Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   119 / 126

354K to 357K   out of 377.2K words

Sannan ya ce ita wannan 'ya yanzu ta zama tasa, yana kuma gayyatarka da duk wani wanda yake sha'awar zuwa, gagarumin shagalin bikin yaran nasa. Hammad da kuma Gimbiya Asma'u."

Baba ya numfasa yana ganin abin kamar a mafarki, ya ce "To ai tun da dai da aure a tsakaninsu, a ganina da an ha™ura da bikin shagalin nan"



Turaki ya ce "To ai Wan gidan mulki ne, abu ne aka yi shi da babu wanda ya sani, kuma ya saSa wa al'adarmu, wands a dalilinta an soke al'adar ma gaba Waya, dan haka dole a yi shagalin bikin domin nuna wa Duniya ita. Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, saboda mutum ne mai mulki mai faWa a ji a garin Agadez. Dan haka nan da mako guda za a yi bikin, duk adadin waWanda za su je, za a Wauki nauyinsu tun daga ™asa Nigeria har can, domin yin wannan shagali" Daga cikin Wakin Uwani ta rafsa wata irin guWa mai Wan karen sauti tana faWin "Alhamdillah" har sai da hankalinsu ya koma kan inda sautin guWar ya fito. Gaddafi dai daga baya ya shigo, suka yi ido huWu da Imrana. Imarana ya tashi ya nufe shi, rungume juna suka yi. Gaddafi ya ce "Imrana, wannan karon nisan kiwon naka har ya kai tsawon wannan lokacin?"

Imrana ya ce "Wani nisan kiwo, kame ni a kayi, a ka kai ni makarantar dole, abubuwa ne da yawa suka faru" Ai tuni suka manta da wani batun ba sa jituwa, saboda girman ala™ar jini, suka din ga murnar ganin junansu.

Daga nan aka shiga shigo da kayan auren Nana, sai da Baba ya saki baki, a ransa ya fara tunanin anya mutanen nan su na da hankali kuwa. Saboda shi yanzu al'amuran abin duniya tsoro suke ba shi.

Domin karrama abin da su Baba suke da shi, su Turaki suka ci abincin da aka kawo musu.

Aka gabatar musu da 'yan uwan Nana, Yaya Atine sai rawar kai take, tana nanata musu ita yayar Baban Nana ce uwa Waya uba Waya, ita ta saki Nono ya kama.

Haushi sai da ya kama Imran, Gaddafi ma ya tsuke fuska ya ce "Matar nan duk abin da aka haWa da ita sai ta yi hauka"

Imrana ya ce "Har da wani ita ta saki nono ya kama, kamar nonon akuya, ko kunya ba ta ji ba, kamar ba da ita aka dinga muzguna wa Nana ba"

Ta din ga rawar ™afa tana jan su da hira, sai da ta ba wa kowa haushi.

Da suka tashi tafiya kuwa, Haka Ummi ta shiga ma™wabta ta karSo kayan da aka shirya, na tukuci da za su tafi da shi, dan kar ma wani ya sanya zalama. Kaji, da kayan snacks masu yawan gaske, da dabino kusan kwano biyar da tasoshin turare.

Turaki ya ce karramawar da aka yi musu ta isa, ba za su karSi komai ba, ai Nana 'yar Sultan ce.

Gaddafi ya ce idan ba su karSa ba, ba za su ji daWi ba.

Baba ya ga za su tafi ya yi musu godiya sannan ya ce "To ba za a kawo mini Nanan ba, ita yaushe zan ganta?"

Imam Zahradeen ya ce "Zaka ganta Baba, sai kun zo Agadez biki, za ku ganta in sha Allah, ga Imrana mun kawo maka har gida ai"

Jiki a sanyaye ya ce "Nanan dai nake son gani, amma shikenan mun gode sosai da sosai"

Imrana ya ce "Tun da ni baya son ganina, bari na biku mu koma"

Cikin sauri Baba ya ce "A'a Imrana, kai ma na yi murna da ganinka"

Suka yi murmushi baki Waya, su Mahmoudu ya ce "Duk wanda za su je, a kira a gaya mana adadin mutane, za a Wauki nauyin zuwansu da dawowar su, sannan kuma idan an gama ganin kayan da su za a tafi. Daga nan suka hau mota suka tafi.

Da suka koma gida, aka fara sauke kaya ana bubbuWewa, Baba komawa ya yi gefe ya fashe da kuka, domin hatta shi akwati guda aka yi masa.

