Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 126

93K to 96K   out of 377.2K words

™asan zuciyarta kamar za ta yi bindiga, saboda damuwa da"

"tashin hankali. Sosai abin da ya faru ya tsaye mata, ta shiga banWaki ta sha kuka. Wai ita Aljani ya kwanta da ita, ta gaba da baya aka ci zarafin ta ta wannan mummunar hanyar."

"Tana kwance a cikin bargo, Hajiya Sa'a ta fita shashashancinta. Wayarta ta fara ringing. Ta janyo ta Waga."

"Muryar Abba ta ji ya ce ""˜anwata, wunin yau ban jiki ba, lafiya kuwa?"" Wani irin abu mai zafi ya taso"

"mata, ya haddasa mata karaya. Muryarta na rawa ta ce ""Yaya Abba ba ni da lafiya"""

"""Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Me ya same ki?"""

"Rasa abin da za ta ce masa ta yi, kawai ta saka kuka. Aikuwa ya rikice ya din ga rarrashin ta."

Da ™yar ya lallaSa ta ta ce masa cikinta ne yake ciwo.

"""To ina Mummyn take? Ba ta kai ki Asibiti ba?"""

Ayshacool

"""Ta kai ni, an ba ni magunguna ma, dan Allah kar ka yi mata zancen, ta yi mini iya ™o™arin ta,kar ka yi"

"mata zancen dan Allah"""

"""No ai ba zan yi mata ba, ba ta san ma ina da lambar ki, mu na magana ba. Ki kwanta ki samu hutu kin ji"

˜anwatax

"""To shikenan na gode sosai"" suka yi sallama ta ajiye wayar, ta kwanta hawaye na ci gaba da bin idanunta."

*

"Yana zaune a cikin mota, yana ™o™arin kunnawa, wayarsa ta fara vibrating. Ya kalli screen Win wayar, ya"

ga ba™uwar lamba. Ya Wauki wayar ya Waga ya saka a kunnensa.

"""Hello"" muryarta ta doki dodon kunnensa. Šan waro ido ya yi, ya gyara zaman sa ya ce ""Wa ke"

"magana?"""

"A raunane ta ce ""Beb abin har ya kai ka manta muryata ma? Shikenan na gode"" ta kashe wayar."

"Da sauri ya bi kiran wayar, amma ta ™i shiga, ya yi ya yi, amma ta ™i shiga, sai ha™ura ya yi ya ja motar."

"Shukura mamakin abin da ya zaunar da shi a cikin mota take yi, bai tafi ba har yanzu, sai dai tana Waga"

"labule, ta hango ya ja motar ya tafi."

"Video call Win Hajiya Amina, Shukura ta gani, ta Waga cikin fara'a tana faWin ""Hajiya Mummy, ya ibada?"""

"""Ibada Alhamdillah, Shukura dan Allah me yasa ba kya ji ne? Ina zaman zamana, ina ibada kin jawo mini"

"Sacin rai da damuwa"""

"Cikin rashin fahimta, ta ce ""Ni Win kuma? Me na yi?"""

"""Baban ki ya kira ni, bai taho ba tukuna yana Abuja. Yana yi mini faWan wai ke ba ki san ™addara ba ne?"

"Doctor Sharif ya kira shi cikin damuwa, yana gaya masa a gaban mutane ki na cewa yana kashe mutane, haka ake yi a kan ki a ka fara rasa Wa? Me yasa ba za ki girma ba ne Shukura"""

"""Mummy ki na ji na, network Win ki mai ™arfi ne ko?"""

"Ta ce ""Eh, ina jin ki, kuma ina kallon ki"""

"""Ina son idan kin je gaban ka'aba, ki yi mini addu'a, muddin a kan gaskiya ta nake, Ubangiji Allah ya shiga"

"lamarina ya ™arfafa mini gwiwa. Idan kuma ba a kan daidai nake ba, Ubangiji Allah ya kawar da kaina"

daga kai. Ya bani juriya da dangana na daina jin abin da nake ji a zuciyata.

"Sai dai kin dawo amma akwai matsala ne fa."""

"""Shukura matsala wace iri ce, za ta sanya musulmi kasa yin tawakkalli?"""

"""Ki bari dai ki dawo Win"""

"""To shikenan, amma gaskiya mahaifinki ya yi fushi bai ji daWin abin da ki ka yi ba sam"""

"Shukura ta lallaSa ta, ta ajiye wayar."

*

"Nana tana jan ruwa a rijiya, tana zubawa a cikin bokitanta, za ta kai banWaki."

