Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
you have a guest tun ɗazu ya kira wayanki baki picking ba,kiyi sauri ki fito haka"
Zarina ji tayi gabanta ya faɗi zare wayar tayi daga kunnanta tare dabin wayar da idanu,cikin rashin fahimtar zancen na Mom ta riƙe wayar tare da nufar hanyar babban parlour.
a zaune ta samesu suna kallon wani tafsir a tashar sunna t.v, tsawaya tayi ba tare da tayi magana ba,su duka kallonta suke musamman Mom ganin yadda ta rame idanunta suka ɗan fito sai fari data ƙarayi tamkar jini zai fito a jikinta.
kasa cewa komai Mom tayi saima miƙewa da tayi ta nufi part ɗinta,sam ba zata iya jure ganin halinda autarta ta take ciki ba,sosai take jin matsanancin tausayinta.
Sufyanne yay ƙoƙarin faɗin.
"yana parlour'n baƙi yana jiranki can"
lumshe idanunta tayi tare da saurin ɗauke kanta tace.
"yaya banso zuciyana ciwo please a barni bana da auran nan"
wani tausayinta yaji ya kamasa hakan tasa yace mata "sorry sweet sisi sabida nema maki mafita akai hakan am sure idan kikai auren zaki daina tunanin gaimu domin nika a film ban taɓa ganin mafarki yazo ma mutum a haka ba,kawai kiyi addu'a everting will be fine dear"
jikinta ta faɗa ta sakar masa kuka saida tayi mai isarta sannan ta zare jikinta ta daga nashi tare da goge idanuta ta nufi parlour'n,baki ɗauke da sallama wacce iya karta laɓɓanta a zaune ta sameshi akan sofa yasha shadda sai murmushi yake,kanta a sunkuye da kuma raguwar sanyin jikin daya rage mata ta nemi waje can nesa dashi ta zauna.
yanayinta ba ƙaramin birgesa yayi ba,cikin son janyota da shira yace.
"beauty ykk na sameki lpa?"
kaita jinjina masa tare da saurin tanne lips ɗinta sabida yadda taji zuciyarta nayi mata wani breating.
da ƙyar ta samu ta gai dashi haka ya dinga janta da surutu bata cewa komai sai uhmm ko ɗaga kai domin ko full face ɗinta ba,numfashi ya sauke tare da miƙewa tsaye yazu inda take zaune ɗan durƙoshewa yay gabanta tare da sanya duka hannayensa ya tallafo haɓarta.
lumshe idanu yay sabida tuzali da beauty full face ɗinta da yayi cikin sanyin murya yace.
"will you marry please beauty i love you so soo much..
*_Bilhas-*
Sarkin fada ne ya bawa Lil prince umarnin zama akan kujerar karagar,yana ƙoƙarin zama sukaji an fara tafi a bayansu gaba suka juyo da kallonsu zuwa ƙofa da sauri Mai martaba khalid ya miƙe tsaye domin wanda ya gani ba ƙaramin bashi mamaki yay ba,yana ƙyautata zonta wannan bashi bane sai dai kurwarsa.
Galadima ne yay dauriyar faɗin "wanene kai mene kakeso da zaka katsewa mutane daga abinda suke".
Murmushi daddijon mutumin yay kana yace.
"a lkcn da zalunci yaga gsky a kuma lkcn da duhu yaga haske a wannan lkcn gaba ɗaya tunanin mutum goshewa yake dan haka nai maka uzurin rashin ganene da kayi dan nasan ruɗewa ce ta sanya hakan,amma idan kai baka ganene niba ai nasan Khalid wazeee bilhas bazai taɓa manta fuskata ba haka ne?"
innalillahi gaba ɗaya jikin Mai martaba Khalid ne ya ɗauki rawa dan yana tabbacin zuwa yanzu tabbas mutumin da yake tunanine bawai kurwaraa bace.
murmushi Waziri yay mai cike da jin daɗi yace.
"bawan Allah meke tafe dakai har haka baka ganin ɗanin sarauta za'ai?"
gyara tsaiwarsa mutumin yay cikin fara'ar data zama jikinsa yace.
