THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   8 / 38

21K to 24K   out of 111.1K words

yana aikinsa,wasu an ƴantasu wasu kuma haryau bauta suke tamkar ba mutane ba,a haka yaci gaba da tafiya harya isa sashinsa yana shiga,ya ajjiye komai dake hannunsa a mazauninsa,zubewa yayi akan italian bed ɗinta tare da jawo pillow ya rungome ya shiga sauke ajjiyar zuciyar kamar karamin ƙaramin yaron da yayi tsere,baisan meke damunsa ba a ƙwana biyunan,amma ya samu kansa dason fahimtar abinda ke faruwa a wannan masarautar,A ranar daya sauka ya sameta zata bar gidan sarautar kamar mahaukaciya,a karo na biyu yaga Fadawa najan Kulsum,abu na uku ga yadda Zaitun ta rasa ranta kuma ya tabbatar ba haka nan ta rasa ran nata ba,ko lkcn tane yayi babu shakka aƙwai silan rasuwan nata,babban tashin hankalin bai huce maganar da yaji Mai martaba ya nayi game da Mai babban ɗaki ba,wacce har yau ya kasa fahimtar wace Mai babban ɗakin,mai yasa ya keson aikata hakan gareta shine tambayar da yakewa kansa daga jiya zuwa yau amma ya kasa samun amsarta,kuma ya ɗaukarwa kansa alƙawari kare rayuwarta haka nan dole ya binciki wanne sashi ne nata daga cikin flats ɗin gidan sarautar.

Da wannan tunanin ya miƙe tare da faɗawa bathroom,ruwa mai zafi ya haɗa a cikin jakuzzi,ka sancewar yanayin garin aƙwai sanyi ga kuma iska mai ƙarfi dake kaɗawa tamkar za'ai ruwan sama,kayansa ya cire tare da ratayesu saman hanger kana ya shiga cikin jakuzzi'n,sannu a hankali yake shigewa jikin ruwan zafin tare da ware laps ɗinsa ruwa na ratsa mararsa dake masa ciwo,lumshe sexcy eyes ɗinsa yayi tare da sanya hannunsa ya shafi saman mararsa wacce ta ɗan kumbura,cije laɓɓansa yayi sbd zafi da raɗaɗin daya saukar masa,ƙara nutsewa yayi cikin ruwan sosai zafin ruwan yake ƙara masa kuzari,wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke kana ya murza zobensa cikin so da ƙauna ya manna masa kiss,zuwa yanzu yama manta da cewa ya ganta cikin lambu,daman burinsa bai huce ya tabbatar da lafiyarta ba,a yadda ya ganta tasha ado kamar wata gimbiya ko sarauniya yasan cewa tabbas ta samu lafiya,ya ɗauki lkc mai tsayi cikin ruwan kafi ya soma wankan yana kammalawa ya ɗauki bathrope ya sanya a jikinsa,kana yayi brush tare da ɗaura al'wala,domin haka tsarinsa yake baya taɓa zama babu al'alwa domin ita kanta kariyace ga mutum,yana gamawa ya fito tare da zama kan dressing mirrow ya juna handrayer ya soma busar da somar kansa,yana kammalawa ya ɗauki body lotion mai ƙamshi da kuma daɗi a jiki ya soma shafawa chocolate naked body ɗinsa mai ɗaukar idanu,bayan ya kammala ne ya ɗauki body spary ya feshe jikinsa dashi,a ɗan gaggauce ya buɗe wadrope ya ɗauki uniform ɗinsa da wando da rigar haɗi da ficap ɗin ya sanya,wow amy colour ya haɗu da chocolate skin ga yadda sumar kansa ta ƙwanta har wuyansa luff sai sheƙi take,ta ƙara fiddo da asalin ƙyan na baƙin balarabe,sosai murɗaɗɗan jikinsa ya amshi kakakin sojoji,a wannan lkcn ko namijine ya kallesa sai zuciyarsa ta buga,balle ƴan mata masu ƙarancin shekaru irinsu Zarina wanda suke Adult,masu tashan balaga wanda yanzu ne lkcn da budurcinsu ke bayyana suke jin kansu tamkar wasu manya,wajan dressing mirrow'n ya dawo kana ya ɗauki turarensa Ohud mood ya goga a jikinsa,sannan ya ƙwashi wayoyinsa da key ɗin motarsa tare da rufe ƙofar sashin ya nufi hanyar Fada.