"Barira ta ce ""Nana ki yi ha™uri dan Allah, jiya na haska ku, ba a son raina ba ne, kuskure ne"" Nana ta ce"

"""Babu komai"""

"Sajida ta ce ""Uban me ki ka haska ki ka gani?"""

"Barira ta kwashe da dariya ta ce ""Ni babu abin da na gani, duk da bai kyautu ba abin da na gani Win."

"Amma Nana mijinki balarabe ne ko bature?"" Nana ta Waga ta kalle ta."

"""Tun da ku ka zo dama bamu taSa ganinsa ba, gashi na gani kamar na mace dogo sosai"""

"Nana ta maze ba ta kula ta ba, ta kwashi kayan ruwanta, ta nufi Wakin su."

"Sajida ta tuntsure da dariya ta ce ""Maganinki da shegen shishshigi, ga shi ta gwale ki"""

"""Shegiya ba, ta fiye jin kan ta,kamar 'yar uban wani, kuma da 'yar uban wanin ce, da ba su kama hayar"

"Waki Waya ba"" Duk abin da suke faWa a kunnen Nana, amma ta yi kamar ba ta ji ba."

"Bayan ta gama wanke banWaki ta fito, ta zo gabansa ta zauna. Ya Waukko sauran kuWin nan, ya ajiye a"

gaban ta.

"Ta kalle shi ta ce ""A ina ka Soye ne, ban gan su ba?"""

"Ya yi murmushi ya ce ""Su na cikin kayana fa, ba ki duba bane ba. A cikin leda suke. Kuma da sun fi haka"

"yawa, Habu ne ya karSa""."

"Nana ta duba kuWin, sai tarin kuWin nijar, na Nigeria ba su dubu Wari da goma ba."

"Ta ce ""Sayyid, idan ka Wan ™ara hutawa, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ne, za mu koma Asibiti a sake"

"duba ka. Da za su kai da na haWa da sauran na guri na, a fara yi maka allurar nan ko guda Waya ce"""

"""A'a, kin manta yanzu mu zamu din ga sayen Abinci. Idan su ka ™are ba mu da hanyar samun kuWi. Kuma"

"da akwai isassun kuWi, gara mu bar gidan nan, da a yi mini magani"""

"""Ni kaina Sayyid ba na son gidan nan. Mama za ta aiko mini buhun barkono, idan aka kawo, na ga ana"

"ciniki, sai mu ci gaba da sayarwa""."

"Ya jinjina kai ya ce ""To, in anjima ki raka ni masallaci"" Ta kalle shi ta ce ""Da gaske masallaci za ka je?"""

Ayshacool

"""Eh, ina son zuwa masallaci. Idan ki ka raka ni, sai ki dawo"""

"Ta yi murmushi ta ce ""To shikenan, Alhamdillah sau™i yana samuwa. In sha Allah zan kai ka. Bari na ajiye"

"kuWin nan, idan na raka ka ma, dan Allah zan je gidan Ummi"" ya jinjina kai. Har za ta tashi ya ri™o ta, ya"

cire hijjabin da yake jikinta.

"˜onuwar da take wuyanta ya gani, ya ™ura wa gurin ido sosai sannna ya ce ""Mene ne wannan?"""

"Ta Wan basar ta ce ""Ba komai fa, Wan ™onewa ne kawai na yi"""

"""Ba Wa ba ne ba, me ya kai ruwan zafi wuyan ki? Waye ya zuba miki?"""

"""Ba wanda ya zuba mini, sha nake yi ya zube"" kawai ya rabu da ita, ba dan ya gamsu da amsar da ta ba"

shi ba.

"Ta tattare kuWin nan, na Nijar ta zuba su a cikin jakar gidan Sarkin Baka. Na Nigeria kuma ta haWe su, ta"

"saka a cikin kayan ta. Ana kiran salla, ya yi alwala, Nana ta ba shi mayafin rawaninsa, ya yafa a kan sa."

"Nana ce ta fito tsakar gida. Barira ta gani, tana girki sanye da wata 'yar riga, milik ce amma ta yi ba™i"

"saboda dauWa, ko brezia babu a jikinta. Ga gashin hammata ya fito zaro-zaro idan ta Waga hannunta."

"Zanin jikinta ma ba™i ™irin, tamkar an yi matsar man ™uli da shi, sai annakiya take yi."

"Nana ta ce ""Barira, dan Allah ko za ki gyara, zamu wuce"""

"Barira ta ce ""Bismillah ki wuce mana"""

"""A'a ai ni da mijina ne"""

"""Ku wuce ba wani abu ai"" Nana ta yi shiru tana jinjina tumasanci da rashin sanin ciwon kai, na mutanen"

"gidan. Babu yadda ta iya, haka ta kammo hannun Sayyid, ya fito ta rufe Wakin. Ya ja mayafin ya rufe fuskarsa da rawanin, saboda yanzu ba ya iya naWa shi, saboda numfashinsa."