"wacce sarautar wanene ya gaji sarautar da za'a naɗashi?"
cikin rashin fahimta sarkin fada yace.
"Malam meke tafe dakai ne haka?"
kallon sarkin fada yayi yace.
"nazo kawo wanda ya dace da kujerar mulkin masarautar bilhas,gsky ce ta dawo yayinda ƙarya zata tattara kayanta tabar wannan wajan ba tare da an kureta ba,Nayjeb bashi shine ya dace daya zama sarki ba,domin a wannan karan wanda ya gaji sarauta gaba da bayanta shine yazo amsar abarsa"
ruɗani kenan gaba ɗaya wajan sun gama ruɗewa da zancen mutumin yayinda Lil prince ya zare idanunsa tare da faɗin.
"Malam banson surutun banza shin har aƙwai wanda ya dace ya gaji wannan kujerar bayanni?"
dry mutumin yayi yace
"ƙwarai da gaske ya fika komai hankali,nutsuwa,ilimi,tausayi,jinƙai,haiba,ƙwarjini ya dawo karɓar kujerar gadonsa a lkcn da bai son cewa shiɗin jinin sarauta bane,ya dawo a lkcm daya dace ya ɗauki fansaaa"
ya ƙare maganar yana kallon Mai martaba,cikin rashin fahimta Lil prince yace.
"shirmen banza idan har bai san ya haɗa jini da sarauta ba tayaya kuma zai zama sarkin bilhas bayan bashi da wata alaƙa da masarautar,shin wai akanwa kake magana?"
wani banzan kallo mutumin ya watsawa lil prince kana yace.
"Sweetheart come in"
tun kafin ya shigo wani sihirhitaccen ƙamshi mai tafiya da tunanin mutum ya cika cikin fadar yayinda wata ƙyaƙƙyawar iska ta fara kaɗawa,wata iskace mai ƙarfi ta fara kaɗawa yayinda garin yay dubu alamun tabbas hadarin dake ƙasane yake yunƙorin zubda ruwa.
sosai yanayin garin yay daɗi iskar kuma ta fara ratsa jikin mutuane zuwa cikin hancinsu,yayinda take tahowa da ƙamshin furannin dake masarautar.
a kasalance ya lumshe daradaran fitinannun idanunsa wanda suke farar tas har wani ruwa suke kawowa sabida haske,yanayin iskar yay dai² da yadda sumar ƙasan wuyansa dake kaɗawa a hankali,cikin nutsuwa haɗi isa da izzar data gama zama a jinin jikinsa yake tafiya harya ƙarasu cikin fadar,cikin kaɗuwa da kuma zallar tashin hankali wanda suka gani gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin...
IS FOR SALE NOT FREE 08119237616
*Wed/Aprl/7*
*9:30pm*
*71-72*
THE BEAUTIFUL PAGE THE AMEZING CHAPTER A WONDERFUL EPISODE🌚
MALEEK!! wani ƙawataccen murmushi mutumin yay wanda ya bai yanar da zallar farin cikin da yake ciki,babu shakka a yau yazu masu da abu mafi farin ciki a yayinda wasu kuma yake abu mafi muni cikin rayuwarsu,tabbas bai yanarsa babbar nasarace ita kuma take nuni da cewa dukkan wata taƙaddama da ake akan kujerar mulkin yazu ƙarshe,basu taɓa wane shiba ko kuma mene matsayinsa,tsoro wani abunne kaɗai zai sanya suce sun manta matsayinsa,wanda a yanzu shima tsoron yakau domin wanda ake dominsa ya zama tahiri.
hannu ya sanya ya sharce zufar dake neman jiƙa masa kayan dake sanye a jikinsa,yayinda wani jiri ke neman ɗibansa ba tare daya shirya hakanma,har yanzu gani yake abu tamkar a mafarki,mafarkinma irinna shirme da shiririta,ƙara murza ƙwayan idanunsa yayi domin tabbatarwa kansa abinda yake gani a gabansa.
