Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   105 / 126

312K to 315K   out of 377.2K words

na ratso bango su na fitowa, suka nufo shi su na yi masa wani irin ihu. Ya toshe kunnunwansa, sai ga waWanda yake gani a suffar tsuntsaye, sun bayyana su na make masu nufo shin. Wata irin guguwa ta tashi a tsakiyar gurin, aka yi wata irin waliya mai ban tsoro sai ga Giyaz ya keto ta tsakiyar gidan tarihin ya bayyana a gabansa.

Giyaz ya nufo shi, wannan tsuntsayen suka yi kansa, shi kuma Hammad ya tashi ya fice daga gurin, jiri yana Wibarsa, ya san ya fito daga gidan tarihin sai dai bai san ina ya nufa ba, kawai ya buWe ido ya gan shi a sahara tare da Mahmoudu.

Ya yi shiru yana kallonsa, sai ga Giyaz ya kuma bayyana a cikin saharar, cikin tsofaffin kayan nan tamkar auduga saboda tsufa. Ga wani irin sauti da saharar take yi, tamkar iskar za ta taso.

Wata irin dariya Giyaz yake yi mai ban tsoro.

Ya ce "Ban sani ba, ko haWuwa da kai ya sanya na ce na fi kowa sa'a a cikin sararin Duniyar nan, saboda aikin da aka bani a kanka, ya sanya na samu 'yanci. Ni ne Giyaz ibn Jaddul Jinn, Waya daga cikin aljanun da suka yi wa kakanninka hidima, daga arshe aka kore shi daga fadar, saboda wani laifi da ya aikata da bai taka kara ya karya ba. Ya tattara iyalansa ya koma Nigeria da zama, ya cigaba da hayyayafa, can ma aka samu waWanda suka ara cutar da shi. Duk da na shafe tsawon shekaru ashirin a tsare, yau wani boka ya bani 'yanci, sannan ya dama mini aiki a kanka. Dan haka ko zamu mutu tare sai na cika aikin nan da na karSa a kan ka" Hammad bai gama gane me Giyaz yake faWa ba, hankalinsa ya gushe.

Bayan ya sake farfaWowa, ya sake tozali da Habu, sai dai ya manta a inda ya san shi, ko ya taSa ganinsa.

Duk iya oarinsa ya kasa tuna komai game da kansa. Shi dai ya san shi mutum ne, duk wani abu da ya shafi rayuwa yana iya tuna shi, amma duk wani abu da ya shafe shi, ya manta.

Ko da Habu ya yi yinurin mayar da shi Agadez, bin sa kawai yake yi, amma bai san waye shi ba, sai dai su na dosar Agadez Giyaz yake bayyana, yana feso mu wata irin wuta mai ban tsoro, a take sai jikinsa ya ara rikicewa ya ji tamkar zai zauce kansa yana wani irin gigitaccen ciwo, bugun zuciyarsa ya aru, ya din ga jin zafin wutar da Giyaz yake feso masa a jikinsa ta na ona shi. Gaba Waya ya rikicewa Habu. A dole suka bar Agadez suka nufi Nigeria. Su na tafe Hammad yana ganin abubuwan da ya lura abokin tafiyarsa wato Mahmoudu ba ya gani. Duk tambayar da ya yi masa a kan waye shi, ya sunansa ya tuna wani abu game da rayuwarsa amma ya kasa.

Da suka shigo Nigeria, suka samu masauki, bai sake ganin Giyaz ba, sai dai lokaci zuwa lokaci wannan zafin jikin yana tayar masa.

Tun da suka shigo Nigeria, yake mafarkin wata matashiyar budurwa, tare a cikin sahara. Sai ya kwaWaitu da son saninta a zahiri. Idan ya kwanta bacci, ba abin da yake mafarki sai wannan yarinyar. A duk lokacin da ya farka, sai ya din ga jin akwai wani abu mai muhimmanci da yake son haWuwa da shi, duk a duniyar da ya farka, babu wanda ya sani, banda iya mutanen da yake iya gani.

