Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   9 / 126

24K to 27K   out of 377.2K words

ba ya ciki."

"Ta tashi a hankali, ta nufi ™ofar Wakin, ta le™a harabar gidan."

"Yana kwance a kan benci, yana bacci ya tada kansa da hannunsa. Gabansa Wan murhun dafa shayinsa ya"

"mutu, ga butar shayin da kofinsa."

"Wasi-wasi ta shiga yi, a kan ko tashin sa za ta yi. Wutar gurin ce ta Wauke gaba Waya, gurin ya gauraye da"

"duhu, aka yi wata irin wal™iya mai hasken gaske, kawai ta ga wannan tsohon a tsaye a kansa."

"Tamkar an dasa ta, ta kasa motsi ta kasa gaba ta kasa baya, aka sake wal™iyar nan, ta sake ganin tsohon"

"nan a tsaye a kansa, sai dai wannan karon ya feso wani irin tartsatsin wuta da ya tilasta mata yin baya cikin matsanancin tsoro."

Ayshacool

"A hankali ta buWe idonta, kawai ta ganshi a tsaye yana kallonta, kamar taSaSiyya haka ta zura da gudu,"

"ta koma kan katifa ta kifa kanta tana haki, saboda tsoro da razani. Maganganun ˜aisar suna nema su fara zama gaskiya a kan mutumin nan. Tabbas ta fara tantamar kasancewar sa mutum. Duk da ta san ba ta da cikakkiyar lafiya ™aisar ya saba tsorata ta, amma ya za a yi a ce mutumin da ta hango yana bacci, cikin"

"abin da bai fi ™ifta ido sau biyu ba, ta gan shi a gabanta."

"A Sangaren sa shi ma mamaki yake yi, me take yi a tsaye a bayan labule a wannan tsohon dare haka?."

*

"Hajiya Sa'a ce take kallon Jamila, tana wani irin mugun murmushi ta ce ""To jamsy me ki ka ce yanzu?"""

"Jamila ta ce ""Ta yaya zan samo miki jinin nata?"""

"""Yauwwa Jamila, ba wani abu ne mai wahala ba, magani zan baki a abinci, ki kai mata ta ci, sai kuma abin"

"da za ki ajiye mata a Waki"""

"Jamila ta ce ""To shikenan, babu damuwa an gama"""

"""Kin tabattar za ki iya?"""

"""Eh mana, me zai hana?"""

"Hajiya Sa'a da Maman Khairat suka kalli juna, suka she™e da dariya, Hajiya Sa'a ta ce ""Yauwwa jamcy, zan"

"gaya miki duk yadda za a yi "" Jamila ta gama wuninta a gidan, sannan ta tafi gida. Sai dai gaba Waya ta din ga jin ta wani iri, tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita."

****

"Tamkar bakin mama ya taSo ™eyarta, haka take washe baki, a gaban malaminta. Ta ce ""Anya ka taSa yi"

"mini aiki mai zafin wannan? Komai ya tafi yadda ake so, wallahi yadda na tsara masa komai haka ya bi,"

"dama abin yana cin sa a rai ™iri-™iri mai kuWi ya zo ta ce ba ta so"""

"Ya yi dariya ya ce ""Mu Win na wasa ne? Gangaran ne ni fa, ai duk taurin bu™ata muka Wauki allo muka hau"

"kan buzu mun gama da ita"""

"Mama ta ce ""Ai kuwa na ga zahiri, malam saura na 'yan matana, a bamu na farin jini. Wallahi duk"

"samarin nasu ba na arziki sai tarkace babu wata mamora a tattare da samarin nasu, ni kuma masu mai™o"

"nake so, inda zamu jingina mu huta, ka san rayuwar ce sai a hankali, ba zan so mu dauwwama a talauci ba, su yi gadon masifa ba"""

"Yayi murmushi ya ce""Tabbas wahala abar gudu ce, za a san abin yi, ki bayar da kuWi, za a sai binta sudan,"

"da ma'u wardi, sai farin goro zan yi musu wani aiki"""

"""To kamar nawa ka ke ganin zai isa?"""

"Ya Wan yi shiru ya ce ""Ba da dubu goma sha biyar, akwai turarukan da zan haWa da su ma, da wasu"

"saiwoyi."" Ganin bu™atar ta ta biya a baya, ya sanya babu fargabar komai ta amince ta Webo kuWi ta ajiye masa, ta yi masa sallama ta tafi."

****

"Bayan sallar asuba kallonsa Nana take yi, tana tuna abin da ya faru jiya da daddare."

