Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 126

153K to 156K   out of 377.2K words

hannunta, ya haska fitila har banWaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta mi™e jikinta yana rawa.



Ya rungume ta ya ce "Ki yi ha™uri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi Sari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?"



"A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube"



Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaSa ta da ™yar, ta gyara jikinta, ta Wauraye jikinta, da banWakin su ka koma Waki.



Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro.



Suka kwanta yana Wan shafa ta, cikin sigar rarrashi.



A hankali ta ce "Sayyid"



"Na'am"



"Da gaske mun fita Wazu ko?"



"Eh mun fita"



"Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?"



"Eh haka aka yi, mun je"



Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?"



"FaWuwa ki ka yi, na ri™e ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci"



Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ™ara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa.

Wannan bafulatanar matar ce, ta ™ara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ™ara rintse idanunta tare da ™an™ame Sayyid.



Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ™yar ta samu ya yi alwala ya yi salla.



Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta Wauke.

Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko Waga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaWa a gona.



Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska.



Ta Wora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin Wakin. A zaton ta, ko banWaki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje.



Da sauri ta bi shi tana faWin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ™o™arin buWe ™ofar. Ta ri™o hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a Waura kamar bai taSa dariya ba, saka hannu ya hankaWe ta, ta faWi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga Waki, ta Waukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi li™is, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take.



"Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri.



Sai da ta Wan haWa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ™ulle. Ta daure ta cim masa.



Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiWanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taSa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba Waya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faWo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta ri™e hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai.



"Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar ra™umi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ™ofar.



Su ka shiga Waki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ™asa fuskarsa babu annuri a ciki.



Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banWaki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi.



"Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar Wakin, yana wani irin huci.



"Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ™asa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri Waya. Ya mi™e ya fara fatali da kayan Wakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuSe tana kallon sa.

Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yin™urin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da Wakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ™asa.

Inda ta yi wa Allah godiya ba su da ma™wabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta dur™usa ta hau aikin gyaran Wakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta dur™usa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a Waki, nan akwai sauro kuma ™wari za su cije ka"



Da ™yar ya tashi, suka koma Waki, ya nemi guri ya kwanta a ™asa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ™aba amma kai na daWa kumbura.

A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ™o™arin Waukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buWe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin han™oro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaWa ta, sai da ta wuntsula Wakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaWa ta. Ya tashi ya koma bakin ™ofa ya yi zamansa.

Da kyar ta sake lallaSa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ™i yi. Ya nemi guri ya zauna ™yam yana kallon ta.



Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo Waki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana mi™a masa kofin kunun. Sai ya mi™o hannun hagu zai karSa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai mi™o mata ba, ya zura mata ido.



Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta dam™a masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ™ame ™am. Ta sake ™o™arin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace.



Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi.



Gabanta ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ™o™arin ganin ta mi™ar da hannun nasa, amma hannun yana ma™ale, kamar an tsotse shi.



Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa Wauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta Webo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buWe bakinsa ba.



"BuWe baninka na baka" Ta yi maganar tana ™o™arin danne hawayen da ke ™o™arin ™wace mata.



A hankali ya buWe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ™o™arin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta.

Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa.

Ta fara ™o™arin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haWiye wani kuma ya zubo.

Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a ma™ale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido.

Ganin yana gyangyaWi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita.



Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida"



Ya kalle ta ya ce "A ina ne?"



"Cikin Budu ne, nan unguwar maharba"



"TaS gaskiya da nisa gurin nan ba kaWan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa"



"Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na ro™e ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah"



Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu"



Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist Win ya bi Nana.



Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa.

Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?.

Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaSa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ™ara bincikawa"

Nana ta ba shi kuWin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma Waki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran SurSushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba.



****



Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro.



Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaWa ™afa ya ™ura wa screen Win wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko Wan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu.

Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai Wan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba.



"Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai".



"So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta.



"Ina ga zan shigo Abuja mu haWu very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?"



"Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faWa fa, ba zan ji daWi hakan ba"



Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faWa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo"



Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing Wina ne?"



Ta gyaWa masa kai tana murmushi.



"Shikenan, i miss you too, ban taSa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido.



Shukura ce ta turo ™ofar Wakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. ˜arara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluSe jikinta.

Ya matsa kusa da ita yana Wan shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?"



"Lafiya ™alau" ta amsa a ta™aice. Šan shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faWa.



Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar Wanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa  daWi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif.



****

Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a ma™ale.

Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya sha™e ta, ko ya hankaWe ta ™asa, sai dai ta yi ™o™arin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a Waki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar Wakin yake duka da kansa. Ya ™i cin abinci ya ™i shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban ha™uri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido.

Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaSi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki.

Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na Soye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci.

Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya.

Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ™ware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta.

Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoSo ta ™u™™ula ya tafi da shi.

Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro.



Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi.

Tana zaune tana tunani, tana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa.

Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ™o™arin tara musu kuWin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar Win ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid Win ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa.

Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya ri™e hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluSe su da bargo.

Sheshshe™ar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daWe yana dauriya, da son Soye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa.



"Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya Wauke shi.

Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta.

Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi Wakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaWan ne.

Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ™arfi.



Jin yadda guguwar ta taso da ™arfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ™o™arin rufe ™ofar katakon da take Wakin. Sai dai tana danna ™ofar guguwar ma na danno ™ofar.



A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ™ofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake.



Da fari yana zaune a guri Waya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan Wakin da hannu Waya, da sauri ta fara  bi tana tattarewa, cike da damuwa.

Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ™arasa maganar a raunane, duk yadda take ™o™arin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ™i cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza.

Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raWaWin da yake ji, ka saita masa

52 / 126