Uwani ta ce "Isa meye haka kuma, ai abin farinciki ne, ka daina kukan nan dan Allah"

Ma™wabta ma ba a bar su a baya ba, suka din ga shigowa, sun Wauka ko kayan auren Jamila aka kawo ko na Suwaiba. Mama ba™in ciki ya cika mata ciki, ganin yadda nata 'ya'yan duk suka zama abin da suka zama, babu wani na kirki, ta din ga cizon yatsan ina ma nata 'ya'yan ta saka aka aura wa buzun ba Nana ba.

Uwani ta ce "Allah ba azzalumin sarki ba ne, Nana ta sha wahala a rayuwa, ta yi Wawainiya da yaron nan, da jikinta da ™arfinta. Allah ya yi tana da rabon jin daWi tun a Duniya"



Ummi ta ce "Wallahi Uwani, Nana ta sha wahala, da shi sosai da sosai, Allah ya nuna ikonsa. Kuma shi ma ya yi halacci"



Uwani ta ce "Ba kaWan ba, Allah dai ya ba su zaman lafiya"



Imran ya ce "Dan ma ba ku ji wahalar da ta sha a Niger Win nan ba, da yawon nemansa" Nan Imrana ya gaya musu abin da ya sani. Yaya Atine ta ja baki ta yi shiru.

Uwani ta ce "To Isa, ina fatan ya zame maka izina, akan abubuwan da ka aikata wa yarinyar nan. Kuma ya zama dole a kira mahaifiyarta a sanar da ita komai, kuma a yi shirin tafiya da ita gurin bikin nan, dan ba za ka ci gaba da wannan jahilcin ba"



Imrana ya ce "To ai a Bauchi muka kwana, an je har gida an kai wa Umma lefen ta gani, an yi mata godiya sannan muka taho nan yau"



Uwani ta ce "Ikon Allah, haihuwa mai rana" Duk yadda Mama ta so Soye Sakin cikinta abu ya ci tura.



Can gidan Umman su Nana, ta yi sujuda babu adadi na tsantsar murna da farinciki. Iliyasu kansa bakinsa ya ™i rufuwa, amma ko kallo bai ishe ta ba. Dan ta wani fannin guduwar Nana, sau™i ya sama mata, dan tun da ya san ya yi sanadin Satan Nana, duk abin da take yi masa baya cewa uffan.



"Mai Jidda kin ga ikon Allah ko? Ashe ta wani fannin gara da Nana ta je neman mijin nata, da tana zaune a nan babu lallai su haWu. Allah sarki rayuwa"



Maijidda ji ta yi kamar ta make shi, ya ga abin Duniya, jikinsa sai tsuma yake yi.



*****

Asal na zaune ta dam™e wayarta iya ™arfinta, saboda ganin hoton katin gayyatar bikin taron bikin Hammad da matarsa, da kuma naWe-naWen sarauta.

Hasna ta ce "Asal, ki ajiye wayar nan ki samu ki saka wani abu a cikinki mana" Ta girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunta.

Ji suka yi an buWe ™ofar Wakin, suka Waga baki Waya. Hammad ne ya shigo, jikinsa sanye da shiga ta alfarma. ˜amshin turarensa ya mamaye Wakin baki Waya.

Hasna ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi. Asal kuwa ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na tsananta bugawa cike da tsoro da fargaba, saboda ba ta taSa tsammanin ganinsa ba. Kuma ba ta san me yake tafe da shi ba. Da yatsunsa biyu ya yi wa Hasna alamar ta fita ta ba su guri.



Ayshercool

08081012143

100

LITTAFIN KUŠI NE, A BIYA KUŠIN KARATU KAN A KARANTA.

0069685771

AISHA ADAM STANBIC

08081012143



Asal ta sunkuyar da kanta ™asa, ji take yi tamkar ™asa ta tsage ta shige, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji.

Ya ™arasa ya zauna a gefenta, ya ce "Me ya same ki haka?" Ba ta Wago ba, ta girgiza masa kai.

Shiru ya wanzu tsakanin su, babu wanda ya yi magana. Ya ce "Tun da ba za ki yi magana ba shikenan" Har ya yin™ura, ta ri™e rigarsa ta ce "Sakina ka zo ka yi ko?"



"A'a, dama ai ni ban kore ki ba, na dai ba ki zaSin zama da ni ne, amma na ga kamar ke da mahaifinki, kun fi gamsuwa da na sauwwa™e miki."



"Dan Allah Hammad ka yi ha™uri ka yafe mini, na san laifukana ba za su ™irgu ba, sai a wannan karon Allah ya tona asirina"



Yayi murmushi ya ce "Ba zan yi miki dole ki zauna da ni ba, muddin kin san zuciyarki haryanzu tana son Omar" Wata irin Wagowa Asal ta yi a razane jin abin da ya ce.