Gurin mai magani na farko da suka fara zuwa da su Habu, wata yarinya ta gifta shi, ya ji wani irin daddaWan sanyi ya ratsa shi, ya din ga jin tamkar ya koma ya bi inda ya ji sanyin nan.

Haka da suka sake haWuwa a gidan Sarkin baka, bai ga fuskarta ba, amma sanyin nan ya ara neman ya zauta shi.

Sai dai ya sha mamaki, da ganin wani zanalelen mutum yana bin ta a baya, sai dai baya iya ganin iyakar tsawon mutumin.

Gaba Waya ya lura, gane-gane da yake yi, shikaWai yake ganin abun sa. Lokaci lokaci ya kan yi mafarki da gidan tarihi, sai dai ya kasa tuna ina ne gurin.

Duk lokacin da ya yi mafarkin yarinyar nan, ya kan tashi da matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ya kan ji dama su dauwwama a cikin baccin nasa ba sai ya farka ba.

Tun da suka fara aiki a gidan Alhaji Zailani, duk lokacin da zai gan shi, yana ganin jini yana bin sa, da wasu anan yara, da wasu mutane su na kuka, amma Alhaji Zailani ba ya ganinsu, sauran mutane ma ba sa ganinsu, sai shikaWai. Hakan ya jefa shi a cikin damuwa, da jin cewa shi wata halittar ne daban, da sauran mutane.

Sai dai babu zato babu tsammani, ya yi ido huWu da ita, da wani yammaci ta fito daga cikin gidan, wannan dogon mutumin yana biye da ita, sai dai ya ga wannan tsohon ne ya dawo matashi, bai bayyana a suffarsa ta tsohon da ya saba fitowa ba.

Sanyin da ya ji ya ratsa shi ya sanya ya rikice, ya udurce a ransa akwai wani abu da bai sani ba, ko yakamata ya sani, kuma wataila wannan da suke tare zai iya gaya masa waye shi, kuma daga ina yake!.



Ayshercool.

08081012143

LITTAFIN KUI NE, VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC

92

Kafin ya yinura ya fito daga Wakin nasu, wanda yake gani Win ya ziro sanda ya hankaWa shi ya faWi sumamme.

Ya fuskanci mutane kowa yana da ahali, uwa, uba, Wan uwa, mata 'ya'ya ya san duk abu ne mai muhimmanci game da rayuwar mutum, amma shi ya kasa tuna komai a kan rayuwarsa.

Su Habu da yake gani a tare da shi, ya san su na yi masa oari amma ba ya jin su sosai da sosai a ransa, yadda za su iya zama wani Sangare na rayuwarsa. Wasu lokutan idan maganar ba ta Wauke ba, ya kan yi musu magana cikin iko da isa, ba tare da jin nauyin hakan ba, shi Mahmoudu sam baya damuwa da hakan, amma su Sule wasu lokutan abin yana sosa musu rai.

Aka ci gaba da tura wa Habu kuWaWe cikin asusunsa.

Yana ta tunanin yadda zai sanar da can gida Agadez cewa, ga fa halin da ake ciki, amma aka din ga tura masa saonni a kan muddin ya kuskura suka koma Agadez, Hammad zai iya rasa rayuwarsa. Ya tura wa Nene saon halin da ake ciki. Ya sanar mata ko an zo an tambayi yana ina ta ce ba ta sani ba kawai. Ya kashe wayarsa ya cire layin ya ajiye, ya samu na Nigeria ya saya ya saka.

Sai bayan kwanaki biyu, aka farga ba a samun lambar Hammad, wayarsa na ajiye a Wakinsa.

Sultan ya ce wa Asal, kar ta kuskura ta gaya wa wani cewar Hammad ya Sace ba a san inda yake ba, ana nan ana bincike a kan nemansa.

Hammad kuwa sai ya kintaci lokacin da Nana za ta zo gidan Alhaji Zailani ko kuma ta tafi, sai ya fito harabar gidan ya zauna, ko kuma ya buWe taga, ya san dole zai ji wannan sanyin. Sai dai duk lokacin da zai ganta, tare da wannan dogon mutumin ne da babu wanda yake ganinsa, sai dai ya fuskanci duk lokacin zai gan shi tare da Nana, ba ya cutar da shi, ko ya yi masa feshin wuta, amma duk lokacin da ya bayyanar masa a suffar tsoho sai ya cutar da shi.

