Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   80 / 126

237K to 240K   out of 377.2K words

ba ta kuma cewa komai ba, sai dai abin ita ma sai ta ji hankalinta ya tashi, ganin har ya fita masallaci sallar magariba Shukura ba ta dawo ba.

Yana dawowa ya dubi Yusar ya ce "Ba ta dawo ba ko?"



"Eh ba ta dawo ba, ko ta biya wani gurin ne?"



Jiki a sanyaye ya ce "Ba na tunanin hakan, ko za ta biya wani gurin, duk faWan da muka yi tana gaya mini, ba ma ta da yawan yawo, ba ta fiye son fita ba, idan ba gidansu za ta je ba. Bari na je gidansu, na kuma je Asibitin na ji"



"To Allah ya sa tana lafiya, to ko haihuwa ta yi a Asibitin suka ri™e ta, na ga cikin nata ma sha Allah ya tsufa sosai"



Ya girgiza kai ya ce "Da haihuwa za ta yi, da tuni an kira ni an sanar mini, bari na je na gani"



Yusra ta ce "To Allah ya sa tana nan lafiya dai"



Ya amsa da Amin, ya fita.



Gaba Waya sai Yusra ta ji hankalinta ya tashi.



Gidansu ya fara zuwa, ya shiga suka gaisa da Hajiya Amina, sai dai bai ga alamar Shukura ta je gidan ba, ya wayance da nufin zai tafi da Haidar, amma Haidar Win ya ™i bin sa.

Hankali a tashe ya tafi Asibitin doctor Sabo, aka ce masa tun safe ta je awo, sha Waya da rabi kuma ta bar Asibitin, kamar yadda har a cc camera ya nuna.



Nan hankalin Sagir ya dunguzuma, ya ™ara ruWewa ya burkice, duk inda yake tunanin Shukura za ta je, ya je bai same ta ba. Wayoyinta da su na shiga, amma suka daina.

Ya tafi gurin 'yan sanda ya kai report Win Satan Shukura, bai koma gida ba sai sha biyun dare.



Yusra na ganinsa ta tashi tana tambayarsa "Yaya an ganta?"



Jiki a sanyaye ya girgiza mata, take gabanta ya faWi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba saboda ka dawo da ni ne ta tafi ba, Ubangiji Allah ya sa ta dawo, ni zan iya tafiya ma na bar muku gidan, idan zamana ne ba ta so ta bar gidan"



"Shukura ba za ta bar gidan nan saboda na dawo da ke ba. Dan kan ta fita mun yi magana ta fahimta da ita, mun daWe mu na magana, ba saboda ke ne ta bar gidan nan ba"



Gaba Waya Sagir ya kasa rintsawa, sai damuwa da tashin hankali, haka ita ma Yusra, ™arshe ma kuka ta saka tana cewa saboda ita ne Shukura ta fita ba ta dawo ba.



*****



Yau da Nana ta bushi iska, harabar gidan ta fita tana zagayawa, sai dai zuciyarta a cunkushe take, gaba Waya tunaninta yana kan Muhsin, kewar Wanta take yi sosai da sosai, ga wannan azzalumar matar ta hana ta tafiya, sai dai ita kanta hankalinta ya rabu kashi-kashi ne, ga tunanin Muhsin ga kuma Sayyid da take ganin samu a lokaci guda take ganin rashi.



Sai a yau ta ™ara tabattar da girma da ™asaitar gidan, ba ta taSa ganin ra™umi da ake faWa ba, sai yau a cikin gidan.

Ban da dawakai, da wasu dabbobin ma da ba ta san sunansu ba, ba kuma ta taSa ganinsu ba.

Asal ta hango hannunta a cikin na Sayyid, an fito da wata dan™areriyar mota, sun shiga an ja sun fice. Nana ta tsaya ta yi shiru cikin damuwa.



Cikin matu™ar farin ciki dattijuwar matar fara ™al, ta mi™e ta rungume Imam Hammad.

Cikin girmamawa ya dur™usa zai gaishe ta, amma ta hana shi ta ce "Ai ni yakamata na kwashi gaisuwa shugabana. Ina ta yi wa Sultan ciwon bakin ban gan ka ba, ya ce a bari ka huta kar wanda ya je gida aka dame ka, har sai ka fito dan kan ka"



Ya yi murmushi ya ce "Na same ku lafiya?"



