THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   22 / 38

63K to 66K   out of 111.1K words

cikin ƙasa da murya yace.
"shirme dai,kiɗe kiɗe kamar dangin jujal,sai kace faɗar Allah da za'ace kowa sai yaje,Allah ya taimaka sai kuje ai"
Yana faɗin hakan ya ɗan ƙarasa gaban Mai babban ɗaki tare da kama hannunta,dai kunnanta yace.
"Ammi babu inda zaki pls ki koma,wancan wajan aƙwai haɗari sam ban yarda da wajan ba"
A hankali ta laluɓi hakansa ta shafi sumar kansa kana ta saki murmushi tace.
"kada ka damu idan ina tare daku nayi imanin babu abinda zai faru,ina baka umarni idan na isa kazu muje tare"
Lumshe idanunsa yay kana ya ɗan ranƙwafa ya rungometa kaɗan a jikinsa,raɗa yay mata a kunne.
Murmushi kawai ta saki tana ƙara shafa gashin kansa.
Hannunta ya kama kana yace su Kulsum suyi gaba zasu zo.
Gaba ɗaya sukai gaba kana yaja hannunta suka fara tafiya.
Yana zuwa wajan masarautar ya saki hannunta kana yay saurin riƙe hannun Zarina wacce take tafiya a hankali.
Can ƙasan maƙoshi yace.
"uhmmm ga Ammi can na kira"
Yana faɗin hakan yay gaba abinsa cikin taƙama da juriya ƙuzari haɗi da izza.

Cike harabar babban filin masarautar yake da mutane,maza da mata manya da yara.
Ɓan garan manyan baƙi daban irinsu,shugaban ƙasa gwamnoni,ƴan majalistu,ciyamomi,kana hakimai,dagatai,masu unguwanni.
Gefe guda kuma ƴan jarida na redio tana gidan t.v
Can ɓarin dama kuma,Mai martaba Khalid ne a zaune bisa luntsumemiyar kujerar sarauta,gefensa na dama Fulanin sura,gefen hago kuma Fulani kilishi.
Ɓan garen dama kuma Prince Najeeb ne zaune bisa ƙyaƙƙyawar kujerar sarauta,gefensa kuma kuyangunsa sane tsaye suna yi masa fita tare da kirari.
Taro yayi taro baka jin komai sai bugun algaita da sarewa haɗi da tamburan masarauta.
Sakin busa shina yana nashi busar mai daɗin gaske da kuma tsari.
Sarkin kirari ma zai zabga kirari yake tare da wanke masarautar tas tun daga kan kakanni da kuma zuwa kan sarki Sufrak,kana Sarki Sudais.
Kabbara akai tare da sakin wata lafiyayyiyar sarewa sosai kewa da son Sarki Sudais ya dawo masu zuciya,wasu kam kuka suka fara sabida rashin babban adalin sarki irin Sarki Sudais babbar illane wa al'ummar gari.
Saifu da yake can gefe tsaye yana jin yadda kansa yake sara masa ga kuma yadda jikinsa yake rawa.
Da sauri ya buɗe idanunsa sabida wata lafiyayyiyar sarewa da yaji an saki.
Durƙusewa yay a wajan sabida jin ƙafafunsa sun gaza ɗaukan gangar jikinsa.
Sosai sarewar ke dagula masa lissafisa runtsa idanunsa yay lkc'n da yaji Sarkin kirari na faɗin.

"Allah yakai haske kabarinsa shugaba ja gaba,sarki mai adalci sarkin da babu kamarka,kayi taka kayi na wasu,Allah ya jiƙan sarki SUDAIS SUFRAK BILHAS"
Gaba ɗaya wajan ya amsa da Ameen
Shikam Saifu shuru yay yana mamaki Sarkin da akewa kirari,shin damar masarutar nan an taɓa sarki mai adaci? Shi sam baiga alama ba.

Su Mai babban ɗaki gefe guda suka zauna cikin ƴan kallo,sabida tsarin zaman masu saka Mai babban ɗaki ciki ba,ita kam ko ajikinta sabida bata san ina take zaune ba.
A hankali idanunta ya fara fidda hawaye sabida sunan Sufrak da taji ga kuma sunan abin ƙaunarta Sudais.
Zarina ce ta masu wajanta ta soma goge mata hawayen fuskarta,duk da bata san kukan mene take ba.

