Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   47 / 126

138K to 141K   out of 377.2K words

ta du™un™une, tana mayar da numfashi. Ta tsorata sosai da sosai, da ™yar ta samu ta yi bacci. Sai dai a cikin baccin ma, mafarkin magen nan kawai ta din ga yi tana bin ta, tana karta mata farata tana cizon ta.



Sayyid kuwa yana jiyo kururuwar Barira, hakan bai dame shi ba, sai ganin Nana da ya yi a zaune, ta haWa kai da gwiwa.

Ya yin™ura ya tashi zaune, bai ce mata komai ba, ya kwantar da ita a kan katifar, ya rufe su da bargo ya rungume ta yana shafa bayanta. Yana jin ta tana kuka, har ta yi ta gaji bacci ya Wauke ta.

Dauriya kawai yake yi, amma ji yake tamkar ya taya ta kukan.



Washegari, Barira ta tashi da matsanancin zazzaSi da ciwon kai, ta din ga yi wa mijin kuka, tana cewa ya mayar da ita gidansu, mayu sun kama ta a nan gidan, ba za ta yadda a kashe ta a banza ba. Babu yadda ya iya ya tattara ta ya kai ta gidansu.



Kwanki biyu da sace kuWin nan, Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi. Dubu talatin ce ta ragu a hannunta, shi ma cikin irin kuWin da ta zuba a jakarta ne suka fita da su. KuWin Nijar Win kuma ba ta san ma ina za ta a canza su ba. Bayan haka tayi tunanin idan Habu ya dawo fa, me za ta ce masa? Ta din ga tunanin yadda za ta yi da dubu talatin Win nan, ba tare da ta rushe gaba Waya ba. Ga shi magungunan da yake sha kawai, na wata Waya dubu goma sha biyu take sayen su.

Sai dai kamar yadda yake nanata mata, ta yi ha™uri, ya sanya ta fauwwala wa Allah lamarin.



Kwana biyar da kwashe kuWin nan, Sayyid ya hana Nana gaya wa kowa. Sai dai cikin dare ba ta iya bacci, saboda lissafi da tunani. Ta kira Ummi ta tambaye ta batun barkono, ta ce ana ta saya, ta sayar da ya kai rabin buhun. Kayan Abinci da Mama ta haWo mata da su, take ta cancana musu.

Da daddare ba ta iya bacci, saboda damuwa da tunani, sai dai abin yana damun sa fiye da yadda yake damun ta. Su ka wayi gari, ya tashi jikinsa babu daWi, yana ta numfarfashi.



Abin Duniya ya ™ara damunta, ya kuma ™i cin komai. Muryar Barira ta jiyo a tsakar gida, da ta dawo, tana maganganu tana ba wa su Sajida labari.



"Mayu sun kama ni a gidan nan, kuma da ™arfina na dawo, wallahi sai sun ci uban su, kurwata ta fi ™arfin mutum".



Sajida ta ce "Ban gane mayu ba, suwaye mayun kuma?"



Barira ta ce "Oho, ki zuba ido ki gani, Allah zai tona musu asiri"



"Ni fa ba na son kurman ba™i, a masu shigowa ne mayun, ko kuma zaunannun gidan"



"Na ce ki zuba ido ki ga ikon Allah"



Bai fi mintuna biyar ba, wani irin haya™i, mai azabar yaji, ya turnu™e gidan.

Nana da take lafiya ™alau ma, ta fara tari.

Shi m tarin yake yi, numfashinsa kamar zai Wauke, ta Waukko mafici ta din ga yi masa fifita. Ta gaji ta tashi, da nufin ta je ta ga me ake ™onawa yake wannan uban haya™in haka. Amma ya ri™e hannunta ya hana ta. Haka suka wuni a galabaice. Sajida ma sai bala'i take yi, tana cewa Barira za ta kashe ta da haya™i.



"Wai Sajida ko ke ce mayyar nan ne?"



"Ke kama bakin ki, wallahi ki ka ce mini mayya, sai mun yi shari'a da ke"



Barira ta ce "Sai ki saurara mini, tun da dai ba ke ba ce" Haka suka wuni, Barira tana gana musu azaba, da wannan azababben abin da take zubawa a cikin murhu.

