Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

BUZU Book 1 to 3 Complete Hausa Novel by Ayshercool

Author :  AYSHERCOOL Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 126

51K to 54K   out of 377.2K words

na son Waukar ta, amma zuciyarta da ™wa™walwarta, na kan kalaman"

"da ko fassarar su ba ta sani ba, sai dai tsananin daWin da suke yi mata, ya sanya ta ci gaba da sauran su."

"Sun shafe lokaci a haka, sannan da ™yar ta tashi ta fara yin wanka, sannan shi ma ya tashi, sai dai kan ya"

dawo tuni bacci ya yi awon gaba da ita.

*

"Tamkar Nana ta taka rawa yau, saboda murnar za su fita yau, ya ce mata tare za su je dubiyar."

"""Amma babu matsala ba za su bu™ace ka ba mutanen gidan? Kar mu yi laifi"""

"""Na gaya musu"""

"Da wuri ta gama komai, suka shirya suka fita tare."

"Ta Waukko dubu goma a kuWin hannunta, ta tsaya ta yi sayayya a hanya, sannan suka tafi."

Asibitin da aka kwantar da Shukura suka fara zuwa.

"Haidar ne ya fara gano ta, ya zabura daga jikin mahafinsa ya nufo Nana da wani irin gudu, cikin"

matsanancin farin ciki.

"Caraf Nana ta Waga shi, ta rungume tana juyi da shi a gurin. Kawai ya ™ara ™an™ame ta ya saka kuka."

"Ita kanta Nana hawaye ne ya cika mata ido, cikin sanyin murya ta ce ""Is ok sweetheart, ya isa haka"" ta yi"

maganar tana shafa kansa cike da ™aunar sa.

"Yanayin kamaninsu da ta gani da Sagir, ya sanya ta gane shi ne mahaifin sa."

"Ta ™arasa suka gaisa, ta ce masa ""Dan Allah a wane Wakin suke?"""

"""Su na ciki room 2 VIP, sai dai ba sa bari a shiga"""

"Ta ce ""Subhnallah jikin har ya yi tsanani haka, Ubangiji Allah ya ba ta lafiya, Hajiyan na ciki ne?"" A fusace"

"Sayyid ya ja hannunta, zuwa cikin asibitin. Sagir ya mi™e da sauri ya bi bayan su, saboda ga Haidar a gurin"

"Nana, shi kuma ya ja Nana sun yi ciki ba sallama ba komai."

"A ™ofar Wakin suka tsaya, Sagir ya ™araso ya ce ""Bari na yi wa Mummyn magana"" ya shiga cikin Wakin,"

"Nana ta dubi Sayyid ta ce ""Daga tsayawa tambaya, sai ka ja hannuna mu tafi ai ba zai ji daWi ba"""

"Wani mugun kallo ya yi mata, da ya tilasta mata yin shiru da bakin ta."

"Hajiya Amina ce ta fito fuskarta Wauke da fara'a tana faWin ""Ga 'ya ta, ga 'ya ta"" ta rungume Nana. Nana"

ta dur™usa har ™asa tana gaida Hajiya Amina.

"""Lafiya ™alau Nana, kin ga yadda ki ka yi kyau tubarkallah? Haidar yau ga Nana"""

Ya yi murmushi yana sake ri™e hannun Nana.

Ayshacool

"Hajiya Amina ta ce ""Allah sarki, tare da mai gidan ku ke ashe, mu na ta ™in abin nan da ganin an zalunce"

"ki, Allah dai ya ™ulla lamarin. Sannu ka ji ya gidan?"" Hannu ya Waga wa Hajjya Amina tare da risunar da"

"kansa ™asa cikin girmamawa, ba tare da ya yi magana ba."

"Nana za ta yi magana, mijin Shukura ya le™o ya kalli Nana ya ce ""Ta ce ki shigo"" mamaki ya kama Nana,"

"amma ta Soye hakan. Ya karSi Haidar saboda kar ta shiga da shi, ya damu Shukura. Nana ta shiga Wakin da sallama, babu haske sosai a Wakin, amma ana iya ganin komai da yake Wakin. Nana ta ™arasa gaban"

gadon da Shukura take. Sai dai ta Wan tsorata ganin Shukura duk a kumbure.

