THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   9 / 38

24K to 27K   out of 111.1K words

tilasta mata hakan tasa tamkar ace numfashinta ya ɗauke ne,tana tsaka da wannan tunanin taji yaja wani wawan birki wanda ya hadda bugewar kanta da jikin ƙofar motar.
Ƴar ƙara ta saki tare da saurin dage goshinta wanda taji yana mata zafi,a hankali ta ɗago kanta tare da runtsa idanunta da ƙarfi sbd yadda wajan ƙeyi mata zugi,ƙwaɓe fuska tayi tare da juya sleepyn eyes ɗinta,rau² tayi da idanu tare da haɗiye ƙwallan daya tarar mata a cikinsu,cikin muryarsa shagwaɓa tace.

"Auchhhii very hurt"ta faɗi maganar lkcn da take sanya hannunta saman goshinta tare daya tsuna fuskarta😟a lamun zafi,cikin juriya da kuma jarumta ta soma juyawa zuwa side ɗin da yake,wani numfashin wahala ta sauke ganin tuni yabar motar,dry ta bawa kanta ganin da gske tsoransa da gske,wani murmushin tayi sai kuma ta murguɗa baki cikin ranta tace.


"he acting like a king"ta faɗa tana leƙa kanta ta window'n motar sai a lkcn ta fashinci shopping yazu,whatever dai taji daɗin fituwarta dan kusan satin guda rabon ta fita waje,sai yau sosai yake ƙarewa gefen titi'n kallo da kuma yadda mutane ke harkokinsu babu wanda ya damu da wani,hakan kuma ya ƙara birgeta cikin ƙanƙanin lkcn ƙuncin dake zuciyarta ya kau,domin ita yarinya ce wacce bata ajjiye damuwa a cikin rant,ta yarda cewa Innallah ma'arsabirin dukkan tsanani yana tare da sauƙi,ta yarda cewa damuwa bata taɓa zama magani,kuma ƙaddara bata taɓa dauwama tana da nata lkcn,haka nan kuma dukkan rayuwan mutum tana tafiya ne da kalan nasa ƙaddara,kamar yadda tayi imanin cewa tata kalan ƙaddarar kene kuma ta shirya karɓarta da hannu bibbiyu,a ƙaro na wajan uku hawaye ya ƙara silɓiyowa ta cikin idanunta,cikin muryarta mai sanyi tace.


"nayi kewanki Mom ina fata baƙya ciki ƙunci da baƙin ciki kamar yadda nake,ina roƙan Allah ya haɗa fuskokinsu kafin ɗaukewar numfashinmu,i luv you Mom ina baƙin cikin ranshinki kusa dani,yaya yaran da basu da iyaye suke ji,yayane yaran da iyayensu suka haifa suka yar suke ji,ta rayuwa da Mom ɗinta na tsayin lkcn mai yawa amma ƙwana 7 kacal ta gagara samun sukuni sbd rashinta,Ya rabbi ka kawo mafita ka kawomin ranar da zan koma wa Mom na"ta ƙare maganar ta ƙara fidda wani kuka mara sauti.

Ta daɗe a wajan kafin ya dawo cikin motar mutane ɗauke da kaya a hannunsu,yana daga cikin motar ya buɗe masu bouth ɗin motar suka fara zuba masa kayan,suna gamawa ya zaro kusan 20k sabbi ƙal ya basu ƙyauta,bai tsaya jin godiyar da yake masu ba yaja motar a guje yabar wajan,jin shassheƙar kuka kusanshi ya sashi juyowa sai a lkcn ya manta tare sukazo wajan,shi mene yasa ma yazu da ita? Taɓe baki yayi a hankali ya kunna waƙar Atif aslam ya shiga bi cikin zazzaƙar muryarsa cikin nutsuwa da ƙwanancewa yake bin waƙar tare da shan vanillah yogourt ɗin dake hannunsa,a haka har suka ƙarasu cikin harabar masarautar bilhas,yana fitowa yayiwa wasu Hadimai nuni dasu ƙwashi kayansa sukai masa ciki,ana haka motar Lil prince tayi parking da ɗan saurin ya fito ganin Zarina wacce ya yini da tunaninta yau.


