Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   33 / 126

96K to 99K   out of 377.2K words

gwaje-gwajen da aka yi masa, da kuma katin da aka rubuta masa magunguna."

"Ya karSa ya duba a tsanake, ya duba Bp Win Sayyid, ya duba ™irjinsa da stethoscope."

"Nana ta ce ""Doctor yaya jikin nasa? Me ka gani?"""

"Bai kalli Nana ba ya ce ""Me yasa ba ku dawo follow up ba"""

"Ta ce ""Ai ba a bamu lokacin dawowa ba. Dama ni ce naga yakamata mu dawo Win. mu na ta ™o™arin"

"kuWin allurar su haWu ne, ko ba su haWu ba, zamu yi ™o™ari ko a anan Asibitin gwamnatin ne, sai mu yi"

"booking a fara yi masa"""

"Likitan ya ce ""Ki na ji na 'ya ta?"""

"Ta ce ""Eh"""

"""Ai mijinki ne ko?"""

"Sayyid ya jinjina kai. ""To a duniya babu wani abu da Allah ba zai iya ba, babu shi. Batun allura ki bar"

"wannan a hannun Allah. Kuma dan babu kuWin allaura ba za a daina ganinsa ba. Zamu ci gaba da gwada shi, mu na ba shi magungunan da suka dace. Idan Allah ya yassare kwa zo a yi daga baya. Kuma jikinsa Alhamdillah da sau™i sosai da sosai. Jinin dai haryanzu bai sauka yadda ake so ba. Amma zai sauka da yardar Allah. Kawai ki din ga kiyaye damuwarsa da Sacin ransa. Idan kuma akwai wani abu da yake damunsa, ki zauna da shi ku tattauna ki ga ta ina za ku shawo kan matsalar?. Amma babu wani abu in sha Allah"" Duk da ba lafiya likitan ya ba su ba, amma kalamansa akwai dattaku da ™warewa a kan aiki a"

cikin sa. Dan haka sosai Nana ta samu relief.

"Ya rubuta musu lambarsa ya ce ""Duk lokacin da za ku zo, ku kira ni, na baku ranar da nake aiki, ya zo ya"

"din ga ganina."" Nana ta din ga yi masa godiya da addu'a shi da iyayensa."

"Sayyid ya ja wata takarda, ya yi rubutu ya mi™a wa likitan. Likitan ya karSa ya duba. Ya yi murmushi ya ce"

"""Madam, ashe kema babu lafiya ya ce na duba masa ke"""

"Nana ta yi murmushi ta ce ""Rashin lafiyata, ai ba komai ba ce a kan tasa, ni na fi damuwa da shi Win dai"""

"""A'a tun da ya nemi alfarma, ai dole a yi masa"""

"Ya duba Nana, ya yi wa Sayyid bayanin laulayi ne kawai yake damunta, ya rubuta mata abin da zai rubuta"

"mata na magani. Ya kuma ba ta gwaje-gwaje. Sayyid ya ™i tafiya, sai da suka yi gwaje-gwajen."

"Suka koma, ya tabattar musu da babu wata matsala, satin cikinta uku da kwanaki, ya rubuta mata"

magungunan da za ta yi amfani da su.

"Suna tafe a adaidaita sahu, Sayyid ya kasa ri™e murmushinsa, ya kai bakin sa kunnen Nana ya ce ""Saura"

"kwana nawa ki haihu?"""

"Ta kwashe da dariya, ta ce ""Ina na sani, ko cika wata Waya bai yi ba ma, mu dai ci gaba da addu'a Allah ya"

"bar mana, ya bamu Wa na gari"""

"Ya amsa da ""Amin."""

"A bakin titi, Nana ta yi sayayyar salak, saboda shi take sha'awar ci. Suka shiga layin gidan na su."

"Su na zuwa gidan, Nana da sauri ta shiga banWaki, saboda fitsarin da ya cika mata mara. Sayyid tsayawa"

"ya yi, yai shiru yana ™are wa Wakin kallo."