"""Sannu Maman Haidar, ya ™arfin jiki?"""

"Ta yin™ura da kyar, Nana ta taimaka mata ta jingina da jikin gadon ta ce ""Jiki da sau™i Nana, dama za ki"

"zo duba ni?"""

"""Haba Maman Haidar, me zai hana? Ni ban za ci za ki kawo yanzu ba ki haihu ba ma. Sannu"" Ta jinjina kai"

"ta dudduba Wakin ta ga daga ita sai Nana a Wakin. Ta kama hannun Nana ta ce ""Na san a zamana da ke,"

"wata™ila na yi miki abubuwa marasa daWi, duk da ina yaba Wawainiyar da ki ke yi da Yarona. Sai dai"

"kowane mutum akwai irin baiwar da Allah ya yi masa, komai kallon ™as™ancin da ka ke yi masa."

"Wannan maganganun nawa, ba sa rasa nasaba, da yawan miyagun mafarkin da nake yi da ke"""

"Gaban Nana ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta kalli Shukura ta ce ""Da ni kuma?"""

"Sai kuma Shukura ta rikice, ba ta san ta ina za ta fara yi wa Nana wannan bayanin ba, amma ta dake ta ce"

"""Mafarkai nake yi marasa daWi, kuma ina yawan ganinki kin zo za ki taimaka mini. Ni dai kawai ki saka ni a addu'a a tsorace nake, ji nake yi tamkar zan bar duniya, ba zan rayu ba""."

"""A'a maman Haidar, kamar ba wayayyi ba, mafarki fa ba gaske ba ne ba, duk da wasu lokutan ishara ne,"

"amma mafarkin annabawa ne yake Wari bisa Wari gaskiya. Sai kuma wasu bayin Allah da a kan yi wa ishara a mafarki. Wasu lokutan shaiWan ne kawai yake wasa da hankulanmu, amma ki kwantar da hankalinki ki saka a ranki babu wani mai yi sai Allah, kuma babu wanda ya isa ya yi miki abin da Allah bai yi miki ba. Sannan in sha Allah zan saka ki a cikin addu'a ba dan ki yarda cewa ganina da ki ke a mafarki a zahiri nice zan taimake ki ba, Ubangiji za mu nufa da bu™atunmu baki Waya, shi zai magance koma mene"

"ne, ki kwantar da hankalinki dan Allah"""

"Shukura ta jinjina kai ta ce ""Haka ne, na gode sosai da sosai Nana, na gode"""

"""Ba komai Allah ya ™ara afuwa, bari na je, na ji an ce ba a bari a shigo a gan ki"""

"""To shikenan na gode"" ta ji daWin kalaman Nana, mussaman da ta yi ta nanata mata, mafarki ba gaskiya"

"ba ne, wasu lokutan sharrin shaiWan ne kawai."

"Nana ta fito daga Wakin, jikinta duk a sanyaye."

"Hajiya Amina ta taso tana faWin ""Nana kin fito?"""

"""Eh Hajiya, Ubangiji Allah ya bata ingantacciyar lafiya, Ubangiji Allah ya raba ta da cikin nan lafiya"""

"""Amin ya Allah Nana"""

"""A'a Hajiya ina Haidar Win?"""

"""Babansa ne ya tafi da shi yanzun nan"""

"Jiki a sanyaye Nana ta ce ""Kash, ban gama ganinsa ba Hajiya"""

"""Ki yi ha™uri, jiransa ake yi, yana tafiya da Haidar ne gurin kakarsa ake kai shi, ni kin ga ga jinya, abin zai"

"yi mini yawa ne. Amma in sha Allah zan saka a kawo miki shi har gida."""

