Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   75 / 126

222K to 225K   out of 377.2K words

bincike a cikin kayan ba.



*****

Ko da Jamila suka dawo Kano, fakar ido ta yi ta jefar da wannan tarkacen da aka ba ta aka ce da su za ta kai jini.

Gaba Waya da ta tuna abin tsigar jikinta take tashi, ta ji ciwon kanta da zazzaSi ya aru.

Gefe guda kuma hankalinta yana kan yadda ta ji Hajiya Sa'a tana faWin za ta sake bayar da Wan Alhaji Fatuhu. Ta jinjina rashin imaninta mutumin da yake fama da karayar arziki ga ciwo, ya rasa wancan Wan kuma a sake bayar da wannan kamar ba a yi masa adalci ba. Sai dai gaba Waya ba ta san ta ina za ta fara ba, tana jin a ranta kamar yakamata ta tseratar da yaron.

A gida ta tarar da Gaddafi, ta sha jinin jikinta da irin mugun kallon da ya yi mata, amma bai ce mata uffan ba. Suwaiba ma ura mata ido ta yi tana bin ta da kallo.

Ta tsuke fuska ta harsri Suwaiba, sai dai Suwaiba ta tuntsure da dariya, kamar za ta shiWe. Jamila ta yi tsaki ta shige Wakinsu.

Ba ta tarar da Mama a gida ba, haka ma Baba.



*****



Shiru Alhaji Zailani ya yi yana kallon Doctor Sharif yana sauraren shi, har ya gama karanta masa abin da Shukura ta je ta same shi ta yi masa.

Ya ja numfashi ya ce "Shikenan, aikinka ya yi kyau Sharif, na kuma gode sosai da sosai da ka ke sanar da ni wannan abubuwan, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Ka je za ka ga sao" Sharif ya yinura ya tashi ya tafi.



Alhaji Zailani ya numfasa a fili ya ce "Duk da kasancewar ki 'ya mafi soyuwa a cikin zuciyata, an zo gaSar da ki ka etare layin da bai kamata ki etare ba, kina oarin tono abin da zai wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali, dan haka ki yi hauri da duk matakin da zan Wauka a kan ki.



*****

Nana ta jingina da jikin gilashin motar, tana kallon tulin yashin saharar da ya mamaye gurin. Fili fetal hagu da dama duk yashi ne. Cikin yanayi mai kama da bacci take ganin abubuwan da ta din ga gani a bacci cikin saharar.

Ko a yanzun ma su na tafe Sayyid kawai take gani a kan raumi yana biye da su a cikin saharar.

Kamar an taSa ta ta Wan yi firgigit ta kalli gurin, haryanzu a titin da ya ratsa saharar suke tafiya, zuciyarta ta yi wani irin bugu da sai da ta dafe irjinta.

Sanyi ta fara yana ratsa ta har cikin ashinta, ta Waga ido tana Wan waige-waige ta ga ta ina za ta gano aisar ko wata bauwar halittar da ba jinsin mutane ba, sai dai ba ta ga komai ba.

Ta sake jingina da jikin motar tana ta karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. A haka har suka shigo cikin gari sosai da sosai.

Nana na son karanta Symbols Win da take gani, amma ba komai take iya fahimta ba saboda rubutun French. Babbar hanya mai Wauke da aton gate ta ciki suka wuce.

Ba aramar gajiya Nana ta yi ba, saboda azabar nisan tafiyar da suka shawo ba, ba su arasa ba sai bayan magariba. Kewar Wan ta ta addabi zuciyarta, tunaninta yadda za ta din ga sintirin tsakanin Agadez da MaraWi a wannan uwar tafiyar kamar ta ya da shege.



Wasu irin gidaje ne manya-manya na alfarma da asaita a cikin gurin.

A ofar wani gida direban ya tsaya, ya cewa Nana ta fito sun zo. Haka ta saukko afafuwanta duk sun yi tsami saboda azabar gajiya.

