Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
prince da kuma Waziri suka ɗago kai suna kallonsa,hatta galadima saida ya kalleshi.
wata wahalliyar zuface ta fara karyowa Mai martaba wani takaici da kumq ladamar bawa Chiroma amana ya ɗarsu cikin zuciyarsa.
wata kam wannan daliline ya sanya boka Gilmas cewa ya hanzarta ɗura Lil prince a kujerar mulki aƙwai guguwar da take shirin tunka rusa,wato Chiroma shine guguwar?.
"Chiroma jeka kawo kayan mudai babu ruwanmu wanda yake da shaidun zama sarki shi zamu naɗa,kuma mulki baya jira saidai a jirasa".
cewar Sarkin Fada.
cikin sauri Chiroma ya fice daga cikin fada ya nufi wani keɓantaccen waje a gidan sarautar.
yana zuwa ya ɗauki wayarsa ya danna wata number ringing ɗin farko aka ɗauki wayar cikin sauri yace.
"lkc yayi ina jira"
yana faɗin hakan ya kashe wayar,wajan 5minutes ta shigo wajan cike da yauƙi hannunta ɗauke da kayanta,tana tafe tana taunar cimgun jikinta duka rawa yake sabida yadda kayan ya matseta.
tana zuwa ta zare ring ɗin hannunta ta miƙa masa tace.
"harka ta kuɗi bana wasa da ita kamar yadda kaban 5.2m akan wannan ring ɗin dole na baka shi,a kuma yanzu zan bar masarautar bilhas"
tana faɗin hakan ta juya da saurin tabar wajan bayan ta bashi zoben.
a can Fada kowa wani murmushin jin daɗi Mai martaba yay tare da kallon Lil prince yace.
"ina zoben dana baka tun shekarun baya..?
zaro idanu Lil prince yay tare da duba yatsun hannunsa,runtsa idanunta yay Allah ya sani shi sham ya manta da amfanin zoben,soyayya ta gigitashi ya bada ƙyautarsa.
cikin ƙasa da murya yace.
"bari na amso na bawa wata kuyanta ajjiya nasan zuwa yanzu bata tafi ba..
*_Kogi_*
numfashi ta kuma saukewa a karo na biyu tana mai ƙara shigar da pillow'n dake kusa da ita.
lumshe idanunta tayi kamar yadda tayi tunanin hakance ta kasance,domin ƙyaƙƙyawar fuskarshi ta fara yi bata gizo a cikin idanunta,sai dai a wannan karan tana mamakin yadda fuskar tashi ta cika kamala,ƙwarjininsa ya ƙara fito fiye da ko yaushe.
ga wani sihirhataccen haske daya kewaye duka sassan jikinsa,babu abinda yake bata mamaki yadda fuskarsa gaba ɗaya babu ɗigun fara'a haɗe rai tamkar zai fasa ihu.
ƙyawawan jajayen laɓɓansa ta zubawa idanu ganin yadda suke sharning su kaɗai tamkar ya shafa lipstic.
ajjiyar zuciya ta sauke tare da ware manyan idanunta wanda suke a rufe,ƙwarai yana da ƙwarjinin da bata isa ta haɗa idanu dashi ba.
sosai yake da haiba da kuma cikar zati,yaushe zata ganshi?yaushe zatai arba da aljaninta?yaushe ne damuwae dake cikin zuciyarta zata kau?tana jin sosai wanda ya zame mata jini da tsokar jikinta,tana jin sonsa yana ratsa dukkan wata gaɓa ta jikinta.
shiɗin gwarzona duk da cewa a mafarki take ganin amma tayi imanin cewa ƙyansa yafi yadda take ganinshi a cikin mafarkinta da ƙwayar idanunta.
a sanyaye ta ɗaga kanta tare da sauke ganinta a kan ƙofar da taji ana turowa,ƙwaɓe fuska tayi tare da lafewa jikin pillow'n.
da sauri Sufyan ya ƙarasu inda take ƙwance yana zuwa ya zauna gefen bed ɗin tare da kama hannunta yace.