Dake yau zamane na sirri wanda Lil prince ya nema wajan Mai maryaba yasa babu mutane da yawa a Fada sai Mai martaba,Tiraki,Sarkin fada,waziri,Sai kuma Lil prince dake durƙushe gaban mahaifin nasa yana son ya bashi damar magana,sbd gaba ɗaya hankalinsa yayi kan Zarina kuma ya tabbatar yanxu Hadima Batul ta kaita lambu shi kawai take jira..

Gyara zama Mai martaba yayi kana yayi gyaran murya a hankali yace "muna sauraranka meke tafe dakai haka Magaji?"ya cilla masa tambayar yaname fahimtar yanayinsa,ƙara sunkuyar dakai Prince yayi cikin dakiya da kuma maida fargabar dake ransa yace.


"Allah ya ƙara maka lafiya da yawan rai daman ina neman kabani dama domin na fiddo da macen da nakeso na aura,domin ina son ajjiye iyali"ya ƙare maganar yana zubawa Mai martaba idanu.


Jinjina kai Mai martaba yayi kafin yayi shuru alamar tunani,wajan sama da 5minutes kafin ya ɗago ya kalli prince yace "Muma zamu so hakan domin mutuncinmu ne zai ƙaro idanun jama'a ace yau Magaji zai ajjiye iyali Thank God,amma kafin nan ,zanso nasan wacece Fulani mai jiran gado?"ya ƙare maganar yana sakin murmushi alamar jin daɗi,Murmushin ƙarfin hali Prince yayi kana yace "Godiya nake ya Abbana,daman ba wata bace face *Kuyanga Zarina* ita nake muradin ƙauna na kasance da ita *ABADAN DA'IMAN* ina fatan zaka bani damar hakan?"ya ƙarashe maganar kansa a ƙasa,Saifudeen dake bakin ƙofar yana ƙoƙarin shigowa yayi saurin tsaya tare da sanya hannu ya dafe saitin zuciyarsa,wani ɗan radaɗi da zafin da yaji tayi masane yasashi runtsa idanunsa,cikin narkakkiyar murya yace "Ya rabb help me"ya ƙare maganar yana jin gina bayansa da jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a faffaɗan ƙirjinsa,ya zubawa Prince ƙanƙantattun idanunsa.
Mai martaba jin maganar Prince yayi tamkar ruwan sama wanda ba'a shirya masa yake sauka,tabbas abinda Magaji ke nema babban abune,baya tunanin ƙalubalan dake gabansu,yasan cewa baza'a taɓa yadda Prince ya hau karagar mulki ba tare daya nuna shaidu guda uku wanda dasu ne aka lamunce munce a ɗana mutum as King of Bilhas,amma shi ya fahimci ba wanne a ransa ba,yaushe Prince ya faɗa soyayyarsa baiwarsa,ya manta cewa auren baiwarsa ya haramta a garesa,wata zuface ta shiga karyowa Mai martaba,wani huci ya fitar mai zafi,kana ya kalli Prince yace "Are you mad,ashe baka da tunani Magaji how baiwarka zata zama matarka kuma Fulanin bilhas you're vry stopid kama sauya wannan banzan tunanin naka mara amfani,idan ba haka ba...."sai kuma yayi shuru ya ƙarasa maganar sbd idanu huɗu da sukai da Saifudeen,maida hankalinsa yayi kan Prince yace "Get out!"ya ƙare maganar yana ɗan ɗaga murya,wani baƙin ciki ne suka sauka zuciyar Prince sbd baiyi tunanin hakan ba,duk da cewa da wahala ya amince amma baiyi tunanin zai kasa amince masa ya samu abinda yake buƙata ba,a karon farko ya tambayi abu wajan Mai martaba amma ya kasa samu,cikin ɓacin rai ya miƙe tare da fice daga Fadar,tsayawa yayi wajan Saifu tare dajan tsaki yace "YOU?"sai kuma ya jinjina kai tare da ficewa daga cikin Fadar,ko inda Lambun yake bai kallah ba sbd yadda ya kejin zuciyarsa babu daɗi,yana zuwa harabar gidan direct motar ya faɗa ya jata da wani irin gudu ya nufi N.S University.