Ya buWe bayan motar ya Waukko atuwar jakar Nana, ya rufe motar, ya yi gaba Nana ta bi shi a baya tana karanto addu'oin da suka sauwwaa.

Cikin wani matsakaicin gida suka shiga, gidan ya awatu ya yi kyau sosai da sosai.

A falon gidan ya ajiye wa Nana kayanta ya ce "Ki zauna ki jira a nan"



Nana ta ce "Amma wa zan jira a nan Win, ban ga alamar akwai mutane a gidan nan ba"



"Za ki gan su, ni a nan aka yi mini umarnin na kawo ki kawai"



Nana ta yi shiru tana nazari, shi kuma ya juya ya fice.

Nana ta din ga rarraba ido, tana son ta yi salla amma babu wanda za ta tambaya. Harabar gidan ta fita saboda ta ga famfo ta yi alwala, ta dawo falon ta yi salla.

Gajiya ta yi ta koma harabar gidan da kayanta, ta zauna tana rarraba ido.

Can ta ji arar mota, aka buWe ofar wani jami'in tsaro ya shigo ya buWe gate Win, aka shigo da wata haWaWWiyar mota aka yi parking Win ta.

Aka buWe ofar motar, sai ga Asal ta fito sanye cikin doguwar riga, ta Waura mayafin a wuyanta, kanta babu Wankwali. Har bakin ofar shiga suka rakata, ta wuce Nana ta shige ciki kamar ba ta gan ta ba. Nanan ma ta yi zamanta ba ta shiga ba, ta jingina da jikin kayanta taka addu'a saboda a gajiye take matua, ga uwar yunwa tana ji ga tulin damuwa.

Sannu a hankali take tuna yadda ta shigo asar Nijar ba ta san kowa ba, da yadda ta din ga raragefe har zuwa kan zamanta da Nene. Sai ta tsinci kanta da tattara su baki Waya tana yi musu addu'a, da fatan dacewa a Duniya da lahira.

Ba ta san iya adadin lokacin da ta Wauka a gurin ba, ta ji muryar Asal a kanta.

"Wai ke wace irin bagidajiya ce, a Nigeria daga wani auyen ki ke ne?" Nana ta Waga kai ta kalle ta.



"Na saka an kawo ki guri, ki shiga ki jira ni kin zauna a waje, na dawo ma kin nemi guri kin zauna ba za ki shigo ba?"



"Ta yaya zan shiga gurin da babu kowa na zauna, ni da ban san ma aikin da ki ka kawo ni na yi miki ba?"



Haushi ya kama Asal, ta ce "To idan kin ga dama ki shigo, idan kuma ba ki ga dama ba, ki yi ta zama a gurin" Ta shige ciki Nana ta bi ta da harara, kamar ba za ta tashi ba, sai kuma ta tashi ta ja kayanta, ta shiga falon ta nemi guri ta zauna a kan kujera. Asal ta saci kallon Nana, da yadda take gudanar da lamarinta cike da arfin hali.



Nana ba ta kula ta ba, ita ma ba ta kula ta ba, Nana ta gaji da zama, ta saukko asa ta mie ta kwanta.

Can Asal ta ce mata "Ga kitchen can, akwai abinci"

Daga haka ta tashi ta bar falon.

Nana ta tashi ta shiga kitchen Win, ta tarar da Abinci, ta Wauka ta ci sannan ta Wan dawo hayyacinta.

A nan falon Nana ta kwana, da Asuba ta yi alwala a harabar gidan, ta koma falon ta yi salla.

Duk wannan abin zuciyarta a cike da zullumin aikin da za ta yi wa Asal.

Da gari ya yi haske, Asal ta fito Nana ta gaishe ta, amma ta yi kamar ba ta ji ba, ta fice ta bar gidan ta bar Nana.

Nana tana nan zaune, aka zo aka wanwasa ofar falon, ta tashi a Wan tsorace ta buWe, wani mutum ya mio mata takeaway ya ce "Ga shi nan, aka ce a kawo miki" daga haka ya juya ya tafi.

