Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
ahankili Sarki Maleek ya fara ɗaga idanunsa saitin inda yake ganin kamar inuwar photo kafin yakai ga ƙarasawa wayarsa ta fara ringing,juyawa yay ya nufi part ɗin da aka saukesa.
yana tafe yay picking call ɗin tare da manne wayar a cikin aljihunsa.
daga can bagaren a garin bilhas Abbu ya gyara zama yace "Maleek bana hausa dakai ka sani ka hanzarta dawowa da zarar an kammala ɗaurin auren nan kaji ko?"
jinjina kai yay danshi yama manta da batun za'a ɗaura masa aure,shurun da yayine ya tabbatarwa da Abbu Maleek ɗin ya amsa kamar yadda ya saba amsa magana.
ci gaba da magana yay "yawwa na gyara part ɗin an zoba komai sabo hatta fadar an sauya fenti tare da wasu abubuwa ka kawai ake jira nayi kewarka dear"
sai a lkcn Sarki Maleek ya lumshe idanunsa tare fa fesar da huci mai zafi yace "missed you too Abbu saina dawo"yana faɗin hakan ya ƙarasa shigewa bedroom ɗin sabida kansa da yaji yana sara masa.
yana shiga ya zare alƙybbar jikinsa tare da zare sauran kayan ya rage daga shi sai boxer jin kamar fever na shirin kamasa ne yay saurin faɗawa bathroom tare da sakarwa kansa ruwan shower,ajjiyar zuciya ya dinga saukewa sosai ruwan ratsa jikinsa tare da dukan kansa.
yana gamawa ya zare boxer ya saƙale tare ɗaukan bathrope ya sanya a jikinsa.
cikin jarumta da kuzari ya fito daga bathroom ɗin ya faɗa kan bed tare da lulluɓe jikinsa da duvet sabida jikinsa da yaji ya fara rawar sanyi,teeths ɗinsa ya datse sabida saman mararsa dake karta masa sai a lkcn ya fahimci ciwon cikinsa keson dawowa wanda rabonsa dashi tun abinda Rinaaansa tayi masa.
sosai jikinsa ke rawa sabida zafin zazzaɓin dake ratsa naman jikinsa.
sabida jikin babu daɗi ga kuma tarin gajiya few minutes bacci yay gaba dashi.
Zarina
"ki shiga cikin ruwan zafin nan ki tabbatar kin ɗauki 30minutes a ciki kinji ko,idam yay sanyi saiki zuba wani kana ki zuba wannan ruwan turaren kiyi wanka da wannan sabolun ok"
kaita jinjina tare da zare ƙaramin towel ɗin jikinta ta shiga cikin jakuzzie'n,ganin hakan ya sanya Mom fita.
kamar yadda Mom tace haka tayi sai gashi jikinta ya ɗauki wani ƙamshi na musamman ko ina na jikinta ƙamshi yake fitarwa,haka ta fito daga cikin bathroom ɗin nan taga wani sabon lotion da aka ajjiye mata cikin sauri ta shafa sabida iskar dake kaɗawa gari da dukkan alamu hadarine ƙwance.
tana gamawa ta gyara kanta wanda ɗazo taje saloon.
wani t.shirt da three gauter ta ɗauka ta sanya a jikinta,sabida daɗin da jikinta yay mata ne ta faɗa bed itama nan bacci ya ɗauketa.
A daddafe yay sallar magrib da isha'i ya ƙwanta sam bai bari ansan cewa bashi da lpa ba,a haka ya ƙwana da wannan ciwon cikin haɗi da marar sam baiyi tunanin zaiga wayewar gari ba.
washe gari
Misalin 11 na safe ƙofar gidan Alhaji Abdallahi ya cika da mutane,duk inda ka gilma manyan mutanene wanda suka amsa sunansu.
wasu daga Istanbul,wasu kuma daga Ghana,wasu daga Cameroon,yadda mutane suka cika ƙofar gidan saika ɗauka bikin ƴar ƴan sarki za'ai ko kuma na shugaban ƙasa.