Saifu dry ya kusa yi amma sbd dry baya tsarinsa infact ma bai saba yinta ba,yasa ya saki wani shu'umin murmushi tare dajan gemunsa ya shafi cikinsa,a hankali ya ƙarasa cikin Fadar tare da zama ya fuskanci Mai martaba kana ya sunkuyar dakai ƙasa ba tare da yace komai ba,Sarkin Fadane ya dubesa yace "Ɗan samari da alama kana son cewa wani abu ko?"Sarkin fada ya faɗa yana kallon Saifu,sai a lkcn Saifu ya buɗe gajiyayyun idanunsa ba tare daya kalli Sarki fada ba,yace "Barka da hutawa Mai martaba"ya ƙare maganar yana sauke numfashi sbd tsayi da maganar tayi masa,baya iya jure magana indai bada Abbunsa ba,Kallonsa Mai martaba yayi yana jinjina ƙarfin miskilancin Saifu,ɗauke wannan tunanin yayi daga ransa kana yace"Saifu ka shirya yau zaka zaɓi Maid mai kula da ɓangaranka"yana gama faɗin hakan ya tura Waziri yace"kaje kasa ayi shela dukkan Kuyangun da ma'a basu aiki ba su fito yanzu"da sauri waziri ya miƙe tare da nufar waje domin ai watar da abinda Mai martaba ya umarce shi.


Zarina ta daɗe zaune a wajan harta shanye Fasadabir ɗin dake hannunta,bayan ta kammala ne ta miƙe tsaye tare da soma zagayawa cikin lambun sbd gajiyar da tayi,cikin nutsuwa take zagayen lambun tana kallon yadda shukokin wajan tare da flowers dake kaɗawa a wajan,komai na wajan birgeta yake a hankali ta shiga tsakanin wasu manyan bishiyo sbd daddaɗar iskan wajan dake kaɗawa,ɗan juyawa tayi jin kayanta ya riƙe wani abu,murmushi ta saki ganin wata tsuhuwar aƙwati tana isa ta zare kayanta,har zata huce sai kuma ta samu kanta da buɗe aƙwatin nan tayi arba da wata ƙyaƙƙyawar takubi haɗi da wata hular zallar azurfa sai sheƙi take,sosai take kallon takubin haɗi da hular wanda kana ganinsu kasan na musammane,samun kanta tayi dasun adanasu dan haka ta hangi wani rami mai zurfi tana zuwa ta ɗauki aƙwatin tare da sakata ciki,kana ta shiga maida ƙasa saida ta cike ramin tas ta baje ƙasar wajan,sannan ta zauna kan kujera tana sauke numfashin gajiya,ta daɗe a wajan sosai sannan ta fara jiyo shelan neman dukkan sabbin kuyangun masarautar,zuciyata ce ta buga da ƙarfin gaske wata fargaba da tsoro ya dirar mata a zuciya,da hanzari da miƙe tare komawa sashin da aka sauketa tana zuwa ta cire kayan jikinta tare da watsa ruwa tana gamawa ta nemi fararan kayanta ta sanya,jikinta na zubar da ruwa ta sanya flat shoe ɗinta ta nufi harabar masarautar domin amsa kira.


