Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   106 / 126

315K to 318K   out of 377.2K words

lokaci, take shirin karSar sa, dan ba ™aramin kewarsa ta yi ba. Dan ta shiga damuwa da tashin hankalin da sai da suka samun matsala da Tafawa bayan Sacewar Hammad.

Tun da Sultan ya ce a kowane lokaci zai iya dawowa, ta sanya aka yi gyaran gidan sosai. Sannan ta fara lissafin canza kuyangin da za su din ga yi masa hidima. Ga Tafawa ya yi mata alwashin idan ba za ta ci gaba da ba shi haWin kai ba, zai nemi wani ya yi masa, ko da kuwa ta kama a salwantar da ran Hammad Win ne baki Waya.

Sai dai duk da tunaninsa na Agadez ya dawo, bai fasa fama da wannan matsanancin zafin jikin ba, da yake jin tamkar ana ™ona shi ba. Sai dai ya rage tashi a kai a kai.

HaWuwar Asal da Nana, ya zame wa Asal tamkar tsintar dami a kala, ta ga idan ta kawo Nana gidan sauratar Agdez, kanta a tukunya yake game da sha'anin sarauta, ga girki ta iya, saboda Hammad na son daddaWan Abinci, ga kuma Nana ba™a ce 'yar Nigeria, babu yadda za a yi ta Wauki hankalin Hammad, saboda ba™ar mace ta haramta a gare su, bisa ga Al'adar Agadez. Sai dai abin da Asal ba ta sani ba shi ne; a rashin sani kaza ta kwana a kan dami.



AREWABOOKS



Tun da Hammad ya sauka a filin tashi da sauukar jirage, gabansaa yake faWuwa, ya kuma rasa dalilin hakan. Jin sa yake yi tamkar yana daf da maganin ™ishirwar da ta addabe shi.

Bayan Nana ta yi amfani da ™arfi, gurin tursasa wa Nana zuwa Agadez, ta sanya Nana cikin jerin waWanda za su yi girkin karSar Imam Hammad.

Gabba Waya gida ya Wauka Hammad zai dawo, bayan shafe dogon lokaci yana jinya. Su kansu wasu daga cikin Imam Imam Win, ba haka su ka so ba duk da abin jita-jita ake ta yi, Sultan bai tabattar da hakan ba, kuma a daren za a yi babban taro tare da 'yan majalisar Sarki, da kuma su Imam na shekara da ake gabatarwa.

Sai dai babu tsammani, su ka ga Hammad ya bayyana a gurin. Tun da ya shiga gurin, ya ji wani irin daddaWan sanyi ya ratsa shi, da kowace irin AC aka kunna, sanyin baya wadatar da shi har cikin ™ashinsa ya ji ya gamsar da shi.

Ya ji wani irin jiri na neman ya Webe shi, amm ya daidaita nutsuwarsa, ya sunkuyar da kansa ™asa ya rabe ya je ya zauna.

Bai Wago kansa ba, ya ji Matawalle na tambayar me ya kawo wannan nan gurin. Aka sanar masa tana cikin masu girki ne.

Bai dai Wago ba sai murmushi da yake yi, saboda barka da zuwa da ake ta yi masa.

Sai dai ™irjinsa ya tsananta bugawa, da aka ce ta zo ta WanWana Abincin, ta nufo inda suke. Ya kasa jurewa ya Waga kansa, sai ya ji kamar sanyin da yake ji yana ™aruwa. Wani abu ya ji mara daWi a ™irjinsa ganin yadda ta Waura rigar girki a kan kayanta, ana ganin shape Win kyakykyawar surar da Allah ya yi mata ta bayyana. Kalar fatarta ya Wauki hanklinsa, tsohon muradinsa na son ba™ar mace ya motsa a zuciyarsa. A kallo Wayan da ya yi mata duk ya nazarci wannan abubuwan ya sunkuyar da kansa. Amma ya nemi ya kasa jure bugun da zuciyarsa take yi babu ™a™™autawa.

Bai ji daWin yadda Matawalle ya saka a ka fita da Nana ba, saboda yadda duk ta rikice a gurin. Sai dai ya yi ta mamakin yadda aka ta shiga cikin masu girki, alhalin tana ba™ar fata 'yar Nigeria.

