Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   116 / 126

345K to 348K   out of 377.2K words

wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk oarin ku Ammi idan Allah bai addara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaWai ne Wan uwana namiji...

"Tashi ka bani guri, kafin bain ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da una ya tashi ya bar sashen ta.



Murmushin fuskar Nana ya kasa Soyuwa, aisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata"



"aisar"



"Na'am"



"Ina yi maka kyakykywan fatan alkhairi na har abada "

Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Har kin mantan Allah ya isan da ki ka yi mini a baya"

Ta katse shi ta hanyar cewa "Duk wanda yake rinjayar da laifukan mutane, sama da alkhairinsu, to zai zama mara adalci"



Ya ce "To ai ni ba mutum bane"



Ta yi dariya ta ce "Ni a gurina kai mutum ne. Alkhairinka ya shafe laifukan ka aisar. Gaba Waya ji nake yi kamar ba ni ba, zan rayu da Hammad Wina, da kuma Muhsin Allah abin godiya kamar komai ba zai wuce ba"



Ya zauna yana faWin "Babu abin da ba ya wucewa sai ikon Allah"



Za ta yi magana ta farka daga baccin da ya Wan Wauke ta.

Da Sayyid ta fara tozali ya ce "Amarya"

"Ango" Ta amasa masa tana murmushi.

"Nene ta ce sai na mayar mata da ke, wai shirya ki za a yi, ba dai yadda zan yi ne, na fi son ta bar mini ke in din ga jin Wuminki. Ke ba kya buatar duk wani gyara, a gyarenki Allah ya yi ki"



Nana ta tashi zaune ta ce "Allah ya shirya mini kai, Nenen zaka gaya wa haka ko? Ni sonake ma na gana da Wan uwana na yi kewarsa"



Hammad ya numfasa ya ce "Kin san Sultan sun samu matsala da Imam Zahradeen, ina ta girgiza miki kai Wazu, ki bari sannu a hankali zai saukko zan san yadda zan yi na shirya su. Amma da farko ji na yi kamar ba zan yafe masa ba. Amma na duba girman abubuwan da ya yi na alkhairi a gare ni. Kuma ni duk mutumin da zai yi abin da zai kyautata miki to ni ya yi wa, dan haka na ji zan mayar da komai ba komai ba. Kin san wani abu ma vie"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Wallahi idan na kalle ki, na kalli Muhsin, sai in ji zan iya yafe wa kowa ma, Duniyar guda nawa take? Allah ya yi mini tagomashi da abin da na san ba dabara ta ba ce ba. Ba zan fasa gode wa Allah ba"

Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya Sayyid. Amma ina da wani roo a gare ka; kamar yadda ku ka soke al'adar haramta auratayya tsakaninku da baaen fata, ina roon ku haramta duk wani nau'i na ta'amalli da Aljanu da shaiWanu"

Ta Wan yi shiru tana satar kallonsa.

Ya ce "Ina jinki"

Ta ci gaba da faWin "Ta'amalli da aljanu, da hana iliminku na addini tasiri a cikin rayuwarku, haWi da rio da munanan al'adu su suka ara ta'azzara wasu abubuwan. Ga dai zobunanka masu Wauke da hadiman aljanu, amma hakan bai hana a cutar da kai ba, cuta mai munin gaske. Su ba su baka kariya ba, su ba su hana a cutar da kai ba. Babu wata halitta da zata baka kariya ko ta hana faruwar wasu abubuwan a rayuwarka. Sai dai duk da wannan abin, ina girmama rio da ibadarka mussaman salla. Kai ma'abocin salla ne. Dan Allah Imam ka ara oari gurin ganin an kakkaSe al'adar amfani da aljanu a cikin harkar mulki. Ga saSon Allah, ga gadar wa zuriya masifa da tashin hankali. Ni da kai Win nan mislai ne akan kanmu, ba zamu yi fatan ire-iren zuriyarmu su gaji wannan bala'in da muka shiga ba. Dan Allah Hammad ka yi oari a yi yai da ta'amalli da su, da kuma duk wani abu da ya shafe su. A Wayanta Allah, a dogara da shi duk ba kwa buatar wannan abubuwan muddin kun rie Allah ".

Ya numfasa ya ce "Maganganunki duk gaskiya ne Ma vie, kuma tuntuni na fara oarin neman maraba da su, ni kaina na daWe ba na son harkar da muke yi da su, amma in sha Allah zan ara arfafa hakan, har abada za a daina amfani da duk wani nau'i na gurSatacciyar al'ada a Agadez"

Nana ta rungumo shi ta ce "Yauwwa farincikina, Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi, ya ara kare mini kai daga dukkanin wani sharrin. Allah ya ara Waukaka mini darajarka zuwa inda zato bai taSa zato ba. Allah ya yi maka kyakykywan tsari daga sharrin duk wani abin i komai anantarsa."