Lil prince's pov
Yana isa Universty'n babu inda ya tsaya sai office ɗin Yazeed yana zuwa yayi knoking nan aka bashi umarnin shiga,yana shiga ya nemi waje ya zaune akan wata duguwar sofa dake office ɗin,dry Murmushi Yazeed yayi cikin shaƙiyanci yace "banyi expecting ganinka ba at this time hope dai lafiya"tsaki Lil prince ya saki cikin ɓacin rai yace "You stopid kada ka ɓatamin rai akan wanda Mai martaba yayi"da mamaki Yazeed ya saki pen ɗin dake hannunsa tare da kallon Prince yace "what wrong with you,do you know what are you try to say,Mai martaba ya ɓata maka rai how?"ya ƙare maganar da mamaki a kan fuskarsa,numfashi Prince ya sauke tare da cije leɓe kana ya dubi Yazeed yace "sabida kawai naje masa da burin ajjiye iyali ina buƙatar aure sbd na samu wacce na keso,na fahimci so yake naita bin yaran mutane kamar wani ɗan akuya shi bai gina rayuwarsa ni bai barni na gina tawa ba,dashi dani mu duka munsan abinda muke ba dai² bane,idan burinsa nabi ƴar ƴan mutane akan buƙatarsa why nima bazai barni nayi tarayya da wacce nake so ba"ya ƙare magana yana dukan pillow'n dake kusansa,jinjina kai Yazeed yayi yana mai jinjina lamarin yau Prince da kansa yake cewa yana son aure,tabbas Allah ne kaɗai yasan son daya kewa wacce yake burin aura banda haka aida baiyi wannan tunanin ba,kafin yayi magana an turo ƙofar office ɗin bakinta ɗauke da sallama,haɗe rai Yazeed yayi kana yace "ke lafiyanki zaki shigomin office without excuse? "ya faɗa yana cillawa Mema harara,zubewa Mema tayi gabansa tare da fashewa da kuka tace "Sir kaji tsoran Allah idan babu duniya aƙwai ƙiyama akan paper ɗinka na rasa damata ta wannan shekaran,tsawan shekara huɗu inayin past akan dukkan exam ɗin da nake,amma yau ka zama sanadin lalata burina da kuma farin cikina,akan wani banzan ƙudiri naka,lallai kayi nasara abinda baka sani ba shine aƙwai Allah kuma yana kallon komai yana jin komai,sannan wannan tarin zunubin da kake aikatawa wa ƴan mata bazai barka ba,Allah ya isa ban yafe ba Ubangiji ya isarmi kuma ya sakamin cikin gaggawar da ikon Allah saika tuzarta ni Maryama Alhassan zan bar maka makaranta zanje ka wanda yake tsumayina domin aurena,nagode Allah da bai baka damar cin burinka a kaina ba,nabarka lafiya"tana faɗin hakan ta fice daga office ɗin zuciyarta nayi mata zafi,wani banzan kallo Yazeed ya watsa mata tare da faɗin "sakalya aƙwai irinki dubu kuma da bazata suke da ƙama"Prince kam damuwar dake ransa ta hanashi tanka masu,daga ƙarshema miƙewa yayi tare dayiwa Yazeed sallama ya fice daga cikin office ɗin,motarsa ya faɗa tare da ficewa daga cikin makarantar gaba ɗaya.



**** ****
Tsaye suke gaba ɗaya sun jere tare dabin layi tamkar za'a raba masu wani abu,a hankali Saifudeen kebinsu da kallo dukkan wacce ya kalla sai yaga tsaftarta ba tayi masa ba,wata ma idan ya ganta sai taɓe baki tamkar yaga kashi,ahaka yayita tafiya harya huce kusan rabin kuyangun baiga wacce tayi masa ba.

