Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
zuciyarsa.
Jarumta da kuzarin daya aro ya sakawa kansa tasa ya samu nasarar ɗaga ƙafarsa tare da cije laɓɓansa ya soma takawa zuwa garesu,yanayin yadda yake tafiya cike da izza da nutsuwa haɗi da taƙama da gadara ya ƙarasa inda suke zaune,yana zuwa ya zube gaban Mai babban ɗaki jikinsa duka rawa yake,ganin yadda ruwan hawayen dake ƙoƙarin ɓoye sune neman fallasa asirin zuciyarsa ta hanyar zubuwa zuwa kan fuskarsa,a kasalance kuma jiki a sanyaye ya ɗura kansa bisa cinyarsa Mai babban ɗaki.
Murmushi Mai babban ɗaki ta saki kafin ta sanya hannunta ta lalubi kansa,hannunta ta tura cikin tsakiyar sumar kansa,wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke lkcn da sanyin hannunta ya ratsa tsakiyan sumar kansa,ƙara cusa kansa yayi tare da sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya mai ƙarfin kaske,sannu a hankali hawayen suka samu nasarar sauka daga cikin idanunsa zuwa kan cinyarta.
Shuru Mai babban ɗaki tayi tana sauraran yadda yake sakin ajjiyar zuciya da kuma yadda ɗumin hawayensa ke sauka kan ciyarta,Zarina ta fuskanta tare da sakin murmushi tace.
"Ɗiyata maza ɗaukomin ƙwarya cikin bedroom"tana faɗin hakan taja bakinta tayi shuru,tunanine daban-daban yake ƙwance cikin brain ɗinta,yayinda shi kuma yake tunanin Mamaynsa wacce ba tafi shekara guda rasuwa ba a hatsarin mota,wannan dalilin yasa ya shiga wani irin hali sosai kewan babunsa ta addabi zuciyarsa.
Jiki a sanyaye Zarina ta miƙe zuciyarsa ji yake babu daɗi,wani matsanancin tausayinsa ya dirar mata,tana ji kamar ta maido da abinda ya keji zuwa wajanta,sai yansun ta fara gasgata abinda ta keji game dashi,shine rauninta kuma shine farin cikinta,tabbas shine “HEART DREAM" ɗinta wanda kullum cikin farkinsa take da kuma tunaninsa,soyayyarsa ba irin soyayyar nan bace wacce ake jinta lkc guda,tabbas soyayyarsa halittace a zuciyarsa,tana cikinsa a ranta sosai fiye da sosai ma,ji take tamkar ta kasance dashi irin kasan cewar nan ta har abada,tana jinsa a jini da gangar jikinta,dukkan wani numfashi nata yana fita da tunaninsa da kuma kewarsa,lumshe idanunta wani abu taji mai ɗumi nabin fuskarta hakan ya tabbatar mata ba wani abu bane face hawaye,daimond ring ɗinta ta murza tare da mannashi a ƙirjinta,jiki a sanyaye ta ƙarasa cikin ɗakin tare da ɗauko ƙwaryar da Mai babban ɗaki tace.
Tana fitowa ta sami Mai babban ɗaki nayi masa raɗa a kunne shi kuma yana sakin wani ƙawataccen murmushi wanda ya bayyanar da zallan ƙyansa da haibarsa haɗi da ƙwarjininsa,sosai teeths ɗinsa suka bayyana sabida lafiyayyan murmushi daya kuma saki,ganinta yasa ya haɗe ransa tamau tare dakau dakau da kansa zuwa gefe guda,janye idanunta tayi daga garesa kana ya ƙarasa gaban Mai babban ɗakin.
"buɗa ki bashi"Zarina ji tayi gabanta ya faɗi amma ta daure ta buɗe ƙwaryar ta tura masa zuwa gabansa,pouting lips ɗinsa yayi ya zubawa damammiyar furar dakan idanu wacce taji zuma da mazarƙwaila,tanƙwasheɓlegs ɗinsa yayi tare da ɗaukan lodayin dubar yayi kana ya ɗibi furar ya sanya bisa bakinsa,lumshe idanunsa yayi sabida garɗi da zaƙin furar daya ratsa kunnuwansa,kasan cewar ba wani abinci yaci mai yawa ba,yasa yasha furar sosai kana ya dubi Mai babban ɗaki kana ya tausasa harshensa yace.
