Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   63 / 126

186K to 189K   out of 377.2K words

miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta.

Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin"



Ta girgiza kai ta ce "˜arnin hawa kaina yake yi na ™oshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma Wakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba.



Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta Soye-Soye amma tuni ta daWe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba.

Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daWin zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana.



Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba Waya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya"



"Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina"



"Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ™arancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta.

Shukura ba ta so ba sam, dan ko ™aunar ganin Sharif Win ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Al™awarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta ha™ura.

Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu.

Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce.

Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba Waya haihuwar ma ta fita daga kanta.

Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuWi, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faWuwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa.



Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta Sungire a gurin ta hau bacci.



Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taSa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar.



Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?"

Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na ha™ura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa"



Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki.

Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan Wan ma ya sake raba ta da shi"



Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faWi"



"Lafiya ki ke kwance a ™asa haka ki ke bacci?"



Ta ce "Bacci ne ya Wan Wauke ni ban sani ba"



Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yin™ura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru.



Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci.

Ta mi™a masa lemon da ta haWa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali.

A ranta take faWin "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani'

Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya Wan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya mi™a mata kofin, ta karSa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana Wan ™ara gyara masa filulluka.

Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin"



Ta ce "Amin Daddy"



"Da lafiyata ™alau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaWunka" ya amsa da Amin yana ri™e hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho.

Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo Wakin, Fadila ta Wan zabura ta ja da baya.

Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ™o™arin yi, ai sai ku rufe ™ofa kar yara su faWo, a lalata mini tarbiyyar yara"

Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya ri™e hannuna, and laifi ne dan ya ri™e hannuna wani abin ki ka ga na yi?"



"Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ™arata ku da Allah"

Ran Fadila ya yi mummunan Saci, ta yin™ura da niyyar, ta Wauki Wan ta ta bar Wakin, amma ya ri™e hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su.

Idan ya ce Suwaiba ba ta ™o™ari a kan rashin lafiyarsa ya yi ™arya, tana iyakar ™o™arinta amma wasu lokutan tana da saurin ™osawa gashi haryanzu azababben kishi na Wawainiya da ita.



****

Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taSa tsammanin,    Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba Waya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan bu™atarsa ta tashi, ya yi kiWansa ya yi rawarsa. Gaba Waya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ™ararta da yake yi, ba yau ba gobe.



"Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada"



Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A Sangaren ™wa™walwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta Sangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin Win aka yi masa".



"Sultan, ka ™i bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faWi gaskiya ko ya ™i Allah"



Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daWi kai ka san irin ala™ar da take a tsakaninsu."



"Amma yanzu ai yanzu a kan gaSar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali"



Sultan ya amsa da "Yauwwa"



BAYAN WATA ŠAYA



Sabo turken wawa, rashin ganin ˜aisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi.

Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ™walam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa.

Ta waiwaya ta lelle™a, amma babu ˜aisar babu alamunsa.

Wani littafi guda Waya tal, ta hango a kan teburin rubutun ˜aisar, ta ™arasa ta nufi teburin ta Wauki littafin.



Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne daban.

Hoton wata al™arya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula.

Ta buWe littafin shafin farko, ta fara karantawa.



"Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin.



"Ka sani,har abada da Wan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ™ai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka.

Ka na bu™atar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taSa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a rasa, ka zubar da jini ba ™a™™autawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka.

Ka kame mutanen gefen al™aryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ™arfinsu da fikirarsu ka gina al™aryar da babu wani mahaluki da zai iya Waga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai bu™ata ta biya.

Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke bu™ata kar ka saurarwa kowa"



Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na Wauki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba"

Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ™ara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa.

Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matu™ar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ™warangwal, Waya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ™ara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana haya™i yana ba™i yana washewa.

A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluSe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ™ara sanya wutar ™ara balbala.

Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam Win akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ™onewa yana kururuwa yana kiran sunanta.

Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faWi ™asa.

A gigice Nana ta farka, ta haWa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ™ullewa da cikinta ya yi haWi da mararta. Ta yin™ura da ™yar ta tashi ta tafi banWaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an Waure mata. Ta yi alawala ta koma Wakinta.

A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa.

"Allahumma ajirni mina narr"

Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daWi ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam.

Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan Waurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daWi, haka nan take lallaSawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu.

Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?"



Ta Wan yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne"



"Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri Waya ya yi ™asa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda Wan yake ta motsi yana danno ta.



Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faWanta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai.

Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido.

Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba.

Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a Waki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin.

Nana ta kwana huWu, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye.

Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba.

Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banWaki, ta Wora abin karin kumallo.

Ta kuwa sha faWa a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta.

Sun gama karyawa, Nene ta shiga Waki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali.

Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?"



"Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya ri™e fitsari" gaban Nene ya faWi ta ce "Kamar yaya?"



"Ji na yi kawai fitsari yana bin ™afata, kin ga" ta yi maganar tana Waga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ™afafuwanta".



"Nana wannan ai kamar na™uda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?"



Duk da ™o™arin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji.



Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin halin ciwo, ba ta iya gane komai.

Nene ta Waukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti.

A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu.

Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ™arshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda Sari kawai take yi a jere.

Ya tabattar mata a cikin Sarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka na™uda take yi.



Gaba Waya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da Wan abin da za a bu™ata.

Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ™o™ari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ™ayyum" ta yi yin™uri sai ga kan Wan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ™arasa ba, ta ji kukan jariri ya cika Wakin.



Likita ta Wago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?"



Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga Wan a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa.

Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen Wa, kamar Wan wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan Wan duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta Wan wannan gurin ya fito?

Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta mi™a hannunta gaba Waya tana ™o™arin karSe yaron daga hannun Likitar a kiWime.



Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buWe idonsa.

A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga ba™in halittu.

Sultan ya ri™o hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?"

Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo.

Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam"

Kawai ya yi shiru kamar sa™ago, sai ™wayar idonsa da yake juyawa.



Ayshercool

08081012143

65

Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai mi™o miki shi za a yi"

Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ™aton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai.

Aka Wora mata shi a ™irjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah.



Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta Wora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi.

Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta.

Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daWi, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka Wauke jaririn aka gyara ta, aka yi mata Winki, sannan aka kai ta Wakin hutu.

Bakin Nene ya ™i rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu ba™uwar su Nana ta haihu.

Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu.

Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daWi, tana tsoron idan ba ta haWu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su ˜aisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi.

Haka dai ta Wan saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene

63 / 126