Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
bacci yatsanta a hannu sai sauke ajjiyar zuciya take,idanu ya ƙura mata yana tuna irin maganganun ta faɗa masa ɗazun,lumshe idanunsa yayi tare da lafewa jikin luntsumemiyar kujerar da yake kai.
Saukar wata ƙarar bindiga a kununwata ya sanya ta farka daga baccin wahalan daya ɗauketa,a firgice ta faɗa kansa sbd tsananin firgicin data shiga,duk da yana cikin damuwa bai hana shi sakin murmushi ba,wannan ƙaran bidigar kuma ya tabbatar masa da cewa shaidar anga watan RAMADANNE kowa ya ɗauki niya,lumshe idanu yayi yana jin yadda ta lafe jikinsa tana sauke numfashi..
Saifu na fitowa daga ɗakin Zarina bayan hasken dake fita ta cikin daimond ring ɗinta,a bakin ƙofa ya tsaya tare dayin wata girgiza saiga wata iska mai ƙarfi ta bayyana cikin abinda bai huce ƙiftawar idanu ba,halittarsa ta rikiɗe ta koma wani zabgegen baƙin dodo👹mara fasali wara kururuwa yayi saika wani hayaƙi na fita ta cikin bakinsa,a hankali jikinsa ya fara zagwanyewa yana ƙasa harya koma tulin wani baƙin yaƙi,wata ƙara aka saki sai kuma yahaƙin yayi sama,a dai² wannan lkc'n kuma Saifudeen ya dawo daga masallaci.
_Masu fitarmin da book waje kuci gaba kada ko fasa domin bazan iya yi da baki ba,ni wlh so nake ku fitarma😂_
*THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE,KAYI PAYMENT DOMIN KARANTAWA CIKIN SAUƘI, 200 FOR NRML GRP, 500 FOR VIP WANDA ZASU SAMU PAID BOOK ƊINA DA NAYI GABA ƊAYA, 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK,SAI Evidence of payment 08119237616*
By
*NIMCYLUV*
*37-38*
#Fasting
Ƙara lumshe idanunsa yayi tare da taune red soft lips ɗinsa,cikin wani yanayi fara fassaruwa a zuciya ya sanya hannu ya shafi sumai kansa,ba tare daya kulata ba cikin zazzaƙar muryarsa mai dadi da amo yace.
"Allahamdulillahi Rabil Alamin,Allah kasa damu da alkairan da suke cikin wannan watan na RAMADAN wata na 9 acikin jerin watannin addinin mulunci,Allah kasanya mu ribaci dare mai matuwar muhimmanci,daren da kowa ke burin da muradin ganinsa,dare mai falala da tarin albarkatu,wato daren LAILATUL ƘAQAR,Allah ya bamu ikon aikata dai² da kuma barin abinda yake ba dai² ba,Ubangiji ka bamu lafiyan yin ibada cikin sauƙi da ƙwanciyar hankali"ya ƙare maganar yana haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo👏🏻.
Tsoron daya gama cika mata zuciya yasanya bata gama tantance cikin wanda ta faɗa ba,wani sihirhintaccen sanyine mai ratsa zuciya da sanya mutum sauƙi ya soma kawowa hancinsata ziyara,lumshe idanunta tayi tare da ƙara tura kanta cikin faffaɗan ƙirjinsa wanda yake abuɗe,har yaunzun jikinta bebar tsoma ba,tunaninta kawai gari babu lafiya,ƙara lumshe idanunta tayi tana jin wata nutsuwa na ƙara ziyartar zuciyarta,turo baki gaba tayi cikin rashin sa'a laɓɓanta suka mannasu saman red nipples ɗinta.
Ɗan rolling eyes ball ɗinsa yay cikin sauri ya sanya hannu ya ɗan daki forehead ɗinsa dake juya masa,wani irin baƙon yanayi ne ya saukar masa a jiki,wanda ya haddawa sassan jikinsa kasala ya soma jinsa wani very weak,ware manyan fitinannun idanunsa yay wanda suka ɗauke da wani baƙon abu a cikinsu ya saukeso bisa kansa,taɓe baki yay tare da sanya hannayensa bisa kafaɗarta,ya ɗan jijjiga murya can ƙasa mai taushi yace.