"Fuskarsa daina zahiri ba ta yi kama da ta miyagu ba, ta kalle shi daga sama har ™asa, babu wata alama da"

"take nuna ba mutum bane, a suffar sa ta zahiri."

"Amma dole tana bu™atar tabattar da waye shi, ta kalli inda yake zaune yana ta fama da radio. Akwai"

"aikin jin radio, sai dai magana ce aiki a gurinsa."

"""Ina kwana?"" Ya ji muryar Nana babu tsammani. Ya Wago ya kalle ta domin ya tabbatar idan da shi take."

"Ta sake cewa ""Ina kwana?"" Šaga mata hannu kawai ya yi, tare da jinjina kai."

"Takaici ya kama Nana, maganar ce dai ba zai yi ba."

"Kawai ta ga ya tashi ya Wauki Wan kurfotin dafa shayinsa, ya zuba ruwa a cikin butarsa. Ya Wauki wata"

"ba™ar leda ya tashi zai bar mata Wakin. Cikin sauri ta tashi ta ce ""Kawo na dafa maka"" ya kalle ta ya girgiza mata kai."

"Ta mi™a hannu za ta karSi butar, ya janye ya ce ""A'a"""

"Ya juya zai fita, kawai ya ji ta biyo bayansa. Ya tsaya ya waiwayo, tana ™o™arin tsare shi da ido, amma ta"

kasa. Ya kuma yin gaba ta sake bin sa.

"Sai ya fasa fitar, ya dawo Wakin, ita ma ta biyo shi ta dawo."

"Ya samu guri ya zauna, yana kallon butar shayinsa yana kallon Nana, da ta maze."

Bayan wani Wan lokaci ya tashi ya fara shirin shiga wanka. Nana ta maze ta Wauki wayarta tana dannawa.

"Sai da ya shiga banWakin, ta bi bayansa da kallo."

"Hajiya Amina ta kira a waya, cikin ikon Allah kuwa bugu biyu ta Waga tana ""Amarya kin sha ™amshi"""

"Cikin jin nauyinta Nana ta ce ""Hajiya ina kwana?"""

"""Lafiya ™alau Nana, ya ki ke fatan kina lafiya? Ina ta kiran wayar ki a kashe"""

Ayshacool

"A nan Habu ma ya karya, ya zauna su ka yi hira da Nana, shi kuwa da ya gama cin abincin sa, ya koma"

gefe ya yi musu shiru.

"Shi ma bai wani jima sosai ba, ya tafi. Gaba Waya zaman shiru ya ishi Nana, shi ba kula ta yake yi ba, sai"

"dai ta wuni a Waki shiru, shi kuma yana waje, yana jin radio da aikin dafa shayi kamar ibada, ko hutawa ba ya yi, har mamaki take yi idan yana gane abin da ake yi a radion."

"Bayan azahar yana kwance, a Wakin, radion ta cika wa Nana kunne, ta dube shi ta ce ""Dan Allah zan shiga"

"cikin gidan nan, na yi musu sallama, tun da na ga alamar akwai mutane a cikin gidan"" ya gyaWa mata kai kawai."

"Ta Wumama ruwa a kan gas, ta shiga ta yi wanka ta fito, sanye da dogon hijjabi. Ta Wauki kayan da za ta"

"saka, ta koma banWaki ta canza ta fito. Doguwar riga ta sako, hannunta ri™e mayafin rigar. Ta cire hular"

"kanta, ta tsaya a gaban mudubi tana shafa mai. Abin ka da mace, kuma amarya, sai ta tsaya a gaban"

mudubin tana gyara fuskarta.

"Ta tsiyayo humra ta shashshafa a jikinta. Ta janyo drower mudubin, inda yake ajiya kayansa ta buWe a"

"hankali, ta waiwaya ta kalle shi, ta ga idonsa a rufe, ta Wauki turaren sa, ta tsiyaya a hannunta, ta shafa a wuyanta."

"Yana daga kwance yana kallonta, ta ™asan idonsa. Sai da ta gama tsaf, za ta fita kawai ya yi gyaran murya."

Ta tsaya ta waiwayo tana kallonsa.

"Ya yin™ura ya tashi, ya nufe ta, ta tsaya ™yam tana kallonsa. Gani ta yi tamkar zai shige cikin ta, babu shiri"

"ta fara ja da baya, sai da ta dangana da jikin bango."

Ayshercool

08081012143

Ayshacool

Page 30

"Zazzaro ido Nana take yi, numfashin ta na neman sar™ewa, saboda tsoro da fargaba."