"""To shikenan, ga wannan a bawa yarona, wannan kuma a saya wa Maman Haidar wani abin, ban san me"

"take so ba"""

"Hajiya Amina ta ce ""Nana har da Wawainiya har haka, dan Allah ki bari kar ki takura kan ki, zuwan ma da"

"ki ka yi na ji daWi sosai da sosai """

"Nana ta ce ""A'a Hajiya, idan ba ki karSa ba ba zan ji daWi ba, dan Allah ki karSa"""

"Hajiya Amina fuskarta Wauke da murmushi ta karSa ta ce ""To Allah ya saka da alkhairi, ki yi wa mijinki"

"godiya ma ya ba wa Haidar kuWi, Allah ya saka da alkhairi. Na ga haryanzu ba ya magana"""

"Nana ta Wan saci kallonsa, ta yi murmushi ta ce ""Ba komai Hajiya"""

"Ganin hirar ta ssu ba zata ™are ba, ya sanya shi yin gaba, Nana na ganin ya yi gaba, ta yi wa Hajiya Amina"

"sallama a gurguje, ta nufi hanyar da ya bi."

"""Shi ne za ka yi gaba ka bar ni?"" Ya waiwayo ya kalle ta ya ci gaba da tafiya."

Ayshacool

"Ta tsaya tana yi wa Nurses Win gurin sallama, ya ja ya tsaya tare da waiwayowa yana hararar Nana. Ta yo"

"gaba tana murmushi, tare da mamakin yadda yake so ta ™arfin tsiya sai ya mayar da ita irin sa, na rashin"

kula mutane.

"Yana zuwa bakin ™ofar fita, ya ja ya tsaya, Nana ta ™araso tana ™o™arin duba, abin da ya hana shi fita"

"amma ya tare ta, shi bai shiga ba, kuma ba dawo ba. Ta le™a ta gefensa, ta ga mene ne ya hana shi"

"wucewa, kawai ta ga Alhaji Zailani, tare da Doctor Sharif, a take gabanta ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta ja ta tsaya cike da razani da fargaba."

Ayshercool

08081012143

Ayshacool

"Alhaji Zailani ma gabansa ne ya faWin, cikin fargaba yake bin ™wayar idon Buzun da kallo, tare da"

mamakin ganinsa a gurin a dai-dai wannan lokacin.

"A hankali Sayyid ya ja da baya, taku biyu, ya sanya hannunsa ya ri™o Nana ta bayansa, ya ba su hanya."

"Alhaji Zailani ji yayi tamkar an zare masa lakar jikinsa, jikin nasa ya yi wani irin sanyi, wani abu mai kama"

"da tsoro ya shige shi. A hankali ya taka ya shigo, yana ™o™arin kallon Nana da ke tsaye a bayan Sayyid,"

"amma Sayyid Win ya hana hakan, saboda yadda ya ™are babbakewa ya kare ta."

"Ita kanta Nana ji ta yi yanayin ta na ™o™arin canzawa, ta saka hannu ta ri™e na Sayyid, tana addu'a a cikin"

zuciyarta.

"Wani irin ba™in ciki ya mamaye zuciyar Alhaji Zailani, ganin yanzu wannan Buzun ne mijinta, da ya aure"

"ta ya san da yanzu bu™atar sa ta biya, wani abin yake hari ba wannan ba, amma Mahaifinta ya yi masa"

sagegeduwa.

"Doctor Sharif ya ce ""Alhaji lafiya kuwa?"""

"""Eh lafiya ™alau"" Har Alhaji Zailani ya yi gaba, ya tsaya ya sake waiwayowa, amma ya sake ido huWu da"

"Sayyid, ya kange Nana, ya kare ta babu yadda za a yi ya iya hango Nana yadda yakamata. Sai da Sayyid ya tabattar Alhaji Zailani ya bar gurin, sannan ya waiwayo ya kalli Nana, yadda duk jikinta ya yi sanyi, ya kamo hannunta suka fita waje."

"Bai dai ce mata komai ba, ta tare musu abin hawa, ta gaya masa inda zai kai su."

