Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   73 / 126

216K to 219K   out of 377.2K words

iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi."



Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita.



Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta Waukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa.

Da Nana ta koma Wakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci.

A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na ba™in da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki.

Sosai matar nan ta ™ara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba.

Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa."



Kwana huWu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ™wan™wasa ™ofar Wakinta.

Ta tashi ta buWe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya.



"Ki sako hijjabinki, ki biyo ni"



Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya.



Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita.

Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar.



Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza ha™uri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?"



"Za ki gani"



"Eh amma na ga dare ne fa"



"Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi Waya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ™wace ta.



Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su.



Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin Wakin Nanan.



Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki Waga mini komai Waya bayan Waya"



Ayshercool

71





Šaya bayan Waya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka.

Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?"



Ta Wago jakar ta ce "Jaka ce"



"BuWe ta ki zazzage na gani" Ta fara kokowar buWe jaka, amma babu gurin da zata buWe ta. Kawai ta ce "Shikenan" ta fice ta bar Wakin.



Can gurin kuma Nana tara su aka yi, su shida. "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya aka kawo ku nan, to zaSo ku aka yi saboda an yarda da amanarku, ana daf da yin taro da Sultan da kuma dukkanin Imams na gidan nan. Dan haka ku aka zaSo za ku yi girki na musamman. Amma ku sani kamar yadda wasu sani wasu ba su sani ba, muddin aka samu wata matsala ko ™ware wani ya yi, a sanadin abincin da ku ka dafa, to ku tabattar da rayuwarku za ku biya. Dole ku yi taka tsantsan ku kula." Matar ta yi maganar daki-daki.



"In sha Allah" suka amsa mata.



Ta ce su bi bayanta, suka je wani ™aton guri, Wauke da nau'oin kayan masarufi kala-kala. Ta yi musu bayanin da su ne za su yi amfani su yi girkin, sannan ya zama dole su sanya wa bakinsu sakata su yi aiki cikin amana, kuma kada wanda ya san su aka zaSa da za su yi wannan girki. Nan ma suka amsa, ita dai Nana sai kallo da ido, dan abubuwan sun daina ba ta mamaki, wannan maganar ce ta sanya aka taso ta a daren nan, sai ka ce wanda za su girkawa wasu waliyyai abinci.



Ko da aka mayar da su Nana gida, ta sha mamakin ganin kayanta a hargitse a cikin Waki. Da mamaki ta ™arasa kan kayan nata, ta WaWWaga.

Cikin takaici Nana ta tashi ta fita, sai dai kowa ya tafi makwancinsa ya kwanta. Kawai ta ji taku a bayanta. Ta waiwaya ta ga Asal na fitowa.



"Har kun dawo kenan?"



"Eh, sai dai na shiga Wakina na tarar da an caje mini kayana an zubar da su a ™asa, ban sani ba ko kina da masaniya a kan haka?"



Asal ta ce "Me yasa ki ka zarge ni?"



"Saboda na ga ba a gudanar da komai a gidan nan sai da izninki"



Asal ta yi murmushi ta ce "Haka ne, kina da kaifin ™wa™walwa kamar yadda na yi tsammani, ni na saka aka caje kayanki saboda na san da wa nake zaune"



"Me yasa ba ki tambaye ni abin da ki ke bu™atar sani ba, za a caje mini kaya"



"Saboda a ™ar™ashina ki ke, a gidana ki ke zaune dole na sani idan da wani abu da ki ke tattare da shi na cutarwa"



Nana ta ce "Kin yi kuskure, dan ina zaune a ™ar™shinki, ina da personal life Wina, da 'yancin adana abin da yake sirrina, bai halatta ki bincikar mini kaya a bayan idona ba. Yaushe na san ki, da zan ™ulla wani abu da zan cutar da ke? Kina gudun hakan ki jawo ni ki ka kawo ni?"



"Yi ™asa da muryarki, kar ki kuskura ki Waga mini murya, kin san matsayina? Za ki iya janyo wa kan ki gagarumar matsala muddin ki ka ci gaba da yi mini magana ba ladabi"



"Babu ruwana da matsayinki, da koma me za ki yi mini, kar ki sake shigar mini Waki ki taSa mini kaya, idan kuma ki ka ci gaba za ki iya binciko abin da zai hana ki sukuni, idan kin ji ba ki yarda da ni ba, ki sallame ni na koma inda na fito, ba zai yiwu na zauna da ke kina zargina kuma kina cin dunduniyata ba."



Asal ta bi Nana da kallon mamaki, amma ta danne mamakinta ta haWiye fushinta, ta ce "Gaskiya ne, kin yarda da kan ki har haka kenan? Shikenan amma idan na ga akasin abin da ya fito daga bakinki, za ki sha mamakin abin da zai faru"



Nana ta yi mata banza, ta koma Wakin nata, ta gyara kayanta tsaf.