"Little tunani ko,yauma heart beat ɗin naki ne,may be wani ƙatun aljanin ke buɗe maki ido"
turo baki tayi tare daya mutsa fuska tace.
"Yaya ko aljanine shi ɗin ina sonsa,ya zama jini da tsokan jikina,yaya zuciyata bugawa yake sabida sonsa,dan Allah yay ka taimaki sister ɗinka ka nemomin shi"
shuru yayi a ransa yana girmama irin son da takewa mutumin da bata san dashi ba,tayaya zai tayata neman mutumin dako a mafarki bai taɓa ganin fuskarshi ba.
tayaya zai nemo wanda babu tabbacin aƙwaishi a wannan duniya may be ba jinsin mutane bane.
"Little shikenan zan tayaki amma ki daina wannan tunanin,jibi yadda soyayya ya ramarki a haka zaizo ya ganki jiki duk ƙashi,maza zo muje *_UNCLE NE..!!_* yazo daga Cameroon daga nan zai huce wani garin,yace yana son ganinki yay maki jajen saceki da akai"
ɗan washe baki tayi hakan ya haddasa bai yanar hqrin makkanta da kuma lumawad beauty points ɗinta,zaman vail ɗin abayarta ta gyara tare da zura bedroom shoe ta miƙe tsaye,hannunta ya kama zuwa cikin babban parlour'n nasu.
a zaune ta samesu Mom,Mamu,Tupic,Abba,Abbu,hannunta ta zame ta nufi inda Abba ke zaune kusa da Abbu tana zuwa ta faɗa jikinsa ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi,kanta Abba ya shafa tare da faɗin.
"Dear wannan mutumin yana wahalar dake ni yaya zanyi na samaki farin cikinki haka ne?"
Murmushi Abbu yay tare gyara zama yace.
"To wanene kuma har haka yarinya take damuwa dashi haka?"
"Wallahi Uncle mu duka babu wanda ya sanshi,a mafarki kawai suka haɗu shine gaba ɗaya tasa damuwa a ranta,na rasa yaya zanyi na sama mata farin cikinta"
cikin zallar mamaki Abbu ya kalli Zarina wacce take ƙwance jikin Abba yace.
"To mene zai hana a haɗata aure da wani ina ganin hakan zai sanya ta daina da damuwa da mutumin da bata tabbacin aƙwaishi a wannan duniyar"
shuru Abba yay yana tunanin maganar Abbu,tabbas idan aka haɗata aure da wani babu shakka hakan zai sanya ta daina tunanin wani daban,kuma auren da zatai zai ɗebe mata kewa harta manta abinda ake ranta da zuciyarta.
numfashi Abba yaja yace.
"ina ganin wannan shawarar taka itane zamubi,daman aƙwai wani ɗan abokina da yake sonta naƙi bashi dama,amma dole yanzu zan amince masa,idan yasu sai a haɗa bikinta dana Tupic tunda Sufyan yaƙi"
Mamu dake gefensu tayi saurin faɗin.
"Babu uban dazai sanya Sufyan ya zauna babu aure,wannan masifar ciwon cikin da yake shi kaɗai bai isa ya sanyashi yay aure ba"
Abbu dake murmushi ya kalli mamu,can cikin ransa yace.
"Ayya har kinsa na fara tausayin yarinyar da Saifudeen zai aura"
a fili kuma ya miƙe tsaye tare da faɗin.
"Nizan tafi daman nazu ganin lafiyar Saifudeen ne,shiyasa nace bari na leƙo nan ɗin,sai kuma munzo ɗaurin auren ƴan uku,kafin nan insha shima Saifu zan tilasta masa yin aure wajan shekara 36 amma babu niya"
gaba ɗaya wajan suka sanya dry banda Zarina data kafe Abbu da idanu,sosai take jin sunan daya faɗa na SAIFUDEEN nayi mata yawo cikin ƙwaƙwalwarta,amma ta kasa fahimtar inda ta taɓa sanin inda taji sunan,idanunta taja ta lumshe tare da janye jikinta daga jikin Abba ta lafe a jikin sofa ta shiga sauke numfashi.
tayayane zata iya rayuwar aure da wanda bata sani ba? tayaya zuciyarta zata iya mantawa da mutumin da take jinsa a jinin cikinta?
tayaya zata iya yiwa wani biyayar aure ba aljaninta ba?
wasu zafaffun hawayene suka fara fita daga cikin idanunta ita kaɗai tasan zafi da raɗaɗin da take ji cikin zuciyarta,lafewa ta ƙarayi a jikin sofar ta shiga sauke numfashi.