Sosai Saifu ya fahimci wajan Zarina zaizo hakan ya sashi saurin riƙe hannunta ba tare da tayi tunani ba,ya soma janta da ɗan saurin.


Wani baƙin ciki ne ya sauka zuciyar Lil prince cikin ɗaga murya yace.

"ohh hello!"ya ƙare maganar cikin ɗaga murya,tabbas yasan dashi yake hakan kuma baisa Saifu ya tsaya ba,saima ƙara tafiya yayi hankali ƙwance.


Da saurin Lil prince yasha gabansu idanunsa a rufe ya ɗaga hannu ya zabgawa Zarina Mari kana ya dubeta yace.


"ohh weldone beby you did again uhm u will pay for ur promise"ya faɗa yana jefa wata uwar harara,sannan ya juya kan Saifu tare da nunashi da hannu yace.

"You! Wai kai wanne power ma kake dashi a gidan sarautar nan da kakeson yin abinda kaga dama kuma a lkcn da kaso ehee answer me?"


Ɗauke kai Saifu yayi daga kallonsa na wani lkcn ya saki hannuta tare da hankaɗata zuwa ga Lil Prince,kamar bazai magana ba sai kuma ya gyara tsaiwarsa tare da soma karkaɗa key ɗin hannunsa,cikin muryar isa da gadara yace.

"idan kai a matsayinka na ɗan sarki wanda suke ta ƙama da ƙarfin mulkinsu haɗi da dukiya ba kaji kunya ƙulla alaƙa da ita ba,to nikam bata tsarina bata gabana kallon baiwa nake mata tamkar yadda aka bani umarni na zaɓi maid,dalilin hakan yasa na ɗauke dan nima ta dingayi min bauta banda haka ko inuwa ɗaya bata isa na haɗa da ita ba,bare kayi wani banzan tunani kaga ni ban hanya na huce ban iya ciwon baki ba"ya ƙare maganar yana jan numfashi mai ƙarfin kanse sbd nauyin da maganar tayi masa,ya daɗe banyi magana mai tsayin haka ba sai yanzu shi yasa yaji maƙoshinsa nayi masa ƙirjinsa nayi masa raɗaɗi,ko ƙara kallonsu baiyi ba ya huce ta gabansu yana tako cike da kamala.


Wani banzan kallo Lil prince ya watsawa Saifu tare da faɗin "tabbas baka san mece Sarauta ba,baka san mene ƙarfin mulki ba,nayi Alƙawarin da ƙarfin mulkin da muke dashi saina a zabtar dakai saina baƙanta zuciyarka da kalalolin azaba mai raɗaɗi nayi alƙawarin kozan rasa komai nawa sai naga ƙarshenka da ƙarfin mulkina"ya faɗi hakan cikin baƙin ciki da ƙonan ran da Saifu ya cilla masa,sosai maganganun Saifun sukayi nasara a zuciyar Prince hakan yasa yaji babu abinda yafi tsana a yanzu sama da Saifu,juyowa yayi ya zuba mata ƙananan idanunsa wanda lkci guda suka ƙanƙance sbd ɓacin rai,cikin maganarsa wacce take nuni da umarni yace.

"After magrib kizo Lambu i want talk to you"yana faɗin hakan yasa kai ya shige hanyar da zata sadashi zuwa flat ɗinsa.

