Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   122 / 126

363K to 366K   out of 377.2K words

ta bakin Alhaji Fatuhu,  ya ce "Zailani wannan shi ne ™arshen duk wanda ya gaza sarrafa ni. Ka kasa kula da ni a lokacin da na kamu da rashin lafiya. Ciwon ™yashi ya kama ni, son duniya, hassada, mugunta, ™eta na bushe na yi ba™i, har ka gaza sarrafa ni kullum burinka biya mini bu™atar duk da na bijiro maka, wanda ina bijiro maka bu™atuna ne, saboda samun sassaucin wannan ciwukan da suka kama ni, ka ™i kulawa ka bani magani. Ga shi biyan bu™atuna ya sanya ka aikata abu mafi muni, ga ™arshe mara kyau"

Alhaji Fatuhu ya sake caka wa Alhaji Fatuhu da yake gani a gabansa. Wata irin zabura ya yi tare da kurma wani uban ihu, jin wani irin gigitacciyar azaba da raWaWi ya ratsa cikinsa.

Abin da bai sani ba, da ya Wauki wu™ar nan kansa y fara cakawa, ya fita waje yana tangaWi, yana faWin "Na kashe ku Win, na fi son duniya a kanku. A lahira rahamar Allah za ta saka na shiga aljanna a Duniya kuma ™o™arina ne zai tara mini abin duniya" Ya din ga surutu yana faWar miyagun ayyukan da ya din ga aikatawa. Kafin a yi ™o™arin ™wace wu™ar ya sake caka wa kansa a cikinsa, ya sulale ya faWi ™asa, jini yana zuba a jikinsa. Yana faWuwa bakinsa a buWe, Aljanin da ya mallaka ya bar gangar jikinsa.



(Ya hayyu ya ™ayyum ya zuljalalu wal ikram Ubangiji Allah ka sanya mu yi kyakykywan ™arshe, Allah ka raba mu da mummunan ™arshe, Allah kar ka sanya mu cuci kowa=ĜOŜ=ĜOŜ=ĜOŜ=Ĝ-Ŝ)



Abin ka da zamani na amfani da social media, a lokacin da Alhaji Zailani yake wannan tamSelen, aka samu masu ciro waya suka Wauki abin da ya din ga yi, suka sanya a shafukan sada zumunta, duk wasu shafukan an sauke videos Win, saboda abin da yake ciki na tashin hankali.

Tuni aka nemo jami'an tsaro, suka Wauki gawar Alhaji Zailani. Sagir ne ya fara gani a social media ya tashi hankalinsa a dugunzume, ya tafi gidan Alhaji Fatuhu ya yi sallama da shi.

Ya kalli Sagir ya ce "Lafiya kuwa? Ko Shukuran ce babu lafiya, na ganka kamar ba a nutse ba?"

Ya ciro wayarsa ya nuna wa Alhaji Fatuhu abin da yake faruwa. Sai da ya jingina da bango sannan ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ya daWe cikin mawuyacin hali, kafin ya daidaita nutsuwarsa ya dubi Sagir ya ce "Shukura ta gani?"

Sagir ya ce "A'a, ai babu waya a hannunta ma"

"To ka yi duk yadda za ka yi, kar waya ta shiga hannunta. Tun da Allah ya riga ya yi masa rasuwa, komai ya ™are. Yanzu muje gurin 'yansanda mu ro™e su a ta™aita lamarin binciken nan, a yi masa sutura a binne shi" Sagir ya sara wa zuciya irin ta Alhaji Fatuhu, a irin abin da Alhaji Zailani ya yi masa, yake cewa su je su karSi gawarsa a binne shi.

Sun sha fama da 'yan sanda, dan hana gawarsa suka yi, sai da aka je gidansa, domin zurfafa bincike. Sai dai da bincike yayi bincike aka din ga gano, abubuwa na tsaface-tsaface da suke Soye a cikin gidan. Sannan aka buWe wayarsa, yanayin tattaunawar sa da wasu daga cikin abokansa, ciki har da Malam Gambo, ya sanya jami'an tsaro kama su.



*****



Sayyid a gurin Asal yake, amma yaje yana damunta. Sai da ya fara shirin tafiya, ta ce masa ya jira tana da ba™i su gaisa.