acan cikin gida angwaye sun shirya cikin wata ɗanyar shadda ta gezna,ba ƙaramin ƙyau sukai ba,musamman Sufyan duk da cewa kamarsu ɗaya amma shaddar tafi amsar Sufyan ɗin sabida yafi Tupic jiki.
cikin shigar babbar riga da kuma baƙar hular tankaran,haɗi da wani black compet shoe.
sai baza ƙamshi suke,suna fitowa Mamu ta rangaɗa guɗa tare dayin juyi a gabansu domin biki yara uku ba wasa ba,murmushi gaba ɗaya sukai tare da rungometa ganin lkc najane,ya sanya Sufyan zare jikinsa ya nufi part ɗin Sarki Maleek ƙarar ruwa da yaji a bathroom ya tabbatar masa da wanka yake,juyawa yay sabida yana da manyan baƙi a wajan ɗaurin auren dan haka yay ficewarsa a cewaraa ya tawo daga baya.
ƙara taro ruwa yay a jikin sink tare da kaiwa fuskarsa ya shafa a hankali ya sauke numfashi tare da ɗago kansa,makeken mirrow'n dake jikin bangon bathroom ɗin.
faffaɗan ƙirjinsa ya zubawa idanu ganin yadda gashi yay ƙwance lub abinsa,ya tsuna fuska yay domin still yana jin ciwon marar,a hankali ya zare boxer dake jikinsa,ɗan ware manyan fitannannun idanunsa yay ƙara dubawa yay da ƙyau still dai abinda yake gani shiɗinne,a hankali ya sanya hannu ya shafi saman mararsa dake dripping ba tare da wani dalili ba,shin daman hakan na kasan cewa? daman mutum na iya fitar da wani abu babu wani dalili?ko kuma ciwon marar sane ya sanya faruwar hakan?ganin bashi da wata amsa ne ya sanya ya ƙarasa gaban shower ya sakarwa kansa ruwa..
sosai yaji daɗin ruwa saida ya ɗauki wajan 29minutes kana ya ɗaura towel a waist ɗinsa ya nufi waje.
ganin idan baiyi da gaske ba kasala na neman rufesa ya sanya ya fara shafa lotion saman chocalate skin ɗinsa,yana gamawa ya ɗauki body spray ya fesa,inda aƙwatin kayansa take yaje yana zuwa ya zauro wata light blue ɗin shadda mai masifar ƙyau,yadda take ɗaukan ido kaɗai zai tabbatar maka da yawa kuɗinsa,cikin zallar izzarsa ya fara sanya kayan a jikinsa,yana gamawa ya warware babbar rigar ya sanya a jikinsa,Wow!! haɗuwar fata mai dubu da kuma blue ɗin abu,faɗin ƙyan da shaddar taiwa fatarsa ɓata bakine.
knoking ƙofar akai juyawa yay kamar zai shuru sai kuma yace.
"come in" da sallama Khamis ya shigo hannunsa ɗauke da wata farar alƙyabba da kuma wani sabon rawani mai kalan dark blue.
cikin muryar nutsuwa Khamis yace.
"Brother gashi ka sanya"ya faɗin hakan yana ware alƙyabbar da mamaki yake kallonsa yana son tambayar a ina ya samu amma girman miskilancinsa ya hanashi tambaya.
ƙwaɓe fuska yay domin kayan sunyi masa nauyi a jiki,bisa dole badan yasu ba ya ware hannayensa Khamis ya zura masa alƙyabbar tare da ɗura masa rawanin.
juyawa yay ya kalli mirrow'n ɗan ware idanunsa yay sabida shikansa ya tsorata da ƙyan da yay,sai a lkcn ya kalli adon alƙyabba farar ce wacce akaiwa ado da light blue ɗin zare,banda zagayayyiyar fuskarshi babu abinda ake ganin,farin bluetooth ɗinsa ya manna a kunne kana ya zaro farin glass ɗinsa daga cikin gidansa ya manna a farar idanunsa.
sandar girmansa ya ɗauka wacce ta kasance ta zallar azurfa ƙara covering jikinsa yay da alƙyabbar kana ya kalli Khamis ɗan gyaran murya yay tare da sauke numfashi wajan seconni yace.