tashin hankali tabbas da ace mutum na iya sauya yau ta koma jibi ko kuma ya sauya jibi ta koma gata babu shakka da yayi hakan kodan samun cikar burinsa,amma ina banda Allah babu mai yin haka,wannan hukuncin lillahi wahidul qahhar ne.
lallai shine bashi da wani babbanci da photocopy ɗinsa,mekennan hakan?kenan ya kashe majine ba tare daya sare kansa ba?shin ya cire shukane ba tare daya cire nijiyar dake ƙasan shukar ba?koko ya manta da cewa shuka bata taɓa yiwowa saida iri shi yake da ƙoƙarin yaga tasa shukar ta fidda tsuro.
wannan wanne irin gagarimin artaban masiface keman zuwar masa ba tare daya shiryata ba.
jikinsa dake rawa ya kama ya riƙe a ƙoƙarinsa nason daina shi rawan.
a karo na biyu ya ƙara ɗaga kansa ya kalli MALEEK wanda ke tsaye yana ɗan juya ƙwayar idanunsa wa al'umar wajan.
da sauri ya janye idanunsa sabida ganin MALEEK ɗin da yayi tamkar zanan SUDAIS SUFRAK WAZEER BILHAS.
Mutanan Fadar kam kowa ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi sabida ƙaɗuwa da kuma ganin abin al-ajabi,yayinda Lil prince ya zubawa Maleek ɗin idanu sabida ganin cikar hallitarsa,kyau,zati,haiba,ƙwarjini,da kuma zallar annorin daya haske fuskarsa,duk da dry ba ɗabi'arsa bace amma yadda fuskarshi ke haske saika ɗauka murmushi yake,musamman yadda beauty point ɗinsa ke lumawa sabida mutsawar fuskarsa.
Gyara tsaiwa mutumin yay tare da kallon Maleek sai kuma yay murmushi,ɗauke idanunsa yayi kana ya ɗan tafa hannayensa yace.
"Oska"
wani ƙatun mutum ne ya shigo kana ganinsa kasan shiɗin ba rainon nan bane,hannu ya miƙa masa yace.
"bani fake face ɗinan"
babu musu Oska ya miƙa masa fuskar dake hannunsa,amsa yayi tare da ƙarasawa inda Maleek yake a tsaye yana zuwa ya saida fuska a dai-dai tasa fuskar ya saka masa,tabba wanda baya wajan yabar kallo.
nan take fuskar SAIFUDEEN BILYAM ta bai yana.
cikin wani sabon tashin hankalin daya shiga Mai martaba,yaci gaba da ƙarewa Saifudeen kallo,cikin rikicewa haɗi da daburcewa yace.
"Captain Saifudeen how zai zama Maleek,wannan maganar aƙwai munafurci a cikinta,kuma bayan kowa yasan cewa Maleek he is no more shine za kaje kayi wani siddabarun naka kazo kace wannan Maleek ne sabida kana son ka mallaki kujerar bilhas ko?"
sai a lkcn Saifudeen wanda yake matsayin Maleek ya ɗaga gajiyayyun idanunsa ya sauke akan fuskar Mai martaba tare da kafeshi da idanunsa masu kaifin gaske.
da sauri Mai martaba ya janye idanunsa sabida wani mugun ƙwarjininsa daya dirar masa,Sarkin fada ne ya kada baki yace.
"a saninmu dai Saifudeen yazo masarautarnan sabida ya bawa Mai martaba tsaro ya kuma kula da shige da fice na wannan masarautar amma yayane zai zama sarki a masarautar bilhas bayan bashi da wani alaƙa da ita?"
gyara tsaiwa mutumin yay kana ya bawa Oska umarnin ya cirewa Saifudeen rigar jikinsa.
dan sauri Saifu ya ɗago kansa ya kalleshi sai kuma ya shagwabe fuska cikin wata tautashasshiyar murya mai sauti da amo da kuma daɗin saurare yace.
