Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   82 / 126

243K to 246K   out of 377.2K words

yi hira sosai mussaman idan ya tarar jikin nasa da sau™i.

Kusan kullum Hajiya Sa'a gani take mafarki take yi, idan aka wayi gari za ta ga Abba bai mutu ba, amma ta ga babu alamun hakan. Ba ta ™ara kiWimewa ba sai ma da aka yi kwana bakwai da mutuwar, kowa ya watse ya bar gidan.

Šakin Abba ta tafi da daddare, ta buWe Wakin tana rintse idanunta tana jin tamkar za ta gan shi ya Wago, da wannan murmushin nasa irin na fuskar mahifinsa.

Amma ta ga Wakin nasa wayam, babu komai.

Wasu irin zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kumatunta, ba ta taSa dana sanin shiga ™ungiyar asiri da duk wasu miyagun laifuka da take aikatawa ba, sai da ta rasa tilon Wan da Allah ya ba ta a rayuwa. Wanda babu irin ™o™arin da ba ta yi, domin ganin ta kare shi da sadaukarwar ™ungiya. Ashe bonono ta yi rufe da Sarawo bayan janyo Jamila cikin harkar ™ungiya, wanda ta yi hakan ne, domin janyo Jamila kusa da ita yadda za ta samu mallakar jinin Nana.

Ta zauna a gaban ™atuwar katifarsa, ta din ga wani irin kuka mai sauti, da sai da ™irjinta ya fara yi mata zafi.



*****



Asal ce zaune a kan carfet, saman kujerar da take kai kuma wani babban mutum ne, cikin shigar buzaye, kansa Wauke da rawani.



"Ki na ji na da kyau ko?"



Ta jinjina kai cikin nutsuwa, ko ™wa™™waran motsi ba ta yi.

"Ina fatan haryanzu ba ki manta dalilin da ya sanya ki ka auri Hammad ba"



Ta amsa da "Eh ban manta ba"



"To barka, yanzu ya dawo, kuma babu abin da zai canza, za ki ci gaba da gudanar da aiki, kamar yadda yake a baya. Ba na bu™atar kuskure ko kuma wani uzuri. Duk wani motsinsa da duk abin da yakamata mu sani mai muhimmanci ki sanar da ni, idan kuma ki ka bari ni na gano ba ki sanar da ni ba, ranki zai yi mummunan Saci"

Jiki a sanyaye ta jinjina kai. "Dole a ci gaba da aiki tu™uru, domin nesanta shi da kujerar Sultan, da mahaifinsa ke ta ™o™arin kusantar da shi da ita, mu na bu™atar kujerar nan ko ta halin ™a™a, dan haka ina nan ina saka miki ido da kuma sauraren ki"

Asal ta sake jinjina kai, jikinta babu ™wari ta tashi ta fice.

Da ™yar take Waga ™afafuwanta, damuwa duk ta cika mata kai, ta ma rasa wane tunanin yakamata ta yi.

Da ta koma gida, ta tarar da hadimai na gyara Sangaren Imam, ga ™amshin turaren sa, da alama bai daWe da fita ba.

Cikin tsawa ta kore su gaba Waya, ta ce su ajiye aikin su fita daga sashen, sannan su kira mata Nana. Jiki na rawa suka ajiye suka fita.

Nana tana tsaka da karatun Alkur'ani sa™on Asal ya iske ta, sai ta hau tunanin kiran me take yi mata. Duk da ta san abin da ta yi mata da safe.

Nana ta tashi cike da ™warin gwiwa, dan ji take yi daidai take da Asal, tun da duk abu dai ba za ta raba ta da ranta ba.

Nana ta shiga fuskarta a haWe ita ma, ta shiga Wakin ta tsaya, tana ta huci tana son ta balbale Nana da faWa, sai kuma ta kasa ganin yadda Nanan ta tsuke fuska ita ma, ta yi mata wani irin kwarjini.

