Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   118 / 126

351K to 354K   out of 377.2K words

su ga abu a du™un™une sai an fassara musu.

Galibi waWanda aljanu ke nuna wa mutum a mafarki, na haWin faWa ne. Abu ne da aka yi shi a bayan idon mutum bai san an yi ba, sai su nuna masa. Kuma ba su fiye nuna abin alkhairi ba sai akasin haka. Wasu idan sun gani su na iya shiru da bakinsu, wasu kuma basa iyawa sai sun faWa. Sai su sanya a din ga yi wa mutanen wani kallo na daban, wasu a dole dalilin hakan kan sanya su fara bayar da magani.

Ke na biyo miki ne ta hanya mai sau™i, saboda bana son tilasta miki, na fi son ki amince da kanki. Sai na nuna miki abin da ya faru da baki sani ba, ko kuma wanda yake shirin faruwa, ko wanda nake hasashen abu ne mawuyaci bai faru ba. Akwai abin da idan na ™yale ki, ki ka tashi da shi a ™wa™walwarki, ba za ki iya yin shiru ba, za ki yi yin™urin Waukar mataki, wanda hakan ka iya haifar da fitina, saboda idan ki ka haifar da matsalar ba ki da maganinta, tun da ba ki amince da bayar da magani ba.

Šan Adam kuna da nau'in ciwo na gangar jiki, da kuma na ruhi, amma ba kwa damuwa da ciwon da yake damun ruhinku, kun fi damuwa da na gangar jiki. Mutum zai iya kashe ma™udan kuWaWe, a kan lafiyar gangar jikinsa, amma sam wani baya yadda ma ruhinsa yana rashin lafiya."

Nana ta ce "Nima ban gane ba"



Yayi murmushi ya gyara zamansa ya ce "Ruhi shi ne asalin rayuwa, da gangar jiki ta dogara a kai, wanda ba a iya ganinsa, ko taSa shi, amma wanzuwarsa ce take sanya gangar jiki motsawa. Ruhi yana da ala™a da hankali domin shi ne, ku 'yan Adam ku ke amfani da shi, gurin sarrafa duniyarku da gangar jiki. Lafiyayyen ruhi da tunani suke samar da nutsatsiyar gangar jiki mai cike da karsashi. Rashin lafiyar ruhi, ta fi ta gangar jiki hatsari. Idan ruhi yana rashin lafiya, yana kashe gangar jiki baki Waya.

Sannan warkar da gangar jiki ya fi sau™i a kan warkewar ruhi. Na san bayan nan nawa sun Wan yi miki tsauri, amma bari na Wan sau™a™a miki bayanan.

Kamar yadda na ce miki ruhinku yana rashin lafiya, tabbas yana yi ciwukan da ido baya iya gani, sai dai ciwon na sanya hankalinku ya ™wace, ku aikata abin da ba shi kenan ba. Misali Alhaji Zailani ruhinsa na fama da ciwon Hassada, amma bai taSa tsayawa ya fahimta ba, saboda hankalinsa ya ™wace har ya din ga aikata miyagun ayyuka. Wasu lokutan ku kan ji duniya ta yi muku zafi, kun tsani komai babu laifin tsaye babu na zaune, yana daga cikin alamomi na ruhinku na bu™atar kulawa ba shi da lafiya. Dan wasu lokutan shi ne yake taSuwa sai hankali ya taSu, nan da nan sai a ce ™wa™walwa babu lafiya, idan ciwon ba shi da ala™a da irin matsalolin da muke haddasa muku a ruhi. Hassada, ™yashi, yawan ™arya ba™in ciki babu dalili, burin gushewar ni'ima ga wani, yawan raya faruwar munan abubuwa. Yanke tsammani daga samun rahama, ko wani abu na alkhairi a rayuwa. da wasu cututtukan ma da ku kan danganta su damu, alamomi ne na rashin lafiyar ruhi, duk da mafi yawa wasu lokutan mu ne muke haddasa rashin lafiya a ruhinku.

Idan ku ka ji alamu na ™yashi ko hassada, ba ku fiye sakankankancewa ku ro™i Allah ya yaye muku ba, ko ku mi™e ku nemi maraba da hakan ba, ba ku fiye Waukarsa komai ba. Sai dai a hankali idan ya tsananta sai hankalinku ya gushe gangar jikinku ta aikata Sarna. Kamar dai abubuwan da suka faru a masarautar su mijinki. Da abubuwan da aka yi masa. ˜yashi, ba™in ciki hassada, son kai, da makamantansu duk larurar ruhi ce da ke kashe gangar jiki.