"ka shirya kayanmu nanda 30minutes zamu huce"
ciki girmamawa Khamis ya durƙosa yace "angama Allah ya ƙara maka lpa da girma"hannu yasa ya dungure masa kai.
hawainiya kenan ko kuma mace ɗawisu amma sarautar Sarki Maleek tada bance da sauran.
hannu yasa a saman handle zai buɗe sai kuma yaji an buɗe murmushi ya saki ganin Sufyan sai washe baki yake.
rungome juna sukai kana Sufyan ya saki murmushi yace "nai fushi har akai ɗaurin aure baka fito ba" jinjina kai yay tare da matsa hannun Sufyan yace "happy marriage life"cikin farin ciki yace "you too boddy nasan yanzu kaima an gama naka ɗaurin auren"lumshe idanunsa yay tare da haɗeye wani yawo mai ɗacin gaske cikin ƙasa da murya yace "muje yanzu zamu huce airport ɗin Abbu nacan jira,but first zan fara zuwa wajansu Abba muyi sallama"a tare suka jera har Khamis daya fito hannunsa ɗauke da aƙwatin kaya.
a babban parlour suka tsaya kamar ance ya ɗaga kansa cikin sauri ya zare glass ɗin idanunsa tare dayin baya sabida jirin da yaji yana ɗibansa.
cikin sauri Sufyan ya taresa haɗi da faɗin "sannu boddy baka da lpa ne?"baki na rawa Sarki Maleek ya nuna makeken photon Zarina dake manne a parlour tare da faɗin "My Rinaa tana ina ka nunamin ita yanzun nan itace yayewar damuwata"cikin rashin fahimta Sufyan yace "Wai Zarina ai yau aka ɗaura mata aure yanzu haka sunyi nisa da inda za'a kaita gidan mijinta Yusuf"cikin kiɗima yasa hannu ya dafe kansa wanda ya keji kamae zai rabe gida biyu,cikin tashin hankali da kuma kiɗima ya fara faɗin "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"hannu yasa ya dafe saitin ƙirjinsa tare da fara tari a hankali,ganin tarin yay yawa ne ya sanya Sufyan yay saurin ɗauko bottle water duk yadda yasu Sarki Maleek yasha ruwan ƙi yay,a hankali tarin ya fara cin ƙarfinsa hannu yasa a bakinsa tare dayin wani tarin saiga gudun jini ya faɗu,cikin tashin hankali Sufyan da Khamis yace "what!! blood"a hankali idanunsa suka fara rufewa yayinda jini yaci gaba da fita daga bakinsa.
da sauri Sufyan da Tupic daya shigo yanzu suka ɗauke tare da nufar mota dashin ganin hakan ya sanya Fadawan suka shiga mota,a waya suka faɗawa Abba da kuma Abbu,cikin tashin hankali da kiɗima Abbu yace maza ayi bilhas dashi.
haka suka nufi airport suna zuwa direct airplane ɗin da aka tana da dominsa,can baya suka ƙwantar dashi Khamis na kusansa,sai kuma fadawa,Sufyan yaso ya bisu amma babu yadda yaso dole saidai daga baya yana kallo jirgin ya ɗaga haka suka koma gida jiki babu ƙwari.
bilhas
cikin nutsuwa Dr yake duba Sarki Maleek tare da gyara masa drip ɗin dake hannunsa.
