Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   112 / 126

333K to 336K   out of 377.2K words

"Wannan ne Wan nata?"

Ya yi murmushi ya jinjina masa kai.

Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?"

Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan"

Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaWai wanda muke ciki Waya da shi"

Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi"

Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa ba™i"

Nana ta ja jikinta ta zauna, ta ™ure Imrana da ido, gaba Waya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa.

Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa.



*****

Jamila ce a dur™ushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta Waga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina"



Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka Waukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. ˜wayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba".

Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?"



"Tun da ki ka iya jure mi™awa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin"



"Wayyo Allahna" Ta faWa a marairaice tana sake dur™ushewa cikin azababben ciwo.



*****

Fadila ce ta fito daga banWain da ta shafe a ™alla awa Waya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana Waga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaSawa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, ™arfin hali kawai yake yi.

Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"

A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos"

Ta Wan yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?"

Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuWin motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daWi ya sake tasowa ba"

Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuWi a hannunta ta ara mini"



Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na Satan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne"

Ta Wan tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuWin sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi ha™uri mu nemo kuWi ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya ™ayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne.

Ya amsa da "Amin."

****

Gaba Waya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta Suya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci Waya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake.

Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?"

Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki Suya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?"

Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi"

Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga Wakin.



****

Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shau™i, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala.

Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren.

Kasancewar daga Nana sai shi a Wakin, ta Wan jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaSar da na fi tsananin bu™atar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?"

Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi ha™uri kaWan za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya ™addara ke ce zan huta a dalilinki."

"Ban gane ba, me ka ke nufi?"



Imrana ya ce "Za ki gane ne"



"Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini"



"To kar Allah ya sa su yafe Win mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar"



Nana ta buWe baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?"



"Eh Win, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wata™ila ma babu wanda ya neme ki a cikin su"



Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen Win babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa"



Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka ™ure ni da ido ne?"



Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka Waure mini kai nake son ka yi mini bayani"



Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa"

Imam Hammad ya ce "In sha Allah"

Kamar yadda suka taru a falo Wazu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar.

Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da ala™a da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi ha™uri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne.

Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba Waya suka Waga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake Wan uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yin™urin tafiya da ™anwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarWa a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi.

Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi ha™uri ya bari ku rayu da ™anwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, ™addara ce ta faWa maka.

Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wula™ance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya ™ara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waWanda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuWin dan kai ka biya masa ba ni ba.

Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen"



"Hammad" Ya mi™e tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke Soyewa?"



Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka"



"Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani"



Mahmoudu shi kansa Waurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana Wawainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?"

Gaba Waya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa.

Hammad ya ri™e rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma.

Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka sa™on cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haWa ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuWaWe domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki.

Sai dai bayan kame ku gaba Waya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi Satan dabo, ga kuma al™awarin da na yi wa Wan uwanta, na zan tabattar da tana cikin ™oshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaSa ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria.

Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!.

96

1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic

08081012143





Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara.

Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri.

Wannan shi ake kira da ga ™oshi ga kuma kwanan yunwa.

Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya Wauki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne.



*****

Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin Satan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare.

Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton Sacewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke Sacewa.

˜arfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a Sall gate Win. Afujajan mai gadi ya buWe gate Win, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba Waya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan.

A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun ™ofar da suka ji ana yi.

Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta Waukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a ™ofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja.

Mai gidan ya ™arasa gaban Yusra, ya karSi jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi.

"Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?"

Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa"

Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo Wa.



*****

Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu ™a™™autawa, ga azababben ciwon mara da ta din ga yi. Ta kwana ta wuni tana wata irin burgima da kuka mai ban tausayi.

Baba ne ya dawo ya tarar da Jamila a cikin wannan yanayin.

Baba ya ce "Rabi wai me yake damun Jamila haka ne, wannan wane irin ciwo ne tun jiya?"

Mama ta ce "Ba fa wani abin ba ne ba, al'ada ce ta zo mata take shan wahala."

"Haba, wahalar ta isa haka, wane irin ciwo ne haka, anya ba za a kaita Asibiti ba"

Mama ta ce "Ba sai an kai ta ba, na bata magani za ta warke"

Baba dai bai ji ya gamsu ba, amma ya ™yale su kafin ta hayayya™o masa da masifa.



*****

Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama.

Tana zaune a Wakinta, Tafawa ya shigo Wakin, ta Waga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba.

"Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata."

Asal ta yi shiru, wani irin ba™in ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a ™o™arin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa.

Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a ™o™o ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya ™ara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa.

Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daWe da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a Soye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da ala™a da ta'amalli da chemicals masu ™arfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila.



Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako.

Nene ta ce "Babu komai, Wa na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a Wakin mijinta"



Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?"



Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je Win ba"



Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku ha™uri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku ha™uri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba."

Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?"

Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa Wan su. Tun da Wansu yana son iyalinsa."



Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daWi, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci.

Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan mi™ewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai

112 / 126