Tsaye suka bar Zarina zuciyarta nayi mata zafi da raɗaɗi,a karon farko ta ƙara tabbatarwa kanta shiɗin bamai damuwa ne da damuwar wani ba,tayi tunanin zai bata kariya zai kula da ita haka nan zai taimaketa sbd fuskar nagartattun mutane da yake da ita,sai dai tayi kuskure shiɗin nada banne kansa kawai ya sani bai damu da kowa ba kamar yadda taga alamu daga fuskarsa,lallai ta yadda ita ɗin bai wace sai dai hakan bazai saka ta yarda ya wulaƙanta ta ba,ya jefeta da maganganu masu baƙanta rai da kuma tarwatsa zuciya,zata nuna masa ita ƴar halak ce kamar yadda bai damu da ita ba haka nan itama bata damu dashi ba,zata ɓoye masa sannan za tayi nisa tashi zata hqr da son ganin fuskarsa da zuciyarta ke ƙwaɗayi,ji tayi a yanzu gaba ɗaya ya siri mata wata tsanarsa ta dirar mata a zuciya da zama dashi ƙwara zama da Lil prince zata koyawa zuciyarta sonshi duk da hakan abune mai matuƙar wahala a gareta.
Hannu tasa ta share hawayen dake ƙwance saman fuskarta kana ta fara tafiya cikin rashin kuzari da kuma sabon yanayin data samu kanta na ƙunci da baƙin ciki.


Saifu yana ƙarasawa flat ɗinsa direct bedroom ya shige yana kallon yadda suke jera masa kaya kamar yadda ya basu umarni,yana shiga ya soma cire uniform ɗinsa kana ya ajjiyesu jikin wadrope,bathroom ya shige yana zuwa ya sakarwa kansa shower.
Sanyin ruwan da yaji ya sauka tsaƙiyar kansa zuwa naked chocolate skin ɗinsa,ya sashi sauke ajjiyar zuciya tare da fesar da wani huci mai zafin gaske,a hankali jikinsa ya soma rawa idanunsa ya ƙanƙance tare dayin wani jaa tamkar an watsa masa barkono,yanayin yadda jikinsa ke rawa ya haddasa miƙewar jijiyoyin kansa wanda suka fito suka jera saman forehead ɗinsa,a hankali gagasar jikinsa ke miƙewa,hakan yasa fresh skin ɗinsa ƙarayin dark itama ta sauya kala,cike firgici da ficewar hayyaci yasa hannu ya hanrgitsa somar kansa gaba ɗaya ya birkice ya zama tamkar wanda akaiwa allurar hauka.



A hankali ta tura ƙofar farlon a hankali kamar wacce ƙwai ya fashewa,cikin fargaba da tsoro da kuma yadda zuciyanta ke beating vry past ta tura kanta cikin parlon tare da soma juyawa idanunta kamar wacce ke neman wani abu,ganin babu kowa a parlour'n yasa ta ƙarasa shigewa cikin,sosai parlour'n yayi mata ƙyau musamman yadda a.c ke ratsa parlour'n ganin bata da wani tym yasa ta soma gyara parlour'n tana gamawa,ta gamawa ta nufi kicthen cikin ƙaramin lkcn ta shirya masa specail night food mara nauyi,bayan ta kammalawa ta goge komai na kicthen kana ta shirya masa wamers ɗin a kan table,miƙewa tayi tare da hamma cikin saurin tayi wanka a toilet ɗin data gani na parlour kana tayi alwala,cikin sauri ta fito tare da gabatar da sallah issahi,tana idarwa ta miƙe a can capert ɗin dake parlour'n lkc kaɗan bacci yayi gaba da ita ba tare data amsa kiran Lil prince ba.



*THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE,IF YOU NEED JUST CONTACT ME 08119237616 200 NAIRA ONLY*
*25-26*

MAGIC#




..Kasan cewarsa Namiji mai juriya da kuma haɗiye ɓacin rai yasa gaba ɗaya ya fita hayya cinsa,yadda jikinsa yake rawa tamkar mazari zai tabbatar maka ba ƙaraƙin ciwo ya keji a cikin zuciyarsa ba,bai san mene rauni ba,haka nan bai san mene karyewar zuciya ba,amma kasan cewa da ita a ƴan ƙwanakin nan zuciyarsa na son karaya,rauninsa na son bayyana wanda kuma hakan ba shine burinsa ba,gaba ɗaya ta hana zuciyarsa sukuni,tunaninta na son tarwatsa masa zuciya,cikin zafin nama yasa hannu ya kaiwa bangon toilet ɗin doka,ƙarfin bangon da kuma girman naushin da yayiwa bango ya haddasa fashewar hannunsa jini ya soma zoba,ganin shower'n na neman bashi haushi ga yadda zuciyarsa keyi masa zafi da raɗaɗi ya sanyashi faɗawa cikin jakuzzie wanda yake cike da ruwan tamkar ƙaramin kogi,a hankali ya fara shigewa jikin jakuzzie'n yayinda numfashinsa ya fara ɗaukewa sbd yadda ruwa'n ya shanye saman fuskarsa,a hankali numfashinsa ya tsaya yawan ruwan da kuma girman jakuzzie'n ga kuma yadda jikinsa ya saki ya sanya gangar jikinsa tayo sama kansa kuma ya nutse jikin ruwa'n haka ya fara yawo saman ruwan tamkar gawa.


