Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
cikin ɗakin mai duhun gaske ga zafi.
Tana ƙwance tamkar mara rai sai fidda numfashi take,rabonta da cin abinci mai ƙyau kuma isshesshe harta manta.
"kee! Maza fice"ya faɗa yana saurin fice sabida zafin daya fara damunsa.
Jan numfashi tayi tare da rarafawa ta fito daga cikin ɗakin,wata ajjiyar zuciya ta sauke tare da zubewa a wajan sabida wata daddaɗar iska data ratsata.
"maza tashi kiyi naki waje"cewar Sarkin tsakar gida.
Kulsum kam jiki a bace ta miƙe gabq ɗaya jikinta rawa yake sabida tsananin yunwa da kuma ƙishirwa mai yawa.
Tana zuwa sashin dazai sa data da ɗakinsu ta yanke jiki ta faɗi tare da soma ƙwarara amai tamkar wacce kayan cikinta zai fito.
Zarina da fitowarta kenan neman bushasshen zoɓo domin yau lemon zoɓo suke sha'awa ta hangi kulsum ƙwance a wajan aman da tayi.
Da ɗan sauri ta ƙarsa wajanta duk da itama bawai lafiyanne da ita ba.
Tana zuwa ta kamota tare da sona jera mata sannu,idanunta cike da ƙwalla,haka ta taimaka mata zuwa ɗaki tare da haɗa mata ruwan wanka,bayan tayi wankan ta shirya ta kalleta tace.
"kina azumi ne"ta ƙarasa maganar da murya irinta masu azumi.
Kai Kulsum ta ɗaga alamar.
"eh"jinjina kai Zarina tayi domin ita kaɗai ne tasan abinda yake damunta.
"Kulsum dan Allah kiya femin a kaina akai maki wannan cin mutuncin,wlh aci zarafin wani akaina gwara banzo duniyar ba"ta ƙare maganar hawaye na zubuwa daga cikin idanunta.
"ke Alkairi ce garemu Zarina,kiyi amfani da damarki domin ki taimaki jama'ar garin Bilhas,aƙwai mutanan da aka ƙwace masu filayansu Zarina aka siyarwa gwamnati,aƙwai iyayen da aka karɓe ƴar ƴar yansu aka aka sai dasu ga wata masarautar,kamar yadda nima aka ɗaukoni daga garinmu na KOGI aka kawoni"
Ambarta sunan garin KOGI da tayi ya sanya Zarina saurin dafe kanta daya shiga juya mata lkc guda,cikin siririyar muryarta tace.
"Ya salam,kogi?"
Ta tambaya tana runtsa idanunta wanda sukai mata jaa sabida ciwon da kanta yake mata.
"Kamar na taɓa jin sunan fa,amma bansan ina ba?"
Wani murmushin takaici Kulsum tayi,cikin tausayawa Zarinan tace.
"ba zaki iya tuna komai na rayuwanki ba,sai wanda Allah ya nufeki sabida sun riga sun hargitsa tunaninki gaba ɗaya,kada kisare domin wannan zoɓen naki ya ɗauke da hanyar da za'a kuɓutar da masarautar bilhas"
Shuru Zarina tayi gaba ɗaya bata fahimtar Kulsum ta tafi tunanin inda ta taɓa jin sunan garin Kogi,ganin kanta na neman tarwatse ya sanya ta ɗauke tunanin daga ranta.
Domin bata fiye ajjiye ɓacin rai ba,tana da sauƙin kai tana kuma da saurin yafiya,amma tana da kafiya da kuma naci akan abinda ta sanya gabanta babu wanda ya isa ya sauya mata shi,ko kuma ya sanya tayi abinda ba tayi niya ba.
Miƙewa tayi ba tare data tanka kulsum ba tayi ficewarta daga ɗakin,ta koma sashin Mai babban ɗaki.
Tana zuwa ta samu Hadima Kaltume harta gama shirya kayan buɗe baki lkc kawai take jira.
Tana shiga ta nufi wani ɗaki inda yanzun a nan take ƙwana.
Direct bathroom ta nufa ta sakarwa kanta shower,ajjiyar zuciya ta shiga saukewa sabida sanyin ruwan daya gama ratsa jikinta.