Washegari ma, azabar haya™in nan ce ta tashi su Nana, numfashin Sayyid tamkar zai Wauke saboda azaba.

Nana dai ta ci gaba da daurewa, amma yamma na yi, Barira ta sake cika kurfoti da gawayi, ta tayar da wuta ta afka haya™in nan.



A fusace Nana ta fita, ta tarar da ita tana ta girgiza kurfotin, tana zuba wani abu a ciki.



Nana ta ce "Barira, dan zatin Allah ki daina zuba wannan abin. Ina da mara lafiya a Waki. Yana da matsalar numfashi, jiya kwana muka yi babu bacci. Kuma da sassafe kin banka wani, kuma yanzu ma ga shi kina sake kunnawa"



Ta kalli Nana ta ce "Ai duk wanda ya hana uwar shi bacci, wallahi shi ma ba zai yi ba"



Nana ta ce "Kamar yaya kenan?"



"Kamar yadda ki ka ji"



"Ni dai koma mene ne, ki yi ha™uri idan ba ki yadda ba, zo mu je Wakin ki ga halin da yake ciki"



"Babu ruwana da halin da yake ciki, kurwata ce ta fi ™arfin duk wani maye wallahi"



Nana ta ce "Barira mu ne mayun da ki ke faWa dama? To Barira ko za mu ci mutum ma ci taki, jiki duk dauWa?"



"Ko ma duk uban mene ne, tun da aka kama ni aka lasa, an ji za™in kurwa ta, wallahi sai mutum ya ci ubansa, miyagun banza kawai"



"Mu ne mayun Barira?"



"Eh ku ne, ko na ce ke"



Nana ta ™arasa daf da Barira ta dam™i tsintsiyar hannun Barira ta ce "Ki ka ce ni mayya ce?" Barira ta yin™ura za ta fizge hannunta, ta yi bala'i. Kawai ta ji jikinta ya yi wani irin nauyi, kuma jikin ya yi mata wani irin sanyi, ta kasa motsa komai. Kawai ta silale ta faWi ™asa.



Ayshercool

08081012143

54



Ihu Sajida ta saka, tare da sauran matan da suke zaune, tamkar ana bajekolin kasuwar ™auye, suka dare ganin daga ri™e hannun Barira da Nana ta yi, ta faWi ™asa. FaWuwar da ba su da tabbacin, tana raye ko mutuwa ta yi.

Wasu suka yi waje da gudu su na ihu, tamkar garken tumakin da ba su san inda suka dosa ba.



Nana kuwa idanunta a rufe, ta nufi Wakin su tana tangaWi, Sayyid kuwa da ™yar ya lallaSa ya tashi yana ™o™arin fitowa, amma mai afkuwa ta riga ta afku. Nana na shiga Wakin ta faWa jikinsa, ya taro ta. Gaba Waya jikinta ya saki kuma ya yi sanyi ™alau, shaidar ˜aisar ya buge ta.



Ya Wauki wayarta, ya tura wa Ummi sa™o.



Tuni aka kira mijin Barira, jikinsa na rawa ya shigo gidan, tare da rakiyar wasu mazan.

Ya dur™usa a kan Barira ya taSa ta, ya Wago ta, sai dai ya ga tana numfashi, sai dai idanunta a kakkafe, ya girgiza ta yana kiran sunanta "Barira. Barira ki buWe idonki. Ki na ji na?" Barira ba ta motsa ba, kuma ba ta yi magana ba. Sai dai numfashinta yana fita normal.



Mijinta ya ce "Dan a samo adaidaita sahu mu tafi Asibiti"



Šaya daga matan da abin ya faru a gaban su ta ce "Wane Asibiti, ai ko an je Asibiti babu abin da za a gani, Nanan za a janyo daga Wakin, a yi wa dukan tsiya a sanya ta tsallaka ta, shi ne za ta tashi, kama mata kurwa ta yi"



Šaya daga mazan ya ce "A'a ba za a dake ta ba, a kai ta dai gurin hukuma, a san abin yi."



