Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   77 / 126

228K to 231K   out of 377.2K words

biyar cif, biyu kamar su Waya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai.



aya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna Waya daga kujerun da babu kowa a kai.



"Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar"



"Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke Soyewa"



Nana ji ta yi ana busar sarewa a ofar bayan su, gaba Waya suka ja gefe domin bayar da hanya.



Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa baa, ya lulluSe kansa da hiraminsa.

Gaba Waya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu asa, Nana kuma ta yi masa uri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya Wauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da aisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?.

Gaba Waya matasan suka mie tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon.

Tamkar yana tausayin asar haka yake taka ta, yana Wan yin rangaji kaWan, sassanyan amshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaWe ilahirin gurin, fiye da amshin turarukan da ke tashi a gurin.

Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da arfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko iftawa ba ta yi.

Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, Waya bayan Waya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo.

Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?"



aya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne"



Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta arshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku"

Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez.

Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol Win unguwar kenan. H.J Agadez.

Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Sai daga bisani ya saka hannunsa Waya a kan irjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode)

Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba.



Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin Wazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta WanWana Abincin nan"



Mutumin ya are musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci.

Nana ba ta san a yadda take iya Waga afafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta arasa gaban teburin. ayar ta din ga bubbuWe Abincin, ta fara WanWanawa.



"Ke kina da gaskiya kuwa? Ki WanWana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa.



Rikicewa ta yi gaba Waya, ya Waga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huWu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruWe.



Ta Webo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi.

Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh.



Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wataila mun yi mata kwarjini ne"



Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin.



Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, haoranta na haWuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta.

Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango.

Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wataila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba Waya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta.



*****



A hankali Nana ta yi juyi, ta buWe idonta ta ganta a Wakin da take kwana.

Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru.

Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daWe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid Wina ne? Tun da dai mafarki ne duk da saui.



Sallama aka yi a Wakin, ta ga Balaraba ta shigo Wakin. Ta ce "Kin tashi?"



Nana ta yi shiru tana kallonta.



"Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaSi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki."



Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da wawalwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba Waya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da jiri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya.



*****



Jamila ta Wauki jakarta Wauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur Win ta kunna musu ashana ta one su.



Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin.

Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a.

Hajiyar ta yi iya oarinta gurin Soye jin haushin Jamila da take yi, ta karSe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuWin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a asa.

Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ungiya wa za ki bayar ne?"

Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba"



"Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?"



"A'a na rage ji"



"To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da Wan Fatuhu"



Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan.



Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?"



Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki i bin umarnin ungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ara bayan tuna ta ona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu.

A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar.



*****

Fafur Nana ta i yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da aisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki.



Nana suna Wakin girki su na ta Worawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki"



Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buata ki zo gurina ki karSi wayar ki kira"

Nana ta Wan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode"



"Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?"



"Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne"



Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga sao can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki"



Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal Win ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita.



Katafaren Wakin bacci ne, mai Wauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki.

Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun Wakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba.

Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ara yi maka gargaWi da jan kunne a kan ka ara kula da kan ka. Kar ka Wauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faWi wani abu da zai rusa shirinmu, mun Soye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin.



"Abii"



"Na'am abin aunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke Soye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na Wauka ina jinya ba a hayyacina ba?"



"Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buatar hutu mussaman a wawalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaWawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai asar nan, a shaida dai kana raye, cikin oshin lafiya"



"Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya are ba"



Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daWi babu ari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai".



"Amma Sultan ko zaka saka na Soye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata...



"Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan Win.



*****



Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faWuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta Waura alwala take ta addu'a.

Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake.

Ko ta ina amshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma.

angaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani bao ne mai muhimmanci zai sauka a gidan.

Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, bao Waya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba.



Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baar shadda, kanta babu Wan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sara da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaWarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sara da ta kwanto har goshinta.

Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baar shaddar sai ta haska shaddar.



Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taSa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen awayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taSa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba.



Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faWin sunan Imam, lokaci lokaci su na haWa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taSa jin Imam Win.



Babban abin da ya Waurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya afarsa a Agadez tsawon kwanaki huWu, ko sau Waya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu aautawa ba.



Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?"



"Ina son na je na yi wanka na kwanta ne"



"Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta"



Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau Waya, ta taSa zuwa idan sun yi girki akwai waWanda suke kaWai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To"



A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta Wauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta"



Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta Wan kwaSe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta.

Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta Waga kai ta din ga kallon awataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci.



Tana saka afarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai Sare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai.

Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet Win Wakin.

Bayan ta ajiye ta yi taku huWu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ara yawa. Ta sauke idanunta a kan aton frame da hotonsa a jiki. Danarewa ta yi a guri Waya, ta kasa motsa ko da afarta.

Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaSa.

an ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza.



"Lafiya dai ko?"



Ya jinjina mata kai alamar eh.



"Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?"



Ramata ta ce "Abinci muka kawo"



"Waye ya yi?"



Ta nuna Nana da ba ta juyo ba.



"Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ame ba ta juyo ba. A wulaance Ramata ta taSa ta ta ce "Ana yi miki magana"

"Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini"

Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa.

Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiWimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba.

Ta sunkuyar da kanta asa, tana jan afafuwanta a hankali.



"Me ya same ki ne?"



Ta girgiza kai alamar ba komai.



"Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai"



"Ba ni da lafiya"



Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki Sata mini rai"



Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya Wauka a hankali ya kai bakinsa yana sha.



Nana kuwa a Wakinta, gaba Waya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaWina a kai kenan aisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alawari ya ce haka? Na haura zan Wauki Wa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana Wauke da ruhin Wan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.



Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa.

Wani irin zafi yake ji a cikin wawalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse.

Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza.

Ya yi wankan ya lulluSo jikinsa da towel.

Asal ta sha kwalliya cikin baaen kaya na bacci.

Ta nufo shi tana rangwaWa, ta cire towel Win da ya lulluSa da shi. Ya Wan lumshe idanunsa saboda amshin turaren da Asal take yi mai jan hankali.

Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam"

"Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi"



"Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?"



"A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba"



Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haWiye ya fasa.

Ya fara oarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daWin ji a cikin sa.



"Imam jikin ne dai?"



Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa.



Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaWan.

Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba.



Bayan mintuna talatin sai ga Asal a Wakin, ta kalli Nana a wulaance cikin isa da

77 / 126