Ƙirjinta tsurawa idanu ganin yadda tagwayenta suka ƙara girma nipples ɗinsu sunyi red,turo baki tayi tare da sanya hannu ta matsesu sosai,Ita sam Allah ya sani bata son wannan abun kunya suke mata,ko brazia bata sakawa sabida sunyi mata kaɗan.
Jin masallacin Bilhas na kira da alamun lkcn buɗe baki yayi.
Ya sanya ta ƙarasa wankan cikin sauri tare dayin brush ta ɗaura al'wala.
Handrayer ta ɗauka tare da junawa ta tsane ruwan kanta dashi.
Bayan ta gama ta ɗaura towel a ƙirjinta kana ta fito daga cikin bathroom ɗin.
Wata blue ɗin abaya ta sanya wacce take ɗauke da pech ɗin flowers masu ƙyau.
Wani pech ɗin vail ta ɗauka ta yane kanta dashi tare da ɗan fesa turare,ko lotion bata shafa ba.
Ta sanya flat shoe wanda Mai babban ɗaki ta bata jiya.
A hankali ta fito daga bedroom ɗin nata,direct wajan daining area ta nufa nan taga Mai babban ɗaki da kuma Kulsum sai Hadima Kaltume suna zaune saman kujera.
Sosai taji daɗin ganinsu sabida suna ɗeɓe mata kewa.
Kejera taja daga cikin jerin kujerun da sukaiwa daining ɗin ƙawanya,cikin ƙaramar muryarta mai cike da rauni tace.
"Ammi barka da shan ruwa"
"yawwa barka ɗiyata yaya kewa?"ta ƙare maganar tana sakin murmushi.
Turo baki Zarina tayi gaba hawayen da take ɓoyewa suka samu damar sakkowa daga cikin idanunta.
"eyee kewanne hadda kuka bayan kuma tijarar da kikai masa"Hadima Kaltume ta faɗa tana sakin dry.
"ohh wai kuka ne?"Mai babban ɗaki ta faɗa lkcn tana sanya yam balls wanda aka haɗashi da naman kaza.
"wai wane ake kewa hakan nifa duk ban gane ba?"Kulsum tayi mgnar tana miƙewa tsaye.
Dariya Hadima Kaltume tayi cike da zolaya tace.
"masoyin ƙwarai mana,kuma na gartaccen namiji mai baiwar ƙyau da Cikar zati,uwa uba ilimi daya gama ratasa jini da tsokar jikinsa,wlh ba kowa ke samun irinsu Captain Saifudeen yay wasa da damarsu ba"Hadima kaltume ta ƙare maganar tana wurgawa Zarina harara tare da gyatsina hanci gefe guda alamar dai haka🤥.
"wai fa irin jan ajin nan na ƙwailaye take masa but am sure komai nisa zata gane Allah ɗaya ne"cewar mai Babban ɗaki.
Kuka Zarina ta fashe dashi tare da faɗawa saman carpet ta fara birgima kamar ƙaramar yarinya,ko da yake ai ita ɗince domin haryan zun bata huce 17years ba.
Lil prince dake bakin ƙofa tun ɗazu yana kuma jin abinda suke faɗi,yay saurin ƙarasuwa cikin babban parlour'n fuska a haɗe ya kalli su Hadima Kaltume da kuma Kuyanga Kulsum yace.
"kai dalla ku ficewa mutane tun bansa anyi maku ɗan banzan doka ba"
Da sauri suka fice daga sashin jikinsu ma rawa sabida wani mugun tsoransa suke musamman Kulsum.
Wajanta ya ƙarasu tare da durƙu sawa daf da ita yace.
"Maza miƙe ki share hawayenki,kada ki damu da abinda suke faɗe ninan zan zama gatanki koda yaushe ko mene kike ɓuƙata ki gayamin"
Ajjiyar zuciya ta soma saukewa a jajjire,kallonta yay yace.
"kinci abinci?"girgiza kai alamar "a'a"
Wajan daining ɗin ya ƙarasa tare taɓe baki yace.
"barka da hutawa mai babban ɗaki ya azumin?"
"Allhmdllah"tace a taƙaice.