"Dr wanne hali yake ciki yanzu?"
cewar Abbu,cikin sarewa Dr ya kalli Abbu yace "bazan iya cewa Sarki Maleek zai rai ko kuma zai mutu ba,domin mutuwarsa ba a hannuna take ba,amma tabbas yana cikin wani hali zuciyaraa gaf take da kamuwa da mugun ciwo,damuwa tai masa yawa dole a kiyaye"
numfashi Abbu ya sauke yace "Innalillahi yanzu Dr mene Abinyi?" gyara tsaiwa yay yace "mafita ɗaya a nema masa abinda zuciyarsa keso shine mafi sauƙi nizan tafi zuwa ko wanne lkcn zai iya farkawa"yana faɗin hakan ya ɗauki first aid box ɗinsa ya nufi waje.
zuba masa idanu Abbu yay ganin Maleek ɗin na sauke numfashi da ƙyar,hanunsa riƙe da saitin zuciyarsa.
lkc guda ya faɗa tare dayin wani fari..
juyawa Abbu yay ya fita tare da nufar parlour anan ya iskesu,kallom yadda take kuka yay kamar ranta zai fita cikin kuka tace "Dan Allah Abbu kada a bari rayuwarsa ta salwanta,ina son mijina anema masa abinda ya keso dan Allah"
jinjina kai Abbu yay kana ya kalleta yace "bansan yaya zanyi ba,amma tashi kije ga mijinki ki bashi kulawa ya kasan ya farka kinan koda abinda zaki masa"jiki na rawa ta miƙe ta nufi ɗakin.
misalin biyu da rabi ya fara buɗe idanunsa da sukai masa nauyin gaske,saurin maida idanun yay ya rufe sabida wani haske daya gani,a hankali kuma ya ƙara buɗe idanunsa harya gama saukesu akan drip ɗin dake maƙale a hannunsa,lumshe idanunsa yay yana zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito,cikin murya mai rauni da kuma sarewa yace "Ya hayyu ya ƙayyumu"da sauri ta juya daga inda take zaune wata zabura tayi sabida ganinsa yana ƙoƙarin zare drip ɗin hannunsa.
jin alamun mutum kusanshi ya sanya ya juya a hankali wacce ya gani zaune gabansa ce ya sanyay sauri mirginawa gefe tare da faɗin "My Rinaaa.
*81-82*
Lumshe idanu tayi lkcn da taji sautin zazzaƙar muryarsa a cikin kunanta,ƙara sautin kukanta tayi tare da cusa kanta tsakanin cinyoyinta taji gaba da rera kuka,ta rasa wanne kuka take,shin kukan farin ciki ne?ko na damuwa da halin daya shiga ta dalilinta?ta kasa fahimtar komai ita kanta tana son taji wasu sirri da aka ɓoye mata,shin mene fa'idar haɗata da Yusuf ansan bashi zata aura ba?
Cikin son tabbatarwa kansa abinda yake gani ya ƙara mirginawa kusanta,tare da zuba mata rikitattun idanunsa wanda suka janye suka ƙara jaa sabida zallar damuwar da yake ciki.
sosai ya tsaya kallonta daimond ring ɗin hannunta daya gani ya ƙara tabbatar masa da cewa itace dai bawai gizo tayi masa ba.
tayaya hakan ta kasance?mene ya saka Abbu yace ya auri Meyrah bayan ba ita yake gani yanzo ba?shin daman Abbun nasa yasan inda Rinaa take?tayaya ya sani?menene makomar Meyrah?kodai mata biyu Abbun ya ɗaura masa aure dasu?
wannan tulin tambayoyin sune a cikin zuciyarsa amma babu wanda yake da amsarsu sai Abbunsa.
tattausan hannunsa ya ɗura a kanta tare da ɗago kan nata baki ɗaya.
ƙara matsawa yay kusanta tamkar zai tsaka ƙirjinsa ya maidata ciki.
ɗaya hannun ya saka ya ɗaga haɓarta dashi nan take full face ɗinta ta bai yana garesa.
saurin runtsa idanunsa yay sabida wani mugun ƙyau da tayi masa a cikin idanunsa.
a hankali yaji gudun zuciyarsa na ƙara domin gani yake har yanzo kamar cikin mafarkin daya saba yake.
soft pink lips ɗinsa ya zubawa idanu ganin yadda take ta taunesu tamkar zata raba gida biyu.
innocent face ɗinta ya zubawa idanu tamkar wanda yake son ganin wani abu.
cikin raunin zuciya da kuma sabon yanayin daya samu kansa ya riƙe tafin hannunta tare da murzawa kaɗan.