"Tun da ya fito Barira take kallon sa, ta na son ganin ainihin fuskarsa, amma ya sunkuyar da kai, kuma ya"

rufe fuskar sa suka fice.

"Su na tafe Yana hutawa, saboda haki, a hankali har suka isa masallacin. Ta ce ""Za ka jira ni na je gidan"

"Ummin na dawo?"""

"""Zan koma gida da kaina"""

"""Har ka gane hanya?"""

"Ya ce ""Eh ki gaishe ta"""

"Nana ta ce ""Ai ba daWewa zan yi ba ma"""

Ya shiga Masallaci Nana kuma ta tafi gidan Ummi.

"Su Nana na fita, Barira ta buga banWakin tsakar gida ta ce ""Ke Sajida kashin dan™o ki ke yi ne? Ki na"

"manne a banWaki yau mijin 'yar rainin hankalin nan dai ya fito. Ashe dole ta Soye shi, fari ne tas wannan gashin da na gani, da gaske nasa ne."""

"Sajida ta fito da buta a hannunta ta ce ""Kai haba, ban gama ba ne shi yasa ban fito ba, zogala na ci da ™uli"

"ya ruWa mini ciki"""

"""Aikuwa kin rasa, ba ki gan shi ba. Sai na ga kamar mata na rako, da na tuna Gali, ga ba™i ga ™eya"""

"Sajida ta ce ""Ba gara Gali ba da nawa mijin? Ke Gali na da tsawo, ni nawa ga gajarta ga muni"""

"""Gaskiya Sajida mijinki akwai muni kam, dogon baki kamar dangin burrai"""

"Sajida ta tsuke fuska ta ce ""Ba na son iskanci kuma. Gara shi dai a kan Galin, da ki ka ce ba ya iya tsinana"

"miki komai a shimfiWa. Kalarsa kalar... Kafin ta ™arasa Barira ta ™unduma mata Ashariya, take faWa ya"

"kaure, suka ci wa junan su mutunci tsaf, suka tona wa kan su Asiri. Suka gaji dan kan su, suka ha™ura."

****

Nana ta bawa Ummi labarin barkono da za a kawo mata.

"Ta ce ""Amma Ummi sai dai a kawo miki nan, can Wakinmu babu gurin da zan ajiye a can"""

"""Bakomai a kawo, kuma nan da nan za ki ga an saye shi ba, ai unguwar nan fuskar jama'a ce, idan ka kasa"

"kaya za ka samu alkhairi"""

"Su na tsaka da hira, babu zato babu tsammani sai ga Saleh ya afko cikin gidan. Wata irin mummunar"

"faWuwar gaba ta ziyarci Nana, bayan da ta gan shi babu tsammani. Duk ya ™ara lalacewa."

"Turus ya yi yana kallon Nana, cikin mamaki ya ce ""Nana, dama kina nan?"""

"""Eh"" ta amsa a ta™aice."

"""Nana da yanzu nine mijinki, amma ki ka guje ni"""

"Ummi ta haWe rai ta ce ""Saleh Nana fa matar aure ce, dan haka babu ruwan ka da ita dan Allah"""

"Saleh ya ce ""Dan matar aure ce, kuma shikenan ba za mu yi zumunci ba? Nana kina lafiya? Na ji an ce"

"wani baroroji aka aura miki ko?"""

"Nana ta haWe rai ta tashi ta ce ""Ummi zan tafi, zuba mini Abincin idan kin gama"""

"Ummi ta ce ""Bari na wanke babban flask, kuma idan Islam ta zo ki ba ta kwano na, dan ba zan bar miki"

"ba"""

Ayshacool

"Nana ta ce ""Gaskiya sai kin bar mini, ki zo Wakina, ki Wauki duk abin da ya yi miki. Kuma a ™aramin kwano"

"za ki zuba mini. Sayyid na yi masa girki, ni zan ci wannan"""

"Ummi ta ce ""Hajiya Nana, an sake haWiyar wake kenan, to Allah ya inganta"""

"""Dawa na haWiya ba wake ba"""

"Tsulum Saleh ya sake cewa ""A nan unguwar gidanki yake kenan? Na ji Ummi ta ce Islam na zuwa gidan"

"naki. Da aka ce mijin naki gadi yake yi"""

"A ™ufule Ummi ta ce ""Dan zatin Allah Saleh ka fita, ba da kai muke magana ba, babu ruwan ka da mu."