Bai ƙara kallon inda take ba ya ƙwashi abin buɗe bakin da Hadima batul tayi a plate tare da gorar ruwa mai sanyi.
Yana zuwa ya sanya hannu ya miƙar da ita tsaye,yana jin yadda take ƙoƙarin ƙwace jikinta tana zabewa.
Cije laɓɓansa yay yana jin yadda wutar sonta sa kuma sha'awarta suna ƙara ƙaruwa fiye da koda yaushe anya bazai aikata abinda Yazeed yace ba kuwa?kai "no"banyi hakan zan watsar da damata,domin na fahimta bata ƙaunar ZINA ko makamancin hakan dalilin hakan ta tsani Saifu tsana mai yawan gaske,zanci gama da kula da ita daga nan harna samu damar da zan mallaketa matsayin matar aure,duk ina da ƙarfin ikon da zan aureta ko tana so ko bata so".
Ya ƙare maganar zucin yana sanya mata soyayyiyar yam a baki,guda ɗaya taci kana tasha ruwa mai yawa,tana gama sha ta miƙe tsaye tare da cewa.
"kana ciwo bacci zanyi"
Idanu ya zuba mata yana jin kamar yaje ya rungometa yay kissing pink lips ɗinta koya samu sauƙi.
A zahiri kuma ya sakar mata murmushi tare da faɗin.
"ok dear i love you"
"thanks"tace a taƙaice.
Girgiza kai yay yace.
"you can say you love me too? Mene yasa ba zakice kina sona ba,bayan nasan cewa aƙwai soyayyata a zuciyarki,matan hausawa ba sam baku iya soyayya ba,da yawanku idan ance maku i love you ba kusan cewa i love you too,wlh na ƙarace maki i love you kika cemin wani thanks saina fasa baki"ya ƙare maganar rai ɓace kana ya fice daga cikin sashin gaba ɗaya.
Da gudu ta faɗa jikin Mai babban ɗaki tana sakin kuka.
"uhm duniya kenan ai,kinƙi mai lallaɓaki yanzun ai zaki so mai takuraki kuma bana da ikon magana,kin ni bani sandana naje ɗaki na gabatar da salla"
"Ammi zuciyana ciwo bana jin daɗi rayuwar nan,wai wacece ni?nina gaji babu wanda zanji daɗi wajansa,kema yanzun kina fushi dani"ta ƙare maganar tana sakin wani kukan.
Kanta Mai babban ɗaki ta shafa tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi.
"Zarina"
Wannan shine karon farko da Mai babban ɗaki ta kira real name ɗinta,lafewa tayi jikinta tana sauke numfashi.
"bansan yaya SAIFUDEEN yake a fuska ba,amma nasan cewa girman addininsa da kuma tsoran Allah da yake dashi bazai taɓa sawa ya aikata abinda kike zarginsa dashi ba,za kiji kunya kuma zaki dana sanin lkc'n da kika fahimci wanene shi ɗin,dake dashi babu wanda na sani,ko duka ƙaddara ne ya haɗani daku,kamar yadda ƙaddara ke bibiyana haka kuma ke bibiyarki,kici gaba da addu'a domin ki samu damar tuna asalinki,kici gaba da addu'a domin neman zaɓin ubangiji,kici gaba da addu'a domin neman kariya daga sharrin wannan masarautar"
Kai Zarina ta ɗaga tare da zubawa Mai babban ɗaki idanu,a ranta tace wata kam duk wani abunda ake aikataw a wannan masarautar tana sane dashi,tana jin tausayin kanta amma a wannan lkc'n tafi tausayin Mai babban ɗakin fiye da kanta.
Hawayen fuskarta ta goge tare da kama Mai babban ɗaki ta kaita ɗaki tare da shimfiɗa mata dadduma domin sallah.
Itama ɗaki bedroom ɗinta ta huce,tana zuwa ta shimfiɗa dadduma tare da gabatar sa salla,tana gamawa ta fara tilawan alkur'ani saida tayi wajan izu uku kana ta gabatar da sallar issha'i da kuma ashan sannan ta cire kayan jikinta tare da sanya wata farar rigar bacci,bed ta faɗa tare dajan pillow ta rumgometa tana jin wani ƙamshi na musamman na dukam hancinta.