kana ya ƙara matsa jikinsa harya kasance komai masu ya zama ɗaya.
lap ɗinsa a saman nata,hakama face ɗinsu na gogar na juna.
hannunta dake cikin nasa ya ɗura bisa saitin ƙirjinsa.
wasu tagwayen ajjiyar zuciya suka sauke gaba ɗayansu.
yayinda sanyin tafin hannunta ya ratsa saman fatar ƙirjinsa,hakan ya sanyashi sakin ajjiyar zuciya wacce take nuni da wani abu na musamman a cikinta.
ana ɓagaren kusan hakanne domin hannunta ne ya sauka akan tsinin nipples ɗinsa wanda suke a bai yane dalilin hakan itama ta saki ajjiyar zuciya.
shuru gaba ɗaya sukai baka jin komai sai sautin saukar numfashi da ƙarar haɗewar teeths ɗinsa wanda har yanzu suke rawa sabida raguwar zafin zazzaɓin da bai gama sakinsa ba.
wani zazzafan numfashi ya sauke mata a saman fuskarta cikin wata kasalalliyar murya mai tafiya da tunanin dukkan wata cikakkiyar mace balle indomie generation like her.
ƙara sauke numfashi yay tare da manne hannunsa a ƙirjinsa cikin son dai-dai ta muryarsa yace.
"Why? mene hakan why Rinaa all this na mene?koke kika zaɓi hakan?hawayena ya zuba dalilinki,na rasa nutsuwata dalilinki,na ratsa farin ciki dalilinki,gashi yanzu zuciyata daf take da bugawa dalilinki?mene yasa kika tafi kika barni?mene yasa kika rabu da zuciyar data mace a kanki,kece farin cikin Maleek,kece komai nasa,bana jin zan iya rayuwa dai-dai da kowa idan babuke,kin zama jinin jikina kece bugun zuciyata,kecw rayuwar da farin cikin Maleek Bilyam Sufrak Bilhas,menai maki da zafi haka?gayamin yanzu na hukunta kaina kona samu ki sassautamin"
Tunda ya fara magana take girgiza kanta tare da ƙara sautin kukanta,bata taɓa tunanin zai buɗe baki yay mata magana ba sabida ganin matsayin da yake a yanzu,sai gashi yanzu ya zage yana gaya mata halin daya shiga dalilinta,shin yanzu ita mene za tace masa?yadda yake sakar mata numfashi a cikin kunnanta tare da murza tafin hannunta,hakan yasa ta kasa daure,sabida ji take tamkar ana watsa mata wani abu a cikin jikinta,ga wata wutar sonsa da take ƙara yawa cikin zuciyarta,runtsa idanu tayi da ƙara sabida soft lips ɗinsa daya sauka a cikin kunnanta haɗe da danshin silava ɗinsa.
ji tayi mararta ta ƙulle ga wani abu dake mata ƙaiƙayi a saman red nipples ɗinta
ba zata iya ba,ba zata iya jure wannan abun ba,hakan tasa ta fashe da kuka tare da cure jikinta waje guda.
a hankali ya ware idanunsa daya gama rinewa tare da janye bakinsa dake kunnanta,a hankali yaji tsigar jikinsa na tashi zazzabin dake jikinsa na ƙaruwa.
ƙara matsawa yay kusa da ita tare da sanya dukkan hannunsa ya ɗagota zuwa kan cinyarsa,henna ɗin manne a yatsun hannunta ya zubawa idanu.
numfashi ya sauke a hankali ya ɗura kansa a shoulder ɗinta tare da zagaye hannayensa a waist ɗinta.
saukar wani abu mai zafi a bayanta ne ya sanya tayi sauri janye jikinta daga nasa tare da kallonsa.
hawayen data gani a saman fuskarta ya sanya tai saurin sanya tafin hannunta ta fara share masa hawayen cikin kuka tace.