Ta ce "Alhamdillah, sannu Imam Hammad, an sha jinya Ubangiji Allah ya sanya kaffara"



Asal ta ce "Wai ni ba za ki yi mini sanun ba, kin maze kamar ba ki ganni ba"



Matar ta ce "Wa yake ta taki, ga mara lafiya"



Gimbiya Bilkisu ta yi musu kyakykywar tarba, aka karrama su da Abinci kala-kala, amma ya ™i ci. Hirar ma idan ta yi sai dai ya yi murmushi kawai, bai fiye tofawa ba.



Bayan sun gama da sashen Gimbiya, suka nufi sashen Sultan.



Imam Hammad na shiga falon Sultan, Sultan ya mi™e cikin farin ciki fuskarsa Wauke da murmushi.



Abdou ma murmushin ya saki, cikin girmamawa suka gaisa.



Imam Nuradden, da Imam Asad duk su na tare da Sultan.

Cikin girmamawa suka gaida Hammad, fuskarsa Wauke da murmushi ya amsa musu.



Sun taSa hira kafin Sultan ya ce "Imam Hammad, zo muje ka raka ni tattaki mana, na mi™e ™afafuwana"



Imam Asad ya ce "Sultan, mu ma mu yi maka rakiyar ne?"



"A'a ku da kullum muna tare ga ba™ona da muka yi shekaru ba ma tare"



Yayi maganar yana ri™e hannun Hammad, suka fita ta wata ™ofa. Imam ya din ga kallon gidan tamkar ba™onsa, kamar ba a ciki yake rayuwa ba a baya.



"Hammad"



"Na'am Abi"



"Kamar wani abu yana damunka, ka gaya mini mene ne"



Imam ya yi murmushi ya ce "Babu abin da yake damuna, idan ma akwai ban san mene ne ba"



Sultan ya ™ara tattara hankalinsa a kan Hammad ya ce "Ka tabattar? ba ka fa da wanda zaka gaya wa dauwarka idan ba ni ba, ka daina wannan zurfin cikin Imam ba na so ka gaya mini"

"Babu abin da yake damun Hammad Winka fa"



Sultan ya yi murmushi yana dafa kafaWar Hammad.

"Ka san haryanzu miskilin Wan yaron nan, mai guje-guje a harabar nan nake gani, ya yi guje-gujensa ya faWi ya ji ciwo, ya zo ya yi ta yi wa Abinsa kuka, ya ce sai na ce ciwon ya daina yi masa zafi, kuma na daki rama masa na daki ™asar na rama masa"

Hammad ya yi dariya sai da ha™oransa suka bayyana ya ce "Duk da wannan gemun na fuskata haryanzu wannan Wan yaron naka ka ke gani?"



"Eh mana, gani nake kamar jiya Sarah ta haifa mini kai. Allah ya jaddada rahama ga Umminka"



Ya amsa da Amin cikin sanyin jiki.



Sultan ya sake numfasawa ya ce "Hammad, haryanzu babu wani abu da ka iya tunawa bayan fara rashin lafiyarka?"



"Ban tuna komai ba"



Ya Wago hannun Hammad ya ce "Bamu san fa inda zobenka yake ba haryanzu, abin ya dame ni, ina tsoron a farga da babu zoben nan, ina tsoron abin da ka iya biyo baya, idan aka gano babu zoben nan"



Ya kalli yatsun nasa ya ce "Abiena, duk abin da Allah ya ™addara zai faru dole zai faru ka daina damuwa. Ni yanzu ina mamakin Mamudu bai san ina Agadez ba ne?"



Sultan ya Wan ji dumm, sai kuma ya ce "Ni na hana a sanar da dawowarka, sonake ka samu lafiya sosai, amma dole za a sanar masa da dawowarka"



Imam ya ce "Ni zan je na same shi, ya ganni a bazata"



Sultan ya ce "A'a zan saka a sanar masa, zai zo har gida ya same ka"



Ya ji daWin kasancewa da mahaifinsa, sai dare sannan suka tafi gida tare da Asal. Duk wunin da suka yi bai ci komai ba, har suka koma gida.



Nana ta kammala aikinta na yau, ta yi wanka tana zaune a Wakinta, tana karatun Alkur'ani. Kawai ta din ga jin kamar akwai wani abu da ba daidai ba.

