Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 126

81K to 84K   out of 377.2K words

take son yin magana da ke"" wata irin zabura Nana ta yi cikin murna ta ™ara"

nutsuwa.

"""Assalamu alaikum"""

"""Mama"""

"""Na'am Nana ya ki ke?"""

"""Lafiya ™alau, ya gida ya su Walida?"""

"""Su na nan lafiya ™alau Alhamdillah, ya mai gidan na ki?"""

"""Lafiya kalau Mama"""

"Sayyid ya ™ura wa Nana ido, yana ayyana abin da take ji a zuciyarta. Saboda fara'ar da ta mamaye"

fuskarta.

"""Ki na ji Nana, ina nan ina ™o™ari, duk yadda zan yi zan zo Kano, na ganku in sha Allah, ki ™ara ha™uri, na"

"san kin yi ki ™ara, ina nan tafe in sha Allah"""

"""Kar ki damu Mama, ni jin muryar nan ta ki ma da na yi, na ji daWi sosai. Kuma in sha Allah kafin ki zo, za"

"mu riga ki zuwa da yardar Allah"""

"""A'a ni Win dai zan zo na gan ku in sha Allah, ina fatan dai babu wata matsala?"""

"""Babu matsalar komai Mama"""

"""Yauwwa Nana, zan ci gaba da jaddada miki, ki ri™e Allah ki ri™e addu'a. Ki bi mijinki ku zauna lafiya. Ina"

"fatan kin fafa sana'a Nana?"""

"""A'a Mama, amma zan fara in sha Allah"""

"""A'a Nana, kullum ki ce mini za ki fara, amma ba ki fara ba. Ina da buhun barkono, zan sayar na turo miki"

"kuWin, ki fara sayar da wani abin. Idan kuma barkonon ki ke so, na aiko miki Nana. Ni dai ban taSa ganin mijin nan naki ba, amma yadda su Fati suka bani labari, da yadda nake jin muryarki, a duk lokacin da na kira waya, ina samun nutsuwa. Allah ya ™ara muku zaman lafiya. Amma ki yi sana'a, tun da mai ™aramin ™arfi ne, ki taimaka masa, kar ki sakar masa nauyi gaba Waya"""

"""To in sha Allah Mama, amma dan Allah ki bar barkonon ki, zan yi sana'ar nan da yardar Allah, na rasa"

"abin da zan fara sayarwa ne. Amma zan fara"""

"""A'a zan sako miki buhu Waya a mota, ki gwada, kar ki zauna haka ba kya juya taro da sisi"""

"""To Mama in sha Allah, na gode sosai da sosai """

"""Yauwwa, haryanzu ba ki da lambar Imrana ki turo mini"""

"Nana ta ce ""Ba ni da ita Mama"""

"""To shikenan, ki gaida mijin naki"" suka yi sallama, ta sauke wayar a hankali, ta yi shiru tana zancen zuci."

"Ta san da Mamanta su na tare da Baba, da ko ba za ta Wauke mata Wawainiyar da take ciki ba, za ta tausaya mata ta taya ta jajanta lamarin. Amma tun da ta je gida ta sanar da Baba halin da take ciki, ko ta waya bai kira ya tambayi ya suka ™are ba, ya kuma mai jikin ba. Dama Mama ba a magana, mutanen da"

"tun da ta yi aure, ba su taSa taka gidan da take ba, yaushe za ta sanya ran su damu da halin da take ciki."

"Tana iya ™o™arinta, gurin rintse idanunta, daga aibun iyayenta, saboda kar zuciya ta Webe ta, ta afka cikin"

"fushin Ubangiji, amma daga yadda Baba ya yi mata gurin aurenta, zuwa yanzu zuciyarta na ™o™arin"

bijirewa.

"""Ya ne?"" Ta ji muryarsa. Firgigit, ta kalle shi ta ce ""Babu komai. Mama na gaishe ka"""

"""Ina amsawa, ina son na yi magan da ita, amma ina tsoron na karSi wayar, maganar ta Wauke"""

"Nana ta ce ""Haka ne, bari na fita da gas Wina waje, na dafa mana taliya, ga kayan miya na aika yaran"

"Ummi, sun sayo mini, ai za ka ci ko?"""

"""Ke ma za ki ci ko?"""

"Ta yi dariya ta ce ""In sha Allah"" Ta Wauki kayan girkinta, ta fita kusa da Wakinta, ta Wora."

