona za ka yi kenan?"

Yayi murmushi ya ce "Haryanzu ba ki san waye Hammad ba, ke Win nake so ne Asmy, babu abin da zai canza a tattare da ke, na ji na daina sonki ko kaWan. Ina son Husna"

"Sake faWa" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.

"Sai kin yi mini wa™a tukuna" Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce "Sai ka biya ni tukuna."



Ya Wan yi shiru ya ce "Ina tuna mutane daban-daban da muka rayu da su a Nigeria, ko ina yayarki Win nan, da ta yi ta Wawainiya da mu? Da 'yan gidanku, da mutumin nan da na tsana, wanda na yi wa gadi da farko. Sai kuma mutanen gidan da muka zauna, da muka yi aure"



Nana ta ce "Gidansu budurwarka ko?"



Ya ce "Eh nan"



"To tashi daga jikina"



Hammad ya ce "Ba zan tashi ba, ai ni ban ce budurwata ba, ke ki ka fara."



Ta yi murmushi ta ce "Babu abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah, ni dai ina ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke a kanmu"

Ya ce "Alkhairi in sha Allah, ni nama manta, yana nemanmu anjima, ban san me zai ce mana ba. Amma ina tsammanin alkhairi daga bakinsa"

"Allah yasa ina fatan hakan nima, amma dan Allah ka sanya baki, na ga ya yi fushi sosai da sosai da Wan uwanka, ko zaka saka baki?"

"Ba ruwana" Ya bata amsa kai tsaye.

Nana ta ce "Kar ka ce haka" Ya mi™e tsaye gaba Waya, sannan ya ce mata "Zan je na dawo, ki yi mana addu'a Allah ya sanya hukuncin da Sultan zai yanke, ya yi mana daWi"

Ya ™arasa maganar yana sumbatar goshinta.



Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faWo turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haWiyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi.

A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa.

Sai kuma ta tsaya ta kasa magana.

Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?"



"Idan da shi me za ki yi?"



"Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana Wan cikinka? A wancan karon ka naWa ™aninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez"



Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da Wan uwanki Tafawa" Ya ™arasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana ™walalo ido waje tana kallonsa.

"Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yin™urin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarSiya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a ™arshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon Wan da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba Waya Hammad bai ji daWin rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buWe baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata.

Abu Waya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya ™ara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. FaWar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne"



A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji...



"Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haWa hanya.

Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah.

A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?"

Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai.

Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba Waya suka Waga kai suka kalle shi.



"Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce Win dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki Wayanku, dan ban san wane irin hukunci za a Wauka

114 / 126