"Nagode sosai Ammi,zanje sallah"ya faɗi hakan a taƙaice,faɗin Ammi da yayi kuma yabi baki Zarina ne kamar yadda yaji ta faɗa,daga haka bai ƙara magana ba,yasa kai yabar sashin gaba ɗaya,yana fita harabar masarautar ya ƙarasa masjid ɗin dake gidan sarautar,yana zuwa yayi alwala ya gabatar da zuhur kana ya zaune ya jira asar,yana kammalawa yayi tiwalan ƙur'ani kana ya ƙarasa,Fada wajan biyar na yamma aka tashi a Fada.
Direct flat ɗinsa ya nufa yana zuwa ya same ƙwance saman sofa tana bacci,bedroom ɗinsa ya nufa yana zuwa ya faɗa toilet tare dayin wanka ya sanya three guater ya faɗa saman bed sai bacci.
*_Kogi_*
Jikin yanayi na kiɗima da kuma firgici boka falha ya ƙara goge gumin da yake zubu masa,abinda yake gani cikin madubin ba ƙaramin gigitasa yayi ba,cikin rashin yadda da abinda yake gani ya soma faɗin wasu ɗalatsiman tsafin da shine kaɗai yasan ma'anarsu,aduk lkc'n daya buƙaci tura masu wani hayaƙi sai wani irin ni'imtaccen haske ya kuro hayaƙin daya tura,ƙara zafafa bincikensa yayi hakan ya haddasa fashewar madubin sabida ya kasa ɗaukan tsafin da yake masa,wata kururuwa ya saka wacce ta haddasa rugujewar wani sashe dake cikin ɗan ƙaramin ɗakin nasa,a gigice ya fara faɗin wasu kalmomi kafin wani lkc saiga wani aljani ya bayyana gabansa,nan ya fara zubawa aljanin wani irin abu mai kama da yawo dalalala haka yak zuba zuwa bakin aljanin,kafin daga bisani ya tsagaita da abinda yake yace.
"Maza jeka na yarje maka wannan lokacin nakane tunda sun tarwatsamin madubin sihirina,tabbas saina kawo ƙarshensu nine aljalinsu saina zame masu masifa maza bisa kanku"yana faɗin hakan ya ɗauki jan ruwa mai kama da jini ya watsa aljanin.
Wata gigitacciyar ƙara aljanin ya saki kafin ya soma wata girgiza mai ɗauke da iska,cikin abinda baifi minutes ba,wata ƙyaƙƙyawar halittar wani saurayi ta bayyana,a ƙaro na biyu ya kuma yin wata girgiza saiga aljanin ya koma CAPTAIN SAIFUDEEN🏃🏻♀️
*Sorry for shurt typing gaba ɗaya yau ina busy da ba zanyi posting ba sai kuma naga rashin da cewar hakan pls bear with me*
_masu fitarmin da book kodaina domin jiya naga posting ɗin da nayi a wani grp, The new emir akan farashi mai sauƙi yake ga dukkan mai buƙata zai biya 200 ta wannan accout ɗin 0116886423 Sulaiman Na'ima S masu buƙatar Vip zasu biya 500 domin samun littafan dana rubuta na kuɗi cikin ƙwanciyar hankali sai Evidence of payment ta wannan number 08119237616_
By
*NIMCYLUV*
*33-34*
#Blood
Wani mugun murmushin aljanin yayi wanda a yanzu ya zama kamilallan mutum mai siffar Saifudeen,ƙara kallon bokan yayi domin ya duba abinda baiyi masa kana yace.