"Nana ta fito bai ce mata komai ba, ta Wauki cylinder gas, ta ce ""Sayyid gas ya kusa ™arewa, idan zaka iya"

"fita in anjima sai mu je titi tare mu Wuro"""

"Ya ce ""To"""

"""Bari na sake Wumama miyar"""

"Ta fito tsakar gidan kenan, Sajida ta ce ""Nana, Allah ya taimake ki, da tuni da ke za a tafi bayar da shaida"""

"Cikin rashin fahimta Nana ta ce ""Shaidar me?"""

Ayshacool

"""Jiya hirar da ku ka yi, har ki ke yi wa Barira faWa, a kan matar nan. Daga jiyan nan zuwa yau magana har"

"ta kai kunnen matar. Ta din ga kuka mijin ya ce ba zai yarda ba da 'yan uwanta. Da yyayyenta ne za su zo su zane Barira. Mijin matar ya hana aka kai ta police station. Tun bayan fitar ku tana can, duk sai da"

"muka je bayar da shaida. Wata™ila dai kafin magariba a sako ta, ta dawo gida."""

"Nana ta numfasa ta ce ""Gara da Allah ya sa ba na nan, dan babu inda zan je, shi yasa a rayuwa yake da"

"muhimmanci mutum ya iya bakinsa. Wannan tara matan da ku ke yi, ku na surutai marasa amfani duk ba hanya ce mai Sullewa ba"""

"Sajida ta ce ""Wallahi haka ne, shi yasa ki ke burge mu ma"""

"""Allah ya kyauta"""

"Har Nana ta yi haWin salak Win ta, ta fara ci, ya lura ba ta fahimci abin da yake faruwa ba, shi ma kuma bai"

"gaya mata ba, ya ci abincin. Ta gama ci ta kalle shi ta ce ""Sayyid, ka yi mini addu'a, Allah ya sanya kar na yi aman salad Win nan, na rufe sauran anjima zan sake ci"""

"""Kin cika yaji, sai kin yi ciwon ciki ko?"""

"Ta Wan waro ido ta ce ""Dama ka gani?"""

"""Eh ina kallon ki"""

"Ta Wan yi murmushi ta ce ""Idan babu yajin, ba zai yi daWi sosai ba. Amma yanzu ya ka ke ji a jikin ka?"""

"""Ba sau™i"""

"""Subhanallah, ba sau™i kuma?"""

"Ya ce ""Eh, kin je ki na hira da likita a gabana"""

"""Amma ko ba komai, ya kwantar mini da hankali, bai ce mini zaka mutu ba, kalamansa sun bani ™warin"

"gwiwar da yakamata na samu"" ta yi maganar ™walla na cika mata idanu."

"Ya girgiza mata kai ya ce ""Kar ki bari su zubo""."

"""To ba kai ne ba, komai na yi sai ka ji haushi na?"""

"Murmushin sa mai matu™ar ™ayatarwa ya yi, ya ce ""Ba haushinki nake ji ba, tsaro nake ba ki, saboda"

"tawa ce nikaWai. sourire (smile) ki yi murmushi mana"" ta no™e kafaWarta tana tura baki,ta juya masa baya."

"Ya matsa bayan nata, ya sumbaci saman bayan ta, ya zagayo da hannunsa ta cikinta, ya kwantar da"

"kansa a kan kafaWarta. Gaba Waya jikinta ya yi sanyi. Damuwa ce ya ziyarce zuciyarsa, jin yadda Nana ta saki jiki sosai da rungumar da ya yi mata, ko ba a gaya masa ba ya san abin da yake ranta, tuna cewar babu abin da zai iya tsinana mata, ya sanya a hankali ya raba jikinsa da nata, wani irin tausayinta na ratsa"

ilahirin jikinsa.

"Ta maze cikin ya™e ta ce ""Sayyid, ya na ji ka yi shiru ne?"""

"Ya girgiza kai ya ce ""Babu komai"""

"""A'a akwai wani abu. Dama likita ya ce mu zauna na tambaye ka, ko akwai wani abu da yake damun ka,"

"haryanzu fa jininka bai sauka ba Sayyid"""

"Ya Wan sake yin guntun murmushi ya ce ""Damuwa ai akwai ta, ba na son Waga miki hankali ne kawai."