"kee!halan baki da hankali ko,ke dolenki sai kin nuna baki da kunya,kinzo kin wani faɗominka salon iskanci,ohh lalatani kikesonyi halan..?"ya ƙare maganar cikin ƙasa da murya tare da sakar mata wani zazzafan huci saman innocent face ɗinta.
Da ɗan sauri da buɗe idanunta lkcn da kamilalliyar muryarsa ta sauka cikin kunanta,cike da tsoro ta jefa idanunta cikin nasa,shima kallonta yake tare daya mutsa fuskarsa tamkar wanda yaga kashi,ƙoƙarin zame jikinta tayi daga nasa amma ta kasa sabida yadda ya riƙe mata shoulder ɗinta,matsu da fuskarsa yay daf da tata kana ya zame bakinsa ya ɗura bisa kunanta,cikin ƙasa da murya mai kama da raɗa yace.
"tabbas bazanyi ƙasa a quiwa wajan karairaya jikinki ba, a duk sanda kika ƙara faɗomin ka,wannan ƙwalƙwalan idanun mai kama da idanun a gwagwa saina ƙwaƙwuleshi idan ya sake kallona"ya ƙarasa maganar lkcn da yake sakinta daga jikinsa ta faɗi ƙasa,direct bedroom ɗinsa ya nufa,yana dab da shigewa ya tsaya cak tare da faɗin.
"ohh ya maza tashi ki haɗamin abin sahur,dan naga ke ƙwailace har yanzun baki gama sanin mene Azumin ba"yana faɗin hakan ya shige cikin bedroom ɗinsa.
Kasa cewa komai tayi sabida wani baƙin ciki da takaici daya ziyarci zuciyarta,wata kam shi harya manta abinda yayi mata ɗazun,har yake faɗin ƙada ta ƙara faɗo masa ka,ƙwaɓe fuska tayi cike da tsanarsa tace.
"Kumi ni ba ƙwaila bace yasin ko ɗaya bazansha ba na rantse"ta ƙare maganar tana murguɗa masa baki😏"mutum sai sheƙan iyayin masifa ai wallahi tunda na fahimci halinka na tsaneka tunda baka da aiki sai lalata ƴar ƴan mutane,ko sonka zaimin illah na hqr dakai ban sonka bazan taɓa sonka ba,i don love you anymore"ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan,ganin dare yana jaa,kuma ba tayi sallan issha'i ba bacci yay gaba da ita,ya sanya ta miƙe tare da faɗawa toilet ɗin dake manne jikin parlour ta ɗaura al'wala,da sassarfa ta fito daga toilet ta shim fiɗa dadduma,kana ta shiga bedroom ɗinta ta ɗauki wani ma dai² cin hijab ta ɗura saman abayar jikinta.
Bayan ta sallame salla'n ne taji an fara kiran salla'n farko ya sanya ta faɗa kicthen a tsora ce,domin bata son wani abu ya ƙara shiga tsakaninsu,tsayawa tayi ta fara tunanin abinda zatai mai ɗan sauƙi, Jallop ɗin couscous tayi masa wanda yaji kayan lambu da manya-manyan kifi marasa ƙaya,bayan ta kammala ta haɗa masa coffee,jiki a sanyaye ta ɗauko na'a-na'a da suger ta soma haɗa masa Vajin mahito,bayan ta kammalawa komai ta nemi wani plate ta zuba masa couscous ɗin a ciki,kana ta ɗauki flast ɗin data zuba coffee tayi waje a nan saman ƙaramin table ta shirya masa,kana ta ɗauki glass cup ɗin data zuba masa Vajin mahito shima taje takai masa,nata abin sahur ɗin itama ta ɗauka tare da shigewa bedroom ɗinta,tana zuwa ta faɗa saman bed tana sauke numfashi,bata daɗe ba bacci yayi gaba da ita (ashe yau aƙwai ɗore😂).