"Gaba Waya Nana ta rasa abin da yake yi mata daWi, ta rasa dalilin da ya sanya, gaba Waya ta rasa abin da"

"yake yi mata daWi. Duk da tana zaton hakan baya rasa nasaba da mugun nufin da Alhaji Zailani ya taSa nuna mata, amma ta rasa dalilin da ya sanya gaba Waya take nema ta rikice, ta fita daga hayyacinta."

"A hankali ta kwanta a jikin Sayyid. Cikin damuwa ya dube ta, ya dafa ta ya ce ""Ba lafiya ne?"""

"Ta ce ""A'a"""

"""To Meyafaru?"""

"""Ba komai"" ta furta a hankali kamar mara lafiya."

"""Ko mu koma gida ne?"" Ta girgiza masa kai alamar a'a."

"""Sannu"" ta jinjina masa kai."

"Sai da suka je daf da titin unguwar su, sannan ta tashi daga jikinsa, tana kallon titin nasu."

"Suka je gurin da za su sauka, ya ciro kuWi a aljihunsa ya mi™a wa mai Napep Win su ka tafi."

"""Sayyid"""

Ya waiwayo ya kalle ta.

"Sai kuma ta yi shiru, dan rasa me za ta ce masa ta yi."

Tsayawa ya yi yana ™are wa ™ofar gidan su Nana kallo. Ko ina faci ga uwar kwata a layin.

"""Bari na shiga na yi musu magana, sai ka shigo"""

"Ya jinjina mata kai ya ce ""Zan je masallaci """

"Ta ce ""To shikenan, a yi mini addu'a"""

"Ya Waga mata hannu, tare da jinjina mata kai, ita kuma ta shiga cikin gidan."

"Sallama ta yi, Nasiru yana tsakar gida yana goge takalminsa, yana ganin Nana ya tashi da gudu ya nufe ta."

"Nana ta rungume shi tana murmushi, ""Nasiru ya garin?"""

"""Lafiya ™alau"""

"""Ina mutanen gidan ne?"""

"""Mama ta Wan fita, Baba kuma ya je masallaci"""

"Nana ta ce ""Samo mini tabarma na zauna a nan, ina su Jamila?"""

"""Jamila daga warkewarta ta tafi yawo, Suwaiba ma ba ta nan"""

"""Ohh ya jikinta kuwa, mu ka yi waya da Ummi, ta ce mini tun da ku ka dawo ba ta da lafiya """

"Nasiru ya ce ""Eh, amma ta warke, Mama ta ce wai me magani ya ce Aljani suka yi wa laifi. Aka yi sadakar"

"™osai, aka dafa zakara aka bin..."

"""Ammm ya jikin Baba kuma"" Nana ta katse maganar Nasiru."

"""To ga shi nan dai, yanzu zai shigo ai ki gan shi"""

"Nana ta Waukko wayarta ta ce ""Nasiru ga wayata, ga kuWi ka yo mini turin fina-finai dan Allah"" ya karSa"

ya mi™e tsaye tare da faWin an gama yanzu kuwa.

"Nana ta tashi ta fara tattare tsakar gidan, saboda yadda aka bar shi kaca-kaca. Ta gama sharewa Baba ya"

"yi sallama, ta Wago ta kalle shi. Da ™yar yake taka ™afarsa yana bin bango. Ya tsaya sororo ya ce ""Ke me ki ke yi a gida kuma?"" Duk da Nana ba ta ji dadin tambayar da ya yi ba, saboda ta san yana tunanin ko auren ya samu matsala ne, amma ta yi murmushi ta ce ""Baba duba ku na zo yi"" Ta yi maganar tana gyara"

masa tabarma a tsakar gida.

"Ya ™arasa ya zauna da ™yar, Nana ta koma gefensa ita ma ta zauna ta ce ""Sannu ya jikin naka?"""