"Ya saka hannunsa ya kamo hannunta cikin nasa, wani irin sanyi ya ratso ta, tun daga tafukan hannayenta"

har zuwa ™afafuwan ta. Ya kama gefen rigarsa ya goge in da ta shashshafa turare a hannunta. Ya saka

"hannunsa a gefen wuyanta, nan ma ya goge wanda ta shafa a nan."

"Na saman rigarta yake kallo, sannan ya kalli idonta. Ta yi tsuru-tsuru a ranta ta ce ""Daga Wan shafa"

"turaren sa, shi ne yake mini wannan tijarar haka"""

"Idonta ta saka kwalli, bakinta kuma ta saka man leSe mai kala, sai girarta da ta gyara. Ba ta gama zancen"

"zucin ba, ya saka hannunsa ya fara goge man da ta saka a leSenta."

"Ri™e hannunsa ta yi za ta yi magana, amma ya yi mata wani irin kallo da ta rasa na mene ne, babu shiri ta"

"yi tsit. Ya goge leSenta tsaf. Ya kalli idanunta da suka sha kwalli, ya mayar da hannun sa kan girarta, ya hargitse gashin girarta."

"Ya zare mayafin rigar da ta Wora a kanta, ya ciro hijjabin da ta shiga wanka da shi, ya hau saka mata."

"Kamar ta rusa ihu ta ce ""wanka fa na yi da shi, ba ka ga duk danshin ruwa a jiki ba?"" Bai amsa mata ba,"

"ya jefa mayafin rigar a kan katifa, ya koma gurin da yake zaune ya zauna. Wani irin takaici ya tokare"

"Nana, kamar ta kurma ihu, saura ™iris ta ce ta fasa fitar, amma ta tuna zaman shiru za ta zauna ta yi a Wakin, ko ma shi ya fice ya bar ta. Ta ja takalmanta ta fice daga Wakin tana haWe fuska."

"Fasalin gidan ya yi mata kyau sosai da sosai, sai da ta zagaya ta bayan wata baranda, sannan ta gano"

™ofar shiga. Tun daga barandar take Wan jiyo hayaniya sama-sama.

"Ta buWe ta shiga da sallama. Samari ne su kusan biyar a falon, su na kallon ball su na ta hayaniya."

"Sallamar ta ce ya sanya su yin shiru, suka amsa mata."

"""Sannunku, dan Allah matar gidan nake nema"""

"Šaya daga cikin su mai ri™e da remote a hannunsa ya ce ""Tana sama"" ya yi maganar yana nuna mata"

upstairs.

"A falon saman benen ta tarar da matar, babba ce mai jiki fara tas da ita, tana shan lemo a kofi tana"

danna remote.

"Ta amsa sallamar Nana, tana yi mata kallon rashin sani."

"""Ina wuni?"""

"Matar fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce ""Lafiya ™alau, zauna mana ga kujera nan"" Nana ta zauna, ta"

"kalle ta ta ce ""Dama ni ce matar mai gadinku, da muka tare, na ga tun da muka zo ba kwa nan, sai jiya na ji motsin mota a gidan, shi ne na ce bari na zo mu gaisa"""

"""Allah sarki, sannu ko? Da maigidan ya ce mini buzaye ne"""

"Nana ta ce ""Maigidana ne buzun, ni bahaushiya ce"""

"""Ohh Allah sarki, ya sunan ki ne?"""

"""Nana"""

"Ta ce ""Ma sha Allah, sannun ki"""

"Nana ta ce ""Yauwwa, idan akwai wani aiki ma, idan ki na bu™ata, idan bai fi ™arfina ba, a yi mini magana"

"zan yi in sha Allah"""

"Matar ta jinjina kai ta ce ""To shikenan na gode sosai"" Matar ta Wan yi shiru tana kallon Nana. Ta yi"

"mamakin yadda yarinyar mace kamar Nana, ta auri Buzu har yake yawon gadi da ita."

"Sanin da Nana ta na idan ta koma, zaman tsuru-tsuru za ta yi da wannan kurman mutumin, ya sanya ta ja"

"ta yi zamanta, ta ci gaba da kallon Tv. Matar kuma ba ta ce mata uffan ba. Can Nana ta ce ""Hajiya ba ki da 'yan aiki?"""

"""Ina da su, ba na zama ne sosai a ™asar, duk sun watse mun ma dai samu saSani ne"""

"""Ke ki ke aikin da kan ki?"""

"""Ni da yara muke yi"""

"Nana ta ce ""Allah sarki, idan kina bu™atar aikin ma, zan din ga zuwa ina yi miki"""

"Duk da tana basar da Nana, sai da ta yi murmushi ta ce ""To in sha Allah"" sai da Nana ta gama kallon,"

sannan ta tashi ta yi wa matar da ko sunanta ba ta sani ba sallama.