Da suka tashi daga taron nan kuwa, da Asal ta gan shi, wani irin tsalle ta yi ta ma™al™ale shi, tana murna cikin matsanancin farin ciki har da hawayenta. Ya Wago ta daga jikinsa yana murmushi yana kallon idanunta, da son gano ainihin abin da yake gani a idanun nata, dan abin da ya faru daren da ya bar Agadez fes yake dawo masa.

Ya tsura wa idanun Asal ido, ya ce "Kin yi kewata har haka?"



"Imam, kusan shekara biyu ba ma tare ka ce ko na yi kewar ka? tu me manques(Na yi kewar ka sosai) Ta yi maganar idanunta Wauke da hawaye. Bai bari zuciyarsa ta ci gaba da raya masa abin da take raya masa ba. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "tu me manques. Na yi kewar ki sosai cherié. Ina fatan kina lafiya babu abin da ya same ki?"



"Ba abin da ya same ni, sai damuwar rashin sanin inda ka ke, ina ka tafi aka neme ka aka rasa haka, ka tayar mini da hankali na shiga damuwa sosai"

Ya yi shiru yana mamaki, Sultan ya ce masa faWuwa ya yi, ya shiga coma na tsawon lokaci, yanzu kuma tana faWin ya tafi ba a san inda yake ba, ga abin da ya faru na ™arshe kan barinsa Agadez yana dawo masa. Sai ya kawar da tunanin komai daga cikin zuciyarsa.

Duk rawar kan da Asal take yi, da murnar dawowarsa gaba Waya hankalinsa ba a kan hakan yake ba. Jin sa yake yi ba daidai ba. Ya yi iya ™o™arinsa ya sarrafa tunaninsa da nutsuwarsa gurin ba ta dukkanin kulawa da kuma lokacinsa, amma hankalinsa na kan abin da shi kansa bai san mene ne ba.

Da dare ya yi kuwa, ya riga Asal kwanciya dan kar ma ta nemi wani abu a tare da shi, saboda fatansa ya gano takamaiman mene ne yake damunsa. Sannan ya yi mamaki rashin ganin Mahmoudu da bai yi ba.

Yana kwanciya bacci surar Nana ta bijiro masa, a ™asan zuciyarsa ya ji bai ji daWin fitowarta a haka ba. Da sauri ya yi istigfari dan gudun kar shaiWan ne yake ™ara ™awata masa ita. Amma duk da haka bai daina ganin ta a idonsa ba, ds yadda ta zuba masa ido duk ta rikice ba.

Ya yin™ura ya tashi zaune, ya ga Asal ta yi bacci, ya yi shiru yana tunanin wa zai tambaya wace ce ita.

Ya gaji da zancen zucin ya matsa kusa da Asal ya kwanta tare da rungume ta a jikinsa. Sai ™amshin turare take yi da alama ta shiryawa dawowarsa sosai.



Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal Win ta canza gaba Waya, tare da yi musu addu'ar samun rabo na alkhairi. Kamar ya tashe ta, sai kuma ya ™yale ta kawai ya lumshe idanunsa yana addu'a a ™asan zuciyarsa yana jiran bacci ya Wauke shi.

Yana tsaye a cikin sahara, ya ri™e akalar ra™uminsa, iskar sahara sai kaWawa take yi, babbar rigar jikinsa na Wagawa, ta cikin iskar yake jiyo sheshshe™ar kukan mace tana faWin "Sayyid" ya waiwaya bai ga kowa ba. ShikaWai ne a cikin saharar, sai dai bai daina jin sheshshe™ar kukan ba.

A hankali ya buWe idanunsa, wannan shi ne karo na bai san adadi ba, yana wannan mafarkin tun da ya buWe ido a faransa. Jin kiran sallar Asuba ya sanya ya tashi ya tafi salla.

Ranar farko da ya sake cin abinci bayan wanda ya ci da ya dawo, sai ya ji kamar ya san WanWanon abincin, amma ya manta a ina ya san shi.

Ranar da ya sake ganin Nana, Asal ta kira ta a kan ta zabga yaji a abinci ya kasa ci, sai da zuciyarsa ta kusa tsayawa, ya din ga jin kamar abu malaman haka ya taSa faruwa, amma bai san a ina ba. Jikinsa ya din ga tsuma sakamakon jin sanyin da ya fara yi, ga kallon da take yi masa da ya sake burkita shi. Ya din ga matsa ™wa™walwarsa, ko za ta ba shi wani abu, amma ya ji ya fara jin jiri.