"Na soka a cikin zuciyata tun bansan wani abu wai shi So ba,na rayu da soyayyarka,kullum kaina abin shirta,kuma kullum abu mafi soyuwa da nake gani cikin bacci na,babban jin daɗin na rayuwa dakai a matsayin masoyi ba tare da nasan kaine abinda nake so kuma nake ƙauna ba,tunda ce banga fuskar da nake gani amafarkina ba,amma hakan basa naƙi amincewa dakai ba,na rayuwa dakai a lkcn da kaina yake a juya,sannan nabar wannan masarautar a lkcn da nasamu kaina,nabar masarautar cikin jimami da kuma kewan wani abu wanda bansan ko menene ba,ashe kaine abinda na bari,na rasa farin ciki jin daɗi ƙwanciyar hankali,kullum zuciyata cikin begenka take,na kasa ci da sha sabida rashinka kusa dani,ina roƙon Allah ya bai yanamin kai koda a matsayin aljanine na yarda na amince zan zauna da kai a hakan,shin tayaya kake tunanin zan rabu dakai a yanzu bayan kasan kaine muradi da fatan Zarina,dan Allah ka daina kuka,zubar hawayenka tamkar zubar dalmane a cikin zuciyata,shin tayaya kake tunanin za'a iya raba uwa da ɗanta?tayaya kake tunanin za'a hana ɗan adam shaƙar iska?tayaya kake tunanin zuciyar Zarina zata daina sonka bai gane rayuwarta ina sonka ina sonka a kullum a kuma koda yaushe har ƙarshen rayuwata"
Wata hawiyar runguma yay mata rai saida tayi ƙara,sosai ya matseta a faffaɗan ƙirjinsa yana sauke ajjiyar zuciyar.
wasu hawayenne suka ƙara fita daga cikin idanunsa.
bakinsa ya tura cikin kunnanta tare da sauke wani zazzafan numfashin,cikin muryar raɗa yace.
"kibarni nai kuka en matana,kuka ya zamemin dole,kece ta farko da kika fara ganin hawayen Maleek,kisan mene yasa?" girgiza kai tayi tana ƙara matse jikinta sabida abinda yake mata a kunne.
murmushi ya saki a lkc na farko yace.
"soyayyarki tayimin yawa,gaki dai ƴar ƙwaila amma kin samu nasarar ƙwace zuciyata,wannan kukan da kika inayi na jin daɗi da farin cikin zuciyata ta samu abokiyar rayuwarta ne,yau zan kasance dake a cikin jikina zanji ɗumin jikinki"
Ɗan waro idanu tayi dan batai tunanin abinda zaice kenan ba,shuru sukai gaba ɗaya suna sauraran bugun zuciyoyinsu dake bugawa a tare.
Murmushi Meyrah ta sauke a zuciyarta tana jinjina ƙarfin soyayyar da sukewa junansu,raba wannan masoya biyun ba ƙarami abu bane,Allah kaɗai yasan son da sukewa junansu.
hannu tasa ta ɗan bubbuga dressing mirrow, a tare suka ɗago kansu,wata kunyace ta kama Zarina cikin sauri ta janye jikinta daga na Sarki Maleek tare da sunkuyar da kanta.
Ganin Meyrah yasa Sarki Maleek haɗe ransa tare da kafeta da idanu tana jiran yaji mene ya kawota wajansa at this time.
kanta ta sunkuyar ƙasa domin ba zata jure ganin ƙwayar idanunsa ba,baki na rawa tace.
"Allah ya ƙara maka lpa da nisan ƙwana Abbu yace kazo kaida Fulani"
bata jira abinda zaice ba tayi saurin barin ɗakin,domin sam ba zata jure ganin abinda ya kewa Zarina ba sai shisshinata yake shiko kunyartama ba yayi.
tana fita Zarina ta sauke ajjiyar zuciya tare da janye jikinta ta miƙe tsaye.
shuru yay mata sai kallonta kawai da yake tamkar zai cinyeta,ganin bashi da niyar tashi yasa ta gyara murya tace.
"Allah ya taimaki sarki Allah ya ƙarawa Sarki yawan rai ya kamata ka amsa kira"
maimakon yay magana sai mirginawa da