Mijin Barira ya ce "Wane irin kar a dake ta, kana kallon halin da matata take ciki"



Ya mi™e ya nufi ™ofar Wakin su Nana, cikin Waga murya ya ce "Kina ina, ki fito ki tsallake mini mata, ki sakar mata kurwa" Sai dai ya ji shiru, babu wanda ya yi magana. "Ki fito ko na shigo wallahi"



Wani ya ce "Kar a yi haka Gali, ka ga matar aure ce, bai kamata a bi abin da mata suka faWa ba, kamata ya yi a zurfafa bincike tukuna, kar a Wauki doka a hannu, a zo daga baya a ji kunya"



Gali ya ce "Malam ni dai ba zan ji kunya ba da yardar Allah, kalli halin da yarinyar nan fa take ciki. Idan ta mutu fa? Wallahi ba zan yarda ba"



A fusace ma™wabcin na su ya ce "To a je Asibiti mana a duba, sai ha™ilo ka ke yi, matarka matarka. Kamar ba nan ka ke jibgarta, ake ™watar ta da ™yar ba, sai da aka haWa ka hukuma ka daina, auren da ko shekara biyu bai yi ba, a lokacin ba ka yi tunanin ta mutun ba sai yanzu?"



A fusace Gali ya ce "Kar ka gaya mini maganar banza mana, ina ruwan ka da dukan da nake yi mata, dama munafunci ne ya sanya ku ke yi mana sulhun?"



Ummi ce ta yi sallama, Sajida ta yi caraf ta ce "Yauwwa ga yayarta, ita ce dama ta kawo ta gidan nan"



Cikin mamaki Ummi ke bin dandazon jama'ar da kallo. Ta ce "Wai lafiya me ya faru?"



Mijin Barira ya ce "Mene ma bai faru ba, kin kawo mana mayya ta kama mini kurwar mata. Dan haka sai ki shiga ki fito da ita ta tsallaka ta"



Tuni idon Ummi ya cika da hawaye, saboda ba ta ™aunar tashin hankali ta ce "Wallahi mu ba mayu ba ne ba. Nana ™anwata ce, akwai dai abin da ya faru amma ba wai Nana ta kama kurwar wani ba"



"To ™arya aka yi mata? Ba ga Bariran can a kwance ba, ta tashi mana".



Cikin tashin hankali Ummi ta ce "Wallahi kaf zuriyarmu babu mayu, Nanan ma matsalar mutanen Soye ne da ita, amma ba maita ba, bari na duba ta" Ta nufi Wakin da su Nana suke. Tuni gidan ya sake Winkewa da mutane, ya cika fal wasu suna a fito da Nana, a zane ta a saka ta tsallake Barira.



A zaune ta tarar da Sayyid, rungume da Nana a jikinsa. Cikin damuwa da tashin Ummi ta ce "Wai me ya faru ne?" Ya yi shiru yana kallon Ummi, sannan ya mayar da idonsa kan Nana.



Ta Wauki wayarta ta kira Baba. Tana jin ya Waga ta fashe da kuka.



Baba ya ce "Ke meye haka lafiya?"



"Baba babu lafiya, dan Allah ka zo gidan Nana, akwai matsala ne"



"Gidan Nana kuma? Ina ne gidan Nanan, kuma matsalar mene?"



"Baba mutanen unguwa sun taru, za su dake ta, kar su kashe ta ni ban ya zan yi ba"



A sukwane Baba ya mi™e ya ce "˜arya ne. Nanan za su kashe mini, ai zan yarda kowa zai iya Waukko magana a cikin ku, amma ban da Nana. A can gidan gadin nata ne za su dake ta?"



"Baba wane gidan gadi kuma, ai sun bar gidan tana nan kusa da ni, ka manta ne? Ka cewa Nasiru ya rako ka ya san gidan"



"Gani nan zuwa" ya kashe wayar ya yi waje da sauri.



Ummi ta tsaya a bakin ™ofar, tana ta ba su ha™uri. Amma sai nema suke yi su ture ta, su shiga Wakin.



"To ban da wula™anci ma, ta shige Waki ta™i fitowa, da yake ba ta da gaskiya. Maimakon mijinta ya fito ya bayar da ha™uri, shi ma ya yi zamansa saboda rashin tsoron Allah, da rashin gaskiya"



Ummi ta ce "Mijinta ba shi da cikakkiyar lafiya, ita ma aljanu sun buge ta, dan Allah ku yi ha™uri" Sai dai abin ya fi ™arfin Ummi, ™o™arin hankaWe ta kawai suke yi, su cimma Nana.