"jeka maza jeka garesu yanzun lkc'n kaɗai ne,lokacin da zaka shaƙƙu da koƙwanto cikin zuƙatansu yayi,lokacin da zaka rusa ɗan ƙaramin farin cikin da suke dashi yayi,wannan shine lkc'n ɗauka fansa,ehh! tabbas fansa zauka ɗauka jekaa!"ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya,ba tare da wani dugun tunani ba,Aljanin najin hakan ya ƙurma ihu tare dayin wani juyi haɗi da katantanwa izuw sama,saiga asalin halittarsa ta bayyana,halitta mai cike da tsoro halittar da dukkan wani ɗan adam yayi tuzali da ita zai iya rasa ransa sabida tsoro da firgici,a hankali yanayin ya soma juyewa jikinsa ya fara shaƙwanyewa zuwa ƙasa,saida ya zagwanye gaba ɗaya kana ya zama wani baƙin haƙi cikin abinda baifi sa'a ɗaya hayaƙin ya tashi zuwa sama.
Bokan naganin aikinsa yaci kuma ɓuƙatarsa zata biya ya saki wani mahaukacin ihu tare da dukan ƙirjinsa iya ƙarfinsa,kafin ya zame ya soma zane jikin wata farar ƙasa wanda akafi sani da duba
**** ****
Zaune suke a babban parlour'n da aka ƙawatashi da kayan alatu na mure rayuwa dajin daɗin,sosai gidan suke cikin ƙwanciyar hankali dajin daɗi kafin ƙaddara tazu ta gilma cikin rayuwarsu,ƙaddara mafi muni domin rashin ɗan mutum a wannan zamanin ba ƙaramin tashin hankali bane.
Ɓatan ZARINA ya zame masu wani miƙe da bazai taɓa goguwa cikin rai da zuciyarsu,hatta gangar jikinsu kewan rashinta suke,sabida sabo da ƙwanciya da tayi a jikinsu,Zarina kenan ƴar gata mai jida dangi gaba da baya ko ina soyayya ake nuna mata,bata tama kuka ba da sunan ɓacin rai saina shagwaɓa,kukanta ɗaya idan tayi mafarkin Heart dream ɗinta,ko kuma ta nemi ring ɗinta ta ɓata wannan dalilai sune kaɗai kesa hawaye fita a idanun Zarina.
Kallonta Abba yayi cike da tausayawa yace "sai yaushe ne hawaye zai daina fita a idanun mace mai juriya,sai yaushe ne damuwa zata bar zuciyar mace mai taƙama da ikon Allah,sai yaushe ne matana zata yarda da ƙaddara?"ya ƙarasa maganar cikin sanyin murya da kuma danne abinda yake ransa.
Kallonsa Mom tayi kana ta saki murmushi tace "ba ina kuka bane dan banyarda da ƙaddara ba,ina kukane sabida tunanin halin da Zarina ke ciki,ina tsoro halinda zata samu kanta,nasanta taƙin cin abinci ko a gida,to ina tunanin inda take aƙwai abincin ko babu,ina take ƙwana ina take dashi ban sabi ba,wannan dalilin shike sani zubar da hawaye"ta ƙare maganar tana goge hawayen idanunta.
Mamu dake gefe tana lissafin mutanan da za'a fiddawa zakka tace "ato Audu faɗa mata dai may be idan kaine zata amince da cewa Allah ɗaya ne,banda sakalci ina damuwa ta taɓa zama magani,bakai kaɗai kikejin zafin rashinta ba,nasan dole zaki fimu jin zafi da raɗaɗi sabida ke uwace,amma dole muyi hqr mu fauwalawa Allah komai".
Abdallahi wanda yake matsayin Abba kamar yadda iyalansa suke faɗa masa,yana numfashi kana yace "Insha Allah ubangiji zai kareta kullum cikin addu'a muke kuma na tabbatar ba zata faɗi banza ba"Mom da tayi shuru tun ɗazu sai yanzu ta samu damar magana tace "insha Allah"
"Mumu ya maganar abincin sadaƙa na almajirai da za'a dingayi da azumi,ina son fitar da duk wani abu da za'ai na azumi bansan ajjiye nauyi a kaina"jinjina kai Mom tayi kafin ta tace.
"Munyi yanke shawarar ɗiban masu aiki domin yin ƙosai da kunu ana rabawa almajirar,sbd idan mukace mune zamuyi abin zaiyi yawa aƙwai aikin gida ko Mamu?"ta ƙarasa maganar tana kallon Mamu wacce take nesa dasu,ajjiye abin hannunta Mamu tayi kafin ta gyara zama ta fuskancesu gaba ɗaya tace.