Ta ajiye Alqur'anin ta tashi ta tafi Wakin girkin Abincin Imam.

Wata mata ta gani ta kawo kai za ta fita daga kitchen Win, alahalin babu wanda yake shiga sai ita sai Balaraba ko Asal.



Nana ta ce "Baiwar Allah lafiya kuwa?"



"Sa™o ne aka bayar, ke ce mai girkin Imam, dan haka ke za ki kai masa"



Cikin rashin fahimta Nana ta ce "Wace ce ke? Kuma waye waye ya bayar da sa™on, kuma sa™on mene ne?"



"Ba ni da lokacin amsa tambayoyinki, babu ruwanki da kuma sa™on na mene ne, ga shi can na ajiye miki a cikin kitchen Win, kaiwa ne kawai naki"



Nana da mamaki ta bi matar ta kallo dan ba ta taSa ganinta a gidan ba.

Ta shiga kitchen Win da sauri, ta fara kalle-kalle tana tsoron kar ta je wani abin cutarwa ne.



Wani Wan kwando ta gani ™arami, an nannaWe shi ba za ta iya ganin mene ne a ciki ba.

Wata zuciyar ta raya mata, ta kwance ta ga mene ne a ciki, wata kuma ta hana ta,sai dai har ta gama grkin dare tana kallon kwandon tana tunanin mene ne a ciki? Waye zai bayar da sa™o babu suna, kuma me yasa sai ita za ta kai? yanayin sa™on dai kamar babu gaskiya a lamarin.



Da fargaba ta haWa da Wan kwandon ta nufi sashinsa gabanta yana faWuwa.



Yau shikaWai ne a zaune, babu Asal. Duk da ruWewar da yake yi idan ya ganta, amma ya ji daWin ganin ta kawo masa Abinci, dan tun safe bai sake cin komai ba.



Sai dai yau ba iya faWuwar gaban yake ji ba, har da wata ™ara, mara daWin ji makamanciyar wadda ya din ga ji daren da zai fara ciwo.



Ta ajiye kwanukan ta ce "Barka da yammaci Sayyid, fatan ka na lafiya."



"Alhamdillah" ya furta ba tare da ya shirya hakan ba, yana mamakin daga ina wannan sautin yake. Ita kanta Nana ba ta zata zai amsa mata gaisuwar da ta yi masa ba.

Ganin babu Asal a gurin, ya sanya Nana zuba masa Abinci da shayi. Ta kalle shi duk da yadda yake yi mata wani irin kwarjini da a baya bata taSa zaton yana da shi ba ta ce "Ko yanzu ma sai na WanWana?"



Ya girgiza kai alamar a'a. Ya sauka daga kan kujerar, yana jin ™arar nan na ci gaba da addabar kunnuwansa.

Cike da son basar da abin da yake ji, dan gujewaa sake faruwar abin da ya faru a wancan karon, ya yi Bismillah ya fara cin abincin.



Duk da a takure yake da yadda take kallonsa, kuma ba zai taSa iya cin abinci a gaban wanda bai kamata ya ci ba, amma ya kasa yi mata magana, kuma bai ji hakan da ya yi a matsayin wani laifi ba a matsayin sa na Wan gidan mulki ba, wanda hakan yana cikin kamewa da suke da ita, musamman ma shi da hakan ya haWu da Wabi'unsa.



"Sayyid, ina jin yadda mutanen gidan nan suke yabon ka, sosai da sosai da yabon karamcinka. Duk da a baya ban so zuwa gidan nan aiki ba, amma sai dai na ji babu daWi da yadda ni ban samu wannan karamcin daga gare ka ba, sai ma ™yama da ka ke nuna mini, da ™abilanci ban sani ba ko dan ni ba ™abilarku ba ce, kuma ba 'yar ™asarku ba ce ba, shi ya sanya ka ke yi mini haka. Amma ina neman afuwa idan na faWi wani abu ba daidai ba ko ya Sata maka rai, bana nufin hakan shugabana"

Gaba Waya babu tsoro ko fargabar Asal ta fito ta tarar da ita a ranta, daWi ma ta ji na ko ba komai yau ta keSe tare da shi.