Tabbas wannan ƙamshin sane shi kaɗai ta sani mai irin wannan parfume ɗin.
Sai a lkc'n ta tuna rigar tana ɗaya daga cikin kayan daya siya mata.
Lumshe idanu ta ƙarayi tana jin wani irin abu na musamman na ratsa zuciyarta da kuma gangar jikinsa,amma sakalcinta ya hana ta fahimci a salin dake ranta.
A haka bacci yay gaba da ita.
*_kogi_*
Sannu a hankali yake taka steps ɗin benen jirgin cike da kuzari da kuma jarumta,yana zuwa step ɗin ƙarshe ya ware manyan gajiyayyun idanunsa da suke a lumshe.
Babban filin tashi da jirgin ya zubawa idanu kamar mai son ganin wani abu.
Yana nan tsaye wani mutum yazu cikin sauri ya miƙa mata wani ɗan ƙaramin abu kana ya juya da azamarsa.
Abin ya zure cikin aljihun wandonsa kana ya ƙarasa sauka daga cikin kan step ɗin.
Ɗan ƙaramin tsaki yaja ALLAH ya gani bai son jira shiyasa yace Abbunsa ya bashi address na gidan da yake ciki yaƙi.
Ya san cewa Abbun nasa bashi da wani gida a nan garin,hasalima mamakin yake da yace yana KOGI yake,basu da wani ƴan uwa a kogi,a cameroon suke kamar yadda shima aka ɗaukosa daga cameroon zuwa illori sabida su ƙwantar da tarzuma,daga illorin kuma ya samu sanarwar an sauya masa aiki zuwa garin bilhas,kuma cikin masarautar bilhas ɗinma gaba ɗaya domin kula da lafiyan Mai bartaba.
A karo na biyu ya ƙara jan wani tsakin musamman ƴan mantan da yaga sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa ɗanye.
Agogon dake manne saman tsintsiyar hannunsa ya ɗan shafa kasan cewar agogon apple ne.
Nan take ya kawo haske,ɗan juya idanunsa yay ganin har sha biyu na dare ya gota.
Da sauri wani mutum ya ƙarasu wajansa tare da duƙawa yace.
"Captain Saifudeen Bilyan hakane?"
Jinjina kai kawai Saifu yay ba tare daya tankasa ba.
Jakar hannunsa ya karɓa tare da faɗin.
"am Kamis yahya ur father's drever les go"yana faɗin hakan yay gaba tare da buɗe boot ya sanya jakar Saifu ciki.
Taɓe baki Saifu yay tare da faɗin.
“Talkative”
Hannayensa ya tura cikin aljihun wandonsa kana ya mara masa baya cike da nutsuwa da kuma izza.
Cike da ladabi Kamis drever ya buɗewa Saifu side ɗin baya.
Sai a lkcn Saifu ya cire kai ya kallesa murya can ƙasa mai ɗan sauti yace.
"jaa jikinka,ni bana da hannu ne halan,ko kuma ni ɗin Sariki ne da motar ma sai an buɗe min"
Murmushi kawai Kamis yay cikin girmamawa yace.
"tuba nake"
Kafaɗa sabi ya ɗaga alamar ko a jikinsa.
A hankali ya zura jikinsa cikin motar kana ya zauna tare da ɗan kishin giɗewa.
Hannunsa ya santa saitin zuciyarsa da har yanzun bai daina har bawa ba,ya ɗan murya tare da dannewa.
Lumshe sleepyn eyes ɗinsa yay tare da lumshe idanunsa cikin zuciyarsa yace.
"rayuwa kenan aduk lkc'n da kaso kare kanka daga wani abun a kuma dai² lkc'nne wani abun ke ƙara shigowa rayuwanka ba tare daka shirya hakan ba,bai san daɗin soyayyar ba,haka kuma bai san jin daɗi ba,yasha wahala sosai a rayuwarka,ka sancewarsa mutum mai ƙarfin guiwa shine ya sanya baya taɓa sarewa da daga rahamar ubangiji,ya sani kuma ya yarda hakan akan cewa komai lkcne,tun yana ƙwana saman ciyawa yaci ganye da ruwan ƙorama,daga nan ya dawo ƙwanciya saman simiti yasha kuma ruwan rijiya,rayuwa na tafiya kuma ƙaddararsa na ƙara sauyawa,daga nan ya koma ƙwanciya saman tabarma yasha ruwan buhal,haka nan ya koma ƙwanciya saman katifa yasha ruwan fanfo,yau shine yakai wani mataki da zai ƙwana saman gado kuma yasha dukkan kalan ruwan daya keso da kuɗinsa da gominsa saɓanin da"
Wani murmushin takaici yay a lkcn baya da aka goranta masa wai bashi da mahaifi shi ɗin shege ne....