"Eh Sultanerh kinyi tunani mai ƙyau domin aikin azumi wahala garesa,sabida ƙishi da kowa keji,zuwa anjima sai a fara neman ma'aikan sannan aje kasuwa asiyo sauran kayan da babu" da "to"Mom ta amsa sabida yanayin damuwa da kuma tunanin ƴarta da take wanda ya kasa mantuwa cikin zuciyarsa,rufe idanunta tayi tana jin yadda zuciyanta ke mata zafi da raɗaɗi na rashin ƴarta ta,Abba ne ya katse masu shurun ta hanyar faɗin.
"nida yanzu ga A.t.m ɗina dukkan abinda kuke buƙata saiku cira,yafi a tsaya lissafin kuɗin,insha Allah zuwa gobe ko jibi zan fitar da zanbayar sabida banson a fara azumi ban bayar ba,haka kuma...."ringing ɗin wayarsa ce ta tsayar dashi daga maganar da yake,wayar ya ɗauko daga cikin aljihunsa,farin ciki fal fuskarsa ya dubi Mom yace.
"A'a Sufyan ke kira da alama sun samu kansu a dajin"yakai zancan yana picking call ɗin tare da sata a speaker.
Sufyan dake can ɓangaren ya jingina da jikin wata bishiyar darbejiya acikin jejin illori,ya lumshe idanunsa lkcn da yaji anyi picking call ɗin nasa,kana ya saki murmushi yana matse hannun Tupic dake kusana,cikin ƙasa da murya da kuma salon shagwaɓ Safyan yace.
"Abbana munshiga damuwa sosai na rashin jin muryarku,munyi kewanku sosai fa har bama iya aiki"ya ƙare maganar yana kallon Tupic wanda ya matsu yaji yaya lafiyan little sis ɗinsu.
Daga can ɓangaren Abbu ya saki wani murmushin jin daɗin muryar ɗan nasa yace.
"ina tabbacin munfiko kewanku komai namu da muke baya tafiya saida tunaninku,kullum cikin zullumi da fargaba muke sabida rashin sanin halin da kuke,Mom ɗinku kullum cikin damuwa take gaba ɗaya ta rabe kamar ba ƙatuwar matana ba"Abba ya ƙare zancan yana jan hancin Mom wacce ta ƙwaɓe fuska alamar taji haushin maganar Abba.
Sufyan ya saki dariya a karo na biyu tare cije leɓensa na ƙasa yace.
"Abba ƴar ƴan Mom zasuci tararnka,ko gaisawa ba muyi ba zaka fara tsukana"Mom dake gefe tayi saurin dawowa kusan Abba tare da ƙwace wayan tace.
"sweetheart yakuke hope komai nrml yaya aikin naku yaushene zaku dawo,muna buƙatarku kusa damu,na gaji da rashinku kusanmu"ta ƙare maganar hawaye na sakko mata,Abba ganin Mamu ta shiga bedroom tun ɗazu ya saka hannu ya jawo Mom jikinsa tare da soma rarrashinta ba tare da yayi magana ba.
Tupic dake tsaye kusan da ɗan uwansa ya turo baki gaba yace. "Mom kuka ko? Har yanzun bakki daina kuka a kanmu,soon zamu dawo gida zuwa goma ga azumi ko biyar,tun ɗazu muna magana banji muryar little ba,where is she?"ya ƙare maganar yana kallon Sufyan wanda yake riƙe da wata ƙatuwar bindiga mai jigida.
"Ayya Tupic daɗin jin muryarku kaɗai zai sani kuka,dan Allah kuyi ƙoƙarin dawowa da wuri,little kuma na ɗaki tana bacci ta tashi da ciwon kai"
Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin "what little babu lafiya tun yaushe ne,wayyo our luv get well soon pls Mom ki kula mana da ƴar ƙaramar ƙanwarmu kice muna sonta da ƙaunarta,bye zamuci gaba da aiki yanzu"yana faɗin haƙan ya ƙatse wayan ya soma harɓi sabida ganin kilmawar ƴan ƙonar baƙin wake da yayi,shima Tupic ya mara masa baya suka fara sakin wutar harɓi,ƙaran harbinsu ya ankarar da sauran sojojin,kafin wani lkcn dajin ya cika da ƙarar bindigo babu abunda kake gani sai wuta da hayaƙi dake tashi zuwa sama.