"Gaisawa kawai suka yi da matan gidan, ta nutsu a kan aikinta. Tana zaune mata na ta shiga suna fita,"

"kowacce da abun da yake kawo ta. Da tana da isasshen guri, a Wakinta, da babu abin da zai fito da ita waje yin girki, balle ta din ga kallon tumasancin da matan suke yi. Har da wadda daga ita sai hijjabi, da zani, babu riga babu brezia. Idan masu gidan suka dawo, haka suke tsallake mata su shiga Wakunan su."

"Tun da Nana ta kammala girki, ta tattara komai nata ta shige Waki."

"Ta ji daWin ganin yadda yau yake iya cin abinci, dan haka ita ma ta zage, duk da ba wani daWi yake yi mata"

ba.

"Saboda rashin kamun kai na matan layin nan, sukan kai har goma da rabi, su na shiga su na fita a gidan"

tamkar bariki.

Ayshacool

"Nana har ta fara murnar abincin da ta ci ya zauna, lokaci Waya ya taso sai da ta amayar da shi baki Waya."

"Tana fitowa daga banWakin, ya ™ura mata ido, har ta ™araso ta kwanta a jikinsa, tana Sata fuska."

Ya ™an™ame ta yana faWin sannu.

""" Šan ka ya hana ni cin abinci, kuma yunwa nake ji"" ta yi maganar hawaye na cika mata ido."

"""Yi ha™uri, sannu, to mu je Asibiti""ya yi maganar a jere."

"""A'a Sayyid, dole mu din ga tattala kuWi yanzu. Yunwa nake ji sosai"" ta yi maganar cikin shagwaSa."

"""Me zan sayo miki?"""

"""Ba komai"" ji ta yi numfashinsa yana fita da sauri da sauri, a tsorace ta kalle shi ta ce ""Sayyid jikin ne?"""

"""A'a"" ya furta a hankali."

"""Dan Allah ka yi ha™uri, da wasa nake yi maka, ai na san mata masu ciki, su na fuskantar irin haka, dan"

"Allah ka kwantar da hankalinka. Ba na so mu zauna shiru, shi yasa na tsokane ka"""

"""Tom"" ya amsa a hankali."

"Kasancewar jikinta babu ™wari, ya sanya ta kwanta da wuri, ganin shi ma ya samu bacci."

"A cikin bacci ta din ga jin wani irin rugugi, tamkar na hadari, ga shi ba lokacin damina ba ne. Ta buWe"

"idonta, ta ji wani irin huci, na fitowa daga gurin da yake kwance, ga wani irin nishi da kakari da yake yi, tamkar an yanka rago."

Ayshercool

08081012143

Ayshacool

"Ta ja ta zauna ta yi shiru, abin duniya ya ishe ta, sai kuma ta koma tunani kamar yanzu ta yi rauni a ibada,"

"shaiWan ya yi galaba a kanta, kan cewar idan ta yi addu'a wahala ta fi tsananta a gare ta. Domin hatta"

"addu'a kwanciya bacci, ranar da ba ta yi ba, sai ta kwanta ta tashi lafiya ™alau, ba mafarkai babu ciwon ™afa ko baya, ko ma jikin baki Waya. Azkar ma ba ko yaushe take iya yi safe da yamma ba."

"Ta yin™ura ta tashi, ta je ta Wauro alwala, ta zo ta sake haska shi, ta ga bacci yake yi, ta nemi guri ta"

"kwanta, ta Wora hannunta a goshinsa, tana karanto addu'oin kwanciya bacci."

*

"Jamila na mi™e a kan katafaren gadon, ga chips a gaban ta, ga kakkauran shayi, hannunta ri™e da"

zu™e™iyar wayarta.

"Abba ne Wan gidan Hajiya Sa'a, yake yi mata magana ta what's app. ""˜anwata, shi ne tun da ku ka sauka,"

"ba ki neme ni ba ko?"""

"""Ba haka ba ne, ba ni da data ne"""

"""Kuma ba ki gaya mini ba, bari na saka miki. Ina Mummy?"""

"""Ta fita"""

"""Wai ina ku ka je ne a Abujan?"""

"Jamila ta yi masa reply da ""Ban san sunan gurin ba, wani gida ne dai mai kyau sosai"""

"""Ok, to dan Allah ki kula da kan ki sosai da sosai, Allah ya bayar da nasarar abin da aka je nema, na ji ta"

"ce taron kasuwanci ne ko?"""

"""Wallahi dai ban sani ba tukuna"""

"""Haka ta ce mini ni, ta tafi da ke ku ka bar ni a gida, ai shikenan"" har za ta rufe data ta ga 10gb na data."