Sai dai a zamana da ke na ™ara fahimtar wani abu, babu abin da ya kai addu'a kusanta mutum da Ubangiji, kuma duk ruhin da yake da kusanci da Allah zaka same shi cikin nutsuwa. Babu wanda ya san inda ruhin Wan Adam yake sai Allah, amma galibi cututtukan da suke ala™a da ™wa™walwa da abubuwan da zuciya ka iya rayawa su na da ala™a da ruhi.

Lokuta da dama sai bawa ya yi ta addu'a, ya ga kamar bata karSuwa, amma tasirin Addu'a da kusanci da Allah na sanya mutum a cikin nutsuwa, ta yadda zai ga wani da irin kaddararaa koma wadda ba ta kai tasa ba, amma ba shi da nutsuwa da kwanciyar hankali.

Yanzu mu tsaya a nan, ma ci gaba wani lokacin, zan je Webo wani magani ne"

Nana ba ta yi magana ba ta ji Muhsin yana kiran sunanta, yana kiran ruwa.

Ba ta motsa ba, ta ji Nene ta tashi ta nemo ruwan ta ba shi.

Abubuwan da suka tattauna da ˜aisar kaf suka dawo kanta. Ya gaya mata wasu abubuwa da hannalinta bai taSa kai wa kai ba. Tabbas Wabi'ar zuciya ce jin ™yashi ko hassada ko son kai wasu lokutan, hakan na nufin ruhin mutum babu lafiya kenan yana bu™atar attention?.



*****

Babu kowa a gidan, Mama ta ritsa Jamila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take tambayarta "Jamila ki gaya mini gaskiya, da gaske ne abubuwan da ki ke faWa cewar kin shiga ™ungiyar asiri, ko kema aljanun ne suka taSa ki ki ke wannan soki burutsun?"

Jamila ta sunkuyar da kai. Ta ta™ar™are ta dun™ule hannu ta Wirka wa Jamila dundu ta ce "Za ki gaya mini ko sai na danne ki da fulo na kashe ki?"



"Ki daina duka na, ba soki burutsu nake yi ba, da gaske nake Hajiya Sa'a ta saka ni a ™ungiyar asiri ba tare da sanina ba. Ta ™ulla ala™a da ni ne, saboda na kawo mata jinin Nana ta ba wa ™ungiyarsu ta yi arziki, da ban kawo jinin Nana ba ta saka ni a ™ungiya. A can aka fara lalata mini rayuwa, sannan tsautsayi ya sake shiga tsakanina da Wanta Abba, cikin jikina da ya fita nasa ne. Shi ya sadaukar da kansa saboda kar da na bayar da kowa a ™ungiya, amma haryanzu aljanun ™ungiyar bibiyata suke yi, suna nema su kashe ni nima, wannan ce gaskiyar da ki ke son ji Mama, wannan ce bayan ita babu wata kuma"

Kafin Mama ta yi magana suka ji muryar Baba yana kuka ya ce "Jamila kin cuci kanki, ba ki kyautawa kanki ba, Jamila ™ungiyar asiri, kuma aka nemi jinin Nana"

"Wallahi Baba ban bayar da jinin kowa ba, ba dan son raina na shiga ba, ban san ya aka yi na shiga ba."

"Rufe mini baki, ni ta wani fannin na gode Allah da na yi wa Nanan aure ma, ta bar muku gidan. Kuma ki tattara yaranki ku bar mini gida Rabi, ko ™aunar ganinki bana son yi. Ku je ku da Allah" Yayi maganar yana kuka. Mama ta rasa bakin magana, tabbas ita da din ga ™ara tunkuWa Jamila jikin Hajiya Sa'a, ba tare da tunanin abin da ka iya faruwa ba.

Daga cikin Waki Jamila na kuka take faWin "Dan Allah Baba kar ka yi mini baki, ka yi ha™uri ka yafe mini dan Allah, ko iya haka na sha wahala, ina kan sha ma na san ba tsawon rai zan yi ba, ba za su bar ni haka ba nima kashe ni za su yi"

"Gara su kashe ki, sai ya fi mini kwanciyar hankali" Ya goge hawayensa ya fice.