Amma duk da haka ta maze cikin dakiya da ™arfin hali ta ce "Amm tambaya nake son yi miki, ban sani ba ko nice a ™ar™ashinki, da zan din ga yi miki magana kina ji na ki yi mini banza"

Nana ta Waga kai tana kallonta. "Ko ba ki gane me nake nufi ba ne? Abin da ki ka aikata da safe"



Nana ta ce "Na gane, gani na yi bai kamata na tsaya ina kallon ku a yanayin da ku ke ba, ko na din ga sauraren maganganunku ba. Hakan zai zama kamar munafunci ne, shi ya sanya na tafi, amma ki yi ha™uri"



Asal ta watsa mata wani banzan kallo cike da tsana ta yi ™wafa sannan ta ce "Daga yanzu aikinki ba iya girkin Imam ba ne ba, har da gyaran sashen sa, ba na bu™atar kowa ya din ga raSar inda yake."



"Amma Waukko ni ki ka yi na din ga girki kawai, ya za ki haWa mini da aikin shara da goge-goge. Kuma masu yin aikin su uku ne, ni kuma nikaWai ce, aikin bai yi mini yawa ba kuwa?"



"Kin san a kan kuWi nawa na biya na Waukko ki? Ko a Nigeria ba na tunanin ko za a sayar da kaf danginku, za ku iya biyan kuWin da na biya na karSo ki ba. Dan haka ina da hurumin sanya ki duk abin da na ga dama"



"To Gimbiya Asal, babu damuwa zan yi abin da ki ke so. Duk da dangina ba za su iya biyan kuWin da ki ka biya ba. Amma na san wata™ila mijina zai iya biya ya fanshe ni" Nana ta yi maganar tana murmushin da Asal ba ta gama gane kansa ba.



Nana ce ta ™arasa aikin gyaran falon nan, ta yi goge-goge. Ha™ur™urtar da kanta ta din ga yi, da ta tuna mijinta take yi wa wannan aikin. Duk da ayyukan sun yi mata yawa. Ita dai fatanta Ubangiji Allah ya sanya Sayyid ya tuna ta domin ta san matsayinta.

Tana kammalawa ta koma kitchen, ta Wora girkin rana. Ta kammala ta kai ajiye.

Ta ™ara goge Wakin saboda ta san halin Asal sai ta tafi za ta huta, za ta sanya a kirawo ta, ta hau yi mata kinibibi da sanabe kala-kala.

Ta gama aikin goge-gogen kenan, ta gano wani photo album. Ta Wauka ta nutsu tana dubawa, duk rubutun French ne a jiki.



Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene.

Ta buWe Waya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ™asa da sunan sarautarsa.

Sai kuma ta shiga wani shafi mai Wauke da hoton Sayyid a ™asa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suSuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album Win nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ™asa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam.

Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?.



Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin Waya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye.



"Imam, wai ina zobenka ne?"

Ta yi maganar tana Wago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune.



"Ya karye yana gurin gyara"



"Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?"



Daidai lokacin suka ™araso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya Sata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa.

Yanzu zan fita, kar ki manta da sa™ona"

Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon.



"Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta.



"Babu komai, gyra Wakin na yi"



"Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce Wakinki? Imam yana da ba™i anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi"

Asal ta Wan yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba.



A Wan corridor Win ta tsaya tana zancen zuci, jin ana maganar zobe. Wane zoben kenan? Ko dai zoben da ya Wauka ya ba ta ne? A'a ba ta tunanin haka wata™ila dai wani abin ne daban.

Gyaran murya da ya yi da ™amshin turaren da ya cika gurin ne ya sanya ta farga ta waiwaya, sai ta ga a kan hanya ta tsaya.

Ta yi taku biyu ta ba shi guri, ya saci kallonta, zuciyarsa ta din ga raya masa son sanin wace ce ita, sanin na sosai ya yi mata tambayoyi game da wasu abubuwa.

Ya haWiye yawu ya zo zai gifta ta, wani irin daddaWan sanyi ya ratsa shi, sanyin da zai yi fatan dauwwama a cikin sa, saboda yadda ya saba da zafin jikinsa, wanda duk sanyin da yake guri, a cikin jikinsa yake jin wannan zafin.

Sai dai wannan sanyin da ya ratsa shi, har cikin ™ashinsa ya ji sanyin.

Ya sake waiwayawa ya kalli Nana, amma ya ga shi take kallo. Ji yake tamkar ya koma da baya ya ™ara samun kusanci da ita, sai ya fi jin sanyin sosai da sosai. Tun da Allah ya jarrabe shi da ciwon nan, bai taSa jin sanyi mai daWin wannan ya ratsa shi ba, kuma ya yi imani da Allah daga jikinta wannan sanyin yake, saboda sun samu kusanci sosai da sosai da zai gifta ta.