Ya tsurawa Nana ido, sannan ya ce "Ta yaya ake so na iya rayuwa babu wannan halittar? Halittar da harshenta kullum cikin yi mini addu'a da fatan Alkhairi take.

Mai Wauke da zuciyar da kullum take oarin kusantar da ni ga Allah, baiwar Allah da kullum burinta ta sadaukar Saboda da komai saboda ni. In sha Allah mutuwa ce zata raba ni da ke rayuwata. Allah ya yi miki tukuci da gidan aljanna. Ina aunrki Asma'u." Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, da ba ta san dalilin canzawarsu zuwa ja ba.



"Nima ina aunarka mijina, irin sosai da sosai, ban san ya zan misalta maka ba"



"Ba sai kin misalita mini ba, na gani a zahiri" Ta sunkuyar da kanta tana Wan murmushi.

Ya ce "Yanzu me za ki shirya mana, na shirin bikin? Sultan ya ce sai an yi biki sosai a Agadez, me za ki shirya mana? Me da me ki ke so?"

Ta girgiza kai ta ce "Kai kaWai kawai nake so, kai kaWai ka ishi Nana komai"

Ya yi dariya ya ce "Zan kawo miki Imrana da Muhsin, har ma da Nene anjima su Webe miki kewa"

Nana ta ce "Amma kuwa da ka kyauta, na gode sosai da sosai"

Ya dungure mata kai yana murmushi.



*****

Alhaji Fatuhu kuwa bacci ne ya gagare shi, kamar yadda dariya ta gagari kare, ya gagara yin bacci.

Idan ya samu baccin ya fara Waukarsa, kawai sai ya ga Hajiya Sa'a, tana kuka tana sake maimaita abin da ta faWa da suka je. Duk yadda ya din ga addu'a, da oarin kawar da tunanin daga zuciyarsa, amma abu ya faskara.

Sai dai ya danne ya ci gaba da addu'a.

Sai kuma doctor Sharif ya faWo masa, da shi ma yake cewa ya yafe masa, to ya yafe masa da ya yi masa me? Gaba Waya sai al'ajabi, ya hana shi yin farincikin dawowar kayansa. Ga shi ya zo gaya wa Alhaji Zailani, tun da dama shi ne abokin kasuwancinsa, amma ya tuna yadda Fadila ta gargaWe shi a kan haka.



*****



Sagir kuwa tun da yaje Abuja gidansu Yusra, hankalinsa ya ara tashi. Jaririn da ya gani da shi yake kamanni, ya yarda jaririn nan Wansa ne, amma babu yadda ba a yi da Yusra ta yi magana ba, ta faWi a ina ta haWu da Shukura ba.

Sai dai ana ta ba wa jaririn madara. Sagir ya ce wa mamanta "Ina ga, zan koma Kano na samu iyayen Shukura na sanar da su cewar, an ga jaririn Shukura"

Maman ta ce "A'a kar ka faWa tukuna, kar a zargi Yusra da wani abu, a ci gaba da addu'a dai da bincike, haryanzu Yusra bata cikin nutsuwarta.

Haka ya din ga sintiri tsakanin Abuja da Kano, ga shi ya kasa gaya wa kowa, saboda shi kansa ya san ayar tambaya za a saka wa Yusra. Sai dai al'amuran Yusran su na ba shi tsoro shi kansa, banda yana sonta kuma ya san halin da ta shiga, lokacin da Shukura ta Sata, da babu abin da zai hana ya ce da sanya hannun Yusra a lamarin Satan Shukura, idan ba haka ba a ina ta samu jaririnta?



****



Labari ya cika ciki da wajen Agadez, kan cewar Hammad yana da Wa, ya auri 'yar Nigeria, haka zalika an soke Al'adar hana auren baar fata.

Wasu daga cikin al'ummar garin hakan yayi musu daWi, mussaman baae, da suka din ga jin tamkar su zuba ruwa a asa su sha.



angaren fararen buzayen kuwa, gani suke yi tamkar rage musu kima ne, da kuma rage karsashin Masarautar.

Cikin marasa gaskiya a fadar Sultan kuwa, cikinsu ya Wuri ruwa cike da tashin hankali, saboda tsoron hukuncin da ka iya biyo bayan tonuwar asirinsu. Ga shi Sultan ya i nuna musu ya san su ne, kuma tun daga ranar da aka kawo bokan nan fadar Sultan, ba a sake zaman majalissar ba.