"Hmm Asal kenan, duk tsawon zaman da na yi da ke, babu abin da ban sani ba, kar ma ki yi zaton ko wani ne ya gaya mini. Saka mini magani da duk wani nau'i na ™o™arin illata ni da ki ke yi, duk na sani, kuma ina kallonki. Ba domin babu yadda zan yi da ke ba, sai domin ina jin tausayinki, kuma ke ™anwata ce"

Zamowa ta yi ™asa cikin kuka ta ri™e rigarsa ta ce "Wallahi na yi nadama Hammad, na san ko ba ka ce mini komai ba, Hakkinka ba zai bar ni ba. Amma ba laifina ba ne ba, ka sani dan Allah ka yi ha™uri ka yafe mini, kar ka sake ni. Wallahi ina sonka"

"Dama ai ban ce zan sake ki ba, mahaifinki ne ya nemi hakan, kuma nima na so aikatawa amma na duba idan na yi haka, ba ki da wata kyakykywar makoma, bayan gama lalata rayuwarki da aka yi. Kuma ba na son asirinki ya ci gaba da tonuwa a idon Duniya. Uwa uba Nana tana ta yi mini magiyar kar na rabu da ke. Na so samarwa kaina cikakkiyar nutsuwa da rayuwa da wadda bata harin komai daga gare ni sai alkhairi, amma ban san me Allah zai yi mini a sanadin yafe miki ba. Asal zaki koma Wakinki bisa sharaWi, dan ta ni ko yanzu ki ci gaba da duk abin da ki ke yi mini, bai dame ni ba; amma muddin ki ka yi wani na yin™urin cutar mini da matata ko Wana, wallahi sai na Waure ki, Waurin rai da rai ma kuwa. Ba zan taSa yin wasa da duk wani abu da ya shafe su ba, dan haka zaki amince da babu ruwanki da duk wani abu da ya shafe su, balle a zo ga batun cutarwa"

Wani abu raWaWi ya tsirga wa Asal,  wai ita ake gindaya wa sharaWi a kan Nana. Sai dai babu yadda ta iya ta jinjina masa kai ta ce "Na amince"



Ya ce "Ki yi tunani da kyau, kar ki saSa abin da ki ka ce daga baya, na Wauki mataki ki ji haushina"



"Na tabattar da na amince"



Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai ™afafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya ™yale ta a gidansa.

Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya Wago ta tsaye. Ya ce "Na saka an Wan yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji ba™in ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba Waya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da Wansa ba. ˜arara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana.



Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarSiya a kan shirin gudanar da bikin Wan uwansa.

Tuni ba™i suka fara hallara, aka Wauke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate Win da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar ba™i a can. Estate Win da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da ™awayenta a Waya daga cikin gidajen.

Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da ™annenta su Walida.

Gaba Waya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma.

Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faWa jikinta ta rirri™e ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi ha™uri dan Allah"

Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya ™are. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma ™oshin lafiya"



"Umma idan ba ku yafe mini ba, hakkinku ba zai bar ni ba, na yi wauta na yi shirme, na bar ku da fargaba da kuma zullumi."



"Duk ya wuce, ya zama tarihi, Alhamdillah tun da Allah ya amsa addu'armu ya haWa mu cikin aminci da kwanciyar hankali." Tuni idanun Nana suka rine zuwa jawur, ta ™an™ame Maijidda duk da babu wata sha™uwar a zo a gani a tsakaninsu, amma wani irin abu ne mara misaltuwa Nana take jin sa a zuciyarta game da Umman nata.

Ta ™wa™ume ta, ta ™i sakinta ta kwanta lamo a jikinta.

Maijidda ta ce "Ai mijin naki ma ya zo mun gaisa, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Na ce a kawo mini jikin nawa na gan shi, aka ce mini yana ™ar™ashin kulawa ta musamman, zan gan shi amma ba yanzu ba" Nana dai babu baki, ba ta iya cewa komai ba. Sai yanzu take ™ara jinjina girman laifin da ta aikata. Ta tuna lokacin da aka raba ta da Muhsin na Wan kwanaki tashin hankalin da ta shiga, ita kuma ta bar gida kusan shekara uku ba ta waiwaya ba, kuma still ana rarrashinta.

Nene ce ta zo, tare da hadimai, da tarin kayan abinci, tare da su Anty Fati 'yan uwan Mai jidda da ta su motar isowarta kenan.

Babu abin da Nana take yi sai gode wa Allah, sai murna suke yi da ganinta, tare da taya ta murnar matsayin da Allah ya Waukaka ta ya kai ta.

Nana ta ce "Nene ga Ummana, Umma ga Mamana ta Niger ni yanzu a iyaye bayan ke, ba ni da wata uwa da ta wuce Nene. A hannunta na haifi Muhsin, ban san ya zan misalta miki ri™on da Nene ta yi mana ba Umma. Ki yi mata godiya."