Meera ce ta ƙarasu wajansu tare dayin sallama,amsa bata sukai kana sukai shuru gaba ɗaya suna sauraran gabatar da Kilisan da ake kana kuma ajera sunayen wanda za'ai dasu.
"Sunana Ameera ana cemin Meera,sabuwar kuyangar Lil prince fatan zamu samu fahimtar juna nida ke"

"insha Allah"
Shine kawai abinda Zarina ta faɗa kana taja bakinta tayi shuru.

Gaba ɗaya wajanne yay shuru ana sauraran abinda Mai gabatar da kililansa yake faɗe.

Cike da mamaki Zarina take ƙara mai² sunan SAIFUDEEN BILYAM BAGAIYA.

Shikam Saifu a kiɗime ya ɗaga kansa yana jin abin kamar a mafalki,mene haɗinsa da wata kilisa,shi baima taɓa gani ba,bai san yaya akeyinta ba,kana kuma bai ta yadda za'ai ya hau wani doki ba.
Ya rabbi meke shirin faruwa ne hakan,wane ya keson tuzartashi har haka.
Miƙewa yay cike da kuzari kana ya dai²ta nutsuwar ya ɗauki al'ƙwarin kozai rasa ransa bazai taɓa tuzarta kansa ba,kana kuma bazai taɓa cewa bazai ba.

Cike da nutsuwa taƙama kuzari tsantsar izza,ya ƙarasa tsakiyar filin idanunsa a lumshe,ɗan buɗe idanunsa yay jin ana sutale masa riga,Allah yasa da singlet a ciki.
Yana ji aka cire masa riga kana aka saka masa wata ta ƙarfe wacce ta ɗan kama jikinsa,kana aka bashi talmin fata ya sanya.
Wasu lafiyayyun dawakai aka kawosu gabansu da fari da kuma jaa,jaan aka kaiwa Prince yayinda kuma farin aka kaiwa Saifu.
Murmushin mugunta Lil prince yay kana ya matsa kusan Saifu yace.
"a shirya yin wata huɗu a ɗakin duhu shine sakamakon wanda ya faɗi ƙasa,kafin wannan kuma lkc'n yarinyar daga mutu a kanta she most be my wify for ever"
Yana faɗin hakan yaka sirkin dake jikin dokin ya ɗane tare da zama bisa kan doki.
A hankali Zarina ta ɗaga kanta tana mai kiran sunan Allah,da kuma taimakonsa,bawai sonshi take ba amma bata burin ya tuzarta cikin mamaki.
Wajanne ya ɗauki shuru ganin Saifu yay tsaye tare da zubawa dokin idanu yana kallon wane zane me kamar rubuta a jikin wuyan dokin.

"babu haɗi tsakanin ɗan nagada da kuma taka hawaye,jinjina ga Magajin masarautar bilhas nasara ta kace"

A hankali Saifu ya mutsa bakinsa kaɗan tare da sanya hannu ya riƙe silkin dake jikin dokin,kafarsa ta dama ya dai² akan mahayin dake jikin ingarman doki.
Bisa mamaki da kuma kaɗuwa a kaga Saifu yay bisamillah tare da hayewa kan dokin kana ya dai² ta zaman,tare da kuma da ajjiye ƙafafunsa a jikin dokin.

"bisa ga alamu ƴan kisalarmu sun shirya dan haka jama'ar waje ku tayani irga 3 muna zuwa zero lkc'n kilisa ya fara"
Gaba ɗaya wajan ya ɗauka da 1 2 3 ana faɗin zero.
Lil prince ya zaburi dokinsa tare da faɗe Saifu da ƙasa kana yay gaba cikin ƙwarewa,nan kallo ya dawo kan Saifu ganin ko mutsawa baiba bare a saka ran zai fara tafiya.
Hannu Saifu ya saka bisa kan dokin tare da shafa gashin kansa wanda yake ƙwace lub lub abin sha'awa.
Girgiza dokin yay tare da ɗaga ƙasa ya fara jada baya,kana ya saki wani hargitsatssan ihu daya karaɗe masarautar gaba ɗaya.
Nan tsuntsaye suka fara shawaƙi bisa sama tare da rera kukansu.
Ɗan miƙewa Mai martaba yay tare da zubawa dokin idanu da kuma Saifu,Zarina kam miƙewa tsaye tayi hawayen da take ɓoyewa ya fara sauka bisa kan fuskarta,Meera ce ta kalleta tace.