A wannan karon ma, jin maganganun nata ya din ga yi da matu™ar muhimmanci. Yaya zai yi mata bayanin ba tsanarta ya yi ba, baya iya tantance abin da ruhinsa da gangar jikinsa ke nufi a kanta ne. Shirun da ta ga ya yi, da yadda yake jujjuya cokalin ya sanya ta yin ajiyar zuciya, ganin alamun sa™onninta na isa kai tsaye inda take so.

Ta nuna masa kwandon da aka bayar aka ce a ba shi, ta tashi ta fita.



Kitchen ta koma tana ™arasa goge-goge, kawai. Sai dai ta ji alamun mutum a bayanta. Ta waiwaya ta gan shi a tsaye a ™ofar kitchen Win, idanunsa jawur, ga Giyaz a gefensa, cikin suffarsa ta tsohon nan mara kyan gani.



Ya fara takowa cikin kitchen Win, yana kusanto ta, gabanta yana faWuwa ta zuba masa ido.



Ya Wago mata wata takarda Wauke da hoton ™warangwal yana ci da wuta, an rubuta Imam Hammad Jalaludeen a jiki.



"Waye ya bayar da wannan sa™on?"



Kan Nana ya sara mafarkin da ta taSa yi, ya fara ™o™arin zuwar mata kanta.



"Waye na ce waye ya bayar da wannan sa™on?" Ya yi maganar cikin wata irin murya da ba ta taSa jin sa da ita ba a rayuwar da suka yi!!!



Cikin rawar murya ta ce "Nima ban sani ba, sa™o ne kawai aka ba ni aka ce na baka"



"Waye? Waye ya bayar da sa™on? Ki gaya mini?"



Ta kame jikinta cikin tsoro ta ce "Ban santa ba wata ce?"



Launin idonsa ne ya fara canzawa, ba™ar ™wayar idon ta Wauke, sai farin kawai.



"Giyaz" Nana ta furta a hankali.



AREWABOOKS.



Jikinsa ne ya fara ™amewa, fitilun kitchen Win suka Wauke gaba Waya, ta ce "A wannan karon me ka ke bu™ata kuma?"



Muryar Giyaz ta din ga ji, yana wata irin dariya. "Ai dama na gaya miki, ki jira dawowata".



"Na fi ™arfinka, a waccan rayuwar da ya yi, da wannan Win ma, na fi ™arfinka har abada".



"Kar 'yar ™aramar ™warin gwiwar da wancan yaron ya baki, ya sanya ki yi tunanin za ki iya yi mini wani abu, mu zuba mu gani".



Nana ji ta yi abu ya faWo jikinta mai nauyi, suka faWi ™asa tare. Wal hasken fitilar kitchen Win ya dawo. Imam ta gani a kwance a gefenta.

Da sauri Nana ta nufe shi, jikinta na rawa za ta taSa shi.



Amma ta ganta itakaWai a Wakin karatun ˜aisar, cikin azama ta tashi tana waige-waige, ta ga ˜aisar a tsaya a bayanta.



"Yana ina?" Ta faWa a sanyaye.

"Na san abin da ki ke ji, amma ya yi wuri, kuskure kaWan za ki aikata ki lalata komai. Kar ki yi mamakin a din ga bibiyarki, saboda zaSar ki da matar nan ta yi a matsayin mai dafa abincinsa, kuskure kaWan ki na iya kwana a ciki ki shiga matsala. Kuma Giyaz zai yi ta tunzura ki, har ki yi wani abin da za ki saka kan ki a zargi. Ki din ga bin komai a hankali"



Nana ta yi ajiyar zuciya, itakaWai ta san abin da take ji, a kan Sayyid. Dan a gare ta gara lokacin da ya Sata ba ganinsa take yi ba, amma yanzu ga ta ga shi, amma ya yi mata nisa.



*****

Sagir kuwa ya zama tamkar zararre, aka kwana uku babu Shukura babu labarinta, sai a kwana na uku ya sanar da gidansu Shukura halin da ake ciki.



Hajiya Amina ta gigice ta rasa inda za ta tsoma ranta. Hankalinta ya yi mummunan tashi.

Alhaji Zailani ya din ga yi wa Sagir bala'i, a kan me tun Satan Shukura bai gaya musu ba sai yanzu.

Aka ™ara sanar da jami'an tsaro, aka kuma baza komar neman Shukura.



****



Ummi ce ta kawowa Baba ziyara, sai dai yanzu Baba duk ya zama abin tausayi, duk inda ya zauna sai da ya ja uban tagumi ya yi shiru, da ya samu dama kuma sai ya hau zancen Nana. Yanzun ma hirar da yake ta yi wa Ummi kenan.