Shuru Mom tayi jinsun kashe wayan,lamo tayi jikin Abba ta soma shassheƙar kuka,sosai take kewan yaranta gaba ɗaya sam ta gaji da wannan aikin nasu,sukenan cikin jeji babu wani jin daɗi daga shan ruwan tirɓaya da cin ganye".
Ta ƙare zancan idanunta na kawo ruwan hawaye,Abbane ya shiga bata baki tare da ƙwantar mata da hankali kana shima ya miƙe tare da nufar waje,yana zuwa ya faɗa cikin motarsa tare dayi mata key ya harbata zuwa bakin get,yana zuwa aka buɗe masa ƙofar a hankali ya cilla kan motar waje.
*_Masarautar bilhas_*
Ƙwanci tashi babu wahala wajan ubangiji,tun muna irga ƙwana kinmu zamu koma irga watanni daga watanni zamu koma irga shekarau.
A kullum ƙwanakin ƙara hucewa suke kamar yarda numfashin mutum kullum ƙara ƙarewa yake,ƙwanakinsa suna ƙara tafiya girma na zuwar masa,babba kuma tsofa ya ziyarcesa.
Ranakunmu na ƙarewa ba tare da mun ankare ba,haka nan kullum zunubinmu ƙara yawa yake ba tare da mun ƙyautata ƙarshanmu ba.
Yau ya kama ranar da ake saka ran ganin watan Ramadan watan dake saka mutane da yawa ruɗu wajan nemansa.
Cike Fada take da manyan mutame irinsu hakimar dagatai da kuma sauran manyan,wanda suka amsa kiran Mai martaba,sannu a hankali suke zuwa tare da ƙwasar gaisuwa wajan Mai martaba,saida kowa ya gama ƙwasar gaisuwa sannan Mai martaba ya gyara zama tare dayin gyaran murya yace.
"Kamar yadda kuka sabisa ga al'ada da kuma tsari irin na wannan masarauta kusan cewa idan watan azumi yayi Hakimai na kawo buhun shinkafa da babban buhu na yatsi guda ashirin-ashirin,sannan Dagatai suna kawo guda goma-goma,sannan masu Unguwanni zasu kawo guda biyar-biyar,haka nan masu Unguwanni suna gayawa Al'ummarsu su kawo gudan ɗai-ɗai,wannan shine tunatarwar dana taraku a nan domin nayi maku,zuwa nan da goma ga wata Ramadan ko wanne mai Unguwa ya tabbatar ya haɗa kayan al'ummarsa ya miƙa ga Dagaci,Dagaci ya bawa Hakimi,Hakimi ya kawo masarauta,wannan shine kawai zaku iya tafiya".
A hankali Saifu ya ɗaga manyan gajiyayyun idanunsa ya mannasu akan fuskar Mai martaba,domin tabbatar da abinda yake,sam ya kasa yadda cewa aƙwai wani shugaba dazai iya aikata hakan wa al'ummarsa,banda haka ace kana matsayin shugaba amma awajan al'ummarka kake neman abu,kuma a lkcn da kowa yake buƙatar lada domin samun da cewa rana gobe ƙiyama,to wai duk yawan abincin da yake buƙata ina zai kaisu? Mene zaiyi dasu har haka?.
Wani huci mai zafi ya fesar da wani zazzafan huci ta hancinsa,lkci guda idanunsa suka rufe tare dayin jaa sbd ɓacin rai,idanunsa ya ɗauke daga kan Mai martaba kana yaja idanunsa ya rufe,sam bazai jure wannan adalcin ba,ya zama dole yabar wannan masarautar da zarar an kammala azumi,cije lips ɗinsa yayi lkcn daya tuna da Mai babban ɗaki idan ya tafi yaya matsayin rayuwarta yake,yasan cewa kowa rayuwansa a hannun ubangiji yake,amma aƙwai sanadi ai,hannu yasa ya shafi sajen fuskarsa.