"My love"
jijjina kai mutumin yay ba tare daya tanka Saifu ba,hakan ya tabbatarwa da Saifu ba shawararsa yake nema ba wannan umarnine,manyan wayoyinsa masu ƙirar iphone 12 max pro,ya miƙawa Oska ya amsa ya zuba a jikin aljihunsa,kana ya ware hannayensa tare da ɗagasu sama kaɗan.
Cikin nutsuwa Oska ya fara ɓalle ma ɓalli rigar jikinsa kana ya fara ƙoƙarin zare masa rigar zuwa sama,shidai yana tsaye kamar sitatue komai masa ya kunce yayinsa zuciyaraa keyi masa tsalle tamkar zata faso waje haka ya keji,abubuwa da yawan gske ne suka haɗe masa a wannan karon,banda kallon mutumin daya kira da my love babu abinda yake.
abinda ya keso ya fahimta shine shin mayafin masa jinin sarautane bai taɓa sani ba sai yanzu?all this da yake faruwa na mene?meye haɗinsa da wata sarauta a bar da bai taɓa sha'awa ba koda wasa,bayan yana kallon yadda shuwagabannin sukewa talakawansu,shin dama wannan dalilin ya sanyashi dawowa yau ba tare daya sani ba.
numfashi ya fesar mai zafin gaske lkcn da yaji an cire masa rigar jikinsa ya rage daga shi sai marar singlet wacce ta kama jikinsa,hakan ya bai yanar da ƙwantaccen baƙin gashin dake ƙirjinsa wanda yake ƙwance lub lub dashi.
ware manyan idanunsa wanda suke a lumshe yay sabida jin an taɓa hannunsa,idanun sane ya saukan akan Lil prince wanda yake tsaye gabansa yana taɓa guron dake damtsen Saifu.
"wannan kaɗai ya isa ya tabbatar maku da waye shi domin kowa yasan babu yadda za'ai guron masarautar bilhas hannun Saifu,ku cire duk wani tunani dake son ruɗa maku ƙwaƙwalwa dan haka Maleek jinin bilhas ne kun gane"
Waziri ne ya gyara tsaiwa wanda tun ɗazu baice komai ba,sai idanu daya zubawa Saifu yana ayana abubuwa masu yawan gaske cikin ransa.
cikin nutsuwa yace.
"Ba wannan muke da muƙatar jiba,yaya akai Saifu yazo masarautar bilhas da niyar kula da Mai martaba ba tare daya san koshi wanene ba?sannan gaba ɗayanmu kowa yasan cewa Maleek baya raye mene shaidar da zai tabbatar mana da cewa shiɗin jinin bilhas ne kamar yadda ka faɗa?"
Numfashi Lil prince ya sauke shi gaba ɗaya tunaninsa yaya akai Saifu ya tsallake tarkon daya haɗa masa?lallai a wannan masarautar aƙwai masu yi masa zagwan ƙasa banda haka tayayane Saifu zai tsallake wannan lukatar masifar daya sanya shi?
Gefe guda kuma Saifu ne ya yage fake face ɗin da aka sanya masa ya koma Maleek ɗinsa zam,a hankali yake tafiya harya ƙarasa gaban mutumin daya kira da sunan my love,lumshe idanunsa yay sabida wani bugun gaske da yaji zuciyarsa tayi masa,a wannan lkcn itace ta faɗu masa domin daman duk wani numfashi da yake fitarwa baya fita saida tunaninta.
ware idanun nasa yay tare da watsasu akan fuskar Mutumin cikin wata sabuwar murya wacce ta bai yana kanta a yanzu yace.
"why all this happen?kasani cikin juyayi ka hautsinamin tunina dan ALLAH ka gayamin waneni?nasan bana da mahaifin daya huce kai,kaine mahaɗin rayuwata kaine mutumin dana buɗi ido dashi,haka kuma kaine farin cikina kaine komai na Maleek,amma yanzu mene ya sanya kake haɗani da abinda ban haɗa jini dashi ba,bayan kaima nasan baka haɗa jini dashi ba,ka sani abubuwa da yawa wanda kawai yinsu nake ba tare dana san dalilin hakan ba,na aiwatar da dukkan wani umarninka sabida nayi maka biyayya duk mene ya sanya kayimin hakan,ka sanya nayi aiki da banawa ba,ban taɓa sanin yaya ake riƙe wata aba bindiga ba sai daka sanyani,ina tsaka dayin tiater a asibiti kace na shirya domin zuwa garin bilhas kuma cikin masarautar,kasa na sauya sunan da banawa sai nayi da gaske nake gane cewa dani ake magana sabida nayi amfani da sunan da yake ba mallakina ba,duk hakan na menene?"