"Sai ta washe baki ta ce ""Har 10gb na gode sosai da sosai"""

"Abba ya ce ""Babu godiya tsakanin, Yaya da ™anwarsa, ki kwanta da wuri ki yi bacci. Ki yi addu'a kuma, sai"

"da safe"""

"""To yayana na gode sosai da sosai"" suka yi sallama, ta rufe laste seen Win ta da online, ta tafi kallon"

videos a tiktok.

"Hajiya Amina ce ta shigo Wakin, ta ce ""Jamila ba ki yi bacci ba?"""

"""Eh Mummy, kin dawo?"""

"""Eh zan sake zuwa wani gurin ne, babu lallai na dawo da wuri, za mu yi meeting, ki yi kwanciyar ki"""

"""To shikenan, sai kin dawo"""

"""Yauwwa amma ba kya bu™atar wani abu, ko jin yunwa ko?"""

"Ta ce ""A'a a ™oshe nake"""

"""To sai na dawo"" Hajiya Sa'a ta fice, ta rufe wa Jamila ™ofar."

****

"Nasiru tun ranar da ya je gidan Ummi, su Nana suka tashi, ya koma gida ya ba wa Baba labari. Baba ya ce"

"""To shikenan ma, ta kwana gidan sau™i, tun da sun samu mafita."

"Ni na san babu yadda za'a yi ma a kore su haka kurum, dan mijinta ba shi da lafiya akwai dai abin da suka"

aikata.

"""Dama wasu Buzaye abin yarda ne, kalli kayan da suka kawo mata fa, Allah ka dai ya san mugun abin da"

"suke aikatawa, har aka kama su. Kai Nasiru to ya gidan da suka koma yake?"" Cewar Mama cike da son jin"

™wa™waf.

"Nasiru na tauna rake ya ce ""Normal dai gida ne, amma da wasu a gidan, wancan gidan da suka baro ya fi."

"Šakinsu ya fi kyau da girma, banWakin har da famfo ga wuta, wannan kuwa gaskiya bai yi kyau ba"""

"Ta sake cewa ""Kuma da gaske mijin nata ba shi da lafiya?"""

"Ya Waga kai ya ce ""Kai, sosai yana daurewa ne kawai, idan ya yi magana haki yake yi fa, wannan karon na"

"ga ya yi magana sosai. Da an yi abu sai ya ce mata Rayuwata, ki yi a hankali ki zauna ki huta"""

"Sai ta sake zabura ta ce ""Au rayuwata yake ce mata"""

"""Kai Mama dan Allah ki rabu da ni, haba wannan tambayoyin kamar a kabari"""

"""Kai a gidan uban wa ka san kabarin, sai ka yi saSo tukuna"" ya yi mata shiru, ya tashi ya Wauki rakensa da"

"yake sayarwa a ™ofar gida, da wu™a ya fice."

*

"Tun da garin Allah ya waye, Nana take tashin sa, amma ya ™i tashi, irin wannan baccin da ta farka ta ga"

yana yi dai shi yake yi.

"Gaba Waya ta tsorata, ga dai numfashi yana yi, idan ta taSa zuciyarsa tana bugawa da ™arfi jefi-jefi."

"Ta saka shi a gaba, ta ma rasa abin da ya kamata ta yi. Ummi takira ta a waya, ta tambaye ta babu"

"matsala babu wani abu da take bu™ata, ta ce mata eh."

"Har sha biyu na rana Nana ta rasa abin yi, ta kunna karatun Al™ur'ani a wayarta, ta ajiye masa sai dai bai"

fi mintuna talatin ba wayar ta Wauke. Ji ta yi ana bubbuga ™ofar Wakin nasu. Ta yin™ura ta tashi ta saka

"hijjabi, ta je ta buWe."

"Sajida ta gani a tsaye, ta Wan saki fuskarta su ka gaisa. Sajida ta ce ""Mun ji shiru ne, ko ™ofa ba ku buWe"

"ba, shi ne na ce bari na ™wan™wasa ko lafiya?"""

Ayshacool

"Nana ta ce ""Lafiya ™alau Alhamdillah, ba ma jin daWi ne daga ni har shi, shi yasa ba mu fito ba, amma"

"lafiya ™alau muke"""

"""Ok Allah sarki, ko dai amarya ce ne, haryanzu ba a gama cin amarci ba?"" Ta yi maganar tana kallon"

Nana.

"Nana kawai ta yi murmushi, ta koma Wakin, ta buWe ™ofar ta saki labule. Dama ta gyara komai a Wakin. Ta"

"dafa shayi da habbatussauda, da citt, kanumfari, kimba, na'ana'a kamar yadda yake dafawa, ta zuba a flask ta rasa me za ta dafa, dan ba ta son cin komai."