Duk lokacin da zai ga Nana yanayin fuskarta na nuna damuwa, dan haka sai ya din ga jin kamar ya je ya tambaye ta mene ne yake damunta fuskarta babu walwala. Wasu lokutan kuma aisar yake kallo, ita kuma sai ta din ga ganin tamkar yana addabarta da kallo.

Ranar da Alhaji Zailani kuwa ya biyo ta, haka kurum ya din ga jin jikinsa babu daWi, tamkar ya bita cikin gidan. Ko da ya ga Nana ta fito a sukwane kuwa, ya san akwai matsala, sai dai Giyaz ya bayyana a lokacin ya shae Alhaji Zailani.

A hankali ya fara lura da tsuntsayen da suke bayyana idan ya murza zoben hannunsa, ko kuma ya matsa jakar fatar da yake ratayawa a wuyansa.

Ya kan tambayi tsuntsayen, ko sun san waye shi? Suwaye iyayensa? Da kuma 'yan uwansa? Tun da su na magana wasu lokutan. Ba sa ce masa komai sai dai su zana masa taswirar gidan tarihin Agadez a asa. Idan ya kalla ya san gurin amma ya manta a ina ne.

Sannu a hankali ya gane, akwai bambanci a tsakanin Giyaz da aisar ranar da faWa ya haWa su, Giyaz ya yi jifa da aisar sai da ya sha mamaki, ganin tsananin kammanin da ke tsakanin Giyaz da aisar.

A ranar kuma ya fuskanci Nana ma tana gane-ganen abubuwan da ba kowa ne yake gani ba, hakan ya sanya ya ji a jikinsa ita daidai take da rayuwarsa, ita ce suke iri Waya. Amma ta yaya? Tun da yana jin Habu da Sule su na zancen Nigeria da Niger, shi da su irin su Waya, ga yarukan da yake iya yi, wanda alamu suka nuna inda suke ba duka yaren da suke yi mutanen gurin suke ji ba.

angaren aisar ma, tun da ya ga Giyaz a tare da Sayyid ya rikice, domin bai taSa tsammanin Giyaz zai dawo ba.

Wataran bayan shafe kwanki biyar Sayyid yana fama da wannan zafin jikin da yake rikita shi. Ga babu magana abinci ma baya iya ci. Ya wayi gari ya Wan samu saui. Har ya ci abinci ya shiga ya yi wanka da la'asar. Kawai ya ji wannan sanyin yana kusanto shi.

Babu tsammani ya ji muryarta, ta yi sallama sai dai ya yi shiru yana tunanin ko tsabar saka ta a ransa ne ya sanya ya ji muryarta. Yana tsaye cak da matajin hannunsa, ya ji muryar yaro a Wakin bai ga yaro a Wakin ba, kawai ya ga ta faWo Wakin.

Su na haWa ido ya ga ta yanke jiki ta faWi. Ya ga aisar ya bayyana ya tsaya a kanta yana huci, shi dai ya tsaya yana kallonsa dan bai san abin da ya yi mata ba. Ya gama ya sanya kayansa Nana ta kwance, amma sanyin da yake tattare da ita na saukar masa da wata irin nutsuwa da daidaita zafin jikinsa.

Tun daga lokacin aka fara dambarwar nan, har ta kai ga Waura masa aure da Nana, ya din ga jin amincewa da auren, shi ne hukunci mafi daWi da zai yankewa wannan rayuwar tasa da yake yi mara kan gado. Ba ya jin ko War sanya Habu ya yi masa duk wani abu da yake buata.

Bayan aurensa da Nana a jikinsa yake jin, samun nutsuwa a tattare da wannan duniyar da kuma kwanciyar hankali, idan ya matsa ya tuna wani abu da ya shafe shi game da ainihin waye shi, sai ya ji damuwa da bain ciki ya mamaye shi.

Habu kuma bai taSa gangancin gaya masa waye shi ba, kawai ya yale shi a kan duk lokacin da ya tuna wani abin ya sanar da shi.