*Afuwa da rashin posting jiya,kusam week ɗin biki ne ga kuma makaranta,so ina neman al'farmar zanna tsallaken ƙwana guda,idan nai posting yau sai jibi,nima ba'a san raina ba amma babu yadda zanyi sabida exam pls bear with me*
_THE NEW EMIR LITTAFIN KUƊI AKAN 200 NAIRA,MAI BUƘATAR VIP ZAI BADA 500 DOMIN SAMUN LITTAFAN DANA RUBUTA NA KUƊI,ZA'A TURO DA ASUSUNA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK,SAI SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08119237616 BABBAN ALBISHIR AƘWAI SABON BOOK ƊINA DA ZAI FITA BAYAN SALLA MAI TAKEN *UNCLE NE..!!* SALONSA NADA BANNE KAMAR YADDA KUKAJI SUNANSA SHIMA PAID BOOK NE A SHIRYA PAYMENT BAYAN RAMADAN_
*NIMCYLUV 🤏🏼🔥*
*45-46*
NIGHT POTING 🌚
Kallamar shege da aka haɗashi dashi ba ƙaramin dakula masa lissafi akai ba,amma kasan cewarsa mutum mara sanya damuwa a zuciya ya tattara kallmar yay watsi da ita,sabida yasan koda shi shegene aiba shine ya haddasa faruwar hakan ba.
Bare yay imani da Allah Abbunsa bazai taɓa aikata wani abu ga wata ƴar mace ba har ace ta samu ciki da haifesa.
Ƙara taune lips ɗinsa yay yana jin kamar ƴanzu abin ke faruwa.
Jin drever'n ya tsaya da dreving ya sanyashi buɗe gajiyayyun idanunsa wanda sukai masa nauyi.
Idanunsa ya zubawa gidan sabida yadda ginin gidan ya birgesa.
Jin drever ya buɗe masa ƙofane ya sanyashi ƙwaɓe fuska kana cikin nutsuwa ya zuro da ƙyawawan ƙafafunsa masu ƙyau.
Hannunsa ya sanya duka cikin aljihun wandonsa kana ya ɗan jin gina da motar yaci gaba da ƙarewar gidan kallo.
Kamis drever bayan ya buɗewa Saifu ƙofa ya zagaya wajan boot tare da ɗauko jakar kayansa.
Wayarsa ya ɗauko jikin Aljihu kana ya kira wata number.
Daga can ɓangaren akai picking call ɗin cikin murya mai daɗi akace.
"tun kafin kace komai naji ƙamshin Sweethert kusa dakai,baza kawomin shi"yana faɗin hakan ya katse wayar.
Dry Kamis yay tare da jinjina soyayyar dake tsakanin Alhji Bilyamin da yaronsa Saifudeen.
Koda yake ba abin mamaki bane,domin ƙarfin soyayar uba da ɗa tafi haka.
Jakar kayan Saifu ya ɗauka kana yay gaba yana faɗin.
"Ƙaramin Alhji biyoni nai maka iso"taɓe baki Saifu yay tare da ɗauke kansa gefe guda.
Cikin nutsuwa da kamala yake bin bayan Kamis har suka isa wani babban parlour dake gidan.
Sosai parlour'n ya birgesa ba kajin komai sai ƙarar Ac'n dake bada iska cikin parlour'n.
Parlour'n yana da part kusan guda huɗu da dukkan alamu ko wanne na aiki sabida yanayin wani ɗan duhun haske kaɗan dake fitowa ta cikinsa,guda ɗaya ne a rufe hakan na nuna shiɗin emty ne.