Lil Prince na barin wajan Zarina ya ƙarasa flat ɗin Fulani kilishi wacce ta kasance mahaifiyarsa,fuskarsa a ɗaure ya faɗa ɗakin yana zuwa ya sameta kishin giɗe akan cousion,Gefenta Hadimanta da Kuyangunta wasu nayi mata fita,wasu kuma na matsa mata ƙarfa,yana shiga yayi gyaran murya gaba ɗaya Hadiman da Kuyangun suka fice daga cikin ɗakin sukayi waje,da ɗan sassarfa ya ƙarasa wajan Kilishi tare da zubewa gabanta ya sauke ajjiyar zuciyar mai ƙarfi kafin ya dubi Kilishi yace.


"Yanzu ni shikenan Mai martaba bazai ta yani samun cikar burina ba,ina Sonta kilishi so bana wasa ba,ina mata son da basan zan iya yiwa wani ɗan adam ba aduniya,Fulani wlh ina sonta da gsky bazan iya hqr da ita ba,kuma inaji a raina bazan iya bin umarnin Mai martaba idan akanta ne,dan Allah ki tayani samunta zuciyata ciwo"

Ya ƙare maganar cikin ƙwantar da murya tare da zubawa mahaifiyar tasa idanu,Numfashi kilishi taja na wani lkcn kafinta gyara murya tace.


"Ba abin mamaki bane dan Mai martaba yaƙi amince da wannan burin naka sabida shima yana buri akan yarinyar,bayan haka kasan cewa a tarihin masarautar bilhas jinin sarauta bai taɓa auren baiwarsa ba,amma ace so sone sonkai yakai yafi,yana da burin akanta ga farin cikina kuma yana sonta,wanne kake ganin zai yihu daga cikin biyun nan,CIKAR BURI KO FARIN CIKIN RAI?"ta ƙare maganar tana yin wani murmushi wanda yake da ma'anoni kala².


Lil prince ne ya dubeta da idanunsa da suka soma sauya kala sabida damuwa kana ya janye idanunsa daga gareta yace.


"CIKAR BURI bai zama lallai ba domin ko babu shi mutum zai iya rayuwa kuma ya samu ƙwanciyar hankali,somin ko burinsa bai cika ba aƙwai wani abun da yafi wannan burin muhimmanci wanda zai sanya ya manta da wannan CIKAR BURIN,
Amma FARIN CIKIN RAI wani abune mai girman gaske wanda idan babu shi zuciya da gangar jiki zai iya samun matasala,farin ciki zaiyi ƙwara daga zuciyar mutum kana baƙin ciki ya maye gurbin farin cikin,samuwar FARIN CIKIN RAI ne kawai zai ɗauke wanda zafi da raɗaɗi da zuciya take ciki,haka shine zai shafe ƙunci da baƙin cikin da zuciya dake cikin idan aka auna wannan abu biyu babu shakka zance FARIN CIKIN RAI GABA YAKE DA CIKAR BURI"ya ƙarasa maganar yana kama hannayenta tare da zuba mata idanu yana son yaji abinda zata faɗa.


Jinjina kai Kilishi tayi alamar gamsuwa da maganar Prince,hannayenta ta zame daga cikin nata kanata ta shafi kansa ciki isa da gadara haɗi da tabbatar da abinda take faɗa tace.