Saifu na shiga bedroom ɗinsa ya faɗa cikin bathroom tare da haɗa ruwan zafi jin yanayin garin ya ɗan sauya,ga kuma ƙuncin da zuciyarsa ke masa,har yanzun yana jin ɗaci a cikin zuciyarsa,runtsa idanunsa yayi tare da shigewa cikin jakuzzie ɗin yana jin kamar yanzun ne take faɗa masa wannan kalaman,wai zai lalata,ƴar ficiciya da ita mene zai ɗauka jikinta,bata san cewa mata basa gabansa ba,ko wacce mace kallon namiji yake mata,balle ƙwaila irinta me take dashi mezai ɗauka wajansa,cikin jin zafin kalamanta ya ƙare shigewa cikin jakuzzie'n yana jin yadda ruwan zafin ke ratsa masa cikin jikinsa,taune red soft lips ɗinsa,a lkcn kuma ƙyaƙƙyawar fuskarta ta soma yi masa gizau cikin idanunsa wanda suke a rufe,ɗan ware laps ɗinsa yayi ruwan ya soma ratsa cikin jikinsa musamman mararsa dake masa ciwo,ganin fuskarta na neman dagula masa lissafi ya sanyashi buɗe fitinannun idanunsa ya mannasu saman gashin mararsa wanda suka jiƙo da ruwa sukai luff saman mararsa,ɗan taune leɓensa na ƙasa yayi yana jin wani iri a zuciyarsa,sai yaushe ne zai daina jin hakan?menene yasa take yawan yi masa ciwo?mene yasa take kumbura? Mene yasa bata...kasa ƙara faɗin abinda ke zuciyarsa yayi,sabida nauyin da maganar tayi masa,yana buƙatar mai bashi farin ciki kusansa,baki yasa ya datse teeths ɗinsa,cikin wata raunanniyar murya yace.
"nayi kewanka Abbuna ika buƙatarka ina son ganinka ƙwarai"ya ƙare maganar yana ficewa daga cikin jakuzzie'n a nutse ya ƙarasa gaban shower ya sakarwa kasan ruwa tare da ɗauraye fresh chocolate skin ɗinsa,brush yayi kana ya ɗaura al'wala,wani blue ɗin towel ya ɗaura a waist ɗinsa,kana ya juna handrayer ya shiga busar da sumar kansa,yana kammalawa ya fice daga bathroom ɗin,lumshe idanunsa yay yana jinsa wani fresh iska na shigarsa tako ina,a kasalance ya nufi wajan wardrupe ɗinsa,wani red ɗin three gauter ya ɗauka tare da sakawa jikinsa,kana ya ɗauni wata farar singlet ya sanya,sosai ƙananun ƙayan shan iskar suka amshi jikinsa,muɗaɗɗan surar jikinsa ta bayyana musamman damtsen hannunsa da suke rarraɓe sabida murɗewa,wayansan ya ɗauka mai ƙirar iphone 11,cikin nutsuwa ya sanyawa ƙafansa bedroom silppers kana ya fito parlour ganin lkci na neman ƙurewa,duk da faɗin Annabine na cewa a jinkirta sahur a gaggauta buɗe baki.
Wata lumtsumemiyar kujera ya nufa wacce take farcing da ƙaramin table ɗin data jera masa kayan Sahur ɗin,photon dake manne saman mamaken screen ɗin wayarsa ya zubawa idanu,lumshe idanunsa yay yana jin wani iri a zuciyarsa,cikin kasala ya buɗe idanunsa tare da lalubu number Abbunsa ya dan nata masa kira,ringing biyu Abbu ya ɗauki wayan,cikin nutsuwa haɗi da ƴar shagwaɓa SAIFUDEEN ya ware laɓɓansa tare da faɗin.
"Abbuna farka da shiguwa wata mai girma da falala"daga can ɓangaren abu ya nisa tare da ɗaukan apple ɗin dake gabansa ya sanya cikin bakinsa kana yace.
"Sweetheart barka dai ya kewata?,nima nayi rashinka kusa dani Yarona"ya faɗa lokacin da yake tauna apple ɗin dake bakinsa.