"""Jiki ga shi nan mu na lallaSawa abu ya ™i ci, ya ™i cinyewa"""

"Ta kalli ™afafuwan nasa ta ce ""Wacce ce take ciwon a ciki?"""

Ayshacool

"Ya ce ""Duka, sai dai wannan ta fi ciwon"" ya yi maganar yana nuna mata ™afarsa ta hagu."

"""To Baba ka je Asibiti?"""

"""Da wane kuWin zan je Asibitin? Na gargajiya zan koma, ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ta dawo da"

"ke gidan nan?"""

"Nana ta yi murmushi mai ciwo tana buWe jakarta, ta fito da leda tana faWin ""Baba idan matsala ta dawo"

"da ni, ba zaka karSe ni ba ko? Ai ka yi mini addu'a ka ce Allah ya bani zaman lafiya, in sha Allah matsala ba za ta kawo ni ba sai alkhairi"" ta yi maganar tana Sare dafaffen ™wan da ta fito da shi daga leda."

"Ta gama Sare ™wan, ta mi™a wa Baba, ya saka hannu ya amshe, yawun bakinsa na tsinkewa."

"""Baba na san ni mai laifi ce a gurinka, na Sata maka rai a kan abubuwa da dama, mussaman na bijirewa"

"auren waWanda ka so na aura, amma ina son mu saka a ranmu cewa, dukkanin su Allah bai ™addara akwai mijina a cikin su ba. Ni yanzu babban fatana ka daina yi mini kallon mutuniyar banza, na san dole na fuskanci tuhuma na abin da ya kai ni Wakin su magadi, amma ba abin da ka ke tunani ba ne Baba, da zan lalace da ban kawo wannan lokacin ban lalace tun a baya ba."" Tuni hawaye ya wanke mata fuska, zuciyarta na wani irin tafasa da raWaWi. Baba bai ce mata komai ba, sai karSe ™wan da yake yi yana"

lamushewa.

"Ta goge hawayen ta, sai da ta Sare masa dafaffen ™wan nan guda biyar, ta Webo ruwan randa ta kawo"

masa ya karSa yana sha.

"Ta Waura alwala ta yi sallar azahar, bayan ta idar, Nasiru ya shigo gidan yana faWin ""Nana ga wayar ki, an"

"ciko miki ita da fina-finai fal"""

"Ta yi murmushi ta ce ""Na gode yaron kirki"""

"Mama ta yi sallama ita da Suwaiba, sai da suka Wan yi turus ganin Nana a gidan babu tsammani."

"""Lafiya dai na ganki a gida? Ba dai auren ne ya samu matsala ba"""

"Nana ta waiwaya ta kalle ta, ta yi murmushi ta ce ""A'a ganin ku na zo yi, na gaishe ku, aurena bai samu"

"matsala ba"" Mama ta kwaSe baki tana rataye mayafinta a kan igiya."

"Nana har kallon Mama take yi, tana mamakin wai ita ba ta san ™arara a fili take nuna ™iyayyar da take yi"

mata ba.

"Nana ta ce ""Suwaiba ya ku ka zo gida?"""

"""Lafiya ™alau wallahi, mu na dawowa Jamila ta kwanta rashin lafiya"""

"""Haka Ummi take gaya mini, shi yasa yau na yin™uro na fito. Nasiru duba idan ya idar da salla, ya shigo ya"

"duba Baban mu tafi, ban yi girki ba"""

Nasiru ya ce to.

"Suwaiba ta ce ""Nana wai waye yake ba ku Abinci? Gidan da ku ke aikin ne suke ba ku?"""

"Nana ta yi murmushi ta ce ""A'a wanda ya ajiye ni ne yake kawowa, ba kuna nan ya kawo muku fura ba"""

"Nasiru ya ce ""Yana waje, na yi masa magana bai kula ni ba"""

"Nana ta yin™ura ta ce ""Bari na yi masa magana"""

Yana zaune a wani dakali da yake kallon gidan su Nana.

Yana ganin ta fito ya mi™e tsaye yana kallon Nana.