"Ummi kin ga Nana haryanzu shiru ko? Babu ita babu Wan uwanta, shi ma tun wannan zuwan da ya yi bai sake zuwa gidan nan ba. Gara shi namiji ne ita kuwa ban san halin da take ciki ba. Nan gida kuma ita Suwaiba yanzu ba ta da maraba da mahaukaciya, na ce a kaita Asibiti babarta ta ™i yarda.

Ita ma Jamila 'yan kwanakin nan, gaba Waya ba na gane kanta, dama kuma babarta ta nuna mini in daina shiga sabgarsu 'yarta ce, saboda abin Duniya"

Ummi ta ce "Gaskiya ne Baba, abin duk babu daWi kam, amma Baba wani abun an bar gini tun ran zane ne, wannan abubuwan tun daga tushe yakamata a ce an yi wani abu na kaucewa farwuarsu, yanzu sai dai a yi ta ha™uri ana gaya wa Allah. Ta dai Wan ba shi baki sannan ta tashi ta shiga cikin gidan.

Suka gaisa da Mama a tsakar gida, suka hau hira.

"Wai ina Jamila ne?"



Mama ta ce "Tana Waki"



"Amma tana ji na zo, ta yi burus?" Ta yi maganar tana le™a Wakin.



Ta tarar da Jamila a kwance ta yi rigingine.



"Jamila yau 'yar shariya ce babu magana ma?"



Jamila ta yin™ura ta tashi zaune, suka gaisa sama-sama.

"Wai ba ki da lafiya ne?"



Ta jinjina kai alamar eh.



"Jamila kin fiye yawan rashin lafiya, Allah ya kawo mana siriki mu sha biki. Ta ga dai mutanen gidan nasu duk sai a hankali, ta yi musu sallama ta tafi.



Hajiya Sa'a tamkar za ta haukace, kwana uku amma sai an yi da gaske take cin abinci kaWan.

Ta rame ta zabge kamar ta shekara tana larura.

Ko gaisuwar aka yi mata ba ta iya amsawa, idanunta suka koWe suka yi jawur.

Mutane da dama sun ji mutuwar Abba, saboda mutuwar fuju'a ga matashi, tana taSa zukata, mussaman Abban da yake mutumin kirki ne, ga girmama mutane.



Ranar da Abba ya kwana uku da rasuwa, Safiyya ta samu Hajiya Sa'a a Waki, ta ce "Hajiya yanzu mene ne abin yi, wani matakin ki ke ganin za ki Wauka a kan wannan lamarin?"



Hajiya Sa'a ta sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Duk matakin da zan Wauka, kafin mutuwarsa yakamata na Wauke shi, dana sani nake mara amfani na janyo yarinyar nan jikina, sannan idan na matsa, tsaf za ta tona mana asiri, dan haka ba zan saurare ta a yanzu ba, ina cikin matsanancin kewa da alhinin rashin tilon Wana. Sai dai wallahi sai ta tafi inda Abba ya tafi, ko da kuwa nima zan rasa raina na"



Jiki a sanyaye ta ce "Hajiya ki bi a hankali, kar garin neman gira a rasa idanu"



"Ki zuba ido kawai" ta faWa a ta™aice tana share hawaye.



Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya sanya Nana farkawa, ta ganta a Wakinta a kwance, ba ta iya tuna abun da ya faru ba tun daga biyo ta da Sayyid ya yi.

Ta kalli ™wan fitilar Wakin a kunne, ta yin™ura za ta tashi, kawai ta takardar nan, da ya nuna mata yake tambayarta waye ya aiko da ita.

A tsorace ta ja gefe, tana kallon takardar. Jikinta na rawa bakinta Wauke da addu'a, ta Wauki takardar ta sake ™are mata kallo. Ta ninke ta ta saka a cikin kayanta, ta shiga banWaki.



*****



Nana na tsaka da aiki a kitchen, ta ji motsi a kitchen Win.

Ta waiwaya ta kalli inda take jin motsin, ta ga Asal.

Cike da takaicin babu yadda ta iya, ta ce mata "Barka da safiya"



"Barka, amm na ce akwai abin da ya faru ne? Imam ya ce lallai a

80 / 126