"Tana nan zaune, sai ga 'yar gidan Ummi ta zo, Islam. Ta kawo wa Nana faten doya da wake, ya sha"

"alayyahu. ˜amshin attaruhun da ya daki hancin Nana, sai da ta haWiye yawu. Ta ba wa yarinyar wayarta,"

ta mi™a mata caji.

"Ta Wan zuba abincin tana ci, ta zuba masa ido, tana tunanin ko Asibiti za ta nemo mota su tafi, amma"

kuma sai ta tuna abin da ya yi jiya ba shi da ala™a da ciwon Asibiti.

"Tana ta tunanin mene ne mafita, kuma ba ta son waWannan maganannun matan, suk san halin da suke"

ciki ita da mijinta.

"Tana nan zaune tana bin sa da kallo, ta jiyo hirar Sajida da Barira, da wasu ma™wabta. Barira ta ce ""Sajida,"

"jiya da daddare, kin ji kamar ana nishi cikin dare?"""

"Sajida ta ce ""Wani irin nishi kuma? Ni ban ji ba"""

"""Wallahi nishi, kamar ana kokowa kamar wani gurnani, ga Amiru ya yi bacci, na din ga jin tsoro na kasa"

"bacci, na ce ko gamo na yi da aljanu"""

"""Ba wasu aljanu, ba wani aljani da yake razana mutum, da wani sauti ko wani abu, duk ™aryar banza ce"""

"""Kai ni dai na tsorata, kuma daga nan haka na din ga jiyo sautin, wajen nan"" ta yi maganar tana nuna"

Wakin Nana.

"Sajida ta yi magana ™asa-™asa, Nana ba ta ji me su ka ce, sai ji ta yi sun tuntsure da dariya. Ta yi ajiyar"

"zuciya, ta fara tunanin ko dai wani gidan za su kama, ta san idan suka ci gaba da zama a gidan nan, asirin su na iya tonuwa, wanda ba za ta so hakan ba."

"Babu tsammani ta ga ya tashi zaune, ta tashi da sauri ta nufe shi cikin kulawa ta ce ""Sannu Sayyid, ka"

"tashi?"" Shiru ya yi yana bin ta da kallo, tamkar ya ga wata ba™uwar halitta daban."

"""Sannu ya jikin naka?"" Yanzun ma bai yi magana ba, ya ci gaba da bin ta da ido. Ta yi ta magana ya yi"

"shiru, tamkar kurma. Can kuma ya tashi ya shiga banWaki ya fito ya nemi guri ya zauna."

"""Sayyid, za ka yi sallolin da ba ka yi ba, Asuba da kuma Azahar, duk ba ka yi ba"" ya yi mata shiru, ya"

"kawar da kansa gefe. Ta tsiyayo ruwan shayi a kofi, ta zo gabansa da cokali ta zauna ta ce ""To Wan sha tea Win, sai ka ci abinci ka yi sallar"" ya kawar da kansa ya yi mata shiru. Ta ™ara matsawa kusa da shi, kawai ya hamSare kofin ruwan zafin ya kware mata, a wuyanta zuwa jikinta. Wata irin zabura ta yi, ta ja da baya tana tsuma, saboda yadda zafin ya ratsa fatarta. Ko kallon inda take bai yi ba, ya ja gefe ya ci"

gaba da huci.

"Ranta ya yi mummunan Saci, amma ta kalli fuskarsa, ta tabattar da yana hayyacinsa, babu yadda za a yi"

"ya yi mata haka, dan haka ta yi shiru ba ta ce komai ba, ta tashi ta cire kayan, ta saka wasu."

"Haka suka wuni a Wakin, bai yi salla ba, bai ci abinci ba, kuma bai yi magana ba."

"Ana yin sallar magariba, ya haura kan katifa ya kwanta."

"A jikin mudubi ta tsaya, tana haska ™irjinta, yadda inda ruwan zafin ya zuba a ™irjinta, ya Wuri ruwa."

"Ta hasaka kan katifar, ta ga ya ci gaba da wannan baccin, mai rabin idonsa a buWe, ta nemi guri a ™asa"

"lungun wardrobe ta kwanta. Sai dai yau ta kwanta cike da fargaba da kuma zullumin abin da zai faru, kar"

ta je ya sake sha™e ta.

"Sam ta kasa bacci, da ta fara sai ta razana ta buWe idonta, dama a kunne ta bar fitila ba ta kashe ta ba."