"Wannan daga ni bazai iya ba,gashi tun farko dokin na neman ka dashi ina da yayi nisa,lusarin namiji"
Wani kallo Zarina tayi mata kana ta ɗauke idanunta a kanta taci gaba da kallon yadda dokin ke katantanwa.

Mai gabatar da kilisar ne yace.

"yaro idan baka iyawa ka bawa maza waje,ka amshi hurunka bisa zama lusari da kai"

Ware manyan gajiyayyun idanunsa yay kana ya sauke wani zazzafan numfashi,a hankali ya kali Daimond ring ɗinsa dake ta zabga haske,hannu yasa ya murzashi kaɗai,kana yaja linzamin dokin gaba ɗaya wajan aka miƙe tsaye jama'ar wajan sukai sabida ganin yadda dokin ya....



*WHO WIN BETWEEN SAIFUDEEN AND LIL PRINCE....?*



The new emir is for sale.
08119237616

*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
*53-54*




NIGHT POSTING 😁🙇🏻‍♀️





Ganin dokin.
Yay wata katantanwa tare da ɗaga ƙafafunsa biyu na gaba ya ƙwalla ihu,kana ya sauke ƙafafunsa bisa ƙasa,cikin tsoro da fargabar dake cin Saifu wacce bata riga ta bai yana saman fuskarsa ba, yaja linzamin dokin lumshe idanunsa yay tare dayin kabbara cikin zuciyarsa,sabida wata zabura da dokin yay kana ya marawa dokin Lil prince baya.
Da sauri Mai martaba Khalid ya miƙe cike da mamaki sabida sam baiyi tunanin hakan ba,wani sautin tambura aka saki wanda ya sanya mutane da yawa suka fara taka rawa.
Fulanin sura sai zabga murmushi take cike dajin daɗi,ɓan garen fulani kilishi kam ji take tamkar ana watsa mata wuta cikin zuciyarta sabida wani turiri da take mata,ɓan gare guda kuma tama falgabar ace Saifu ne zai zama winner,idan hakan ya faru mene matsayin Lil prince?
Zarina kam sam hawaye yaƙi tsayawa a idanunta,sai tsalle take tana juyi tamkar ƙaramar yarinya.
Dan tabbas idan Lil prince yay winner hakan na nufin sunyi nisa da Garkuwarsu kenan,idan kuma Saifu yay nasara tabbas jin daɗinsu zaici gaba da tabbata ita da Mai babban ɗaki.
Wani mahaukacin gudu dokin yake haɗe da zabura sama,yayinda Saifu yake riƙe da linzamin dokin yana ta addu'ar samun nasara.
Lillahi wahidul ƙahhar kenan,Allah me kowa mai komai mai yin yadda yasu a kuma lkc'n da yasu.
Bisa mamaki aljabi dokin Saifu yazu ya huce na lil prince.