Sufyan kam kasa cewa komai yayi ya cika yay fam sabida zallar takaicin abinda Mamu tayi masa,gefe guda kuma Tupic ne yake tayi masa dry,Mom kam shuru tayi tana tunanin yadda za'a aurar mata da yarinyar da ƙarancin shekaru.
Abba da Abbu ne suka fita suna tafe suna yin maganar auran da kuma yadda zai kasance nanda sati biyu masu zuwa,da wannan maganar Abbu ya shiga mota Yahaya drever ya jashi.
Bilhas
Dukkan inda yake tunanin ganin Meyrah yaje babu ita babu labarinta.
haƙiƙa rashin ganinta ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba.
cikin wani sabon tashin hankalin ya dawo cikin Fadar ya shaida masa abinda yake faruwa.
sabida tashin tsoro da fargaba yasa ya kasa faɗin komai sai kallon Lil prince da yake.
wajan 20minutes Chiroma ya dawo hannunsa ɗauke da Zoben bilhas,yana zuwa yace.
"ga zoben bari naje kawo sauran kayan"
da sauri sarkin fada ya dakatar dashi da faɗin.
"A'a hujja gudama ya isa ina tunanin sai a fara shirin naɗaka kawo zoben"
cikin farin ciki Chiroma ya nufi wajan da kujerar karagar da sauri sarkin fada yace "stop it's fake ring...
THE NEW EMIR
*BY*
*NIMCYLUV*
*69-70*
*NOT EDITED*
Da sauri Chiroma ya ɗago kansa da zallar mamakin yadda zoben ya zama fake,bayan yana tabbacin wannan shine asalin zoben da ake takama dashi a gidan sarautar,zoben da ko wanne sarki yake fata da kuma burin ganin ya samesa domin shine zai maka damar samun kujerar mulkin,tabbas idan akace wannan zoben fake ne babu shakka shima Mai martaba Khalida tsuhun sarki shime kawai an naɗashi ne kawai amma ba'a tabbatar da ingancin zoben ba,bare a ɗauki mataki akai.
idan har wannan ring ɗin fake ne abin tambayar a nan shine ina Real ring ɗin yake?ina ya shiga?.
ko kuma Meyrah ta yaudaresa ne bawai na gskyr ta bashi ba? kai hakanma bamai yiwuwa bane dole tabbas wannan shine ring ɗin da ake buƙata,kuma ya zamana dole a ɗurashi kan karagar mulki shima ya fara gudunar da kalan nashi tsagwaran zaluncin mulki wanda ya buɗi idanu yaga tsuhun Sarki Khalid wazeer bilhas ya nayi.
Mai martaba kam wani shu'umin murmushi ya saki wanda shine kaɗai yasan ma'anarsa,cikin dakiya da rashin nuna jin daɗinsa ya miƙe tsaye tare dayin waje.
yana fita harabar Masarautar ya zaro wayarsa a cikin aljihu ya dailing wata number ringing biyu akai picking call,cikin ƙasa da murya ya fara magana yana magana yana tafiya zuwa sashin lambun daya daɗe bai shiga ba.
babu inda ya tsaya sai ƙasan bishiyar fasadabir cikin zallar makirci yace.