****

"Shukura ce tare da Sagir a zaune a cikin mota, ta zuba wa ™ofar gate Win Asibitin ido. Ya ce ""Ya dai? Ki"

"shiga ki fito ina nan ina jiran ki"""

"""Wallahi haka kurum gabana yake faWuwa, ko hanyar Asibitin nan ba na son na ni an faWi sunan ta"""

"""Shukura duk saboda da Wan ki ya rasu, ban taSa ganin mutum mara tawakkalli kamar ke ba"""

"""Ba haka ba ne, wallahi yanzu ma ban da Mummy ta matsa, ba zan zo ba, bari na je na dawo"""

"Sagir ya ce ""Tom ki yi masa sannu, ni na zo na duba shi dama"" ta jinjina kai ta fice daga motar."

Ayshacool

"Tana shiga cikin Asibitin, ta din ga jin kamar a lokacin ne, za a yi mata aiki a cire Wan cikinta, wata irin"

fargaba da yanayi mara daWi ta din ga ji a jikinta.

"Ta ci gaba da jan ™afafuwanta, jiki babu ™wari ta nufi Wakin da Hajiya Amina ta kwatanta mata. Sai da ta"

"yi knocking sannan ta tura ™ofar ta shiga. Fadila na zaune a gefen gadon kusa da Alhaji Fatuhu, ga cikinta"

"ya yi wani irin girma, tamkar tana yin™urawa Wa zai faWo. Sai dai gaban Shukura ya yi mummunar faWuwa,"

"ganin yadda Alhaji Fatuhu ya koma. Dogon mutum mai jiki, mai hasken fata, ya koma ba™i ™irin ya yi wata irin mahaukaciyar rama, jikinsa tamkar fata kawai aka yafa wa ™ashi. Ta ji kanta ya sara, wani irin abu ya soki zuciyarta. Wani irin wari Wakin yake yi, tamkar na mushe, ga shi dai babu ™azanta a jikinsa, ga Wakin a share a goge yana ™amshin turaren wuta, amma ita warin mushe ta din ga ji, da ba ta san daga"

ina yake fitowa ba

"Fadila tana yi mata sannu da zuwa, amma ba ta kula ba, ta ™arasa kan gadon, ta zaune. Yana daga zaune,"

"ya kalle ta ya yi murmushi tamkar mai raWa ya ce ""Shukura"""

"""Daddy, haka jikinka ya koma?"" Ta yi maganar cikin matsanancin tashin hankali, da tuni hawaye ya"

wanke mata fuska.

"Ya ce ""Alhamdillah, ai na ji sau™i ko Maman Muhsin?"" Fadila ta jinjina kai hawaye na zubo wa daga"

idonta ita ma.

"""An ce mini kin haihu Wan ya rasu, ban zo na duba ki ba, na haWu da wannan larurar"""

"Cikin kuka ta ce ""Dan Allah ka yi ha™uri ban zo na duba ka a kan lokaci ba. Ban zaci abin ya kai har haka"

"ba"""

"Ya yi murmushi yana jinjina kai, aka turo ™ofar Wakin,gaba Waya suka waiwaya Doctor Sharif ne ya shigo,"

tare da wata nurse.

"Yana ganin Shukura ya yi murmushi ya ce ""Hajjaju kwana da yawa, ni da na yi zaton zuwa yanzu ma, kin"

"dawo mana awo? Ya gida ya mai gidan?"""

"""Lafiya kalau"" daga haka ta ja baki ta tsuke. Sai da ya sha jinin jikinsa, da irin amsawar da ta yi masa."

"Ya kalli Fadila ya ce ""Uwar biyu, ya mai jikin?"""

"Fadila ta ce ""Alhamdillah mun gode Allah"""

"""Ma sha Allah. Na ce ki je a duba ki, idan inducing Win ki za a yi, idan ma tiyata ya kamata a yi miki to."

"Amma kin ™i"""

"""Kar ki soma yarda, a kashe miki Wa, gara ki je wani Asibitin"" tsit suka yi baki Waya, suka waiwayo su na"

kallon ta.

"Jikinsa ne ya yi wani irin sanyi, wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa. Cikin damuwa ya ce ""A kashe mata Wa"

"kuma Shukura"""

"""Nawa ba a hannunku ya rasu ba?"""

"""Kuma ai ba kya ce za a kashe mata Wa ba, nakin ma, Allah ne ya kawo ajalinsa"""

"Shukura ta ce ""Ba zan dai sake zuwa Asibitin nan na haihu ba. Daddy Allah ya ™ara afuwa. Maman"

"Muhsin sai anjima Allah ya raba lafiya"""

"Fadila ta ce ""Amin, mun gode sosai da sosai Shukura, ki gaida gida. Mummy ma an ce ta tafi Umara ko?"""

"""Eh wallahi. Allah ya raba lafiya"" har Shukura ta fice, jikin Doctor Sharif tsuma yake

28 / 126