A can yankin kogi.
Boka Gilmas ne zaune bisa wata fatar kura,gaban ɗauke da wata ƙwarya wacce take cike da jini gefensa kuma huta naci sai kuma wasu manyan layoyi wacce suke ɗauke da wasu sunaye marasa harafi,gefensa kuma wani baƙin matashin saurayine wanda ya kasance yaronsa,komai tare suke aiwatar dashi,su kashe mutum kosu haukatasu ba komai bane wajansu duk inda kake neman zallar mugunta ka samesu kagama,sam babu Allah a ransu.
Matashin baƙin Sarauyinne ya leƙa ƙwarya kana ya kalli boka Gilmas yace.
"babu da wani sauran lkc'nfa ya kamata kayi wani abu ina tsoro fa" Dauwas ya ƙare maganar yana cilla wani abu bakin nan take saiga wani baƙin hayaƙin mai duhun gaske ya shiga fitowa ta cikin baƙin nasa.
Ganin hakan ya sanya boka Gilmas ke cewa da wata mahaukaciyar dariya har saidai manyan haƙuran gabansa suka bai yana ne,cikin ƙanƙanin lkc kuma ya haɗe rai tamkar bashi ne yay wannan dariyar ba.
Wani baƙin ƙyalle ya ɗauka tare da sanyashi cikin ruwan,kana ya fara karanto wasu manyan ɗalasiman tsafi mafi muni da sauran wanda yake.
Wata guguwace mai ƙarfin gaske tare da wata ƙatuwar murya mai amsa kowwa ta cike ɗan ƙaramin ɗakin da suke ciki.
Gaba ɗaya ginin ɗakinne ya ɗauki rawa lkc'n da guguwar taci gaba da tsananta,a hankali iskar ta fara raguwa wata ƙara aka ƙwalla daga samansu cikin dakiya Dauwas yace muna buƙatar taimakonka kafin nan maza dawo halittar da zamu fi gamsuwa da aikinmu.
A hankali wata halitta ta fara bai yana gabjejiya baƙa wuliƙ mai manyan kunnwa sai fukafukai masu yawan gaske a jikinta,gaba ɗaya harshen halittar a waje yake sai dalalar da wani kalan baƙin yawo take.
Boka Gilmas ne ya haɗe fuska tare da faɗin.
"ba wannan halittar muke magana akai ba,kaga aiki zaka mana kuma zamu biyaka da abinda kace"
Wata girgiza halittar kana tayi wani ihu cikin wata sautin murya mai amsa kowwa mara daɗi tace.
"ina tsananin tsoro dajin falgabar ko mawa waccen kamilalliyar halittar wacce karanma saida nayi jinya sosai jikina yasha wahala,sautin takalmansa ka ɗai ya sanya na zauce bare nayi idanu biyu dashi,ina neman gabafararka a nan"
Wata zabgegiyar wuƙar tsafi ya ɗauka ya laftawa Aljanin,cikin gargaɗi yace.
"koda zaka rasa ranka dole ne ya zame maka kayi wannan aikin,wa kakeso na ɗauka yay,Aljani Kumdak yana tare da Zaitun,sai makahun Aljaninmu shima yana masa aikin tsawon shekaru masu yawa bai taɓa gajiyawa ba,saika daba zuwa zakai kayi ƙwanaki a jikin bil'adam ba zakaimin musu.
Azabar da Aljani murufu ya jine ya sanyashi ƙwala ihu wanda ya cika ɗakin har wani baƙin hayaƙi yay tsartuwa daga bakinsa.
"zanyi zanyi zanyi na tuba kayafan ko zan rasa raina a wannan aikin na yarda zanyi wayyooooo"

"maza koma halittar da nake buƙata kafin fushina ya kufce a kan ka"

Babu ɓata lkc Aljani murufu yay wata girgiza saiga Saifudeen zaune gabansa ya sunkuyar da kansa idanunsa yana zubda ƙwalla,sosai yaji a zaba a wuƙar tsafin da aka shafa masa a jikinsa,wacce ya kejinta tamkar wuta.

Gaba suka tsaya suna kallon ƙyawon halittar daya koma haka nan suka amince tabbas aikinsu a yau zaiyi yadda sukeso.

"maza jeka garesa gashi can bisa ingarman farin doki,maza gashin yana sukuwa bisa lafiyayyen doki,gashi can jeka jeka kada lkc ya ƙure mana"

Yana faɗin hakan ya ɗauki wani baƙin abu ya wasa bisa fuskar copyn halittar Saifu,cikin ƙaramin lkc Aljanin yay girgiza a karo na biyu kamar ƙiftawar idanu suka nemesa suka rasa..
Wannan kenan.

Zaune suke a babban parlour suna shira cikin mutuntaka,duka sun saka sabbin kaya masu ƙyan gaske,kana ganinsu kasan cewa yau ɗin babbar ranace a garesu baki ɗaya.
Mom itace gefen Alhaji Abdallah yayinda Mamu ke zaune bisa wata kujera hannunta riƙe da lemon tsami tana matsewa sabida lemon citta da take sonyi.
Ɗago kai tayi ta kalli ɗan nata bayan ta gama matse lemon hannunta tace.