Da ɗan sassarfa take da tafiya kanta a ƙasa zuciyarta na bugawa sabida lattin da tayi,yadda take tafiya tsakani da Allah a gareta sauri take,amma a zahiri wata irin tafiya take mai ɗaukan hankalin dukkan wanda yayi arba da ita,kanta a ƙasa take tafiya yadda take daka ƙafarta a hanzarce ya mawa ma dai² cin waist ɗinta damar juyawa cikin uniform ɗinta,can nesa da inda ya baro taja ta tsaya,wani murmushin gefen baki yayi tare da taune laɓɓansa,haka yaci gaba da takawa har zuwa ƙarshe baiga wacce tayi masa ba,bare har yayi tunanin cin abinda ta girka,Waziri ne yace "Duba da ƙyau yaro wannan sune sabbin kuyangunmu na wannan masarautar"baiko kalli inda waziri yake ba,yaja ya tsaya tare da lumshe idanunsa na wani lkc kana ya waresu a kanta,yadda take mamular laɓɓanta ya sashi saki tattausan murmushi,sosai tsoran dake kan fuskarta ya bayyana,gaba ɗaya ta hana kanta sukuni,cikin ya shafa kana ya gyara tsaiwarsa tare da haɗe ransa tamkar bai taɓa dry ba,cikin kausasshiyar murya mai daɗi wacce take nuni da wanda yayita umarni yake badawa yace "you the last person"a tsorace Zarina ta ɗaga idanunta ta saukeso a kansa,wani hawaye ne ya soma zubuwa daga cikin idanunta,kasa tamkashi tayi sbd wani irin ƙwarjini da yayi mata,wata tsawa Waziri yayi mata yace "ahir ɗinki ƴar talakawa maza jeki zuwa bauta"ya faɗa yana ƙara sauke mata wata tsawar,gaba jikin Zarina ya ɗauki rawa wani tsoro ya ƙara kamata a karo na biyu,kasa takawa tayi bare tayi tunanin zuwa inda yake tsaye,a hanzarce Waziri ya ɗaga wata ƙatuwar bulala zai shimfiɗa mata a baya yaji anyi saurin riƙe hannunsa tare da faɗin "No!..




*THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE IF YOU NEED JUST CONTACT ME 08119237616😍200 NAIRA ONLY*
_THIS BOOK IS FOR SALE KADA A FITARMIN DASHI WAJE IF YOU NEED THE NEW EMIR JUST CONTACT ME 08119237616 200 FOR NRML GRP 500 FOR VIP WANDA ZASU SAMU PAID BOOKS ƊINA._


*23-24*

PROMISE#

BE WITH SOME ONE WHO LIKE TO STAY WITH YOU.



Da sauri Waziri ya ɗaga kansa sama domin yaga wanda ya hanashi dokan Zarina,mamaki yayi ganin Saifu tsaye a gabansa yana danna waya, gaba ɗaya bama su yake kallo ba,yaushe har yazu wajan hartakai gaya riƙe masa hannu,hannunsa ya sauke ƙasa wanda yake ɗauke da bulalar kana ya kalli sauran Kuyangun yace.

"kowa ya koma masaukinsa kafin a ƙara nemanku"

Zarina wata sassanyar ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare dayiwa Allah godiya domin ta gama tsorata kuma ta saddaƙar Waziri zai zabga mata wannan bulalar,akaro na biyu ta kuma sauke ajjiyar zuciya,a hankali ta ɗaga jiƙaƙƙun idanunta ta sauke a kansa,da sauri ya janye idanunsa daga gareta tare da haɗe fuskarsa tamkar bashi ba,sunkuyar da kanta ƙasa tayi ta shinga wasa da hannunta,gefe na zuciyarta kuma tana jin wata nutsuwa na ratsa zuciyarta da gangar jikinta,a dukkan lkcn da tayi arba dashi tana jin wani different feelings a kansa,tasha zama tayi tunanin mene hakan mene yasa take jin wannan yanayin game dashi amma ta gagara sanin dalili,tana son ƙara kallonsa amma sam ba zata juri ganin abinda take gani a cikin idanunsa ba,ɗan tsaki kaɗan yaja kafin ya sauke numfashi mai ƙarfin kaske,cikin nutsuwa ya juya tare da nufar wata haɗaɗɗiyar mota kirar ferari,har yayi nisa sai kuma ya tsaya,ba tare daya juyowa ba yace.