"Na rantse da sarkin dake busamin numfashi harna shaƙa na fesar,saina mallaka maka farin cikin ranka,idan har banyi haka ba tabbas ban cika ƴar wacce ta haifu wajan iyayenta ba,kaine magajin Mai martaba haka kuma kaine Sarkin gobe,jeka abinka ka ɗauka cewa ka samu farin cikin ranka,sannan kayiwa Mai martaba akan idanunsa kada ka bijirewa umarnisa ka barshi shima yayi fafutukar samun cikar burinsa,keja ɗan nagada wanda aka haifa ga daular mai ciki a yanzu a wannan nahiya tamu ta Bilhas"


Wani farin ciki ne ya cika zuciya Lil prince cikin zumuɗi ya ɗura kansa bisa cinyar Kilishi yace.

"nasan kina raye bazan taɓa kuka ba,tabbas kinamin sahihiyar ƙauna fiye da Mai martaba shiyasa nake ƙaunarki fiye dashi"

Kunnansa ta murɗa da ƙarfi wanda ya sashi sakin ƙara kaɗan,sakina tayi tace "ɗan nema dukkanmu iyayenka ne ya zama dole kayi biyaya wa abinda mukeso,maza jeka nema zan saka ayimin iso wajan Mai martaba"


Miƙewa yayi tare da shafa kansa yace "zandai bar maki ɗakinki amma ban iya bacci yanzu sai naje na rage zafi da ita"ya ƙare maganar yana fice daga cikin ɗakin.

Dariya tayi kana ta ɗauki Apple guda ta sanya abakinta,tana jin soyayyar Prince na ƙara shiga zuciyarta musamman idan ta hangesa saman karagar mulki idan Mai martaba yayi murabus,tana zaune Hadimanta da kuyangunta suka shigo,da kallo ta bisu kafin tace.

"ina Kuyanta Kulsum ne?"

Da sauri Hadima Batul tace "Ai ranki ya daɗe Lil prince magaji mai jiran gado ya sanya akaita ɗakin duhu"ta ƙare maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa.

Jinjina kai Kilishi tayi kafin tace "da kyau halan laifi tayi masa naga ta fiya rawar kai"ta faɗi maganar tana taɓe baki alamar ko ajikinta,nan ta sanya akayi mata kiran jakadiya tana zuwa tace tayi mata iso wajan Mai martaba,babu daɗewa Jakadiya ta dawo tare da faɗin "Mai martaba ya riga daya ƙwanta sai dai a tara zuwa gobe".

Wata tsawa Fulani kilishi ta watsawa Jakadiya tare da nunata da hannu tace.

"wannan shirmen na gaji dajinsa bana da ikon ganin mijina yau ace Fulanin sora bata bada umarni ba,gobe ace kaza haba bafa baiwa ce ni ba,kisan duk yadda kikai gobe na samu ganin Mai martaba"tana faɗin hakan ta miƙe tare da tattare Alƙyabbar jikinta nufi bedroom ɗinta.


Lil prince na zuwa sashinsa ya huce bedroom kana ya cire kayan jikinsa ya nufi bathroom,wanka yayi sannan ya sanya wasu kayan bacci masu ƙyau,kana ya zaune gefe guda yana jiran zuwa Zarina,sama da 2hours yana zaune babu ita hakan kuma ya tabbatar masa da baza tasu ba,kuma yasan babu wanda ya hanata sai wannan wawan cike da takaici ya ɗauko wata ƙwalbar giza ya fara zubawa cikinsa,saida yayi tatil sannan ya faɗa bed yana surutai a haka bacci yayi gaba dashi.