"Na fahimci Saifudeen ba shine matsalarmu ba,daman ance makashinka yana tare dakai,a kullum a kuma koda yaushe nunamin yake yana sona bai damu da mulki ba,dalilin hakan yasa na bashi yarda fiye dasu Galadima,Waziri,Tiraki,sai gashi shida nayarda dashi shine yaymin zagwan ƙasa,ina son duk yadda za'ai kada ka kuskura ya samu damar dazai hau wannan kujerar mulkin tabbas idan yahau zai jawa kansa masifa wacce bai taɓa sanin da akwai irinta a wannan duniyar nan ba"
yakai ƙarshen maganar yana sauke idanunsa akan wani tudun ƙasa,ci gaba da tafiya yayi harya tsaya kan ƙasar da haka kurum yaji hankalinsa bai ƙwanta da wajan ba.
daga can ɓangaren boka Gilmas yay dry mai yawan gske wacce take fidda wani sauti mara daɗin gaske,tabbas wannan ranar yake jin tsoron zuwanta ranar daya san babu wani sauran raguwar wani abu da Chiroma zai ya daɗe yana son fahimtar da Mai martaba wannan abun amma ya gagara fahimta ko kaɗan,amma gashi yau da kansa ya fahimci abinda yake faruwa tsakaninsa da Chiroma,yau ɓoyayyan sirrin da yake ɓoye ya tuna kansa ba tare da wani tsananin bin cike ko kuma tada hankali ba.
a karo na biyu ya ƙara ware hangamemen bakinsa ya ƙwarara wani uban ihun daya haddasa fitowar Dauwas daga cikin wani surƙoƙin ɗaki.
gaba ɗaya yankin ya ɗauki sautin ƙatuwar muryarsa wacce take fidda sauti mara daɗin ji.
dukkan ɗakin girgiza yake har wani ɗan ƙaramin haƙine ke fitowa daga cikin bakinsa.
lkcn kaɗan wani surƙomemen baƙin aljani mai kawona wajan biyar ya bai yana gaban boka Gilmas,banda huci da kumbura hanci babu abinda aljanin yake.
sai dalalo da dugun harshensa waje yake yayinda wani baƙin yawo ke biyo bayan harshen nasa,dukkan yadda kakai kaga inda tsayinsa ya tsaya ka faɗi ƙarya,shi kansa Dauwas saida ya firgita da ganin wannan mummunar halittar mara fasali.
tsaigai tawa yayi da dry kana ya shiga faɗin wasu kalmomin siddabaru haɗi dana tsafi,wani jan ruwa ya ɗauko ya zuba a wata ƙwarya kana ya yafa wani baƙin ƙyalle nan take kujerar masarautar bilhas ta bai yana cikin ƙwarya,sai haske take tamkar yanzu aka gama ƙerata.
haka ya dinga tsubbace-tsubbacensa daga ƙarshe ya daki kan aljanin tare da faɗin.
"Tashi wannan aikin na kane kaine kaɗai zaka iya,ina son ka zama aljanin dukkan wanda ya kuskura yahau wannan ƙawataccen kujerar muddin ba Magajin Mai martaba ne,idan kasa wani abu ya gagareka ko kuma kayimin kuskure cikin aikina babu shakka nine ajalinka kasan kuma zan iya,dukkan abinda kake buƙata an baka saida kashanye jinin jarirai guda 10 kafin ka amince da hakan maza jeka"
wata girgiza Aljanin yay sai gashi ya ƙwala wani ihu tare da ware fuka-fuskansa ya ƙara wata girgizar a karo na biyu,ɓat ya ɓace daga wajan.
wata dry Boka gilmas yay kafin ya daki ruwan dake cikin ƙwaryar saiga Aljani Gumfak akan kujerar mulkin garin bilhas..
Wani murmushin gefe baki Mai martaba Khalid tsuhun sarkin bilhas ya saki tare da sakin wata dry a lkc guda,gyara tsaiwarsa yay lkcn da yaji boka na faɗin.
"Duk wanda ya sake yahau wannan kujerar saidai uwarsa ta haifi wani badai shi ba,dan haka ka ƙwantar da hankalinka dole ne magaji yahau wannan kujerar mulkin dole ne ya gudanar da mulki kamar yadda kaima kayi babu shakka Magaji zai zama sarki"
Cikin farin ciki da kuma jin daɗin Mai martaba ya kashe wayar ba tare daya kuma cewa komai ba,lambun ya shiga ƙarewa kallo kamar mai neman wani abu kamar ance kalli gefenka yana juyawa yay tozali da.
a can fada kowa cikin son kawar da abinda yake ransa,ya saki murmushi tare da kallon sarkin fada yace.