"Haryanzu ina tunanin inda su Habu suka tafi, suka bar ki da Wawainiya, Kodayake ko suna nan ma, kula"

"da ni ba dolen su ba ne. Sai wahala ki ke sha, wallahi idan ina tuna hakan, sai na ji tamkar numfashina zai"

"Wauke a cikin damuwa nake sosai da sosai. Ba na son saka ki a damuwa ne kawai""."

"Nana ta tattara hankalinta ta matsa kusa da shi, ta ri™o hannunsa, ta kalli idanunsa da suka yi jawur."

"""Idan su Habu ba hakkinsu ba ne kula da ki. Ni yanzu ya zama ha™™ina, na san ba a banza Allah ya haWa mu ba. Mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana komai da sau™i. Amma ina fatan dan Allah ka daina damuwa, idan ciwon nan ya matsanta maka a jikina nake ji, ka daina ba na so"" ta ™arasa maganar cikin"

shagwaSa.

"KafaWarta ya ciza cikin wasa, yana rungume ta. Tamkar ba a cikin damuwa suke ba, suka ci gaba da raha,"

"duk da yadda hayaniyar mata ta cika gidan, tamkar a na taro, saboda dawowar Barira, an cika gidan ana mayar da yadda aka yi."

"Ana fara kiran sallar magariba, ta kai masa ruwan Wumi banWaki ya yi alwala."

"""Za ka je masallaci ne?"""

"""A'a a nan zan yi"""

"""To yi sallar. Nima sai na yi muje mu Wuro gas, ko rabi ne sai kuma na sayo gawayi, Ummi ta bani kurfoti,"

"na din ga haWawa da shi"" Ya jinjina mata kai ya tayar da salla."

"Yana kallon ta ta idar, ta buWe jakarta ta Webo sauran kuWin da suka dawo da su, ta nufi wardrobe ta"

haWa su da waWancan kuWin. Kawai ta ga kayan wardrobe Win a hargitse.

"Mamaki ya kama ta, ta san Sayyid ba ya taSa mata wardrobe, kuma ita ba a haka ta bar wardrobe Win ba."

Ayshacool

"Ta janyo jakar gidan Sarkin baka, ta duba ta ga kuWin nijar a ciki. Ta laluba ta Wauki ledar, da kuWin"

"Nigeria ke ciki ta rasa. Ta watso kayan wardrobe Win gaba Waya, tana ™ara haskawa da fitilar wayarta."

"Yana tsaye yana kallon ta. Muryarta na rawa ta ce ""Sayyid"""

"Ya kalle ta. ""KuWinmu, kuWin da ka bani na saka a cikin wardrobe na...naa..ajiye a nan ban gani ba, ko ka"

"Wauka?"""

"Ya yi shiru yana kallon ta, a zuciye ta nufi hanyar fita daga Wakin, ya ri™e ta. Jikinta yana tsuma take"

"™o™arin fizgewa amma ya ri™e ta yana girgiza kai ya ce ""Kar ki yi magana, ki yi shiru ko waye mu bar wa"

"Allah. Tun da na shigo, na ga alamar an buWe Wakin. Kuma laifinmu ne, da ba mu saka mukulli ba, muka rufe Wakin kawai."""

"""Sayyid ba a yi mana adalci ba. KuWin Abincinmu da maganinka, sun kwashe gaba Waya wace irin masifa"

"ce wannan? Daga wannan sai wannan ya ake so na yi ne?"" Ya ri™e ta gam yana shafa bayan ta, a hankali ya ce ""Ki yi ha™uri, ki daina Waga murya, akwai Allah"""

"Kuka take yi iya ™arfinta, tana sheshshe™a, ya rungume ta gam a jikinsa, shi kansa ya ji zafi da raWaWin"

"satar da aka yi musu. Ba iya kuWi ba, har da wasu daga kayan amfaninsu na Wakin an Wauka, ya san kuma"

"hakan sabon ™alubale ne, saboda ba su da wata hanyar samun kuWi a yanzu."

"Ji ya yi jikin Nana ya saki, kuma jikin yana Waukar sanyi. Karkarwa ta fara yi, tamkar ana jona mata"

shocking.