Ana haka sai ga ma™wabcin su Nana, tare da jami'an tsaro. A dole mutanen suka saurara. 'yan sanda suka ce, a tafi da Barira Asibiti, abin da likitoci suka ce, da shi za a yi amfani.



Ana haka Baba ya ™araso, cikin tashin hankali.



Ummi na ganin sa ta yi ajiyar zuciya. Ummi ta ce "Baba ka zo?"



"Eh, ina Nanan take, kuma uban me ta yi za a dake ta da?"



"Ai gama 'yan sanda sun zo, saSani suka samu da wanda suke zaune gida Waya, shi ne suka ce mayya ce"



Baba ya ce "Maita kuma? In ji uban wa?"



Mijin Barira ya ce "Ga shaida Baba, kalli matata a baje a kwance"



"Kuma sai ka ce 'yata mayya ce? To wallahi ™arya ne, kaf danginmu babu mayu, ku dai nemo wani abun, ba maita ba wallahi" 'Yan sanda suka shiga maganar, aka tafi da Barira Asibiti.



Sai da aka bar 'yan sanda biyu, gudun abin da ka iya faruwa, saboda matan da abun ya faru a gaban su, su na ta ™ara balbalawa wutar fetur. Tare da mayar da abin da aka yi da wanda ma ba a yi ba. Gaba Waya zancen ya zagaya unguwa.

Har sha Wayan dare case bai ™are ba, Nana ta farfaWo ta ga Ummi a Wakin su, ga duhun dare ya fara yi.



"Ummi lafiya kuwa?"



"Ina fa lafiya Nana, meya haWa ki da mutanen gidan nan, ga shi ana cewa ke mayya ce".



"Mayya kuma?"



"Eh mana, yanzu case na hannun 'yan sanda, Baba yana can tare da su, ana jiran likitoci su faWi sakamakon binciken su."



Nana ta gaya wa Ummi iya abun da ta iya tunawa. Sai dai ta sha mamaki, ta ji wai Baba ya zo kan matsalar ta.

Ta kalli Sayyid da yake kwance lamo, abin Duniya duk ya dame shi.

Sajida ta haWa kayanta, ta gudu ta ce ba za ta iya kwana da Nana a gidan ba.



Sai zuwa da safe, Likitoci suka tabattar da anemic shock ne ta samu, bayan binciken ™wa™waf da suka yi, suka gano ta yi Sari sati biyu baya, ta kuma zubar da jini sosai ba ta je Asibiti ba. Ta zo ta yi zazzafan zazzaSi na typhoid amma suka ala™anta hakan da mayu, nan ma ba a je Asibiti ba. Hakan ne ya haddasa faWuwar ta. Bayan fito da sakamakon, mijinta da 'yan uwanta suka ce ba su yarda ba, sakamakon ™arya ne kawai aka gaya musu.

Ga Barira ta farfaWo, tun a cikin daren ma, har ta ci Abinci, amma suka ci gaba da surutu a kan Nana mayya ce.



Ummi tare da su Nana ta kwana, saboda tsananin tsoro. Dan da gidanta akwai guri can za su tafi ma. Sai dai tashin hankalin abin da ya faru, ya sanya jikin Sayyid rikicewa gaba Waya, ya zamana kamar ma ba ya gane wanda yake kansa.



Hankalin Nana ya yi mummunan tashi, ga shi babu isasshen kuWin tafiya Asibiti. Ta kuma san tashin hankali, da damuwar abin da ya faru ne, ya sanya jikin nasa ™ara rikicewa.



Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi, ga matan gidan kowacce ta koma gidansu, sun ™i dawowa gidan wai tsoro suke ji.

Ummi ce ta yi sallama, Nana ta amsa ta yi mata izini ta shiga Wakin. Hannunta ri™e kular Abinci. Ta kalli inda Sayyid ke bacci a wahale, numfashinsa na fita sama-sama. Cikin damuwa Ummi ta ce "Yanzu Nana haka jikin nasa ya koma?"



"Wallahi Ummi, gaba Waya hankalina a tashe yake"



"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ana wata ga wata"



Cikin damuwa da rashin fahimta ta ce "Me ya faru?"