"fake ring? but how can that happen? bayan ga tambarin masarauta nan ajikin zoben kuma idan fake ne babu yadda za'ai aga zanan tambarin masarautar a jiki"
kallonsa sarkin fada yay tare da sakin murmushi yace.
"congrat Chiroma am just joking is not take ring is real finally are the Emir of Masarautar bilhas"
wata wahalalliyar ajjiyar zuciya Chiroma ya saki tare da faɗaɗa fuskarshi da murmushi,daman ya sani da wahala ya zama jabo yana da tabbacin akan zoben da kuma wanda ya bashi zaben,cikin jin daɗi da kuma tsananin farin ciki ya isa inda haɗaɗɗiyar kujerar mulkin take ajjiye,gaba ɗaya mutanan wajan suka miƙe tsaye domin girmamawa,cikin issar daya keji tazo masa ya nufi zama akan kujerar runtsa idanunsa yay tare sa sakin ƴar ƙamar ƙara sabida abinda yaji wani irin..
Cikin jin daɗi Mai martaba ya nufi wajan daya hangi wani lafiyayyen nunannan fasadabir daya faɗo ƙasa sabida tsananin nunar da yayi,wajan ya ƙarasa tare da sanya hannu ya ɗauki fasadabir tare da nufar hanyar fita,yana fita harabar masarautar yanu wajan wani fanfu dake kusan masallacin bilhas,wankewa yayi kana ya juya ya nufi fada cikin tafiyar issarshi wacce take tare dashi duk da cewa mulkin ya riga ya tafi.
yana zuwa cikin fadar yaga gaba ɗaya an miƙe tsaye dan haka bai nuna alamun wani abuba shima ya tsaya domin ganin abinda zai faro dan yana da tabbacin a yau Chiroma saidai wani bashi ba.
Tun kafin ya zauna akan kujerar wani zazzafan zafi da huci ya daki jikinsa,ga kuma wani abu tamkar allurar da yaji sun dira cikin tsakiyar kansa.
cikin fitar hayyaci da kuma tsananin azabar daya keji ya matsa daga kusan kujerar wacce bai riga ya zauna ba,a ƙasan lafiyayyiyar daddumar dake shimfiɗe a fadar ya faɗi ya zauna yana maida numfashi.
cikin takaici da kuma baƙin cikin abinda ya sameshi ya ɗaga jajayen idanunsa ya sauke a fuskar Mai martaba Khalid,wani murmushi Mai martaba yayi tare da ɗauke idanunsa daga gareshi ya kalli Lil prince wanda yake tsaye ya harɗe hannayensa.
a zahiri idan kaganshi zaka ɗauka hankalinsa yana ga abinda yake faruwa a cikin fadar ne,amma a cikin zuciyarsa tsananin damuwa da kuma zallar tunanine yay masa yawa,a yanzu bawai mulkin yake buƙata ba gaba ɗaya tunaninsa yana ga yadda zai ya samu farin cikinsa Zarina.
a wannan karan ita kawai yake muradi da kuma fatan gani,sosai zuciyarsa ta azabtu da rashin ganinta.
saukar muryar sarkin fada ce ta sanya saki numfashi tare da ɗaga idanunsa ya kalli sarkin fada.
hakan da yayne ya tabbatarwa sarkin fada cewa lil prince baiji abinda yace ba,cikin farin ciki Mai martaba ya mai²ta abinda sarkin fada ya faɗi ta hanyar faɗin.
"Magaji matso kusa lkcnka yayi a wannan karan ababu abinda zai hana ka zama sarkin bilhas..