"Cikin matsananciyar damuwa, ya zauna da ita a jikinsa, ya Wauki wayarta da ta saki a gurin, yana haska"

"fuskarta. Ya ga hawaye na fita ta gefen idonta. Hannayenta da ™afafuwanta su na lan™washewa, goshinta"

kuma yana tsatstsafo da gumi.

"Jin ta ta yi, jingine da wani abu da ba ta san ko mene ne ba. Ta shafa abin ta ji ™urzunu-™uruzunu, tamkar"

"dutse. Gurin ba™i ™irin duhu ya gauraye gurin, ko tafin hannunta ba ta iya gani. A hankali haske ya fara"

"shigowa gurin, har gurin ya yi haske ba ki Waya. Ta Waga kanta ta ga ba ta iya gano ™arshen Wakin."

"Jin tari ta yi a bayan ta, ta waiwaya da sauri, ta ga ˜aisar a zaune lulluSe da wani abu mai haske sosai."

"""˜aisar. Ba ka da lafiya?"" Ta yi maganar tana nufar inda yake."

"Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta sake cewa ""Dama kuma ku na rashin lafiya, kamar ka canza gaba Waya"""

"ya yi murmushi ya ce ""Mu na rashin lafiya mana, guba na ci"" Ta waro ido ta ce ""Guba kuma? Me yasa?"""

"""Tsohon nan na jikin mijinki, ya bani."""

"""Kuma ka sha? Wai meye ala™ar ka da shi? Kuma dan Allah me yasa yake bibiyar mijina?"""

"""Ba wannan ba, me yasa ki ka kira ni?"" Cikin mamaki ta kalle shi ta ce ""Kamar yaya? Ni ban kira ka ba ai"""

"""Fushi da Sacin rai, duk wanda ki ka yi tamkar kin kira ni ne. Kuma ni yanzu ba ni da wani tasiri sosai,"

"saboda jinya nake yi. Babu wanda ya san ina nan. Giyaz ya saka ni a gaba, ya mamaye Library Wi na, yanzu rashin ganina zai sanya ya ci gaba da cutar da ku. Ba zan iya wani abu ba sosai yanzu, sai dai zan iya tasiri a kan bil'adama."

"Duk ba wannan ba, duba can."""

"Ta Waga kai ta kalli inda ya nuna mata, Library Win ˜aisar ta gani. Ta ga gangar jikin Sayyid a kwance."

"Tsohon nan ya WaWWaure shi da wata irin igiyar ™arfe. ˜asan gadon da yake kai kuma, wata irin wuta ce take ci a ™asa. Nana ta zabura a rikice, ta ce ""Wannan ai Sayyid ne"""

"""˜warai shi ne, ba wani ba. Kuma Giyaz shi ya sanya masa matsalar da ku ke ciki na auratayya. Sai dai"

"abu Waya zan iya gaya miki. Matsalar zuciya da hawan jini da yake fama, wannan ciwo ne yake damun sa. Amma Giyaz na assasa wani abin. Kuma... Amma dai shikenan"""

"Nana ta buWe baki za ta yi magana, ya ce ""Kar ki tambaye ni komai, kin san sharaWin. Kalli"" ya yi maganar"

yana sake nuna mata gurin.

"Alhaji Fatuhu ta gani, ta yi ™uri da ido ta ce ""Kamar na san wannan"""

"""Ba kama ba ce ba kin san shi, ciwo ne da zafin sihirin da aka yi masa ya mayar da shi haka. Sai kuma"

"albishir da nake yi miki, da ™anwar ki ta zama cikakkiyar 'yar ™ungiyar asiri. Šayar kuma wannan bararojin da ta taSa baki magani, ta aura mata Wanta, wanda yake ba™in aljani ne. Kuma ta tarkato kan iyalanta duk su na jikinta. Kuma kowanne akwai abin da yake mora a jikinta. Ke in ta™aice miki ma, a"

kowane lokaci za ta iya rasa hankalinta ko ma rayuwarta gaba Waya.

Ayshacool

"Shikenan bissalam"""

"""˜aisar"" sai kuma ta yi ido huWu da Sayyid."