"Allah ya sa ba wani abin ake kuma shirya mini ko wani tarkon ake shirin yi mini da ke ba" Ya yi maganar a zuciyarsa.

Nana ta yi mamakin dalilin da ya sanya shi tsayawa haka.

Zuciyarsa ta din ga raya masa ya koma da baya, daf da Nana, ko zai fi kin sanyin yadda yake so.









AREWABOOKS



Nana ta ce "Sayyid ko wani abu ka ke bu™ata ne?"

Sai da ta yi maganar sannan ya farga, bai ce mata komai ba kawai ya fice ya bar gurin.

****

Shukura ce a zaune ta takure jikinta, tana kallon kwanon abincin da aka kawo mata, Abinci mai rai da lafiya sai dai ko sha'awar kai wa bakinta ba ta yi ba, duk da uwar yunwar da take ji, tamkar ta ci babu.

Shiru ta yi tana tuna yadda bayan fitowarta daga Asibiti suka yi karo da wani mai adaidaita sahu.

Ya fito yana jarabar sai ta biya shi, duk da shi ne da laifi, amma ta kasa fitowa daga motar, ta sauke gilas ta ce ya gaya mata dammage Win nawa ta yi masa ta biya shi. Daga sauke glass Win nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi ta ganta a wannan Wakin, da sai dai a zuro mata abinci kawai.

Ba ta iya banbance adadin lokacin da ta kwashe a gurin ba, sai dai ta kintaci lokacin salla ta yi.



Babu tsammani ta ji an buWe ™ofar Wakin, hakan ya sanya ta kalli ™ofar da sauri.

Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba.

Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido.

Duk da ta Wan razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba.



Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?"



Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba"



"Ko me yasa?"



"Saboda jikina ya daWe da bani hakan"



"Ta yaya kenan?"



"Na daWe ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani"



"Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba"



"Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda Wa na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne"



Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na Soye komai, sai dai kashi kin za™e Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni Waukar matakin da ya dace a kan ki ba"



Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?"



"Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba"

Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.



"Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi ya™i da shi ba, amma abu ya gagara. Na faWi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuWaWe yadda zan yi nesa da talauci.

'yar makarantar da nake ta™ama da ita, abubuwa suka nemi ™wace mini, bayan faWuwa a jarrabbawa. A ta™aice dai a makaranta na samu ™ungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matu™ar sau™i.

Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ™ungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban Wa na Sadik, na kaWu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ™ungiyar, duk da na bayar da waWanda ba jinina ba a ™ungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata bu™ata ta sake taso mini, wadda biyan bu™atar na bu™atar na ™ara taka wani matsayi a ™ungiyar.

Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ™yallen jini a ™asan shimfiWarta ta tashi da ciwon na™uda ta mutu a gurin haihuwa.

Hakan ya sanya dukiyata ™ara haSaka, na yi kuWi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaWai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ™ungiyar asiri nake samun kuWina.

Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ™ungiyar asiri, ya fi ni samun kuWi, kuma duk inda muka je an fi son sa.

Bayan na auri Amina, aka bu™aci duk wani Wa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ™ungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin Wacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ™a™™autawa. Karo shida na shidan saura ™iris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaWan ba, sai dai a yi ta saka mata jini.

Ba a taSa gane Sari take yi ba, an zata larura ce kawai,  Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ™a™™autawa.

Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta.

Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba Waya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba.

Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male.

Na rirri™e ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana ri™e mararta, a dole  na Wauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata.

Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin.

Na takurawa mai scanic Win ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba Waya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding Win yake ba a scanic Win, sai dai a ci gaba da bincike.

Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ™ungiyar asiri nake, ban taSa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba.

Na biya mai scannnic kuWi, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba.

Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke.

Na daWe ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic Win aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba.

Sai ya ce mini idan na ce haka na ™aryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuWin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa.

Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta."



Cikin matu™ar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buWe ido a duniya ba ta taSa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.



Cikin matu™ar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buWe ido a duniya ba ta taSa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.

Da ™yar ta harhaWo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?"



Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya Waure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taSa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar

82 / 126