*_Kogi_*
Hannu tasa ta murɗa handle ɗin ƙofar tare da buɗewa ta fito daga cikin bathroom ɗin,a kasalance kuma a sanyaye ta ƙarasa gaban dressing mirrow inda kayan shafanta yake ajjiye.
stool ta jawo ta zauna kana ta ƙurawa makeken mirrow'n dake manne a bango ɗakin,wasu zafaffun hawaye masu zafin gaske ne suka zamu nasarar fita daga cikin idanunta,wayarta dake side ɗin mirrow'nce ta ɗauki ƙara alamar kira ya shigo,a hankali ta miƙa hannunta tare da ɗaukan wayar idanunta ta lumshe hakan ya ƙara bawa hawayen da manne cikin ƙwayar idanunta damar gangarowa,a jin wani sabon kiran ya shigone ya sanya ta ware manyan idanunta wanda suka ƙanƙance sabida yawan kukan da take da kuma zallar tunanin rashin mafita akan lukutar masifar dake shirin tunkarota,sam koda wasa bata taɓa tunanin cewa maganar da Abba ya faɗa na cewar zai mata aure da gaske ba,tayaya zataiwa Aljaninta kishiya a cikin zuciyarta?bata jin koda wasa zata iya zaman aure da waninsa,shi kaɗai take muradi da kuma fatan kasan cewa dashi,kasan cewa kuma irinta har abada ɗinnan, babu abinda zuciyarta ke muradi sama dashi a wannan lkcn,sosai kunnuwanta keson jin daddaɗar muryarsa,idanunta na ƙwaɗai tuwa dason ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa mai cike da gwarjini da kuma haiba,babu abinda gangar jikinta ke murada sama dajin ɗumin jikinsa,sosai sonsa da kuma zallar qaunarsa keson zautar da tunaninta,ba tajin komai haka kuma bata ganin komai sai tsaftatacciyar soyayyarsa wacce a kullum take ƙara yawan a cikin zuciyarta.
a hankali ta janye idanunta daga kan makeken screen ɗin wayarta,wayar wacce ta kasan ƙirar iphone11 max pro ita ta ajjiye akan dressing mirrow.
cikin kasalan data gama zama a jikinta ta ɗauki wata lafiyayyan body lotion na carrot cikin nutsuwa ta fara shafa man a saman soft fresh skin ɗinta,sosai ta shafe ko'ina na jikinta,cikin ƙaramin lkcn skin ɗinta ya fara sharning musamman santala-santalan cinyoyinta.
bayan ta kammalane ta ɗauki body spray ta fesa a saman fatar jikinta,cikin nutsuwa ta miƙe ta nufi wajan wardrobe wata lafiyayyiyar arabian abayar ta ɗauka tare da vail ɗinta.
bayan ta kammala sanya unders ta zura abayar a jikinta tare da rolling kanta da vail ɗin abayar hakan ta haddasa bai yanar long hair ɗinta wanda yake ƙwance har bayanta.
ɗan ya mutsa fuska tayi tare da sanya hannu ta danne saitin zuciyarta haɗi da murzawa kaɗan,cikin siririyar muryarta wacce take fita a hankali ta ware laɓɓanta tace.
"Ya rabbi ka baiyarmin abinda yake alkairi a gareni,ubangiji ka bai yanamin aljanina koda shiɗin da gaske aljanina ba mutum ba,ina sonsa a yadda yake na kuma amincewa rayuwa dashi a duk yadda na sameshi,wannan aure idan shine silar yayewar damuwata Allah kabani ikon jure hakan,amma nasan dukkan wanda na aura bazai taɓa jin daɗin zama dani ba,bazan iya bashi kulawar daya dace ba amatsayinta na mijina ba,Ya see this innonce Zarina helf her ya rabbi"
lumshe idanunta ta kumayi kana ta waresu a karo na wajan biyar kenan taji wayarta ta fara ringing,bedroom flat shoe ta sanya a ƙafarta tare da sanya hannu ta ɗauki wayar ganin sunan Mom na yawo saman screen ɗin ya sanya tayi pic tare da ƙwaɓe fuska.
gyara zama Mom tayi jin tayi picking call ɗin ta kalli Sufyan dake gefenta tace.
"my luv