"""Kin tashi?"" Ta yin™ura ta tashi zaune, tana kallon Wakin."

"Sayyid ya ce ""˜aisar Win ba shi da lafiya ne?"" Ya yi maganar yana tsare ta ido."

"""Wane ˜aisar Win?"""

"""Tambayata ki ke yi?"" Shiru ta yi, ita ba ta iya tuna koma ma a cikin abin da ya faru ba. Idonta ne ya"

"sauka a kan kayan da suke gaban wardrobe a ™asa, sai kuma abin da ya faru ya faWo mata. Afujajan ta tashi ta sake nufar wardrobe Win, tana zazzage kayan tana kuka."

"""KuWin nan fa babu su, an kwashe ki daina wannan dube-duben"" ya zauna ta yi shiru ta sanya kayan a"

gaba tana kallo.

"Ya yi mata shiru ya ™i kula ta, ya kwanta a kan katifa, yadda take a hasalen nan, idan ya matsa faWa za su"

yi. Cikin ™an™anin lokaci nannauyan bacci ya yi awon gaba da shi.

"Barira na kwance a Wakinta, ta yi WaiWai tana bacci, ta ji kamar ana karta mata farce a ™afafuwanta. Har"

"ta maze ta ci gaba da bacci, amma ta ji an cigaba. A fusace ta ce ""Gali meye haka, za ka din ga karta mini"

"faratanka, ina cikin bacci ne?"" Shiru bai amsa ba. Ta laluba ta ji yo ™eyarsa a can ™arshen gado, yana"

"bacci. Ta koma ta kwanta, amma ta ji an cigaba, ta tashi zaune tana zabga ashariya."

"Ta kunna fitila, ta ga babu kowa. Ta yi tsaki ta sauka daga kan gadon, ta fito tsakar gida domin ta yi fitsari."

"Bayan ta fito daga banWakin, kanta ko Wan kwali babu, kawai ta yi karo da Nana a tsakiyar tsakar gidan tana yi mata wani irin mugun kallo."

"Ta haska Nana ta ce ""Nana lafiya kuwa?"""

"Sai dai Nana ba ta yi magana ba, ta sake haska ta, za ta yi magana. Ta ga ta rikiWe ta zama wata irin"

"™atuwar mage, ba™a ™irin, girman ta ya yi na tunkiya ™osashiya da ita, ta yo kanta tana buWe ha™ora."

"Da gudu Barira ta shiga Wakinta, tana ihu tana kiran sunan Gali."

"""Ke mahaukaciya, mene ne haka za ki din ga ihu kina kiran sunana a tsohon daren nan?"""

"Ba ta ce masa uffan ba, ta du™un™une, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ™yar ta"

"samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta."

"Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haWa"

kai da gwiwa.

"Ya yin™ura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya"

"rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya Wauke ta."

"Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan."

"Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaSi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya"

"mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu."

"Kwanki biyu da sace kuWin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi. Dubu talatin ce ta ragu a"

"hannunta, shi ma cikin irin kuWin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. KuWin Nijar Win kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin Win nan, ba tare da ta rushe gaba Waya ba. Ga shi magungunan da"

"yake sha kawai, na wata Waya dubu goma sha biyu take sayen su."

"Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi ha™uri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin."

"Kwana biyar da kwashe kuWin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci,"

"saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haWo mata da su, take ta cancana musu."

"Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake"

"damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daWi, yana ta numfarfashi."

"Abin Duniya ya ™ara damunta, ya kuma ™i cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana"

maganganu tana ba wa su Sajida labari.

"""Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ™arfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ™arfin"

"mutum""."

"Sajida ta ce ""Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"""

"Barira ta ce ""Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri"""

Ayshacool

"""Ni fa ba na son kurman ba™i, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"""

"""Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"""

"Bai fi mintuna biyar ba, wani irin haya™i, mai azabar yaji, ya turnu™e gidan."

"Nana da take lafiya ™alau ma, ta fara tari."

"Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai Wauke, ta Waukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi,"

"da nufin ta je ta ga me ake ™onawa yake wannan uban haya™in haka. Amma ya ri™e hannunta

33 / 126