"Wai har ka manta har ubanmu ka saka a rufe saboda kuWinka, dan rashin kunya kuma, ka zo zaka addabe mu?"""

"Sum-sum Saleh ya fice daga gidan. Ummi ta zubawa Nana tuwon shinkafa da miyar yau™i, har da man"

"shanu, Nana sai haWiye yawu take yi cikin farin ciki, kamar ta dur™usa ta ci a gurin."

"Ummi ta shiga Waki, ta Waukko wa Nana dambun kifi ta ce ""Ungo, jiya na yi shi aka kai mini shago, na"

"Webar miki"""

"Nana ta karSa tana murmushi ganin sa fal a roba, ta ce ""Allah ya yi miki abin da ki ke yi mini na alkhairi"

"na gode sosai"" suka yi sallama Nana ta fita."

"Tana cikin bin wani lungu, ta ji Muryar Saleh na kiran ta. Ta ™ara saurin da take yi, amma ya cimma ta."

"""Nana dan Allah ki saurare ni""."

"Rikicewa ta yi, gani take a kowane lokaci za ta iya ganin Sayyid, ba ta san da wani yaren za ta yi masa"

bayani ba ya fahimta.

"""Nana ki tsaya ki ji mana"""

"""Wallahi zan yi maka ihun kwarto, wace irin jaraba ce wannan ina ruwan ka da ni ne?"" Ganin tana Waga"

"murya, kuma Akuyarsa ta yi kuka a unguwar, ya sanya sum-sum ya koma da baya."

"Tana zumbuWa sauri, ta je gida, ta san yana can yana jiran ta. Kawai ta ci karo da shi a wani lungu, yana"

"zaune a kan wata sokawe, ya jingina da jikin bango, shikaWai ™wal a layin. Sai da ta razana, ta waiwaya"

"bayan ta, cike da tsoron ko Saleh ya biyo ta."

"""Sayyid me ka ke yi a nan kuma, ba ka shiga shiga gida ba?"""

"""Ba zan iya shiga nikaWai ba"" Ta mi™a masa hannu ta ce ""Taso mu tafi"" ya mi™a mata hannunsa. Sai dai"

"tun da ya saka hannunsa a nata, sai da ya kalli fuskar ta."

"Da suka je gidan, dan™am da mata, ana ta hayaniya. Ya rufe fuskarsa Nana ta yi sallama. Gaba Waya suka"

"yi tsit, suka zubo wa su Nana ido, musamman ganin hannunta ri™e da na Sayyid."

"Kawai ta ja hannunsa, suka nufi Wakin su."

"""Nana kun dawo"" Sajida ta yi maganar, tana kokowa da zaninta tana fitowa daga Wakinta, saboda kar su"

wuce ba ta gan su ba.

"""Eh sannun ku"" daga haka ya tura ™ofar ya fara shigewa. Suna shiga Wakin matan suka saka shewa, Waya"

"ta ce ""In dai Namiji ne, yarinya za ta gama wannan iyayin ne"""

"Nana su na shiga Waki Sayyid ya tsare ta da ido ya ce ""Nana ba ki da gaskiya"""

"Gabanta ya faWi cikin tsoro ta ce ""Me na yi?"""

"""Gumi ki ke yi a iya goshin ki, da karan hancin ki. Kuma tafin hannunki ya ya sanyi, zuciyar ki na bugawa"

"da ™arfi kuma da sauri. Kin yi wani abu da ki ke Soye mini ko?"" HaWe rai ta yi ta fara ™o™arin ™wace"

hannunta daga nasa.

"Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce ""Ki daina fushi, ba zan iya barin, duk wani abu na ™i ya tunkaro"

"rayuwata da ke ba, ki daina fushi"""

"""To sai ka din ga zargina da rashin gaskiya"" ta faWa a hasale."

"Ya girgiza kai ya ce ""Ba zargin ki nake yi ba. Na tabattar da wani abu ya faru ne, da ba za ki so na sani ba,"

"idan na sani zamu samu saSani. Kin manta mu ba kamar sauran mutane ba ne. Kuma ina iya jin abin da yake ranki, kin manta ne?"" Ya yi maganar yana murmushi da shafo fuskarta. Dole ta saki murmushi."

"Nana dai ta din ga yi wa Allah godiya, da ba ganta da Saleh ba."

"Nana tana yi wa Allah godiya, ganin yadda jikinsa ya yi kyau. Duk da yana haki bai daina ba, amma yanzu"

"yana cin abinci. Sayyid na matu™ar son zuwa masallaci salla, amma dole yake ha™ura. Saboda da gayya"

"matan gidan suke wata shigar, duk da ba tsayawa kallon su yake yi ba. Ga shi ba ya son kallo, amma yana"

fitowa sai su yi shiru su zura masa ido.