Cike da karaya, da matsanancin tausayin ™anwarta ta ce "Mai gidan nan ne, ya je ya same ni, ya bani dubu goma sha biyu, wai ga sauran kuWin ku nan, ku tashi. Ba ya son tashin hankali, kuma ga sauran 'yan hayar sun ce ko ku tashi, ko ya mayar musu da kuWinsu su tashi. Nayi-Nayi ya ™ara wani abu, tun da ko wata ba ku yi ba, amma ya ™i wai wannan Win ma da ™yar ya samo su ya kawo."



Nana ta jingina da jikin bango tana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"



"Nana mene ne abin yi yanzu?"



Nana ta girgiza kai, jiki a sanyaye ta ce "Ban sani ba Ummi"



"To ko wani gidan za a nemo? Sai na koma na neme shi, na ro™i alfarmarsa?"



Ta girgiza kai ta ce "A'a Ummi, an riga an yi mini mummunan tambari a unguwar nan, abu ne mai wahala ma mu sake samun wani gidan a unguwar nan"



"Bari na kira Baba na ji me zai ce"



Nana ta ce "A'a Ummi, kin san halin Baba, kar ranki ya Saci"



"To Nana ya zamu yi, dole a kira shi mu ji me zai ce" Ummi ta kira lambar Baba, yana Waga wayar muryarsa a sama ya ce "Ya kuma aka yi, ba an kashe case Win a gurin 'yan sanda ba?"



Ummi sai da ranta ya sosu, amma ta maze ta ce "Baba ba wannan ba ne. An kori su Nana daga gidan da suke ne, mai gidan da suke ya ce sai sun tashi"



"To sai kuma aka yi yaya? Ni zan nemo musu wani gidan? Ko kuma mijinta ne yakamata ya nemo musu wani?"



"Baba ka fa zo gidan nan, ka ga halin da mijin nata yake ciki na rashin lafiya, saboda haka aka kore shi daga gurin aikin gadi. Dan Allah Baba ka yi wani abu a kan yarinyar nan. Nana yarinya ce ™arama pressure ta yi mata yawa."



"To Ummi ya ki ke so na yi? Ni dai nan gidan babu gurin da zan ajiye ta, ita da mijin nata, idan kuma ke ki na da guri ki taimaka ki ba su. Idan ba haka ba ta nemo 'yan uwansa su Wauke shi, su rakata inda danginsa suke. Kin san dai nan gidan idan ta dawo, abin da za ta ci ma aiki ne. Nima yanzu sai abun da aka samo aka bani"



Hawaye ya cika idon Ummi, cike da takaicin yadda Baba bai fiye damuwa da damuwarsu ba. Ta ce "Baba da ina da inda zan ajiye Nana da mijinta, wallahi ba zan kira ka ba"



Nana ta ce "Ummi, dan Allah ki katse kiran nan, nima ba zan koma can gidan ba."



Tarin Sayyid ta ji, ta mayar da hankalinta kan sa, ta nufe shi tana faWin "Sannu Sayyid"



"Ki ba ni ruwa" ta amsa da to. Ta Waukko ruwan leda, ta buWe masa ya tashi zaune ta fara bashi.



"Sannu Sayyid" Ummi ta faWa cikin tausayawa, kallo Waya ta yi masa ta gane yana jin jiki. Da da ne, kome za a yi,ba zai bar gashin nan a buWe ba. Amma yanzu ba ta gashin yake yi ba, ga fuskarsa duk ta kumbura. A zuciya irin ta Nana, ta san ko a titi ta tsince shi a wannan yanayin, ba za ta iya tafiya ta rabu da shi ba, balle mijinta.



˜arar da wayarta ta yi ne, ya sanya ta dawo hayyacinta. Ta Waga wayar tare da yin sallama.



"Ke Hansai, ina ta kiran wayar ki, amma ki ka ™i Wagawa?"



Ummi ta ce "Eyya, ba haka ba ne Uwani,ba na kusa ne, ya gida ya mutanen garin?"



"Lafiya ™alau, ya na ji muryar ki ™asa-™asa, laulayi ko rashin lafiya"



Ummi ta yi ya™e ta ce "Ba gara a ce laulayi nake ina kwance ba, da abin da yake faruwa"



"Subhanallah, meyafaru?" Kasancewar Uwani kaka

47 / 126