Tafiya Abbu ya fara harya isa gaban ƙawatacciyar kujerar mulkin da ake taƙaddama a kanta,cikin ɗaga murya yace.
"Sabida ƙwato maka ƴan cikinka,nayi hakanne kuma sabida ka tsira da ranka,sabida nayi imani da Allah dukkan wanda ya kashe ahalinka da zarar yasan kana raye kaima sai yabi diddiginka yaga bayanka,nayi hakanne sabida ka kai lkcn da zaka ɗauki fansar jinin iyayenka,nayi hakane kuma sabida ka girma ka zama sarki kamar yadda mahaifinka yayi dukkan abinda kaga nayi wanda kake ganin ba dai-dai ba gaba ɗaya nayi shine sabida dakai MALEEK!!"
ya ƙare maganar yana ɗaga murya,cikin toshewar ƙwaƙwalwa da kuma juyayin daya shiga ya fara girgiza kansa tare dayin baya,cikin takoshewar murya yace.
"No!! Abbu kada ka gayamin cewa bakai ne mahaifina ba,kada ka rusamin farin cikin da nake ciki idan ina tare dakai,kada kace zaka raba zuƙatanmu ta hanyar faɗin wata kalma wacce zatai dai-dai da bugawar zuciyata,na roƙeka Abbu koda abinda zaka faɗa gsky ne kada ka faɗeshi bana buƙatar komai sai kai dan Allah kazo mu koma inda muka fito please"
kansa ya kisa a wuyan Abbu a kuma dai-dai lkcn wace zafaffun hawaye suka shiga fita ta cikin idanunta,yayi hakanne kuma sabida kada jama'ar wajan suga rauninsa akan Abbun nasa.
wani murmushin takaici Abbu yay cikin ƙasa da murya yace.
"am so sorry sweetheart banyi hakan dan nai hurtting ɗinka ba,amma ya zama dole na faɗi abinda yake ɓoye na tsawon shekaru masu yawan gaske,kayimin afuwa amma dole ne susan sun kashe macijine ba tare dasun sare kansa ba"
Galadima ne yay gyaran murya yace.
"itafa kujera bata jira saidai a jirata idan baku da wata hujja muna iya ɗura Lil prince domin shine ɗan gado gaba da baya kuma..."
da sauri Lil prince ya katseshi ta hanyar faɗin.
"ohhh koda wata shaida ya bayar ai babu wani wanda ya dace da wannan kujerar saini domin nine magajin wanda yay murabus akan kujerar dan haka bamu buƙatar jin wannan ƙanzon kuregen kun gane"
Dariya Abbu yayi yace.
"a yanzu zan faɗa maku hawaye Maleek da kuma yadda akai ya zama magajin wannan kujerar da asalin labarin shine..
*_Kogi_*
kasa ce masa komai tayi sai jajayen idanunta da suke ɗigar ruwa ta zuba masa,duk yadda taso ta ware laɓɓanta domin ta faɗa masa wata maganar kasawa tayi.
hannunsa ya janye daga jikin fuskarta cikin farin ciki yace.
"i'm happy sosai nai farin ciki wannan shurun naki ya tabbatarmin kin amsheni matsayin mijinki nanda sati biyu masu zuwa,nagode Allah ni Yusuf dana samu wannan beauty gril ɗin matsayin matar aure thank you"
ɗan ware manyan idanunta tayi tare da juyashi a saman fuskarsa wacce sai lkcn da samu damar ganinta.
sosai yake da kyau dukkan abinda wata ƴar mace zata buƙata wajan ɗa namiji yana dashi amma yaya zatai?zuciyarta ta riga data bawa wani tuntuni bata jin zata iya yi masa kishi domin hakan kamar cin amana tayi.
janye idanunta tayi daga kansa,daimond ring ɗin hannunta ta shiga murza wanda ƙwana biyu yay ɗan duhu amma yau cikin ikon Allah sai haske yake.
miƙewa yay yace.
