Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   89 / 126

264K to 267K   out of 377.2K words

kai ta, ta tsaya saroro tana kallon Wakin, ta Waga kai ta kalli agogon Wakin, ™arfe Waya da rabi na dare.



"Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa.



"Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado.

Ta yi ™yam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana ™ara ™arewa Wakin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake Wakin ya fara damunta.

Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa.



"Me yasa ki ka fito?"



"Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a ta™aice.



"Ohh yi ha™uri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haWe rai.



"Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman.



Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faWo ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu.



Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?"



Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?"



"Šakin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki.



"To mu je can Win, nima ban ci komai ba, wata™ila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin"



Nana ta ™ara haWe rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana bu™atar duk wani abu da zai ™ara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai".



"Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, Wauki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon.

Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi Wakin da aka ajiye ta.

Sosai ta fara ™o™arin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin.

Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta.

Har za ta yin™ura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya ™ule ta, ta ™uduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan.

To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta.

Gaba Waya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta ha™ura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta.



Sai dai ta ™i yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yin™urin yi mata wani abin.



Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn ˜aisar.



Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluSa da wani ba™in mayafi.



Ya kalli fuskarta da ke Wauke da damuwa ya ce "Ya dai?"



Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?"



"Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?"



Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka da lafiya ka ke kwanciya a nan gurin"



"Lafiyata ™alau. Na Wauka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?"

Ta nemi guri ta zaune a gefen ˜aisar ta ce "Ni fa ba na ™aunar mutumin nan, fatana kawai ya bani Wa na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni"



˜aisar ya ce "Waye ba kya ™aunar yanzu?"



"Sayyid"



"˜arya ki ke yi" ta ce "˜arya kuma?"



"Da dai ban san halinki ba ne"



Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko ™aunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba Waya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna"



˜aisar ya yin™ura ya tashi zaune, yana ™ara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai Sulle muku ba"



"Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na bu™atar sa a rayuwata gaba Waya" ˜aisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake.

"˜aisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba.

Mi™ewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?"



"A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita".



Nana ta saka hannu ta Wan ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali.

Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi ba™i ™irin tamkar an ™ona shi.

Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?"



"Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye.

Gaba Waya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba.

Har gari ya yi haske, tana zaune a ™asa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin ˜aisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai.



"Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da ˜aisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin ™i." Sosai take son mantawa da tunanin ˜aisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin ˜aisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki.



Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya Wan tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haWi da uwar harara.



Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga Wana"



"Ka daina danganta mini Wana da kanka, ba shi wata ala™a da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa.



"Ba shi da ala™a da ni, sai da ˜aisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah"



"Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba Wa na na gani ya zo hannuna ba".

Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa.

Ta Waga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faWi, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka.

Ta sunkuyar da kanta tana haWe rai.

Ta sake Waga ido ta suka haWa ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin ™aunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake ro™onki, ki bani dama ki ji ta bakina"



"Ni babu abin da zan ji, na ce maka Wana kawai nake bu™ata"



Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina"



Wata irin Wagowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haWe bakinsu.

Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya ™arfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin Wan Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta ™yale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya Wago fuskarta yana kallonta.



Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taSa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ™aunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar.

"Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a Wakin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar Wakin, ta bi bayansa da harara.



Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri Waya da na jikin babansa, sai ™o™arin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai ™amshin turare yake yi.

Hammad ya saka hannu ya karSe shi fuskarsa Wauke da murmushi har da wata irin Soyayyiyar ajiyar zuciya.



Hammad ya ce "Mu je ko?"



Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba Waya, ina jin ban kyauta ba gaba Waya"



"Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah"



AREWABOOKS



Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi al™awarin babu abin da zai sake haWa ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da Wan nan ba, saboda ya saSa al™awarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara al™awari. Amma kai ma Wa ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba"



"Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini"



Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya mi™a mata Muhsin ta karSe shi, suka shiga mota.



*****

A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karSi ayabar nan ya ci?"



"Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba Waya"



"Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karSa ta ci, dan aikin da aka yi ya Saci ya lalace."



Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya"



Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce."

Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.



Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai ™amshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka.



Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?"



"Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da Wa, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya"



Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?"



Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi ha™uri ki bani lokaci, ina kan bincike ne"



"Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga"



Sultan ya ce "Na sani, ki yi ha™uri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza ha™uri da samun nutsuwa.



Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa.

Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba Waya suka zuba masa ido suna kallonsa.

Hammad ya nemi guri ya zauna a ™asa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?"



Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da ha™uri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faWa. Ina cikin hayyacina na faWi abin da na faWa, kuma da shaida a kan abin da na faWa".

Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo Wakin shima."



Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai"



Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?"



Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa"



Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karSi hukuncin laifina, na aikata abin da ya saSa wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a ™asar nan"



Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?"



Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun Soye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar ™asar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta ™ar™ashin ™asa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki Waya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san ha™i™anin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu.



Abin ya Waurewa Sardauna kai, gaba Waya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara.



Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haWu da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi ™o™arin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba"



Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?"



Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria"



Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?"



Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba"



Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daWe, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaSi"



Hammad ya mi™e ya ce "Ina zuwa"

Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta ™o™arin basu amsa da rufa wasu abubuwan.



Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da Wa a hannunta.



Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haWe rai ta sunkuyar da kai.

Kafin su ™ara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa ™asa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin.

A sukwane Sultan ya mi™e tsaye. Imam Hammad ya karSi Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad Win sa yana ™arami.

Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri Waya. Ya mi™a hannu ya Wauki Muhsin yana faWin "La haula wala ™uwwata illa billah"



Su kan su Sardauna da Matawalle, ™ura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri ™arya ne ya ce wannan Wan ba na Hammad ba ne ba.



Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da Wa"



Sultan ji yake yi tamkar ya haWiye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana mi™awa Hammad hannu ya Wauke shi.



Sardauna ya mi™e ya ce "Yanzu ina uwar yaron take"

"Tana nan" Imam ya faWa yana sunkuyar da kansa ™asa.



Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na bu™atar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu.

Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai."



Nene ta ce "Ranka ya daWe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da

89 / 126