"follow me"yana faɗin hakan ya buɗe side ɗin drever tare da zama a ciki yana jiran ƙara suwarta,ta daɗe a tsaye kafin ta fara takawa zuwa wajan motar jiki a sanyaye ta buɗe side ɗin mai zaman banza ta zauna,lumshe idanunta tayi tare da cure jikinta waje guda ta shiga sauke ajjiyar zuciya,ba tare daya kulata ba yayiwa motar ke tare da fice daga cikin masarautar gaba ɗaya.


Kasan cewarsa ƙwararre a harkar dreving yasa cikin nutsuwa yake murza kan motar hankalinsa ƙwance,tym to tym yakan ɗan lumshe idanunsa sabida daddaɗar fresh air ɗin dake kaɗawa a kan titi wacce take bada wani sanyi na musamman,sanyi ne wanda baisa takura a jiki,hasalima saidai kaji nutsuwa tazu masa,ƙara lumshe idanunsa yayi tare dajan motar da gudu domin bai saba dreving a hankali ba,a zahirin gsky dreving kawai yake amma hankalinsa nakanta musamman yadda yake hangota ta gefen idanunsa ta cure waje guda tamkar maijin sanyi,bai taɓa waiting time a kan mace ba,bare har ya zauna yayi tunaninta,some time yanawa mace kallon mace mai rauni wanda damuwarsu ke bayyana a fili,tabbas mace abin tausayice duba da yadda maza ke amfani da rauninsu hatta kai ga sun cusa masu wani baƙin ciki da kuma ƙunci a zuciyarsu,yana jin tausayin mace baya da burin wulaƙanta mata,hakan yasa bai taɓa jin wani feeling akan kowa wacce mace, bare harya ɗarsawa zuciyarsa wani abu game da ita.
Amma yau an waye gari tunaninta ya tsaya masa a zuciya,yayinda yake jinta a dukkan wata gaba ta sassan jikinsa,yana jinta sosai a jikinta,bai san mene hakan ba,bai kuma san tayaya hakan ya kasance ba,bashi da burin yin wata soyayya ga wata macen bare under age like her yafi yadda cewa kawai tausayinta ya keji,amma kuma yawan tunaninta da yake na mene?wannan shine abinda ya faɗu masa a yanzu,a karo na biyu ya taɓe baki haɗi da cije lips ɗinsa na ƙasa,cikin zazzaƙar muryarsa mai sanyin gaske a bayyane yace.


"We have a the same ring that why i'm always think about her nothing else"

Tunawa da yayi tana cikin motar yasa shi haɗe ransa tamkar bashi yayi magana yanzu ba,hannunsa yasa a hankali tare da turashi cikin tulin sumar kansa ya hargitsa,cikin yanayin mood ɗin daya samu kansa ya sauke wata sassanyar ajjiyar zuciyar tare da fesar da wata zazzafar iska ta cikin bakinsa.


Dukkan yadda zuciyarta take muradi da kuma ƙwaɗayin ƙara ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta kasa bata dama sabida wani irin bugawa da ƙirjinta yake very past tamkar wacce ta shekara tana gudu,ƙara haɗe jikinta tayi waje guda tare tura fuskarta tsakiyar cinyoyinta,wasu taƙwayen hawaye ne suka shiga sauka daga cikin idanunta,da saurin ta sanya wani ta toshe bakinta dan ba taso ya fahimci halinda take cikin bare yayi tunanin wani abu a ransa,amma zamanta tare dashi tamkar takura ne da kuma hana sukune,a dukkan lkcn da sukayi kusa da juna tana ji tamkar su shekara a hakan,sabida sanyi da nutsuwar da take samu a garesa,amma ƙwarjinsa yake hanata sauke uwa uba kuma wani magaɗisu dake fituwa cikin idanunsa,ba zata iya jure haɗa idanu dashi,tabbas idan aka

8 / 38