"Ita kanta Nana lamarin gidan ya ishe ta, ba ta ™aunar zaman gidan nan ko kaWan."

"Maman Nana ta aiko mata da barkonon nan, har da awon kayan Abinci, tamkar ta san a halin da take ciki."

"Ummi da kanta, ta je ta Wauki barkonon, domin kuwa Nana daina zuwa gidan Ummi ta gaba Waya saboda"

Saleh.

Ayshacool

"Abu kamar wasa har zuwa wannan lokacin, Sayyid ya kasa gane kansa, abin ya fara damunsa sosai da"

"sosai. Ga shi ya kasa cewa Nana komai a kan hakan. Ita ma kuma ba ta ce masa ba, sabgoginta kawai take yi."

"Tun Yamma Nana, ke ™o™arin shirya duk abin da za su bu™ata, saboda washegari za su tafi Asibiti, kuma"

"sammako take so su yi, saboda su ga likita da wuri."

"Sai dai duk dauriya kawai take yi, wani irin zazzafan zazzaSi ne a jikinta, ta kasa cin abinci. Babu abin da"

"take son ci, sama ds kazar da Habu ya kawo farkon auren su. Ga shi ba ta son yin duk wani abu da zai Waga wa Sayyid Hankali. Ta fuskanci ko saSani suka samu, ™aramar magana sai ta sanya ya fara haki, ya fara nema ya faWi."

"Tana ™ofar Wakinta, tana soya miya, su Barira su na hira, tana yi wa wata ma™wabciyar su kitso. Suke"

"zancen wata mata a bayan layin, wai sai mijinta ya neme ta ya rasa, sai a yi kwanaki ba a ganta ba, sai bayan wani lokaci a tsinto ta a wani gurin, ko a ganta a Waki."

"Barira ta kada baki ta ce ""Amma ta mayar da mijin nan tasono, ™arya take yi gantalinta kawai take tafiya."

"Meye matan auren ba sa yi yanzu?"""

"Sajida ta ce ""A'a Barira, ki daina cewa ™arya ne"""

"""Ke wallahi, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, a gidan uban wa Aljani zai Wauke mutum ya kai shi"

"wani gurin? Ke ni fa da ake cewa ana ganin aljanu, ko su tsorata mutum ban taSa yadda ba, iskanci ne"

"kawai da ™aryar banza ce, ba wani aljan duk 'yan iska ne kawai."

"Nana ta ji wani abu mai zafi ya soki zuciyarta, duk da ba da ita suke ba, kawai ta ™ura wa Barira ido, ko"

™iftawa ba ta yi.

"Tun Barira ba ta ankara ba, har ta lura, take ta ji tamkar an kwarara mata ruwan sanyi a jikinta, sai kuma"

"ta Wan tsorata ta ce ""Nana lafiya kuwa?"""

Ayshercool

08081012143

Ayshacool

"Tun da Jamila ta koma gida, jikinta a sanyaye yake, gani take yi, duk wanda ya ganta ya san abin da ya"

"faru da ita. Mama kuwa baki ya ™i rufuwa, saboda Jamila ta zo da abin Duniya. Kuma kamar yadda ta"

"gaya mata, sarin kaya ta raka Hajiya, babu wani bincike ta yarda da hakan ta amince."

"Ta zo ba ta iya bacci sam, da ta kwanta bacc6, sai ta ga tamkar za ta buWe ido, ta sake ganinta, a wannan"

gurin da suka je da Hajiya Sa'a.

"""Jamila"" Suwaiba ta kira sunanta, ta waiwaya ta kalle ta."

"""Wai ya na ga ki na abu kamar mara gaskiya ne?"""

"Gaban Jamila ya faWi ta ce ""Me na yi na rashin gaskiyar, me ki ka gani?"""

"""To ai gani na yi kin kasa sukuni, ki na ta wani mutsu-mutsu gaki nan dai"""

"""Dan Allah Suwaiba ki ji da abin da yake damun ki, ni babu abin da ya same ni, lafiya ™alau nake """

"Suwaiba ta ce ""To ai shikenan"""

****

"Nana duk sammakon da suka yi, su ne na goma sha Waya, a gurin ganin likita."

"Wajen sha Waya na safe aka zo kan su, Nana suka shiga, sai dai wannan karon wani likitan daban suka"

"samu. Suka gaisa Nana ta yi wa likitan bayanin komai. Tare da ba shi takardun

32 / 126