Shuru Saifu yay yana jin wani daɗi da nutsuwa na ratsa zuciyarsa,jin muryar Abbunnasa ya ɗauke masa kaso 90 na cikin damuwan dake cikinta,ƙara lafewa yay jikin kujerar tare da shafa lafaffan cikinsa,cikin ƙwantar da murya yace.
"Abbuna ina son ganinka pls kabarni nazu wajanka ko naji sanyi a raina pls Sweetheart"ya ƙare maganar yana langaɓar dakai gefe yana jin soyayyar mahaifin nasa na ratsa zuciyarsa da kuma sassan jikinsa.
"zani umara so nazu tafiya dakai amma ganin kana wani aikin na rabu dakai zuwa aikin hajji maje tare"
"ohh da gaske har Ramadan ya huce bazan ganka ba?wlh ban iya jurewa inada damuwa"ya ƙare maganar yana pouting lips ɗinsa"
Murmushi Abbu yay kana yace "ohh ni barni da iya abinda nace kada ka ƙaramin,zuwa 10 ga Ramadan zan turo jet ya ɗaukkomin kai zuwa Kogi"
"Thank you sweetheart,ya Mai ran ƙarfe ita har yanzu babu ranar dawowarta ne?"cewar Saifu ya ƙare maganar yana kurɓar Vajin mahito ɗin da Zarina ta haɗa masa,wani ɗan yaji-yaji da kuma sanyi ne ya ratsa cikin ƙirjinsa wanda ya haddasa masa lumshe idanunsa wanda bai shirya ba,sosai yaji daɗin Vajin mahito ɗin,sun ɗan jima suna shira da Abbu kafin ya tsinke kiran ya maida hankalinsa kan Sahur ɗinsa ganin lokacin na neman ƙurewa,ƙofar bedroom ɗinta ya zubawa idanun sabida jinta shuru da yayi,taɓe bakinsa tare da ɗaukn spoon ya soma cin couscous ɗin baifi rabi yaci ba,kana ya ɗauki coffee yasha sosai,yana kammalawa ya miƙe tare da nufar bedroom ɗinsa,direct wajan fridge ɗin ɗakin ya nufa,yana zuwa ya ɗauki fresh milk tare da ɓalle murfin ya manna saman laɓɓansa ya soma sha a hankali,saida yasha sosai kana ya ajjiye,ya ɗauki gorar ruwan swin yasha,bayan ya kammala ya ajjiye komai a muhallinsa,kana ya shige toilet ya wanke bakinsa yana fitowa ya ɗauki jallabiya fara tas ya sanya a jikinsa,kana ya ɗauki dadduma da casbawa ya sanya wayansa a charge kana ya fito daga bedroom ɗin,yana fitowa ana kiran assalatu,sosai yayi mamakin rashin ganinta a parlour'n,har zai fice sai kuma ya nufi bedroom ɗinta,ɗan waro manyan idanunsa yay ganinta ƙwance tsakiyar bedroom tana sharara bacci hankali ƙwance,dariyar dake manne cikin bakinsa ce ta suɓuce ganin ko Sahur ba tayi ba,gadai abin sahur ɗin a ajjiye a ƙasa,cikin ɗan ɗaga murya ya shiga faɗin.
"kee! Kee! Kee!"ya faɗa yana ɗan buga ƙofar ɗakin.
Firgigit ta farka daga baccin daya ɗauketa,hannu tasa ta shiga murje idanunta tana mamakin yadda bacci yay gaba da ita ba tare data shirya ba,taɓe baki yay kafin yace.
"halan har anfara shan Azumin ko sahur ba'ai ba,ohh ya maza je sallah Lokaci yayi"ya faɗi hakan yana sauke numfashi sabida tsayin da mgnar tayi masa,yana faɗin hakan ya fice daga bedroom ɗin,tare da nufar Majid ɗin Masarautar bilhas.