"ban taɓa jin fargabar irinta yau ba,sosai nayi mummunar mafarkin akan Jikata,tabbas tana cikin halin damu bamu isa mu ƙwaceta ba,sai dai Ubangijin rahama ya kareta da kariyarsa,amma yau kam da tunaninta na wuni,duk yadda nakai dason manta abun amma nagagara,nasan kina jin baƙin ciki fiye da yadda mu muke ji,ke uwace amma ba yana nufin zaki sanya kanki cikin damuwa bane Sultaner Innallah ma'assabirrin,ki ɗauki hakan matsayin ƙaddararran abu da ubangiji ya shirya faruwarsa tun kafin a haifi ita kanta Zarina,sannan muci gaba da addu'a insha Allah ta kusa bai yana nan kusa inaji a jikina"

Da "Allah yasa"suka amsa bata gaba ɗaya,ita dai Mom shuru tayi sabida ita ɗaya tasan abinda yake damunta,cikin sauri ta maida ƙwallar idanunta tare da sauke ajjiyar zuciya.
"kai Abdallah maza jeka saka a ƙarayin addu'a akan wacce ake sannan kayi sadaka"
Kallonta sai kuma ya miƙe cikin girmamawa yace.
"to Mamu bari naje"
Yana faɗin haka ya fice daga cikin gidan zuciyarsa fal tausayin matar tasa,yana son ya rarrasheta amma idanun Mamu ya hana.
Yana fita ya shiga cikin motar tare dayin horn mai gadi ya buɗe masa,ya fice daga cikin gidan.
Fitar keda wuya wata lafiyayyoyiyar farar mota tayi parking a compound ɗin.
Drever ne ya buɗe motar ya fito,kana wasu ƙyawawan matasa masu jini a jika suka fito daga cikin motar.
Kana ganinsu kaga ƴan uwan juna ko kuma nace twints sosai suke kama komai nasu iri ɗaya ne,amma ɗaya yafi ɗaya jiki ɗaya kuma yafi ɗaya tsayi.
Da gudu suka afka cikin parlour'n suna faɗin
"Mom.. Mom..Mom"
Cewar Tufic kenan,cikin ɗaya murya Sufyan yace.

"our little Baby where are you baby we are back"ya faɗa cike da murna da kuma farin cikin ganin ƙanwar tasa.

Jin shurune ya sanya tupic ƙara faɗin.
"Mom..Mamu..Abba kuna inane gamu mundawo cikin yardar Ubangiji"

Mom dake zauna saman sofa tayi saurin miƙewa tsaye tare wajan parlour'n da gudu,wani farin cikin ya lulluɓeta,tana zuwa sukaci karo da juna da sauri suka zame hulunan kansu kana suka rungometa ɗaya ta gaba ɗaya ta baya,sai juyi suke da ita suna murnar ganin mahaifiyar tasu.
Mom kam kukan farin cikine ya ƙwace mata ta ƙara rungome yaranta tare da shafa sumar kansu.
Sufyan dake gabanta ya zare jikinsa tare da langwaɓar dakai yace.

"Mom mene wannan kuka fa"
Ya ƙare maganar yana sanya hannunsa bisa fuskarta ya goge hawayen.
Cikin saurin Tupic shima ya zame jikinsa ya ƙarasu wajan Sufyan yace.

"ohh our beatiful Mom kalli zaratan sojojinki sun dawo cikin ƙosshin lafiya so ki daina pls kudan muji daɗi muma"

Murmushi ta saki tare da miƙa masu hanneyen tace.

"ohh gime me five"
A tare suka tafa hannayensu kana suka ƙare rungometa,a hankali ta sumbaci ƙoshinsu tare da shafa sumar kansu,hannayensu taja suka nufi cikin parlour'n
Mamu suka samu a tsaye tana sakin murmushi da gudu suka ƙarasu wajanta suna faɗin.

"we miss you Grandma munyi kewanki sosai granny yaya jikin da ƙafa,fatan matana bata cikin halin ciwo"

Tupic ya faɗa yana rungometa,hannu tasa ta dungure masa kai tace.

"ɗan nema da kuka dawo ba wajan uwarku kukai ba,za kazu kaimin daɗin baki nina fasa saki zaka ban"

Sufyan ne yay murmushi dan bai fiya magana ba shima yace.

"ayya granny saki fa,to mu zauna dawa kuma?

Ya ƙare maganar yana kallon jikin bangon dan gaba ɗaya manyan photonan Zarina da sukai mata na album babusu,shuru yay kawai ba tare da yace komai ba ya fuskanci granny da take faɗin.