"Ta sauka ta fita, sai dai tana fita ta yi kiciSis da shi, sai da ta tsorata, yana tsaye a bakin ™ofar shiga cikin"

"falon gidan, yana jiran ta"

"""Lafiya? Ya na ganka a nan?"" Yana ganin ta fito kawai ya yi gaba ya bar ta a gurin. Ba ™aramin ™uluwa"

take yi da wannan dunkun-dunkun Win da yake yi ba na rashin magana.

*

"Babbar mace ce a ™alla za ta yi shekara talatin da bakwai zuwa da takwas, hannunta ri™e da waya take"

"kaiwa tana komowa a Wakin, ta sake kai wayar kunnenta."

"""Hello Yaya kina ji na? Dan Allah maganar nan da gaske ki ke?"""

Ayshacool

"Daga Waya Sangaren matar ta ce ""Oho ban tabattar ba, amma kin san babu lallai a yi jita-jita da irin"

"wannan maganar, amma abu mafi sau™i ki saka lokaci mu je mu tabattar"""

"""Yanzu Yaya idan maganar nan ta tabatta, baban su Imaran ya kyauta mini? A yi auren yarinya ta amma"

"a kasa gaya mini an yi mini adalci a haka? Ba fa shikaWai yake da hakki a kan yarinyar nan ba"""

"""To yaya za ki yi maijidda? Kawai mu shirya mu je shi ya fi sau™i"""

"Gyaran muryarsa da ta ji ya sanya ta kashe wayar babu shiri, tana faWin sannu da zuwa."

"Ya ™ura mata ido ya ce ""Meye haka na ganki wani iri?"" Ta so ta jure zuwa ya samu nutsuwa su yi magana"

"ta fahimta, amma ta kasa. Cikin damuwa ta ce ""Labari na ji wai an yi wa Nana aure, shi ne nake son in tabattar"""

Nan da nan ya haWe fuska tamkar tasowar hadari lokacin marka-marka.

"""Wato ba zaki fasa kiran tsohon mijinki ba ko Maijidda, ni fa na gaji ba zan lamunci wannan iskancin naki"

"ba na shekara da shekaru"""

"Cikin ™o™arin kare kanta ta ce ""Ka yi ha™uri, wallahi ba kiransa nake yi ba. Da Yaya nake waya wallahi"""

"""Bani wayar nan"""

"Ta Soye wayar a bayanta ta ce ""Wallahi ba da shi nake waya ba, Yaya ce"" za ki bani ko sai na Sata miki rai."

"Ta mi™a masa wayar tana kuka ta ce ""Dan Allah baban su Walida, ka bani wayar nan, hankalina ba zai"

"kwanta ba sai na tabattar da gaskiyar maganar nan"""

"Ya tsaya cak yana kallonta ya ce ""Allah wadaran halinki, ko kunyar Ubangiji ba kya ji, babu wata Nana da"

"aka yi wa aure, tsohon mijinki ne ki ke bibiya, tirr da halinki"" fashewa ta yi da kuka, tana sheshshe™a mai cike da ™unar rai."

*

"""Zan yi wanka"" ya yi maganar yana tsare ta da ido."

"Nana ta Waga kai ta kalle shi, ta ce ""To ka yi mana"""

"Ta yi magana tana Sata rai, tare da mayar da hankalinta kan wayarta, da ta gano tarin fina-finai a ciki."

"Tun bayan da Hajiya Amina ta bata wayar, ta nunawa Nasiru, ya karSi wayar ya fita da ita gurin abokan sa aka yi turi, ba ta taSa sanin da su a wayar ba."

"Shiru ya yi yana kallon Nana, ganin ba ta gane abin da yake nufi ba. Kawai ya shiga banWakin."

"˜ofar banWakin ta bi da kallo, gaba Waya ta kasa gane kansa, babu yadda za ayi ace mutumin da yake da"

"taSin hankali, ya din ga gudanar da al'amuransa cikin nutsuwa. Sai dai kuma wannan shirun nasa ma,"

"yana ™ara tabattar da taSin hankalin nasa. Duk da ma ba wannan ba, hankalinta ya fi karkata ga son sanin ainihin waye shi."

"Ya shafe tsawon lokaci a banWakin, dan sai da Nana ta manta da shi ma, sannan ya fito. Jikinsa sai tsuma"

yake yi.

"Ya nufo kan katifar da Nana take kai tsaye, bai ce mata uffan ba, ya zazzageta ya janye bedsheets Win da"

yake shimfiWe a kan katifar ya du™un™une a ciki.