Yana fita ya ci karo da Ummi, ta kalle shi ta ce "Baba fita zaka yi, ina ta sauri saboda na cim maka, ina ta kiran wayarka amma ba ta shiga"

Ya ce "Eh, fita zan yi Allah ya sa dai lafiya?"

"Lafiya ™alau, mu shiga daga ciki"

Ya girgiza kai ya ce "Ba na son sake shiga cikin gidan nan"

Ummi ta ce "Amma Baba meyasa, magana ce mai muhimmanci"



Ya ce "Ki yi ta a nan kawai"



Jiki a sanyaye ta ce "Ranar da 'yan uwan mijin Nana suka zo gurinka sun je gidana" Sai Baba ya gyara tsayuwarsa, ya ce "Yaya aka yi suka san gidanki?"



Ta ce "Nima ban sani ba, amma har magana na yi da mijin Nana, ka san lokacin da suka samu matsalar nan, da ba shi da lafiya sun zauna a unguwarmu"



"Haka ne, amma nifa ban yarda da abin da suka gaya mini ba"



Baba ya nuna wa Ummi guri suka zauna, ya ce "Ummi da gaske ke kin yadda?"



Ummi ta ce "Baba ga zahiri nan kana gani, tun daga Nijar suka taho fa. Sun gaya mini ma an so gyara maka gidan nan ka ce ba ka so"



Ya ce "Bar ni Ummi, ni yanzu na shiga hankalina da al'amuran rayuwa, babu abin da ya kai kwanciyar hankali da nutsuwa daWi" Nan ya bata labarin halin da suke ciki da Jamila.

Jikin Ummi ya yi sanyi sosai da sosai, ta ce "Baba idan ka kori Jamila ina za ta je yanzu? ˜addara ce Allah ya aiko dole a yi ha™uri da ita. Yanzu dai sirukanka za su ranar Lahadi idan Allah ya kaimu, sun kira ni a waya, an ce ba a samun lambarka. Mijin Nana ya sai duk wani abu da za a tarbi 'yan uwansa da za su zo. Kawowa kawai za a yi kafin su iso. Dan Allah ka kwantar da hankalinka ka bar batun Jamila mutanen nan su zo lafiya su tafi lafiya.



*****

Asal na kwance a gadon Asibiti, Hasna na gefenta ta ri™e hannunta, sai uban kuka take yi.



"Hasna wallahi ina son Hammad, ji nake mutuwa zan yi idan ya sake ni, ga shi haryanzu ban san a wani bugiren ya ajiye ni ba, bai sake ni ba, bai ce mini komai ba. Babanmu ne duk ya janyo mini da zigar Imam Omar."



"Asal ki yi ha™uri mana, kar ki illata kanki a kan sa, shi fa yanzu ya samu wata ne da yake rawar ™afa a kanta, ke sai ki kashe kanki fisabilillahi"



"Hasna ba ki san me nake ji ba, wai ni ce nake da kishiya, wadda na Wauka ™as™antacciya mara galihu na shiga uku"

Hasna ta rungume ta, ta din ga rarrashinta tana yi mata nasiha.



Kwanan Yusuf huWu da mutuwa, tsufan Alhaji Zailani ya sake fitowa, duk ya fita hayyacinsa ya yi wani iri. Alhaji Zailani ya zo duba shi, yana ta rarrashinsa yana ba shi ha™uri. Mutane jefi-jefi na shigowa su na yin gaisuwa.

Wani mutum ne ya yi sallama, suka amsa masa ya shiga, duk suka bi shi da kallo, dan babu wanda ya san shi a cikinsu.



AREWABOOKS



Sai da suka Shukura ta biyo bayan mutumin, sannan suka rikice gaba Waya suka mi™e, banda Alhaji Zailani. Hajiya Amina ta nufi Shukura da gudu har tana neman faWuwa, ta rungume ta cikin tsananin tashin hankali da manakin ganinta ta ce "Shukura, ke ce? Ina ki ka shiga aka din ga neman ki, ina cikin jikin naki?" Wani irin tausayin Hajiya Amina ya shiga ran Shukura, ta rungume Hajiya Amina tana kuka.