"Suwaye ba™in kai a Agadez? Umma ce? (Da yake haka yake kiran Nene, kamar yadda Mahmoudu yake kiran ta)"

"Ba ita ba ce"

"To suwaye?"



"Ba™i masu muhimmancin gaske ne, za ka gani"



Ya ce "To bari na je masallaci, kafin su zo" Ya yi alwala ya fita falo, ya ga Nene tare da wata mata da namiji da alamu suka nuna mata da miji ne. Su na ganinsa suka ™ara nutsuwa, domin sukan ji zancensa a bakin Nene. Cikin girmamawa suka risuna su na gaishe shi. Ya amsa yana mamakin dalilin shigo masa da ™ato haka har cikin falo. Ya dake ya ce "Umma dama ke ce ba™uwar, ta dage kar na fita sai kin zo?"



Ta yi murmushi ta ce "Ba ma nice ba™uwar ba, ga ba™in nata nan" Ta yi maganar tana nuna masa mata da mijin. Ya yi shiru yana kallonsu, ba su yi kama da 'yan Nigeria ba, sun fi kama da hausawan Niger, mussaman daga yanayin hausar su.

Nana ce ta buWe ™ofa ta fito, da gudu ta nufi Hajara ta rungume ta, Muhsin ya biyo bayanta ya ja ya tsaya a kusa da mahaifinsa.



"Hajara, dama zan sake ganinki?"



"Gani kuwa shugabata" Hajara ta yi maganar cikin girmamawa.



Nana har ™asa ta dur™usa ta gaida Auwwal, takaici ya kama Hammad, haryanzu Nana ta kasa gane mene ne matsayinta. Banda haka ya za a yi ta dur™usa har ™asa tana gaida mutumin da shi kansa ya girme shi, da ma dattijo ne da sau™i.



Nene ta ce "Nana ba girmanki ba ne, ai shi yakamata ya gaishe ki"



Shi ma a tsorace ya ce "Wallahi kuwa"



"Kash, Nene ba ni da wani girma, ni na kasa jin girman nan. Meyasa ba zan girmama mutane mafiya karamci a gare ni ba?" Ta taso tana kallon Sayyid fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Wannan gidan su ne je, lokacin da na baro Agadez na nemi Nene na rasa, a can gidansu aka Waukko ni. Sayyid lokacin da na zo Niger na sauka a MaraWi, ba ni da kowa sai Allah, Allah ya dubi zuciyata ya ji ™aina ya haWa ni da mutane masu karamci. Wannan su ne sanadin haWuwa ta da Nene." Nan ta kwashe komai ta gaya masa. Sannan ta Wora da cewa "Ina tambayar Nene su, ta ce mini sun tafi ci rani can ™asar Mali. Sai yau Neme ta kira ni ta ce mini sun zo Niger, su na Agadez za ta kawo su mu gaisa. Ni na so mu je har inda suke amma ta hana" Kukan da Nana take yi kawai ya tabattar masa da ba ™aramin karamci suka yi mata ba.

Ya taka ya ™arasa gaban Auwall da kansa yake ™asa, ya mi™a masa hannu su yi musabaha. Da kyar ya iya mi™o masa hannu.

Suka gaisa Hammad ya dafa kafaWarsa ya ce "Na gode sosai da sosai. Mutane a zamanin nan abin tsoro ne, amma ka zama mutum na farko gurin bawa matar da baka sani ba taimako.

Na gode sosai da sosai, dama Umma uwata ce, kai ne dai ban sani ba, tabbas tana bani labarinku. In sha Allah ba zaka sake zuwa Mali ci rani ba, da yardar Allah  na gode sosai da sosai Allah ya biya ka"

Ya kalli matarsa ita ma ya yi mata godiya sosai.



Tare suka je Salla da Auwwal, Hajara ta yi nufin Waukar Muhsin, amma ya ™i saboda ™yuya.

Hadimai suka gabatar da Abinci, da abubuwan sha daban daban. Sayyid a dole yake Waga ™afa a wasu abubuwan duk da azabar kishin Nana da yake yi. Ya yi iya ™o™arinsa a kan kar ya yi wani abu da ran su Auwwal zai sosu ko na Nene, ko dan albarkacin Wawainiyar da suka yi da Nana.