Idan ya kwanta bacci baya mafarkin kowa, sai wannan dai gidan tarihin da yake gani, sai kuma ya din ga ganin wasu abubuwan da suka faru a arnukan baya a wannan gidan sarautar, har ma da mutanen da suka yi rayuwa a gidan. Wasu lokutan har a zahiri yana ganinsa a gidan tarihin amma bai taSa tuna a ina ya san gidan ba, sai dai bai manta abin da ya faru na arshe a gidan ba, na firfitowar wannan halittun daga Wakunan tarihin. Sai dai yana yawan ganin gidan, sakamakon aljanun da suke tattare da zobensa da kuma jakar fatarsa, ainihinsu mazauna gidan ne, kuma su ma su kan yi kewar gidan, tun da duk inda yake ya murza zoben sai sun zo. Lokacin da aka yi aurensu, aka kai Nana wannan aljanun na zobensa ne suka din ga rangaWa guWa.

A duk lokacin da yake son ya yi wasa da hankalin Nana, sai ya murza zoben hannunsa, idan ya danne jijiyar da ke wajen eyarta, sai ta yi bacci. Haka zalika yadda yake ganin gidan tarihin nan, haka ita ma take ganinsa.

Da wannan aljanun yake amfani ya burkita mata lissafi, ya yi abu da ita a zahiri amma ta din ga ganin kamar a mafarki ne. Haka zalika Giyaz da yake taka rawa gurin addaba musu, tare da cutar da su, da abubuwa na ban tsoro. arfin ibadar Nana ne ya sanya suke samun sassauci a wasu abubuwan. Nana ba ta taSa sanin amfanin zoben nan na hannunsa ba. Ya Wauki zoben ya ba wa Nana kyautarsa, saboda abin da yake ji a zuciyarsa game da ita. Saboda a jikinsa yake jin zoben na da muhimmancin gaske, dan haka ya Wauka ya bata.

aisar ya yi ta gargaWin Nana a kan Sayyid, saboda yana jiye mata tsoron Giyaz, da kuma kar Aljanun da yake ta'amalli da su, su cutar da ita.

Duk da yadda aisar yake jin haushin Sayyid, da yadda Nana ta saki jiki da shi suke rayuwa, amma ya taka muhimmiyar rawa gurin ara jirkita hankalin Nana, da sauaawa Sayyid Win wasu abubuwan. A sakamakon yarjejeniya da suka yi da hadiman jikin zoben Sayyid, a kan za su ba shi wasu labarurruka da suka faru a wasu zamani da suka shuWe, tun kafin a haife shi a cikin Duniya, bisa yarjejeniyar idan suka cutar da Nana ba za su taSa zama lafiya ba.

Duk da tsamin alaar da ke tsakanin Giyaz da aisar, amma yana jin daWin ganin Wan nasa, bayan shafe shekaru masu yawa bai gan shi ba. Ya na tsananta cutar da Nana da Sayyid, saboda ya muzgunawa aisar.

Ko lokacin da ya bi Nana, har ya duba Baba, a zahiri ya ga ullin da aisar ya yi a afar Baban, kuma da aljanun jikin zobensa, ya warware ullin.

Rayuwarsa da Nana yana saka shi jin wata nutsuwa a tattare da shi, ga alaar Giyaz da ta aisar da ta shafi rayuwarsa da Nana. Sau Waya ya yi mafarkin Sultan, ya gan shi cikin damuwa da tashin hankali, ya farka a rikice da sunansa a bakinsa amma bai iya tuna ko waye shi ba.

Can Agadez kuwa, bayan Satan Hammad, aka ankara da Sacewar Mahmoudu, hakan ya sanya Sultan cewa duk inda Hammad yake yana tare da Mahmoudu. Sultan ba ya iya cin abinci, ba ya isasshen bacci saboda tashin hankalin rashin sanin inda Hammad yake. Ga shi Soyewa suke ta yi, duk da yadda Tafawa da muarrabansa ke ta oarin bin diddigin gano abin da Sultan yake Soyewa.