Saifu's pov
Cikin fitar hayyaci da kuma goshewar tunani yayi saurin ɗago kansa sama daga cikin jakuzzie ɗin,wata nauyyiyar ajjiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare fesar da wani zazzafan huci ta cikin bakinsa,a hankali ya ɗaga lashes ɗin idanusa wanda suka jiƙe da ruwa sukai zara-zara,cikin abinda baifi 3seconds ba ya buɗe gajiyayyun idanunsa wanda sukai jaa,sabida ruwan daya shigesu,luff yayi cikin jakuzzie'n ya shiga sauke numfashi,mene hakan ke nufi akan hakan ya kasa control kansa? Dalilin hakan ya kasa danne bacin rai da damuwan dake ransa? Mene yasa yake abu kamar zautacce ba tare da yayi tunanin hakan zai faru ba,mekenan all this na mene? A hankali ya sanya hannunsa saman goshinsa tare da murzawa,cikin wata ƙasalalliyar murya yace "ya rabbi meke shirin faruwa,ohh God save me"ya faɗa yana taune laɓɓansa wanda sukayi jaa sabida taunesu da yayi,yasan dukkan lkc'n da yayi hakan there's something big gonna happen to him..
A kasalance ya miƙe daga cinin jakuzzie'n kana ya ƙarasa gaban shower'n ya ɗauraye jikinsa tare dayin brush ya ɗaura alwala..
Batherope ya sanya a jikinsa yana fitowa ya ƙarasa wajan wardrope ɗin da kayansa suke ciki,wani ƙaramin wando troser ya ɗauka ya sanya kana ya saka wata ƙaramar singlet.
Wata farar jallabiya ya ɗauka ya sanya a jikinsa kana ya fesa wani parfume wanda yake sawa idan zaiyi sallah,paryer mat ya shimfiɗa kana ya tada da sallah cike da nutsuwa,yana kammalawa ya fara tilawan alkur'ani cikin ransa,bai ƙwanta ba sai wajan 2 shima ya daɗe yana juyi akan bed kafin wani wahalallan bacci ya samu nasarar yin gaba dashi.



*_Washe gari_*
A hankali ta buɗe idanunta sosai tayi mamakin ganinta ƙwance a ƙasa,kai ta ɗaga domin ganin lkc da ɗan sauri ta miƙe tsaye ganin shida ta kusa,da ɗan sassarfa ta zura flat ɗin shoe ɗinta ta nufi toilet,alwala tayi kana tayi brush tana fitowa ta tada sallah akan abinda ta ƙwanta,bayan ta idar tayi lazumi ta miƙe domin shiga kicthen nan idanunta ya sauka kan table ɗin data jera food warmers ɗin akai,wajan ta ƙarasa ganin kamar ba'a taɓa abincin ba,amma domin ta tabbatar da abinda take tunani,wani baƙin ciki taji a zuciyarta ganin babu abinda ya taɓa,wasu ruwan hawaye taji ya sauka daga cikin idanunta,wata kam duk irin abinda tayi masa bai taɓa ba,lallai ta ƙara yarda ya maidata baiwa,share hawayen fuskarta tayi kana ta ƙwashe kayan ta nufi kicthen,tana zuwa ta juye abincin cikin wani babban flast kana ta wanke dukka flast ɗin..
Tsayawa tayi tana tunanin tayi masa girkin ko kar tayi,daga ƙarshe ta yanke shawararyi masa,cikin sauri ta haɗa masa kunun gyaɗa da kuma masa,kana tayi masa farfesun zallan kayan ciki wanda yaji kayan ƙamshibayan ta kammala ta haɗa masa fruit salad,tana kammalawa ta jera masa komai kamar jiya..
Fruit salad ta ɗiba tasha dan bata fiya cin abinci ba,wani jug mai kyau ta ɗauka ta zuba kunun gyaɗan sannan ta ɗibi farfesun kayan cikin ta zoba cikin wani flast,ma dai² cin basket ta ɗauka ta zoba kayan ciki ta rufe da wani ƙyalle,cikin ɗan saurin da take dashi ta ɗauki basket ɗin tayi waje.

A hankali ta dinga satar hanya tana fakar idanun mutanen waje,harta ƙarasu wani haɗaɗɗan sashi dake cikin gidan sarautar mai ƙyan gaske,wani numfashi ta sauke na wahala kana ta zobawa wajan idanu musamman ƙofar glass ɗin tana tunanin ta

9 / 38