Har da kyautar kayan wasan Yara, suka kawowa Yarima Muhsin. A hirar ta su suke gaya wa Nana haryanzu Allah bai ba su haihuwa ba. Ta yi ta musu nasiha da basu misalai masu kwantar da hankali.

Sai isha'i suka tashi tafiya, Hammad ya yi musu alkhairi, tare da jaddada musu godiya, ya kuma gaya wa Auwwal lokacin da zai zo MaraWi, ya ba shi katinsa ya ce idan yaje ya nuna katin za a bari ya gan shi, zai ba shi abin yi.

Bangaren Nana ma, kyaututtuka ta ba wa Hajara sosai, da ta ce ba zata karSa ba, abin da suka yi wa Nana, dan Allah suka yi mata, Nene ta ce mata ba a mayar wa da masu mulki kyauta.

Sai da Nana ta karSi lambar wayar Hajara, ta din ga yi musu godiya kamar ta tsuguna musu. Hammad ya Wauki Muhsin ya ce da kansa zai mayar da su har gidan da Nene take, kasancewar a gurinta suka sauka a Agadez. Daga can ya so wucewa gurin Asal da Muhsin dan yana kyautata zaton bata taSa ganinsa ba, amma Nana ba ta sani ba, tsaf za su iya yin faWa a kan hakan. Kuma da gaskiyar Nana kome nene Asal ce ta janyo, kuma duk abin da Nana za ta yi domin ta ba wa Wanta kariya. Bugu da ™ari kuma ba ya son duk wani abu da zai kawo musu matsala, saboda wata irin kwanciyar hankali ya tsinci kansa a ciki. Ga taraiya da soyayya da yake samu daga gurinta. Duk da haryanzu Giyaz yana taSa shi. Amma idan yana tare da ita, da ya gaya mata alamomin da yake ji, take yi masa addu'a ko ma muraran ta ga Giyaz Win tare da shi.

Ya tattara hankalinsa a kan Nana da ta nufo shi, ta sanya doguwar riga ta cika ta, rigar ta zauna a jikinta.

Ta ce "Wannan kallon sai ka saka na faWi tukuna?" Yayi murmushi ya ce "Sai na ri™o ki kafin ki faWin.

Ta yi murmushi ta zauna a kusa da shi, ta kai kofin hannunta bakinsa ya buWe baki yana sha. Ta ce "Amma ka yi sauri fa"



"Eh, ina kai su na juyo ne, in sha Allah idan muka haWu a MaraWi, zan sama masa aikin yi"

"Gaskiya ka kyauta, Allah ya saka maka da alkhairi" Ta ci gaba da ba shi labarin irin taimakon da suka yi mata.

Ya ™are mata kallo sannan ya ce "Lokacin mu na Nigeria, ba wuya kin samu rabo, Allah ya sa Niger ma haka ne, Allah ya sanya ™ani ko ™anwar Muhsin sun samu a cikin nan"

Nana ta tura baki ta ce "Sai Yarima ya shekara biyar"

"Wace shekara biyar kuma? Kowa so yake sai ya karSe shi, Zahradeen nata masifa, ga Sultan ya ce gobe na kai masa shi, amma idan Allah ya sa ki ka haihu, ko an ™wace shi mu na da wani ko?" Kawai ta yi shiru tana murmushi, dan ji take gara ta haifi wasu a ™wace da a ™wace mata Muhsin.

Su na hira ta Wauki wayarta, za ta nuna masa abu, sai dai tana buWe data videon Alhaji Zailani ta fara cin karo da shi a dandalin sada zumunta.

Mi™ewa ta yi tsaye jikinta na wata irin tsuma, kamar za ta zare. Ya karSi wayar hannunta ya kalli videon. Ya ajiye wayar ya ce "Shiyasa wasu lokutan shafukan sada zumuntar nan duk ba su da wani amfani"

"Sayyid ba ka gane waye ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ni ban san shi ba"



"Ba ka tuna Alhaji Zailani ba?" Ya yi shiru ya tafi tunanin, kamar ya san sunan, can kuma ya ce "Na tuna, mutumin da muka fara gadi a gidansa da su Mahmoudu. To Allah ya kyauta ke mene ne naki na shiga tashin hankali haka?"