"Ta ™arasa ta ce ""Sayyid, zo mu je ku gaisa da Baban"""

"""Wai in shiga?"""

"Ta ce ""Eh, ku gaisa da Babana ka duba shi"""

"Nana ta yi gaba ya bi bayanta,"

"Gaba Waya suka zubo masa ido, sai dai kansa a sunkuye, har suka isa gaban Baba."

"""Sannu"" ya furta a hankali yana tunanin ko haka ya kamata ya ce?"

"""Yauwwa sannu, ya iyalin?"""

"Ya ce ""Alhamdilillah"""

"Baba ya ce ""To madalla"""

"Nana ta ce ""Sayyid, ga ™anwata wadda su ka zo ranar, ga mamana, ga kuma Nasiru da suka zo a tare"""

"Bai kalli inda Mama take ba, ya ce ""Sannu"""

"Yanzun ma kwaSe baki ta yi ta ce ""Ji wata irin gaisuwa, haka ake gaida sirikai?"""

"Nana ta ce ""Ki yi ha™uri, ba hausa sosai ne"""

"Buzu dai bai tanka musu ba, ya mi™a hannu ya Wora a kan ™afar Baba, ya ce ""Allah ya sauwwa™e"""

"""Amin na gode"" ya Wan jima yana kallon ™afat, sannan ya Wauke hannunsa, ya saka a aljihunsa, ya ciro"

kuWi ya ajiye wa Baba a gefen ™afarsa ya tashi tsaye.

"Nana ta bi kuWin da kallo, ba tare da ta san ko adadin nawa ba ne ba."

"Baba ya ce ""Duk wannan haka, to na gode sosai Allah ya yi albarka"""

"Nana ta ce ""Baba bari mu tafi gida, Allah ya baka lafiya ya ™ara afuwa, dan Allah a gaida Jamila idan ta"

"dawo"""

"Sayyid tu ni ya yi waje, domin shiga gidan su Nana ji ya yi tamkar ya yi tsirara, gaba Waya idanun"

mutanen gidan da bai saba da su ba ya ji ya takura masa.

"Suwaiba ta ce ""Ke Nana wai mijin nan naki kamar dodo, baya sauke wannan takunkumin na fuskar shi,"

"ko ba shi da ha™ora ne?"""

Ayshacool

"Nana ta yi dariya ta ce ""Biyo ni waje na saka ya sauke miki rawanin ki gan shi. Baba Allah ya sauwwa™e"

"idan Jamila ta dawo a yi mata sannu"" Nana ta ja takalmanta ta yi waje."

"Tana fita waje, ta yi karo da Gaddafi. Turus Nana ta tsaya cikin tsoro, sai ma ta rasa me za ta ce masa."

"""Nana me ki ke yi a gida?"""

"""Zuwa na yi duba Baba, ina wuni?"""

"""Lafiya ™alau, ya ki ke ya gidan?"""

"""Lafiya ™alau, ashe ka dawo"""

"""Eh na dawo shekaranjiya"" Nana ta yi tsuru-tsuru, tana hango Sayyid da ya tsaya yana kallon ta, ya tsuke"

fuska tamkar ya fashe.

"""Amm ai tare ma muke da shi"" ta faWa cikin kame-kame."

"Gaddafi ya waiwaya, ya kalli Buzu ya mayar da idonsa kan Nana ya ce ""Amma babu wata matsala dai"

"ko?"" Nana ta jinjina masa kai."

"Gaddafi ya saka hannu a aljihunsa ya Waukko kuWi ya mi™a mata ya ce ""Ga wannan, kya sai wani abun"""

"Ta saka hannu biyu ta karSa, tana mamakin yadda duk Gaddafi ya canza."

"""Nana duk yadda za a yi, ki ri™e auren ki, ki ™addara wannan shi ne zaSi mafi alkhairi da Allah ya yi miki,"

"kin san zaman gidan nan namu ba daWi ne da shi ba"""

"Nana ta jinjina kai ta ce ""Na

18 / 126