Kasan cewar Wata ne mai girma da falala ya sanya aka cika masjid ɗin,sosai yay mamakin rashin ganin Mai martaba da kuma Lil prince,daga Waziri sai Tiraki da Sarkin fada sai kuma Fadawa da kuma hadimai,ganin lokacin na ƙurewa Liman baizo ba,ya sanya SAIFUDEEN shigewa gaba tare da ja masu sallah,cikin nutsuwa da kamala haɗi da jarumta ya soma rera ƙira'a a cikin suratul Anbiya'i,shuru cikin masallacin yayi baka jin komai sai sautin daddaɗar murya yana karatu cikin nutsuwa,yayinda yake fidda komai na makarijil huruf,bayan anyi sallama wani ya buƙaci SAIFUDEEN yayi masa ƙarin bayani akan muhimmanci bin jam'i,taƙwashe ƙafa SAIFUDEEN yayi tare da fuskantar jama'ar dake cike a masallacin kana ya soma bayani cikin harshen Larabci inda da yawan mutane sukai mamakin jin LARABCIN da yayi ya juye tamkar ba baushe ba,bayan ya gama sannan yayi bayani da hausa,da yawan mutane sunji daɗin bayanin da SAIFUDEEN haka suka shagala suna ɗaukan fatawa har rana yayi.
Mai martaba.
Surutu tai kawai yake shi ɗaya cikin wani ɗaki shi kaɗai,yana zaune tsirara yayinda ya tisa wata ƙwarya gaba yana juyawa,yana jin ana kiran salla'n asuba amma ko a jikinsa,cikin abinda baifi fitar numfashi ba.
Wani ihu mara daɗi da kuma amo ya fara cika ɗakin kafin da bisani wani baƙin dodo mara ƙyau da tsari ya bayyana.
A hankali dodo ya soma riɗewa yana komawa halittar mutane,wata ƙyaƙƙyawar matace ta bayyana,a hankali kuma tayi girgiza sai gashi ta koma siffar Zaitun😱babu ko banbanci.
Tana zaune kanta a ƙasa idanunta na zubar da ƙwallah bata ko motsi,wani jan abu ya zuba mata aka,kafin wani lokacin ta farayi masa aman kuɗi kamar hauka,saida kusan cika masa gabansa da kuɗi akan,ya ƙara zuba mata wani abu,da ƙarfi ta saki wata ƙara tare dayin wata girgiza,sai gashi ta ɓace ɓat.
Miƙewa yay tare da sanya kayansa kana ya ƙwashe kuɗin ya zuba cikin wata aƙwati,bayan ya kammala ya fito tare da sanya remote ya rufe ƙofar,a zaune ya tadda Fulani Kilishi ta idar da sallah,bai kulata ba bai gama idar da abinda yake ba.
Toilet ya faɗa tare da sakarwa kansa shower bayan ya kammala ya fito sanye da bathrupe a jikinsa,yana zuwa ya samu fulani Kilishi ƙwance saman bed ɗinsa,kallonsa tayi tare da faɗin.
"yanzun kenan ko Azumi ɗaya ba zakai ba?,saika gama cika umarnin boka?"
"kin faɗi amsar tambayarki ai,ina da wani babban aiki a ƙasa wannan shine dalilin"yana faɗin hakan yay ƙwanciyarsa tare dajan duvet ya rufe jikinsa,murmushi kawai tayi masa tare da ficewa daga ɗakin.
Lokacin gari har yayi haske tana fita ta haɗu da Waziri,Fuska ta saki tare da faɗin "A'a Waziri ne da sanyin safiya haka"fuska ya haɗe babu yabo babu fallasa yace "Eh fa nine,ina shi Mai martaban?"
"Baya jin daɗi yau babu zaman Fada"kafin yay magana Lil prince ya fito shigar kau ƙyau yaci Alƙyabba,Fulani kilishi ya kallah yace.
"Fulani barka da hantsi"dry tayi kaɗan tace "Yawwa barka,ga Waziri ka gaidashi mana"baice bata komai ba,yayi gaba ya barsu tsaye a wajan.
Waziri ma baice komai ba,ya juya tare da nufar ɓanga rensa,da kallo Kilishi ta bishi kana ta girgiza kai tayi flat ɗinta ciki da izza da taƙama.
Zarina.
Ƙwance take sai juyi take saman cinyar Mai babban ɗakin tana fidda numfashi irin na masu azumi,sosai Azumin ke bata wahala sabida rashin sahur da ba tayi ba.