"Dan Allah Sayyid ina son zuwa Nigeria" Ta yi maganar cikin tsoro da tashin hankali.



"Sati uku da gama hidimar nan ki ce za ki Nigeria, a ™alla nan da wata biyu nake son mu je tare"

Sai ta rikice masa gaba Waya a kan ita fa dole Nigeria take son zuwa. Abu kamar wasa ya Wauka da wasa take yi, sai da ya ga ta yanke jiki ta faWi, jikinta ya yi sanyi ™alau. A hankali ya Waga kai ya kalli tsuntsun da yake shawagi a saman Wakin, da hakan ya tabattar masa da ˜aisar ne ya zo mata.

A ransa ya ™udurce lallai a shirya tafiya Egypt Win nan, kafin su zo su ci gaba da samun matsala, su sake hana su zaman aure cikin kwanciyar hankali.

Sai dai idan ya ce a yi mata passport a Niger, zai Wan Wauki lokaci, dan haka ya yanke shawarar za su je Nigeria a yi mata, sai su tafi. Har wajen ™arfe goma na dare yana tare da Nana, sai dai ba ta dawo hayyacinta ba. Ya kira Asal ya gaya mata Nana babu lafiya, dan haka ta yi ha™uri ba zai samu damar dawowa a ranar ba.

Asal kamar ta haWiyi zuciya ta mutu, gani take kawai faWa yayi, dan ya zauna ya kwana a gurin Nana, amma babu yadda ta iya. Shi kansa sai da ya raya za ta yi tunanin hakan, amma babu yadda za a yi ya tafi ya bar Nana a wannan yanayin.



Duk yadda su Sagir suke yi wa Shukura Soye-Soye, sai da ta san Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa.



Hajiya Suwaiba ce ta fara ganin Videon nan, sai ba ta yi wa Alhaji Fatuhu magana ba, ta je gurin Fadila. Fadila ta Wan yi mamakin ganin Hajiya Suwaiba a falon ta.

Bayan sun gaisa ta ce "Fadila, ko Daddy ya gaya miki abin da yake damun sa?"



Fadila ta ce "Wallahi bai gaya mini ba, na yi na yi ya ™i ya gaya mini"



"Kin ga wani video"



Fadila ta karSi videon tana kallo, jikinta ne ya hau karkarwa ta ce "Wannan ai Alhaji Zailani ne? Wai yana nufin Alhajinmu ya yi wa abin da yake faWar nan?"



"Nima abin da ya Waure mini kai kenan"



Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama, ya ga duk sun zubo masa ido, kamar marasa gaskiya.



"Lafiya kuwa?"



Hajiya Suwaiba ce ta yi kokarin cewa "Daddy wani abu muka gani, shi ne dama abin da ka ke Soye mana?"



"Me na Soye mukun?"



Ta mi™a masa wayarta, yana kalla ya ajiya, ya zauna cikin damuwa, ya ce "Koma mene ne ya faru, ya riga ya faru, dan Allah a bar maganar nan ta wuce"



Hajiya Suwaiba ta ce "Amma ya batun maganganun da ya din ga faWa, yana cewa shi ya yi maka sihiri?"



"Suwaiba a bar maganar nan dan Allah"



"Amma ya zaka ce a bar ta, mutumin da ya tsugunar da mu, ya saka mu a wahala, to wallahi ni dai ban yafe ba."



Fadila ta sha mamakin abubuwan da ta ji a videon nan, kuma ta tsorata imani ya ™ara shigarta, sai dai tun da ta ji Alhaji Fatuhu bai musa ba, to tabbas an yi hakan.



*****

Nana Bakinta ya ™i rufuwa, wani irin farinciki take ci, ganin sun kama hanyar Nigeria.

Ta din ga tuna lokacin da ta yi balaguro, daga Nigeria zuwa Niger tsawon shekaru, ta tafi zuciya a cunkushe cike da rashin sanin makoma, sai dai kyakykywan ya™ini da dogaro ga Allah. Sai ga shi a wannan karon ta nufi zuwa gidan, cike da farinciki da kwanciyar hankali. Ta so tahowa da Muhsin, amma Hammad fafur ya hana, wai sai zo Waukarta zai taho da shi.