Alhaji Fatuhu ma cikin matsanancin mamaki yake faWin "Ikon Allah, Allah da girma da iko yake. Sannu Shukura" Alhaji Zailani dai yana zaune yana kallon su, bai ko motsa ba.

Idanun Shukura suka sauka a cikin nasa, ta ji tamkar ta yi tsalle ta sha™e shi, saboda wani abu mai Waci da ya tsirga mata.

Mutanen da ya sabauta rayuwarsu, duk ga su a tare da shi a zaune.

Ta ce "Mummy wai na ga rumfa a harabar gidan nan, me yake faruwa ne?"

Hajiya Amina ta ce "Ba wani abu bane ba, Shukura ina ki ka tafi?" Kan ta ba wa Hajiya Amina amsa ta dur™usa ta gaida Alhaji Zailani ya amsa mata cikin damuwa ya ce "Shukura kin sanya mu a tashin hankali, meyafaru wannan bawan Allah kuma waye?"

Shukura ta numfasa ta ce "Garkuwa aka yi da ni, wannan mutumin Likita ne, shi ne wanda ya taimake ni, a gidansa na ™arasa jinya"

Suka gaisa da mutumin, Alhaji Fatuhu ya din ga yi masa godiya. Hajiya Amina ta ce "Daddy, ba ka ga Shukura ba, Shukura ce fa ta dawo" Ya sauke numfashi ya ce "Na ganta"



Alhaji Fatuhu ya ce "Haba Zailani, amma atleast yakamata ka yi farincikin dawowarta ko, yarinyar da ake ta nema ba a gani ba, ta dawo kuma ka yi fuska"



Alhaji Zailani ya ce "Ni yanzu ta mutuwar Wana nake yi, dan Allah ku ™yale ni" A burkice Shukura ta ce "Wane Wan nasa?"

Tsit suka yi aka rasa mai yi mata bayani, Alhaji Zailani da kansa ya gaya mata Yusuf ne ya mutu. Shukura ta gigice cikin matsanancin tashin hankali ta hau kuka, tana faWin "Shi ma ka kashe shi ko? Da ni ba a kashe ni ba sai ka kashe mini Wan uwa, wallahi ba zan yadda ba sai na tona maka asiri Duniya kowa ya san abin da ka ke yi" Likitan da ya rako ta, ya tashi tsam ya yi musu sallama, ya ce zai dawo.

Duk yadda suka so Shukura ta nutsu amma ta ™i, ta din ga surutan da ba su gane kansu ba, kuma Alhaji Zailani ya yi mursisi ya yi shiru.



*****

Nana jikinta har wani she™i yake yi, ta yi kyau sosai da sosai, sai dai ganin Hammad ya yi mata wahala, saboda yana ta kai kawon shirin bikinsu. Yadda ta lura lamarin ba da wasa suka Wauke shi ba, sai gayyatar mutane suke yi. Bangaren Sultan yana ta shan suka, da ™orafe-™orafe, a kan ya ci mutuncin Al'adar da aka gada daga iyaye da kakanni. Bai tsaya a iya nan ba, ya ayyana rushe majalisar Imam da ake da ita. Ya sauke Tafawa, ya sauke Sardaunanda wasu daga cikin mu™arrabansa, tare da cewar za a ayyana waWanda za su maye guraben su, a lokacin shagalin bikin Hammad da matarsa ta Soye da zai bayyana wa Duniya yanzu.

Nana a ranta take ™ara jinjina ikon Allah, sai dai tana ganin lamarin bikin nasu, kamar a ™asar turawa, sun yi aure sun haihu har da Wa, sannan za a yi shagalin bikinsu.

Gefe guda sannu a hankali take ™ara yi wa kanta fashin ba™in, bayanan da ˜aisar ya yi mata a game da rashin lafiya da ya ce ruhin Wan Adam yana yi. Kuma ga yadda ta fuskanta, babu wani magani tattare da hakan face ka yadda kana da ciwon, sannan ka tsananta addu'a Allah ya raba ka da shi.

Tabbas ko a kankin kanta ta ga misali, ta ™ara samun nutsuwa da yarda da komai lokaci ne, lokacin da take addu'a Allah ya kawo mata Wauki a kan matsalolinta, gani take kamar ba za su wuce ba, kamar waraka ba za ta zo ba. Ashe wannan addu'a da take yi, ke ™ara samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali, tabbas banda haka, da irin azabar da ta ci da tuni ta amince da al'amarin bori, ko ma haukace saboda wahala da yadda ratuwarta ke tafiya kamar ba ta mutane ba.