"a'a nagaji daku gaba ɗayanku ku hanzarta nema matan aure nan kusa"

Da saurin Tupic yabar wajan domin yasan yanzu zata fara zazzaga masifarta ta akan sunƙi aure.
Sufyan ne ya ƙwaɓe fuska yace.

"Ai kinji matsalarki granny daga dawowa"pillow ta ɗauka zata cillo masa yay saurin cafewa tare dayin bayan Mom ya rungometa yace.

"Mom"

Dariya Mom ta saki tace
"gidanku Tagwaye yanzu granny kukema haka ko wlh...."

Kafinta ƙarasa Mamu tayi saurin ƙatseta da faɗin.

"Da ubanku Audu kuke ba dani ba,wannan saƙiyanci kuma ga Sultaner nan uwarku da ita kuke"
Ta ƙare maganar tana nufar ɗakin tare da mitar "haka nan ɗirka ɗirka samari har biyi suƙi aure babu gaira babu dalili idan baku da lafiya saiku faɗa muji"

Ita dai Mom shuru tayi domin tasan halin Mamu kuma laifin yaranne da suka taɓota,kallonsu tayi kana ta dungurewa Tupic kai tace.

"ga maganɗisun daya taɓota nan ai,baza ta zaɓo maka cikin matan ƙauye babu ruwana"

"Mom ina little beb ne nasan yanzu tana gida babu makaranta tunda week end ne,kuma beb bata fita yawo,and duk ina photonanta na parlour babu ko guda?"
Sufyan ya faɗi maganar yana yarfar da hannunsa.

Murmushi tayi tace.

"tana lpa fa,nina aiketa,maza kuje kuyi wanka sannan kozu cin abinci"

Gaba ɗaya suka amince da maganarta,haka suka shige bedroom,a nan saɓon faɗa ya tashi idan kowa yace shine zai fara wanka,hayaniyarsu ta sanya Mom leƙowa da mamaki take kallonsu tace.

"yau ni Sultaner naga abinda yafi ƙarfina,har yanzu baku daina wannan faɗan a tsakaninku ba,maza Tupic yi baya ka bawa Sufyan waje.
Turo baki yay kamar ƙaramin yaro yace.

"Mom."

Sufyan gwalo yaywa Tupic kana ya shige cikin bathroom,hqr ta bawa Tupic harya sakko daga fushin da yayi.

Bayan sunyi wanka Abba ya dawo suka gaisa sosai yay murnar ganin zaratan yaran nasa,cikin da farin ciki ya rungomesu.
Ganin magrib na shirin zuwa ya sanya Sufyan faɗin.

"Mom"

Ɗago kai tayi cike da fargabar abinda take tunanin zai tambayeta,kallonta domin sosai ya hango abinda idanunta keson ɓoyewa yace.

"Mom Ina Zarina is there any problm mene kike haiding ne"

Kafin Mom tai magana Abba yace.

"An sace zarina tsayon watanni taƙwas kenan"

A tare suke miƙe tsaye tare da faɗin "What.."

Masarauta.
Yadda Saifu ke sarrafa linzamin dokinsa tamkar wanda ya ƙware ya sanya mutanan wajan sanya ihu wasu hadda taka rawa.
Duk yadda Lil prince yasu ya huce Saifu abin gagararsa ya,cikin bushi yasa ƙafa ya daki ƙafar dokin Saifu mai makon dokin ya faɗi saima ƙara gudu da yayi.
Harya kai ga sunje ƙarshe sun ƙara juyowa sosai Saifu ya bawa lil prince ta zara,a hankali ya runtsa idanunsa sabida wani abu da yaji ya daki kansa ya shige,sunan Allah yasu furtawa amma laɓɓansa sunyi masa nauyin gaske,cije bakinsa yay sabida tsananin ciwon kan daya shigesa lkc guda ba tare daya shirya hakan ba,dishi-dishi ya fara gani a cikin idanunsa ko gabansa baya iya gani.
Hakan ta sanya dole ya saki linzamin dokin idannunsa ya ƙara runtsa wanda take wasu zafaffun hawaye suka fita a cikinsa,a karo na farko daya zama lozer cikin rayuwarsa,yana jin yadda dokin yake ƙoƙarin jan kansa amma ya kasa,yana kallon yadda Lil

22 / 38