Nana ba ta sake ganin Asal ba sai dare, ba ta saurari Nana ba still. Ta cika gidan ita da awayenta, suka hau saman bene, suka kunna kaWe-kaWe har kusan Waya na dare su na abu Waya, suka hana Nana bacci.

Sai gefin Asuba suka daina wannan shirirtar, Nana ta din ga mamakin ita Asal zaman kanta take yi ne, ba ta da magabata ko kuwa?

Sai washegari sannan ta saukko asa, a lokacin awayen nata duk sun tafi.

Ta kalli Nana ta ce "Daga yau kar ki ara kwanar mini a falo, ga Waki can kusa da kitchen, a nan za ki din ga kwana. Na kawo ki ne duk da ba yanzu ne za ki yi aikin naki gaba Waya ba, amma za ki din ga yi mini girkin Abinci da ni da awayena, da sauran aikace-aikacen gida.

Abu na farko dalilin da ya sanya na Waukko ki, ke ba abilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu

Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaWai za ki yi mini"

Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch Win za a kai ta aiki ba, wannan zuaiyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuWi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaSi kowa ba sai ita?.

"Ba kya ji na ne?"



"Na ji"



"Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so".



Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faWin asar nan ki rasa wanda za ki Waukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba"



"Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana miewa tsaye.

Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki buata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ulewa.



*****



Gaba Waya Shukura ta burkicewa Sagir, ba Waga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja Waya take harkokinta, da gaske take oarin gano abin da mahaifinta yake Soyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta.

Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar.

angarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ara gyara shi, aka haWa gidan gaba Waya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya Wau harama.

Duk yadda ya so ya lallaSa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.



Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon awayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya oarinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta.

Tana tsaka da nazarin yadda za ta Sullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati Waya zamu bar nan, zamu je asalin inda na Wauke ki ki yi mini aiki a gurin"



Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?



"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a taaice.



*****

Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu.

Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta orafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita.

Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka.

Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.



"anwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da Sarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"



Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi hauri ka yi aurenka kawai, ina roon Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"



"A'a ki daina faWa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana arfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta.

Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta uro mata ido tamkar ba ta taSa ganinta ba.



"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.



Jamila ta ja tsaki, tana oarin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"



"Na'am mene ne?"



"Ki Wauki saonki mana"



Cikin rashin fahimta ta ce "Wane saon?"



"Na cikin jakarki"



"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?"



"A'a ni tuni kawai nake yi miki da saonki na cikin jakar"



Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani saon? Mio mini jakar dai na gani"



Suwaiba ta ce "A'a ba zan taSa miki jaka ba"



Jamila ta janyo jakar ta fara buWewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura iris ta kurma ihu, ta rikice gaba Waya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita.

Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana yayatawa tana kallon Jamila. Gaba Waya Jamila ta kiWime ta rasa abin da yake yi mata daWi, gaba Waya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta.



*****



Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan afafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan.

Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan bain ciki.

Da yar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?"



Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa Waya daga kujerun da ke ajiye a gurin.

Alhaji Zailani ya zauna suka ara gaisawa



"Bani labari, ya aka yi saui ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?"



Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan Waurewa da nake ji a jikina ya yi mini saui, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daWewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux



"Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?"



"A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba"



Alhaji Zailani ya mie ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi"



"Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?"



"Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin unar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taSa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba.



*****



Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faWa cikin matsanancin Sacin rai.

"A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba Waukar ta aiki muka yi saboda buatar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haWa kai ku yi mata haka wannan wulaanci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar asarmu ba"



"Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da Wa ma"

"Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da arfi da kuWi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba"



"Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba tai yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba"



"Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku"



Ta kwaSe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya Sata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?"



"Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi oarin hana Asal Waukar Nana.



*****



Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan.

Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai.

Ta sha aiki ta gama, ta Wan zauna a falo tana hutawa, sai ga Waya daga gayyar awayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi"

Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka"

"Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa"



"Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu"



"Ke, kin san wace ce ni

75 / 126