Galala ta saki baki tana kallonsa.

"Lallai babu alamar hankali a nan"" ta faWa a zuciyarta. Sai dai ta lura da yadda jikinsa yake ta tsuma da"

rawar sanyi.

"Ga garin babu sanyi sam, ita gumi ma take yi, amma ta ga yana ta tsuma. Ya jima sosai a haka, daga"

"bisani ya tashi tsaye, ya nannaWe bedsheet Win ya ya jefe mata a ka, ya wuce gaban mudubin."

"""Ya haka, me yasa ka jefo mini?"""

"Waiwayo wa ya yi mata wani mugun kallo, ya juya ya ci gaba da abin da yake yi."

"TaSe baki ta yi, ta tashi ta Waukko wani zanin, ta shimfiWa ta zauna. Hannunsa Wauke da robar mai, ya"

nufo ta.

"Ya ajiye man a gefenta, ya zauna ya juya mata bayansa."

"˜uri ta yi wa bayansa da ido, daga bisani ta ce ""Me za a yi ne?"""

"Ya Wauki robar man, ya saka mata a hannunta, ya nuna mata bayansa da hannunsa."

"A Wan tsorace ta ce ""Wai taSa ka zan yi?"""

Ya juyo gaba Wayansa ya zuba mata ido.

"Nana ba ta taSa ™are masa kallo ba, sai yanzu. A hankali ta fara jin sanyi yana ratsata, bugun zuciyar ta"

ya fara ™aruwa.

"Cikin sauri ta ce ""To juya"" ya juya mata. Ta Waga robar man ta na kallo, duk rubutun jiki da french ne, ba"

ta iya gane komai ba.

"Ta tsiyayo man, sai ™amshi yake yi, hannun ta har rawa yake yi, ta kai hannunta bayansa. Sai dai tana"

"Wora hannunta ta ji tsigar jikinta ta tashi, sanyi na ™ara ratsa ta."

Ayshacool

"Ta ture gashinsa gefe, ta fara shafa man a bayansa, sai dai tana shafa masa, yanayinta yana canzawa"

"zuwa wani abu, da ta kasa tantance mene ne."

"Tsayar da hannunta ta yi a guri Waya, ta ™i gaba ta ™i baya, jin zuciyarta na rayo mata wani abu a game da"

"shi. Haushin kanta ne ya kama ta, kawai ta ja da baya ta haWe rai. Ya sake waiwayo wa ya kalle ta. Kamar wanda aka yi wa dole ya ce ""Sanyi nake ji"""

"MurguWa baki ta yi, ta ja jikinta lungun katifa, ta yi masa shiru. Ganin ba ta da niyyar sake taSa shi, ya"

sanya ya tashi ya nemi guri ya kwanta a ™asa.

"Shiru ta yi tana zancen zuci, iya tsawon rayuwarta, ita ba ta taSa kai hannunta jikin wani namiji tana sane"

"ba. Kuma ba ta taSa jin abu makamancin irin haka ba, a tattare da wani ba."

"'ki shiga hankalinki Nana, kar wannan farar fatar ta ruWe ki"" wata zuciyar ta gargaWe ta."

"Guntun tsaki ta yi, ba tare da ta shirya ba."

"""Ya dai?"" Muryar ˜aisar ta dawo da ita tunaninta."

"Ta kalle shi, yana ta haWa wasu abubuwa a cikin kwalabe."

"""Kai ne ko?"" Ta yi maganar a Wan ™ule."

"""Na yi me?"" Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba."

"""Ka fi ni sani ai"""

"˜aisar ya girgiza kai ya ce ""Sanin gaibu sai Allah ai, ban san me na yi miki ba"""

"Nana ta ce ""Ka sani"""

"Ya Wan kalle ta, kawai ya bushe da dariya ya tashi tsaye yana faWin ""Kar ki damu, yanayi ne da bil adama"

"su kan kasance a ciki, ai ba ki yi wani abu ba, ba abin damuwa ba ne ba. Kuma ni bani da hannu a wannan lamarin. Sai dai ina tunatar da ke, kafin ki yi aika-aika ki tabattar da wane ne shi"""

"Banza ta yi masa, ta nufi wata ™ofa da take buWe."

"A hankali ta buWe idonta, tana kwance a kan katifarta, ta kalli gurin da yake kwance, yana nan kamar"

"yadda ya kwanta. Ya dun™ule jikinsa guri guda, jikinsa ko riga babu. Ta shafa jikinta ta ji gumi take yi,"

amma shi alamu suka nuna sanyi yake ji.

"Ta

9 / 126