Ta kalli yadda a yanzu ba ta aikin fari bata na ba™i, sai dai kawai a kawo mata ta ci, ta yi ibada ta kwanta. Sai dai ta dage da ro™on Allah, kar Ni'ima ta sanya ta shagala da neman kusancinta da shi.



****

Gidansu Nana, Mama ta yi mamaki, ganin Uwani ta zo ranar Asabar, wai zata kwana, da azahar ma sai ga Ummi da uban kayan cefane, har ma da Yaya Atine.

Mama ta ce "Wai lafiya duk na ganku, meke faruwa ne?"

Uwani ta ce "Kamar yaya meke faruwa? KarSar kayan auren Nana muka zo ayi da mu mana"

Ta yi saroro ta ce "Nana kuma, wace Nanan?"

"Nana wacce da wacce ku ke da ita a gidan nan? Ba dangin mijinta ne za su zo daga Agadez ba?"



Mama ta ce "Ban fa gane ba, yaushe aka ganta"



Uwani ta ce "Ke Ummi, ba ku gaya mata ba ne?"



Ummi ta ce "Ina ga Baba bai gaya mata ba, Nana tana Agadez can hannun dangin mijinta, gobe in Allah ya kaimu za su zo kawo kayan aurenta"



"Shi ne kuma dan munafunci ba a gaya mini ba? Kuma wane irin kayan aure kuma bayan wanda aka yi"

Ummi ta ce "Wallahi nima ban sani ba, sai dai sun zo za mu ji"

Mamaki ya cika Mama, domin babu wanda ya tsaya ya yi mata cikakken bayani, kamar ma ba a son ta ji abin da yake faruwa.

Washegari tun ™arfe sha Waya na safe, gidan abincin da aka sai Abinci a hannunsu, suka kawo abinci mai rai da lafiya cikin kuloli na alfarma. Baba ya din ga shiga yana fita, shi fatansa kawai ya ga Nana ba wai abin da za a kawo na auren ba.

Da azahar motoci biyu suka iso, Waya guda Waya ta alfarma Waya kuma ta matafiya.

˜aton carfet dama aka shimfiWa a tsakar gidan, aka shirya wannan uban kayan Abincin.

Manyan mutane ne, farare sol Turaki da Matawallen Agadez, sai kum Tafida, sai kuma Imam Zahradeen, Mahmoudu Sulei, sai kuma Imrana.

Kai tsaye Imarana ya nufi Baba, aikuwa Baban ya rungume shi yana fashewa da kuka. Yadda ya ga Imarana a nutse cikin kamala kawai ya sanya shi mantawa da tarin ba™in cikin da yake ciki, kuma sai a lokacin ya gazgata mutanen nan da gaske suke.

Imrana ya ce "Baba kar ka yi magana, ka ga mu na tare da ba™i" Baba dai kai kawai ya iya jinjinawa yana sake ri™e shi, kamar zai sake guduwa.

Ta taga Mama take Wan le™owa, ta saki baki tana kallon ikon Allah, suturar jikin buzayen kawai ya fallasa cewar a cikin rufin asiri suke, ba ™ananan mutane ba ne.

Bayan Baba ya Wan nutsu, duk sun nemi guri sun zauna, suka gaggaisa. Imam Zahradeen ya ce "To Baba mun sake dawowa, mun zo mu cika al™awari da muka Wauka, waWanan 'yan uwan mahaifinmu ne, ga shi muka zo tare da su"



Suka sake gaisawa Matawalle ya ce "Šan uwa, Sultan ne ya aiko mu wakilci mussaman, mu zo mu yi godiya, mu jinjina wa namijin ™o™arin da ka yi, na aura wa Wanmu 'yarka ba tare da sanin waye shi ba. Ha™i™a mu yarinyarka alkhairi ga ahalinmu da ™asar Agadez baki Waya ma. A madadin Sultan Jalaludeen ya ce "Mu ce maka mun gode, mun sake gode wa. Mu na tafe da dukiyar aurenta, kamar yadda ake yi wa kowace 'ya da ake yi wa kabilar buzaye.

118 / 126