Nene ta ce "Dama idan uwa ta yi wa Wanta abu, sai an yi mata godiya ai hakkinta ne ta yi"



Ta mi™a wa Maijidda hannu suka gaisa, su Anty Fati suka hau yi mata godiya. Nene ta ce "Ni ina ™aunar Nana saboda Allah, dan haka duk abin da na yi mata ina jin kamar na yi wa Wan cikina ne"



Sam ranar Nana bata rintsa ba, ji take yi tamkar mai Jidda ta mayar da ita cikinta, gani take idan ta yi bacci zai zamana abin da yake faruwa mafarki ne.



Aka din ga Wawainiya da su, Maijidda da ta taho da 'yan kayanta, na ™ara gyara Nana, yadda ta ga Nene na faWi tashi a kan Nana, sai ta kasa komai.

Washegari su Imrana suka iso, mota uku ta 'yan Kano, hatta Suwaiba da ba ta da cikakken hankali, da Jamila da babu cikakkiyar lafiya, haka Mama ta tarkata ta taho da su. Saboda a yi komai a kan idonta.

Ana cewa ga motar su Baba can, Nana ta zabura za ta yi waje, Nene ta ce "Nana ya haka? Dole fa ki canza yadda ki ke gudanar da al'amuranki, da da kuma yanzu ba Waya ba ne ba. Ki bari za su shigo ai.

Ummi ce ta fara shigowa, suka rumgume juna ita da Nana suka fashe da kuka. Su Uwani ma suka shigo gaba Waya sai falon ya kaure da koke-koke.

Uwani da Ummi kamar su haWiye Nana, Uwani ta ce "Ummi ke ce haka? Kin ga wani irin kyau da ki ka yi?" Nana ta yi murmushi.

Ta ri™o hannun Jamila cike da farinciki, duk ™asan zuciyarta cike yak da mamakin, yadda ta ga Jamila ta yi wata uwar rama mai ban tsoro.

Duk da ba miji Waya suke aure ba yanzu sai da Mama ta yi turus ganin Mai Jidda, ba ta taSa zaton za ta ganta gurin bikin Nana ba. Ta ganta tsaf da ita cikin nutsuwa.

Uwani ta zauna kusa da Maijidda da su Anty Fati, suna hirar yaushe gamo.

Nana dai kasa hirar ma tayi da su, gaba Waya kunyarsu ta hana ta cikakken sukunin haWa ido da su.

Bayan sallar isha'i, barori suka nemi da a yi shiru, Imam Hammad zai shigo. Aikuwa kamar ruwa ya cinye kowa aka yi shiru.

Shi ne ya shigo tare da Mahmoudu, da hadaimai biyu, suka tsaya a bakin ™ofa shi kuma ya shiga. Yana ganin Uwani ya saki murmushi, ya tafi gabanta ya dur™usa.

Ta ce "Šan nan, dama babban mutum ne kai? Ka gane ni?"

Ya ce "Ša ba zai manta uwa ba ai, kuma Wan halak baya manta alkhairi. Ba zan manta da ke ba, Allah ya saka da alkhairi"

Ta ce "A'a ai Wa baya yi wa uwa godiya, mun same ku lafiya?"

Ya ce "Alhamdillah" Ya kalli Ummi da take ta murmushi ita ma, ya ce "Babbar Yaya, fatan kun sauka lafiya, kuma kun ji daWin ™asar tamu"



Ummi ta ce "Alhamdillah, mun same ku lafiya?"



Ya ce "Lafiya ™alau, ina sake amfani da wannan damar, gurin sake baku ha™uri, da abin da Asmy ta yi, duk laifin a kaina yake, nine mai laifin amma ina bayar da ha™uri dan Allah a yafe mana. Sannan ina sake yi muku godiya sosai da sosai, Sultan ma ya ce a gaishe ku"

WaWanda ba su san shi ba, suka din ga yaba kyawu da kamalar Hammad.

Daga nan ya nemi zai tafi da Nana, za ta je gurin su Baba inda suka sauka su gaisa, sannan a dawo da ita.



Su na shiga mota, ya kwanta a jikin Nana yana sauke numfashi ya ce "Da na yi niyyar idan aka gama taron nan, ki yi kwana biyu ki huta, sannan ki tare amma gaskiya yanzu na fasa, ji nake kamar na gudu da ke"



Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bari a kwana biyun"



"Ba zan iya ba, ana tashi kawai a kai mini ke gida, gidanki ya kammala komai an saka mana, mukaWai muka rage mu shiga" Yayi maganar yana sumbatar bakinta.

"Ya naga jikinki

119 / 126