"Allah yaja da ranka ya ƙara maka lafiya amma adubi talakawanmu yanzu ana hali na rashin wada taccen abinci ga rashin kuɗi da ake,tabbas akace za'a karɓi wani abu wajansu za'a takurasu sbd da yawancinsu abinci ci wahala yake masu,a yafemi idan na faɗi ba dai²" Hakimin Kantagari ya ƙarasa maganar yana sadda kansa ƙasa alamar girmamawa.
"karya kake ɗan talakawa ahir ɗinka,har Mai martaba ne zaiyi magana wani ya tanka?cewar sarki fada,Hannu Mai martaba ya ɗagawa Sarkin fada tare da faɗin"basshi bana magana biyi gaba ɗaya ko ɓacen da gani".
Gaba ɗaya suka miƙe tare dayiwa Mai martaba sallah suka tafi.
Bayan fitarsu Mai martaba ya dubi Saifu dake tsaye bayansa yace.
"yanayin zamanka zai sauya zaka koma da safe,da yamma kuma kana hutawa"jinjina kai Saifu yayi ba tare da yace komai ba.
Suna zaune a fada Lil prince ya shigo cikin shigarsa ta alƙyabba yayi ƙyau sosai,yana shiga ya zabgawa Saifu harara kana ya ɗauke kansa ya zube gaban mahaifin nasa kana ya ƙwashi gaisuwa,Waziri ne ya dubi Prince yace.
"Magaji ka yini lafiya?"ya ƙare maganar yana sakin murmushi domin a duniya yana ƙaunar Prince,wannan dalilin yasa Mai martaba ƙaunar Waziri tare da yadda dashi.
Shuru Lil prince yayi ba tare daya amsa gaisuwar da Waziri yake masa ba,kallon Mai martaba yayi kana ya sunkuyar da kansa ƙasa yace.
"Dan Allah kaji tausayina kabarni na samu farin cikina,ina sonta sosai bana sonta yayimin illah,kai shaidane ban taɓa ganin wata ƴar mace nace ina sonta da aure ba,dan Allah ka yar jemin kai shedane inayin dukkan abinda kakeso kuma ka umarceni akai,Allah da gaske nake son ZARINA"
Wani ɗan ƙaramin tsaki Saifu yaka jin yadda Lil prince ya cika kunnansa da surutu,jiyayi zaman fadar ya ishesa kuma daman lkcn tashi yayi dan haka kawai ya fice daga cikin Fadar gaba ɗaya ya nufi lambu.
Idanun Waziri ne yayi jaa kana ya ɗauke kansa tare da maidashi wajan Mai martaba domin yaji abinda zaice,wani Murmushi Mai martaba yayi kafin ya kalli Prince yace.
"Komai kakeso a nan duniya inayi maka,baka taɓa kukan babu ba,a wannan karan tunda kaji nace A'a saika samamin lafiya tun kafin fushina ya kufce a kanka,kaine ka kawota gidan ko ni?shin daman na kawota ne domin ka ganta kace kana so,kaje ka nemi duk wacce tayima ni kuma a gobe zan ɗaura aurenka da ita,bana son dugun zance tashi a gabana"wani ɓacin raine ya sauka a zuciyar Lil prince,cikin fushi da kuma ɓacin rai ya fice daga fadar.
Zaune ya sameta akan sofa tana yanke farce,wata duguwar sofa ya samu ya zaune,ɗan lumshe idanunsa yayi wanda suka janye sbd ɓacin rai,a hankali ya buɗe idanunsa ya mannasu akan ƙafarta wacce take fara tas baƙi gashi yayi ƙwance luff sai ƙyalli yake,haka nan ya samu kansa da kasa ɗauke idanunsa daga kan yatsun ƙafarta wanda suke jere abin sha'awa,ɗan juya eyes ball ɗinsa ya juya haka nan ya samu kansa dajin haushinta wanda bai san dalilin hakan ba,yadda tsigar jikinta ke tashi ya tabbatar mata cewa idanunsa na kanta,wani sanyi taji a ranta da kuma wata nutsuwa ta musamman na shigarta,cikin yanayi na shauƙi da kuma so,ta ɗago idanunta tare da saukesu a