Wani part yabi a hankali ganin Kamis yabi hanyar yana zuwa bakin ƙofa yaga harya kai jakar ya fito,sai da safe yay masa kana yay hanyar ficewa daga cikin gidan baki ɗaya.
Hannunsa ya ɗura bisa handle ɗin ƙofar kana ya ɗan tura a hankali.
Yana shiga ya jingina da jikin ƙofar tare da zubawa Abbunsa nasa dake zaune bisa kan duguwar sofa yana shan coffee idanu.
Ganin Abbun nasa ya sanya yaji zuciyarsa tayi masa sanyi,raunin dake ɓoyewa ya bayyana a fili sabida idanunsa daya sauya kala tare da ɗan janye kaɗan.
A hankali Abbu ya ajjiye glass cup ɗin hannunsa bisa senter table take gabansa,ajjiyar da yaji ana saukewa da kuma yanayin kallon da yaji ana binsa dashi ya tabbatar masa cewa sanyin idaniyarsa ya ƙarasu gareshi.
Murmushi yay mai ɗan sauti dan yashan halin Saifu sam ko kaɗan bai gajiya da kallonsa tun yana ƙarami haka yake.
Shi yar mamaki yake idan yaga yana binsa da kallon ƙurilla sai yaga kamar wani abune a jikinsa.
Kansa ya ɗaga tare da sauke ganinsa bisa ƙyaƙƙyawar fuskar ɗan nasa,shima ƙuri yay masa da idanu ganin zallar damuwa da rauni sun bai yana saman fuskar Saifu'n.
Sai yanzu yasan dalilinsa nason zuwa yaga gansa,ya tabbar yaje gejin da bazai iya danne damuwarsa ba,haka kuma baison wani yaga rauninsa idan ba shi ɗin daya saba gani ba.
Ɗan juya masa idanunsa yay tare da ware hannayensa alamar yazu garesa.
Da sauri Saifu ya zare picap ɗin kasan tare da cilli da ita kana ya ƙarasa wajan Abbun nasa da raguwar kuzarinsa.
Yana zuwa ya faɗa jikin Abbu tare da sakin wata nauyayiyar ajjiyar zuciya,sai a lkcn hawayen da suke ƙwance cikin idanunsa suka samu damar silaluwa daga cikin idanunsa.
Shuru Abbu yay yana sauraron ajjiyar zuciyar da Saifu yake saukewa ajajjere,a hankali ya sanya hannunsa cikin ƙwantacciyar sumar kansa ya soma shafa masa ita tare da hargisata haɗi da ɗan bubbuga bayansa.
Wajan 10minutes suna haka jin ya ɗan lafa da sauke ajjiyar zuciyar ya sanya Abbu faɗin.
"bata amince ba halan?"ya faɗa yana ƙara shigar da Saifu cikin jikimsa sabida jikinsa da yaji ya saki.
A hankali Saifu ya ɗaga jajayen idanunsa tare da saukeso fuskar Abbu.
Yayinda shima Abbun shi yake kallo.
Runtsa idanunsa yay da ƙarfi yana yawon bakinsa nayi masa ɗaci,murya can ƙasa wacce iya Abbunne kaɗai zai iya jin abinda Saifu'n ke faɗa yace.
"Abbu zargina take"ya ƙare maganar yana pouting lips ɗinsa.
"zargi?to for what reason?"
Lumshe idanunsa Saifu yay yana jin maganar nayi masa nauyi a laɓɓansa,cikin dakiya da jarumta ya riƙe hannun Abbun tare da faɗin.
"Abbu waini ɗan iska ne fa tace,wallahi Abbu ni babu macen data taɓa birgeni bare nayi tunanin aikata wani Abun,akanta kawai na saɓawa Ubangina wanda yanzu haka na kejin kunyarsa matuƙa"
"mene ka aikata na saɓun Ubangijin Sweetheart?"
Turo baki Saifu yay tare daya mutsa fuska,kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Abbuna i kissed her kuma na rungometa bansa menesa na aikata hakan ba,amma Abbuna ina sonta i want to marry her"ya ƙare maganar yana ƙwantar da kansa bisa ƙirjin Mahaifin nasa.
Murmushi kawai Abbu