Bai tsaya kammala karin kumallon ba, ya tashi ya fita ya je ya samu Sultan, baya ya kammala zaman Majalissa, yake ce masa shi fa haryanzu bai ga Mahmoudu ba. Sultan ya ce masa ya yi tafiya ne, amma zai dawo. Haka kurum ya ji bai yadda da hakan ba, amma bai kuma cewa komai ba.

Cikin hikima ya tambayi Asal inda ta samo Nana, ta sanar masa da a gidan Abincinsa na MaraWi take aiki, ganin ta iya girki ya sanya ta kawo ta gidan, domin ta din ga dafa masa abinci.

Sai dai a kullum abubuwan da Nana take yi, su na ™ara dagula masa lissafi nesa ba kusa ba.

Matsin lamba da Hammad ya yi ya sanya aka sako Mahmoudu, kuma Matawalle ya jaddada masa lallai kar ya kuskura ya gaya wa Hammad komai a kan zuwan da suka yi Nigeria, kuma kar ya gaya masa Waure shi suka yi.

Hammad bakinsa ya ™i rufuwa, bayan ganin Mahmoudu da ya yi, saboda yadda yake jin Mahmoud a rayuwarsa ba ya jin Zahradeen yayansa da suke uba Waya haka. Sai ya yi ta yin™urin ya yi wa Mahmoudu bayanin abubuwan ban mamakin da yake gani game da Nana, amma sai ya kasa. Babbn abin da ya sake Waure masa kai da ita, shi ne lokacin da ya hana ta cin ayaba. Ta karSa ta ci, a lokacin ya ga ˜isar a tare da ita. Ganin ˜aisar ya ™ara hargitsa masa lissafi, saboda yana ganinsa hoton suffar Giyaz ya faWo masa, amma ya manta a ina ma ya san fuskokin. Sai daga baya sannu a hankali ya tuna yadda Giyaz y fito masa a gidan tarihi, amma wanda ya gani tare da Nana bai kai wancan tsufa ba.



Gefe guda kuma ˜aisar da Giyaz su na ta dambarwa, Giyaz ya ce ba zai taSa rabuwa da Nana ba, ya mantar da Hammad wace ce Nana da duk wata rayuwa da suka yi a Nigeria saboda ta ci gaba da shan wahala.

Bokan da ya sanya Giyaz aikin Satar da Hammad kuwa, hankalinsa ya dugunzuma bayan da shi ma wands ya ba shi aikin, ya matsa masa lamba da masifar ya aka yi Hammad ya dawo Agadez bayan an ce har abada shi da Agadez.



"Ya kai Giyaz, ina al™awarin da muka yi da kai? Na baka 'yanci bisa sharaWin za ka yi mini aiki, amma kwatsam sai na ga wanda na baka aikin a kansa ya dawo Agadez"



Giyaz ya ce "A cikin aikin naka wanne ne ban yi ba? Na mantar da shi waye shi, na mantar da shi, ya bar Agadez ya yi nesa da ita, kuma ya yi. Ni da kai ba na tunanin akwai wanda yake bin wani bashi, na cika sharuWWanka kaf da muka yi yarjejeniya a kai"



Bokan ya ce "Amma ai ga shi ya dawo Agadez cikin ™oshin lafiya a hayyacinsa"



"Eh, ai ba mu yi da kai zai bar Agadez har abada ba, na kuma yi iya abin da muka yi sharaWi a kai"



"Kar ka fusata ni, ka sanya na sake kama ka na rufe ka, ni bami yi haka da kai ba"



Giyaz ya ce "˜arya ne, ni dai ka kama ni ka sake kulle ni, ba za ka iya wannan ba. Kuma duk abu dole na zauna inda zan iya ganin Wa na. Kuma ina nan ina ci gaba da gudanar da aikin da ka bani bisa yarjejeniya, tun da haryanzu ina nan tare da shi ban bar shi ba"



Bokan ya ce "Waye Wan naka, kuma a ina yake?"



"Babu wannan a cikin yarjejeniyar aikina da kai, ka bar zancen a yadda na bar shi kawai"

Bokan nan ya san faWa da Giyaz ba abu ne da zai haifar musu da Wa mai ido ba, sai dai dawowar Hammad mayar musu da aiki baya ne.