Kanta Mai babban ɗaki ta shafa tare da faɗin "Ɗiyata afuwan an kusa buɗe baki sorry dear,kinyi sake na rashin sahur da baki ba"
Turo baki tayi gaba tare da ƙara shigewa jikin Mai babban ɗaki,wasu hawaye ne suka silalo ta idanunta,cikin muryar irinta masu Azumi tace.
"Ayya Ammi bacci ne fa,kuma mugunta ta hanashi tashi na,Allah Ammi sam bashi da..."kasa ƙarasa maganar tayi sabida daddaɗan ƙamshinsa daya daki hancinta,lumshe idanu tayi tana jin wani iri a ranta sam ko sau ɗaya bata ƙaunar ganinsa.
Yana tsaye sanye da wani red jeans,sai black t.shirt sai zabga ƙamshi yake,fuskarsa na fidda hasken musulunci,haiba da cikar zatinsa sun ƙara ƙaruwa fiye da da.
Pouting lips ɗinsa yayi,kana cikin nutsuwa ya ƙarasa cikin wata ƙyaƙƙyawar kujera irinta sarauta ya zauna akai,cikin tausasa harshe yace.
"Ammi barka da hutawa ya baƙo a baki"
"Allahamdulillah,baƙo kuma gashi saura few minutes mukai ɗaya"
Jinjina kai yayi tare da kallan inda take ƙwance ya taɓe baki yace.
"Ammi wannan fa kamar me shirin mutuwa?"
"Ƙaniyarka nace ƙaniyarka soja,ai laifin kane ƙaƙi tashinta a barci tayi sahur?ɗan waro manyan gajiyayyun idanunsa yay tare da nuna kansa da hannu alamar "Ni?".
Kafin yay magana Masallacin Bilhas sun ƙwala kiran salla'n magrib,da gudu ta miƙe daga jikin Mai babban ɗaki jikinta duka rawa yake,da sassarfa ta nufi wajan daining area inda Hadima Kaltume ta jere kayan buɗa baki,kafin ta ƙarasa jiri ya ƙwasheta ji kake timmmm.
_MASU FITAR DA BOOK WAJE ACI GABA DA GASHI WLH NA GODE,INA GANIN SABBIN MASU SIYAN BOOK ƊIN TA HAKAN😂_
_THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE KAYI PAYMENT AKAN 200 VIP KUMA 500 DOMIN SAMUN DUKA PAID BOOK ƊINA, SAIKA TURO KUƊIN TA ACCOUT NO 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S, UNION BANK, SHAIDAR BIYA 08119237616_
By
*NIMCYLUV*
THE NEW EMIR
*39-40*
#Fall in love
BONUS
YOU GUYS YOU DON PASS MY POWER WLH,ANY TIME A ƘARAN YAWAN FREE PAGE,OHHH THIS PAGE IS FOR YOU FANS SAHIHIYAR ƘAUNA NAKE MAKU,WANDA SUKAI PAYMENT KUMA DAN ALLAH KADA SU FITARMIN DA BOOK WANNAN KAWAI NA BAKU DAMA KUFITAR.
Ƙarar faɗuwata da yaji ya sanyashi juyawa a hankali tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa wanda suke a lumshe,Sosai ta bashi dry ganin yadda tayi ɗai² saman carpert sai fidda numfashi wahala take,juyawa tayi tare da sanya hannuta ta ɗura bisa lafaffan cikinta wanda ta kejinsa tamkar zai rabe gida biyu sabida tsananin yunwa da ƙishin dake damunta.
Danne dryar dake cinsa yay kana ya sanya hannu ya shafi ƙwantaccen gashin dake manne a ƙirjinsa sunyi lib-lib gwanin sha'awa.
Lumshe idanunsa yay kana a hankali ya zamo ƙasa tare da sanya tattausan hannunsa ya miƙar da Mai babban ɗaki tsaye kana ya ɗauki sandar da take using dashi wajan tafiya ya riƙe a hannunsa
"Ohhbyaa Ammi maza je buɗe baki domin samun falala"ya ƙare maganar yana zaunar da ita a kan kujerar dake