Sai da suka samu saSani kafin ta taho, dan cewa ta yi muddin Asal zai kai wa Wanta gara ta ha™ura da tafiyar. ˜arshe sai da suka kai shi gidan Zahradeen, sannan ta hakura ta taho.

A garin Bauchi ta fara yada zango, duk da nan ma abin da ya faru ba zai taSa gogewa daga cikin ™wa™walwarta ba. Mama tana ta kiranta a waya ta ji ko ta kusa ™arasowa.

Ko da Nana suka isa, Iliyasu ta fara gani a ™ofar gida, ya tsaya yana washe baki, ganin Nana ta fito daga dan™areriyar mota da aka kawo ta a ciki.

"Maraba, sannunku da zuwa, sannu da zuwa"

Ita Nana ma abun da yake yi matan, kunya ya din ga bata. Ta tarar da su Adda Maryam da Fati da wasu daga dangin Umman, duk sun cika gidan. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana. Suka din ga yi mata barka da zuwa.

Nana ta sha karramawa, mijin umman sai nan nan yake yi da ita, yana washe mata baki har da yi mata raha.

Baba ya din ga kiran Nana yana tambayarta sai yaushe zata ™araso. Ta ce masa ai ta sauka a Bauchi, sai ta kwana biyu za ta zo. Gaba Waya bai ji daWin hakan ba, saboda yadda yake Alla-Alla ta zo ya sake ganinta.

Sai da Nana ta kwana uku a Bauchi, Mama tana a kaita tasha a saka ta a mota, ta ce ai direbanta yana nan a Bauchin bai tafi ba.

Suka sake Waukar hanyar Kano, jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fika. Nana ta yi kewar garinta na haihuwa ba kaWan ba.



Da sallama Nana ta shiga gidansu, Iya suturar jikinta, da yadda ta yi kyau mai Waukar ido ya sanya Mama yin saroro da kasa amsa mata sallamar. Nasiru ne ya fito da gudu yana faWin Oyoyo ga masarautar Agadez da kanta. Masu arzikin zinare, masu kyauta da dama hagu ma ba ta san ana yi ba. Barka da zuwa Garkuwar matan Agadez ke ta Afrika ma gaba Waya." Kawai Nana ta tsaya tana murmushi, Jamila ta fito daga Wakin, ta zo ta rungume Nana, sai Nana ta manta da batun wata Mama, ta hau murnar ganin 'yan uwanta. Nasiru ya je ya Waukko mata Akwatinta a mota.

Nana ta dake ta ce "Mama ina wuni?"



A dole bisa ya™e Maman ta ce "Lafiya ™alau Nana, ai kasa gane ki na yi, irin wannan gwala-gwalai haka. Ai na zata ba zaki sake saka su ba, dan kar ki yi almubazzaranci tun da da muka je fama aka yi ta yi da ke, ki ka ce ba kya so"



Nana ta yi murmushi, tana tuna karatun da ˜aisar ya yi mata, amma ta ce "To Mama yana iya, masu abu da abinsu, an ce mini haka suke adonsu, idan ka je gari ka ga 'yan gari da jela, aka ce kai ma ka nema ka ma™ala. Gaba Waya Mama ba ta san ba™in cikinta ya fito muraran ba.

Baba ma da ya dawo ya ga Nana, bakin nan a buWe ya din ga murna yana yi mata maraba. Babu laifi sun yi nata karSa mai kyau. Ta yi musu tsaraba mai yawa sosai kamar yadda ta yi wa mutanen Bauchi.

Da daddare suna Waki suna ta hir da Jamila, take gaya wa Jamila abun da ta gani a waya, Jamila ta ™ara bata cikakken labarin abin da ya faru, da yadda Hajiya Sa'a take bayar da 'ya'yan Alhaji Fatuhu har ma da rashin lafiyar da Alhaji Fatuhun ya yi sai da ta bata labari. Jikin Nana ya din ga tsuma ta shiga tashin hankali, ta ™udurce a ranta lallai a washegari za ta je gidan Alhaji Fatuhu, za ta je.

Suwaiba ma ta dage ta din ga yi wa Nana hira, duk da galibin

122 / 126