Mahmoudu tunanin Nana ya addabe shi, tare da ganin rashin dacewar abin da ya faru. Ga shi alamu sun nuna ™iri-™iri Hammad bai san ya je ya yi wata rayuwa a Nigeria ba.

Ya kuma san muddin ya ce zai je Nigeria sai Hammad ya bi ba'asi, kuma kwana Waya ko biyu ya yi kaWan ya je ya nemi Nana, balle ya yi masa ™aryar kasuwanci zai je. Ya sha tambayar Mahmoudu a kan ko akwai wani abu dayake damunsa, saboda yanayinsa ya nuna akwai damuwa. Amma ya kan ce masa babu komai.

Hammad ya ce wa Asal baya bu™atar sake ganin Nana. Sai murna take saboda ta zata munin Nana yake gani, shi kuwa mafita yake nema, daga burkicewar da yake yi a duk lokacin da ya ganta. Sai dai kuma kwana biyu da ya daina ganinta sai ya shiga damuwa, ya zamana duk ranar da bai ganta ba, sai ya ji shi tamkar a kurku, wunin ranar bai yi masa daWi ba sam.

Yana zaune a Wakinsa, yake kallon yatsunsa babu zobe guda Waya, wanda shi ya fi kowanne muhimmanci. Shi dai Matawalle ya ce masa duk wanda ya tambayi zoben ya ce an kai zoben gyara ya samu matsala. Ya kalli tagullar hannunsa, ya din ga murza ta a hankali yana zancen zuci. Saboda gaba Waya a rikice yake, kasancewar Nana ta kai masa abinci tana ™amshin turarensa da yake amfani da shi. Shi dai ya san babu wanda ya bawa turaren, kuma mai aiki kamar Nana ba za ta iya sayen turaren ba, kuma babu yadda za a yi a ce satar turaren ta yi har ta samu ™warin gwiwar shafawa. Yadda take yi masa wasu abubuwan kai tsaye wasu lokutan abin yana ba shi mamaki sosai da sosai.

Ganin ya yi hasken wutar Wakin tana Waukewa tana kawowa, daga baya ta tsaya, sai ga wani Wan gajeren abu a ya bayyana da tsawonsa bai fi 'yar tsana ba, kansa duk wasu ™ayoyi.

Hammad ya zuba wa abin ido, ganin yana motsi.

"Tuba nake shugabana na tsorata ka, ni ne aljanin da aka wakilta hidima ga duk wanda ya Wauke da wannan tagullar, tun da ka ke ba ka taSa nema na ba sai yanzu, me ka ke bu™ata?"



Hammad ya ce "Waye kai?"



"Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar"



Hammad ya zuba ido sosai, ya ga Wan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ™asa yake ja.



Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba"



Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban"



"To ina zoben nawa yake?"



"Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matu™ar ™auna a matsayin tukuicin soyayya"



Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni Win?



"˜warai ya shugabana"



"To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?"



Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huWu, ala™a huWu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huWu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma ala™ar mata da miji da kuma uba da Wa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya Sace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme.

Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ™araso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana wa™a. Daga nesa kaWan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.



*_ina zana ganka_*

*_sa™o zana baka*_

*Hotona da naka*_

*_Ko ina zana bika*_

*_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_

*_Zuciyata na baka duk masu ™in ka su daina shakka*_

*_Rayuwata na baka_*

*_Ni ta ya zan guje ka*_

*_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_



Gaba Waya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ™wa™walwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?"

Ya daWe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina wa™ar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare"

Ya jinjina mata kai.



"Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi.



Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana.

Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar MaraWi, zai kai wa Nene ziyara ne.

Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi ha™uri.

Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta ™i gaya masa ha™i™anin gaskiyar waye Muhsin.

Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma.

Kwanansa Waya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya Wauki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru.

Hammad kuwa ya lallaSa Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin ba™in abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaWin kallonta.

Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya ™i ce masa komai.

"Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka ™i gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar".

Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?"



"Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faWi amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?"

"Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taSa ji game da wani mutum ba"

Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?"



"Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce"



"Ka na da mata fa a Nigeriar nan"



Hammad ya kalle shi yana jiran ™arin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan ra™uma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka

106 / 126