Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   117 / 126

348K to 351K   out of 377.2K words

da mu, za a kawo dukiyar aurenta Nigeria za kuma a yi bikin aurensu sosai da sosai. Duk abin da za mu gaya maka yanzu ba za ka fahimce mu ba, saboda a cikin damuwa ka ke, kuma abubuwan da suka faru su na da tsawo da sar™a™iya akwai bu™atar a yi maka bayani daki-daki. Ba Nana ba hatta Imrana yana tare da mu a Agadez, akwai tarin bayanai da sai ka nutsu, an yi maka bayani zaka fahimce su"



"Amm bawan Allah, ni ko yanzu a shirye nake, mu tafi Agadez Win na karSi 'ya'yana. Bayan Nana kuma me ya haWa ku da Imrana"



Imam Zahradeen ya ce "Alkhairi ne, a cikin satin nan, zuwa mai kamawa in sha Allah; za a sake turo maka ba™i daga can. Kuma za a yi bikin su al'ada saSanin yadda ya gudana, kuma za a yi maka bayani kamar yadda nake nanata maka. Amma kafin nan mu na son za a gyara maka gidan nan, ko kuma a canza maka wani"



Baba ya girgiza kai ya ce "Ba na bu™atar haka, muddin Nana yake so, babu amfani a raina inda ta fito, ni dai fatana na gansu cikin ™oshin lafiya"



Zahradeen ya ce "Ba raina maka aka yi ba, matsayinka da girmanka ne ya sanya za a yi maka." Fafur Baba ya ™i yarda da hakan, da kyar suka rarrashe shi suka tafi, dan cewa ya yi ba za su bar ™ofar gidansa ba, ba tare da ya ga yaransa ba.

Kasancewar duniya makarantar da ko babu malami, ta biya maka darasi dole ka Wauka ce, ta karanta wa Baba darasin da duk son abin Duniyarsa, yanzu tsoro yake ji.

Zuwansu Imam Zahradeen babu wanda ya sanarwa, saboda gani yake yi tamkar ™arya Buzayen nan suka zo suka sharara masa.

Ya kasa gaya wa kowa, sai Uwani ya kira ya sanar mata. Sai dai a ™arshen maganar Baba ya ce "Amma Uwani ni ban ji na yarda ba, ji nake kamar ™arya kawai suke yi ban ji na yarda ba"

Uwani ta ce "Alhamdillah, ni dai na ji na yarda har cikin zuciyata. Ko ba hakan ba ne, ina fatan Allah ya tabattar da shi ya zama gaske. Wallahi zuciyata ta daWe tana bani, mijin Nana ba ™aramin mutum ba ne, to ita Nanan da gaske tana gurinsu, kuma har da Imrana sun haWa ku ko a waya ne?"



Ya ce "A'a, shiyasa na kasa yarda ma gaba Waya"



"Isa, yarda ni dai na gama ta, zamu du™ufa mu ci gaba da addu'a in sha Allah Nana suna cikin kwanciyar hankali tare da Wan uwanta" Kalaman Uwani suka Wan ™warara wa Baba gwiwa.

Bayan sallar isha'i ya shiga gida, yana zaune yana jin radio, Mama tana cikin Waki tare da Jamila da ta koma so silent, ko magana ba ta iya yi.

Ihun da Jamila ta yi ne, ya sany Baba jifa da radio ya tashi tsaye yana rarraba ido.

"Mama! Mama!! Dan Allah ki taimake ni, dodon ™ungiya zai shanye mini jini. Hajiya Sa'a kin cuce ni, kin cuci rayuwata, na kasa samun aminci da salama. Na baku Abba me kuma ku ke nama a gurina?"

Cikin rashin fahimta duk suke kallon Jamila, Baba ya ce "Me yarinyar nan take faWa ne haka?"

Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa."

Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?"

Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni"

Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faWa wai?"



"Baba ri™e hannuna, Baba ku taimake ni"



Ya ™arasa ya ri™e hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar Sarna, Baba hakki ne zai yi ajalina"



Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?"



"˜ungiyar asiri, Baba ™ungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana"



Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka.

Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faWa, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wata™ila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga"



Alhaji Zailani ne a dur™ushe a gaban gawar Wansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya Waga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya ™o™arinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raWaWi da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko ™wa™w™waran motsi.

Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta Sata, ga kuma mutuwar Yusuf.

Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daWewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daWi.

Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a Waki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon ™ungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara.



Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata.

Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman.

Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari"

Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?"

"To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?"



Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana bu™atar gyara ai"

Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta ™udurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar.

Shi kansa Hammad ya so a ™yale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba ™aramin kyau take yi ba.

Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya ™ara sanya ta farin ciki.

Hammad ya ce ta fita ta Wan zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta.

Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga ra™uma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake.

Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani"

Shi ma yana murmushin ya Wago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba"



Nene ta ce "Ni Win ko? Ka sanni ne?"



Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu"



Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba"



Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni Walibin marigayi Sa'adu Aska ne"



Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?"



Sarkin baka ya ce "˜warai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada"



Nene ta ce "Ikon Allah"



Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka"



Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana Waukar Muhsin.



Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?"



Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daWe ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaSe ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke ™asar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru"



Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne Sarnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya"



Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haWa ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban du™usa ko in ce ˜aisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba"



Nana ta ce "Amma saboda me?"



"Saboda Webo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin."



"Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira."



"Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah.

Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuWi, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani"



Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu"



"Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa ™arya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke ta™ama da su, su na amfani da ku, da da™ile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban ™i ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da Sawon gyaWa,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faWa, da ™o™arin kashe mana magungunanmu. Sai a  ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda Waci, hanta ba ta son Waci, amma Allah ya halicci maWaciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son Waci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba Waci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya ri™e abin da yake ganin shi ne dai-dai "

Nana ta Wan yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya ri™e abin da yake ganin shi ne dai-dai!"



"To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai"



99



1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic

08081012143





Har Nana za ta sake magana, Nene ta ri™o hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin Wan tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Šan uwa idan muka kuma haWuwa zamu tattauna sosai mu gaisa.



Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba Waya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar ™alubalanta a kan hukuncin da ya zartar.

Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuSi Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya Wauka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake.

Duk yadda ta kai ga ™o™arin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya ™i ko kallo ba ta ishe shi ba.

Ranar ™arshe ma da ta je Wakinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana ™aunarki bana ™aunar ganinki, tun da har za ki yin™urin sabauta mini rayuwar Wa, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taSa tsammani ba, fice ki bar mini Waki kafin na yi miki illa" Abin ya Waure mata kai, bata taSa tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba.



Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba Waya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya ri™e istigfari ba dare babu rana, gaba Waya yaransa sun watse babu wani na kamawa.

Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaSe, jiki babu ™wari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba.

Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba Waya babu wani mai Wan dama-dama"

Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba Waya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta"

Baba bai Soye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar ™ungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un"



Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye.

Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuWin da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna ba™in ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida"

Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi.

Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karSi lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?"

Baba ya girgiza kai ya ce  "Ban karSa ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar ™arya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa"

"Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faWa, masu sar™a™iyar gaske"

Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi"

Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi"

Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa.



****

Nana ce a tsaye, tana kallon ˜aisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji.

Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "˜aisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?"

Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaWo yanzu ta ware ma"

Nana ta ™arasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?"

Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?"

Nana ta Wan yi shiru tana kallon tsuntsuwar.

Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?"

Ta gyaWa kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa ˜aisar ina Haulat? Ka fara son nata?"



"Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta.



Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?"

Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan.

Nana ta numfasa ta ce "˜aisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haWa ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi"

Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daWi da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza"



Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?"



"Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa"



Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "˜aisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daWi ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai"



"Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai.



"Ba haka ba ne, duk da ta wani fannin haka Win ne, muguntar ce da takaicin ™in yarda da abin da na zo miki da su.

Mafarki ya kasu kashi-kashi, duk da shi ma ina kan bincike a kansa. Akwai mafarkin da yake daga Allah ne, akwai mutanen da akan yi wa ishara a cikin bacci, na kusantowa ko kuma faruwar wani al'amari da bai faru ba kwata-kwata. Wasu kuma a nuna musu makamancin abin, wasu kuma

117 / 126