WaWanda ba su san Nana ba, suka din ga sintirin gidan Sultan, su na son ga Nana, amma Nana na kauwwame a sashin Sultan.



Tuni labari ya ishe Asal, wanda hakan ya sake gigitata, tamkar za ta yi hauka. Wani irin so da matsanancin kishin Hammad ya din ga taso mata, ji take yi tamkar za ta yi hauka. Gani take yi ta asaanta ta tozarta, a ce Nana ce kishiyarta, matar da ta Wauka tamkar baiwar da ta saka kuWi ta saya, amma yanzu ita ke da komai, ita kuma tana gefe ta zama 'yar kallo.

Wasa-wasa Asal ta daina cin abinci sai kuka, ga Tafawa ba ta ita yake yi ba, ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke musu kawai yake yi.



Duk matsanancin kishin Hammad, haka ya yale Nana da Imarana, suka kasance tare suna ta hira irin ta 'yan uwantaka, tare bawa junansu labarin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa.



Ya ce "Bari na nuna miki wani abu" Imarana ya Wan tashi ya fita, sannan ya dawo, ko da ya dawo ya mia wa Nana waya.

Nana ta karSi wayar tana kallonsa, ya yi mata alama da ta saka a kunnenta.



Nana ta saka wayar a kunnenta, zuciyarta na Wan bugawa da sauri.



"Assalamu alaikum, Nana" Muryar Ummansu ce ta doki dodon kunnuwanta, a wani irin rikice Nana ta tashi tsaye, ta rasa ina zata dosa ta ce "Um..umma, muryarki ce ke ce?"



"Nice Nana, kina nan lafiya?"



Nana ta durushe a kan gwiwoyinta, ta ce "Umma, bani da bakin da zan yi miki magana, bani da idon da zan iya kallonki, ni mai tarin laifi ce"



"Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin oshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko afata na taho,amma sun ce na yi hauri kaWan"



Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi hauri Umma" Imrana ya karSe wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haWa ku ba, nema take ta rikice"



****

Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaSa shi a kan ya ci abinci, amma ya i ci, saboda shikaWai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon ungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi.

Ga jikinsa sai yi masa wani irin raWaWi yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya i Wagawa.

Daga arshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta Wauki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama.

Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani Wagowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba.



Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu wari ya ce "Ya dai? Meyafaru?"

Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan"

Ya waro ido ya ce "Yusuf Win?" Ta jinjina masa kai.

"Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da Wana gida"

Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta kan wayar.



*****



Gidan Baba ya zama tamkar maabarta, babu walwala ko kaWan, ko aunar tunkarar gidan baya son ya yi.

Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan.

Jamila kuwa kullum tana Waki, dan ta sha baar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba.

Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba Waya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa.

Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danareriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai yalli take yi ta shigo layin.

Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya Waukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya Waga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a ofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar.

Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka araso inda yake.

Suka durusa har asa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi.

Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da bai ne daga Agadez"

Baba ya Wan yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya mie ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya Waukko tabarma ya shimfiWa musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne bain, kawai ya ga Sulei ya je ya buWe motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiWar. Shi dai Baba duk abin ya Waure masa kai, tsoro ya shige shi.

Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba"

Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani.

Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?"

Baba ya ce "Gaskiya dai"

"Bai ka yi daga Agadez"



"To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba Satan kai ku ka yi ba?"



Mahmoudu ya ce "Ba mu yi Satan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata"

A razane Baba ya Wago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya rie rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar Wan uwanku, shi ma daga arshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar aramin yaro.



Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi hauri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne"



Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen.

Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni uruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu"



Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haWina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba"

Imam Zahradeen ya lura ran Baba a Sace yake.

Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, Wan uwana ne, kuma Wa ne ga Sultan na Agadez."



Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali.

Ya ce "an sarki ne zai zo baro asarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?"



Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake, rashin lafiya ce ta kama shi"



"To yaya za a yi a ce Wan sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix



Zahradeen ya ce "Baba ba dunguzuma maka hankali za mu yi ba. Mun zo mu sanar da kai batun zuwan bainka ne daga Agadez, kafin su zo Win."



"To wai su zo, su yi mini me?"



" 'yarka Nana, tana gurinmu tare da Wanta Muhsin"

Baba bai san ya aka yi ya tashi tsaye ba, yana zazzaro ido ya ce "Nana Asma'u dai 'ya ta? Yaya aka yi ku ka same ta? Tana ina? Kun taho mini da ita?"



Mahmoudu ya mie tsaye ya ce "Baba shi ne bayanin da muke yi maka, Nana tana tare

116 / 126