Lambar Mahmoudu da ta i shiga, sai aka yi ta tracking lambar Mahmoudu, aka gano last inda ya yi amfani da ita a Nigeria ne. Aka din ga bin diddigi har gidan Alhaji Zailani, aka tafi da motoci gaba Waya aka kwaso Buzayen layin kaf. Sai da aka zo Agadez, sannan aka tantance su bayan da aka fahimci su ba su san komai ba, hasali ma wanda ake maganar a kansa ba su san waye shi ba. Aka Wauke Mahmoudu daga cikinsu, aka din ga tuhumar sa, ina Hammad yake, amma ya i magana saboda yana jin tsoron gargaWin da aka din ga yi masa, a kan muddin Hammad ya dawo Agadez mutuwa zai yi.

Mahmoudu ya sha azaba kala-kala, tamkar ba zai yi rai ba, sai da ya ji azaba sannan ya gaya musu cewar Hammad yana Nigeria. Aka saka shi a gaba zuwa Nigeria, aka taho da Hammad. Sai dai tunda aka taho da shi, sai wawalwar ta sak burkicewa, tunaninsa ya rikice.

Bai gama tantance waye shi ba, hankalinsa ya dawo ba, sai da aka fitar da shi Faransa. Dama wawalwar a hargitse take, baya tantance komai, sai dai sannu a hankali tunaninsa na rayuwar da ya yi a Nigeria, ya shafe gaba Waya.

Sai ainihin tunaninsa na waye shi ya dawo masa. Ganin ya dawo hayyacinsa ya daina iface-ifacen da yake yi, ya nuna ya gane Sultan da Matawalle, suka yi farin ciki sosai, suka tambaye shi ko ya tuna abin da ya faru da yaje Nigeria, sai ya rikice yake tambayar me ya kai shi Nigeria. Daga nan kawai sai suka Soye masa, suka ce jinya kawai ya yi mai tsawo a faransa. Likitoci suka din ga ba shi kulawa a kan matsalar zuciya da yake fama.

Can a Agadez kuma, aka ci gaba da azabtar da Mahmoud a kan lallai sai ya faWi dalilin da ya sanya, ya sace Hammad ya tafi da shi Nigeria.

Ga Tafawa ya matsa a kan lallai sai an faWi inda Hammad yake, tun da an doshi shekara biyu, babu wanda ya gan shi, ko kuma a ba su dama su je su duba shi, su gan shi ido da ido su tabattar yana raye babu wani abu da ya same shi.

Sai dai Hammad ya kasa yarda da cewa, tsawon wannan lokacin, jinya yake yi. Tiryan-tiryan abin da ya faru na arshe daga gidansa, zuwa gidan tarihi daga nan kuma sai ya rikice ya kasa tuna komai.

Ya ce wa Sultan lallai a kawo masa Mahmoudu, Matawalle ya ce "Ko ka tuna wani abu ne? Me Mahmoudun zai yi maka?"



Hammad ya ce "Babu komai, ni ba na jin daWin zama nikaWai ne, na saba duk inda nake mu na tare, ni dai a kawo mini shi"



Matawalle ya ce "Ka yi hauri, Likitoci sun ce ba a buatar kowa ya zo inda ka ke ne"



Ya yi shiru yana tunanin, ina Asal da ko sau Waya ba ta zo ba ita ma. Sai dai a jikinsa ya din ga jin kewar wani abu mai muhimmanci a tare da shi, kamar yana jin matsananciyar ishirwa.



Sultan kuwa ya sanar da Asal batun ganin Hammad, amma ya ce mata rashin lafiya ce ta kama shi a Niemey, aka kai shi wani Asibiti a can, daga baya a ka kai shi faransa. Duk da ta yi mamakin yadda za a ce rashin lafiya ta kama mutum, a kai shi Asibiti amma ba a nemi ahalinsa an sanar da su ba tsawon shekaru.

Sai dai hakan ma sai da ta gaya wa Tafawa. Ya ruWe ya rikice dan ya so a ce wani mummunan abin ne ya samu Hammad.

Tun da Asal ta ji labarin Hammad zai iya dawowa a kowane

105 / 126