Ta kulle Wakin ta koma ta Waga katifar Wakin, ta Waukko wata jaka, a cikin jakar ta zuba duk tarkacen kayan Sayyid. Ajiyar zuciya ta ts yi, da tayi wannan dabarar ta Soye su. Haka kurum take jin kayan na bu™atar sirri.

Ta nemi guri ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, tana tunanin yadda rayuwa ke ta jujjuyata.



*****



Shukura na zaune a Wakinta tamkar zuciyarta za ta yi bindiga ta fito, Sagir ya buWe ™ofa ya shigo Wakin. Kallo Waya ta yi masa ta sunkuyar da kai. Tuni t yi shirin kwanciya baccinta, sai ™amshin turare take zubawa.

Ya sha manyan kayansa, hannunsa ri™e da ba™a™en ledoji. Ya zo ya zauna a kusa da ita, tamkar ta kifa masa mari haka take ji.



"Wai har kin yi shirin kwanciya? Na zata zaku gaisa tukuna sai ki kwanta" Mugun kallon da ta yi masa ya sanya shi haWiye maganar da ya yi niyyar yi.

"Ga wannan naki ne" Ya yi maganar yana ajiye mata ledojin hannunsa.

Ba ta kalli kayan ba, kuma ba ta motsa ba.



Ya matsa kusa da ita, ya ri™o hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta.

Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaWan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana bu™atarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba.

Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya dur™usa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka ma™ale a ™irjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ™una, tamkar ta tashi ta bar gidan.



Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani Wan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ™oshi da shi da Yusra.

Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira.

Sai gurin Waya saura sannan suka tashi suka kwanta.

Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita.

Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya Waki da ke cikin Wakin.



Washegari sai ™arfe sha Waya na safe ya shiga Wakin Shukura.

Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura.



"Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea.



"Ina kwana" ta faWa a ta™aice.



Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taSa ledar ta yi.



"Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taSawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa"



"Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana bu™atarka a kusa da ni, kaWaici nake so"



"Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa.



˜o™arin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba.



Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai.



Cikin kwantar da murya, yake ™o™arin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banWaki ta bar shi a gurin.



Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daWi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take Wauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini.



*****



Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a Waukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin.

Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi.



Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu ba™a™en buzaye ne.



Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani Waki.

Katafaren Wakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ™amshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faWuwa da jin irin ™amshin da yake tashi a Wakin.

Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta Waukko.

Ta Waga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames Win da ke Wakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba.



"Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ™arasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta Waga kai ta kalli yadda ginin Wakin yake da matu™ar tsayi.

Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin.

Bayan sun sha™e teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita.

Su na tsaye Nana ta kalli agogon Wakin, ™arfe goma na dare.

Wani ™aton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "WaWanan ne suka yi girkin?"



Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daWe"



"Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba Waya rabin hankalinta ba ya jikinta.



Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaSo ta, ta saka ta a cikin masu girkin"



Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice.

Wata ™ofa aka buWe, wani matashi ya shigo fuskarsa Wauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faWuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya Waura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. ˜irjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa Waya da Sayyid Win.

Tunani ta fara yi ko Giyaz da ˜aisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani.

Šaya bayan Waya suka din ga shigowa, sai da ta ™irga mutum biyar cif, biyu kamar su Waya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai.



Šaya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna Waya daga kujerun da babu kowa a kai.



"Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar"



"Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke Soyewa"



Nana ji ta yi ana busar sarewa a ™ofar bayan su, gaba Waya suka ja gefe domin bayar da hanya.



Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa ba™a, ya lulluSe kansa da hiraminsa.

Gaba Waya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ™asa, Nana kuma ta yi masa ™uri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya Wauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da ˜aisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?.

Gaba Waya matasan suka mi™e tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon.

Tamkar yana tausayin ™asar haka yake taka ta, yana Wan yin rangaji kaWan, sassanyan ™amshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaWe ilahirin gurin, fiye da ™amshin turarukan da ke tashi a gurin.

Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ™arfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ™iftawa ba ta yi.

Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, Waya bayan Waya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo.

Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?"



Šaya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne"



Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ™arshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku"

Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez.

Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol Win unguwar kenan. H.J Agadez.

Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ™ame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Sai daga bisani ya saka hannunsa Waya a kan ™irjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode)

Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba.



Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin Wazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta WanWana Abincin nan"



Mutumin ya ™are musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci.

Nana ba ta san a yadda take iya Waga ™afafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ™arasa gaban teburin. Šayar ta din ga bubbuWe Abincin, ta fara WanWanawa.



"Ke kina da gaskiya kuwa? Ki WanWana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa.



Rikicewa ta yi gaba Waya, ya Waga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huWu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruWe.



Ta Webo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi.

Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh.



Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wata™ila mun yi mata kwarjini ne"



Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin.



Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, ha™oranta na haWuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta.

Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango.

Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wata™ila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba Waya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta.













*****



A hankali Nana ta yi juyi, ta buWe idonta ta ganta a Wakin da take kwana.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da

73 / 126