"beauty zan tafi sai gani na biyu wanda daga shi kuma saidai ki ganni as ur husband"
samun kanta tayi ta jinjina kai cikin shauƙinta da ƙaunarta ya fice daga cikin parlour'n.
hawayen da take ta maƙalewa tun ɗazu suka samu damar sauka cikin idanunta.
lallai idan ba mutuwa yay ba to ba'a gama jarabtarsa da wasu abubuwan ba,ita dai wannan abubuwan da suke faruwa sunyiwa tunanin yawa sun girmi brain ɗinta,shin yaya zatai da soyayyarsa wacce tayi mata muguwar kamo tun ƙuruciyarta.
ta amince koda soyayyarsa itace ajalinsa bazata taɓa haɗashi da wani a kuma zuciya ɗaya ba.
a kasalance ta miƙe ta nufi hanyar babban parlour nanta tarar da Abba shida Mom suna duba wasu saitin kayan ɗaki a cikin waya da alama kuma odersu za suyi,ba tare data kulasu ba ta nufi bedroom ɗinta kai tsaye kan bed ta faɗa tare da zame vail ɗin da tayi rolling kanta dashi.
hannunta ta rungume a ƙirji ta soma shassheƙar kuka.
sosai tayi kuka mai tsuma zuciya a haka wani wahalallan bacci ya ɗauketa.
a can parlour kuma Mom ce ta kalli Abba tace.
"a tunanina ba wannan hanyar ya kamata kabi ba,zaifi kyau abar yarinyar nan ta auri wanda takeso"
kallonta yayi yace."ohh kema shashancin nata za kibi?wanda takeso nasan ba zata sameshi ba,da alama aljanu suka buɗe mata idanu banda haka ba tayaya mutum dan yay mafarki da wani zaice shiya keso,nafa masa auri sati biyu nan da kwana uku xuwa biyar za'ai bikin shima Tupic ya fito da wacce ya keso gaba ɗaya zan haɗasu kima gaya mata aure ita da Yusuf babu fashi..
*_Bilhas_*
Rana mafi muni da baƙin ciki ranar da dukkan wani dake cikin garin bilhas bazai manta da ita ba,wato ranar da aka wayi gari da mutuwar SARKI SUDAIS.
a cikin daren da zasu riski ajalinsu naje tirakarsa domin yin wata muhimmiyar magana,bayan mungama ɗansa wanda bai huce shekara guda biyu da haihuwa ba ya maƙalemin duk yadda nasu yaje ga mahaifinsa ƙi yayi.
hakan tasa Sarki Sudais yace naje dashi zuwa safiya a kawoshi,babu musu na ɗaukesa muka shige sashina.
da farin ciki matata ta amshe ta haɗa da yaron wajanta.
a tare muka ƙwanta gaba ɗaya asuba nayi Maleek ya tashi ya fara kukan Abbi Ummi,cikin sauri nai al'wala shima ya nuna yana so haka nayi masa na fita zuwa masallaci ba tare dana tafi dashi ba.
tun kafin na isa masallaci naci karo da jama'ar masarautar sun cika harabar masarautar,da sauri na ƙarasa wajan mutanan nace lafiya.
cikin kuka Galadima yace.
"a daren jiya Sarki Sudais ya haɗu da ajalinsa shida matarsa tare da ɗansa Yarima Maleek"
tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana sabida tsabar tashi hankali kallonsa kawai nake ba tare da nace ƙala ba,banda sauke ajjiyar zuciya babu abinda nake,nidai kawai na jishine amma ban yarda da abinda yake faɗa ba,a wannan lkcn dan salla ta zama dole ne ya sanya naje masalaci