THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   33 / 38

96K to 99K   out of 111.1K words

zauna kan wani stool kana ya zubawa mayukan wajan idanu.
daga ƙarshe ya ɗauki wani lotion mai ƙamshi wanda ya san bazai masa illa a saman fatarsa ba.
a hankali yake murza lotion ɗin a saman fresh chocolate skin ɗinsa,yana gamawa ya ɗauki comp ya fara gyara sumar kansa.
kana ya shafa wasu lafiyayyun mayuka masu ƙyan gske.
wani parfume ya fesa wanda ya kasance body spray.
yana gamawa ya ƙarasa gefen mamakin royal bed ɗin mamaki yay ganin wata red ɗin jallabiya mai taushin gaske a saman bed ɗin.

ɗauka yay ya warwareta taɓe baki yay yana mamakin komai sai an sanya abunda zai nuna na sarauta ne,sosai jallabiyar tayi masa ƙyau kasan cewarfa red saita haska chocolate skin ɗinsa.

lumshe idanu yay sabisa ƙamshi jallabiyar da kuma taushinta,hannayensa ya zura cikin aljihun jallabiyar kana ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar yana tunanin wani abu.

yana nan tsaye yaji ana knoking door ɗin bedroom wajan 3minutes kenan ana buga ƙofar cikin ɗan hasala yace.

"in"

A tsorace Meyrah ta shigo cikin bedroom ɗin,kasa kallonsa tayi sabida wani ƙwarjini da yay mata ga kuma wani sahihin ƙamshi da take fita jikinsa.

zama yay a gefen ɗin tare da jawo wayarsa,cikin nutsuwa ya fara danna password ɗin dake wayar cikin manyan ha rufar ya rubuta RUHINA yana rubutawa wayarta buɗe take makeken photonta ya bai yana cikin wata orange ɗin abaya da alama lkcn azumi ne,domin ta ɗan faɗa haka kuma ya ƙarawa fuskarta ƙyau.
pink lips ɗinta ya zubawa idanu gani sai sharning suke gaba ɗaya ta jiƙasu da yawo.
lumshe idanu yay sabida tsigar jikinsa da yaji yana tashi.

sosai ta shagala da kallonsa,mamakin girman kai da kuma miskilancinsa take,duk da cewa sarauta ba ƙarya bace amma shi nasa na dabanne.
komai cikin shanƙamshi yake yinsa.
numfashi ta sauke tace.

"Allah ya taimake ya ƙara maka lafiya daman Abbune yace nazo nai maka sallama zani gida"

saukar muryarta ya sanyashi ware fitinannun idanunsa wanda suka soma janye sabida wani hurt feeling da yaji yana kamasa.
ɗan ware manyan fararan idanunsa yay a kanta tare da juya eyes ball ɗinsa.
shi yama manta da cewa an shigo cikin bedroom.
taɓe yay ganin tana sunne kai a ƙasa.

kamar mara lafiya haka ya buɗe bakinsa yace.

"your accout details"

ya faɗa tamkar wanda akaiwa dolen magana,wata farar paper ya ta ɗauko a jaka ta rubuta masa,kana ta miƙa masa.
bashi da alamar karɓa hakan ya sanya tace.

"gashi"

ya tsuna fuska yay still kuma bai amsa taba,yana ta danne danne a waya tana zaunw taji notification a wayarsa dubawa tayi nan taka alart ɗin kuɗi na kusan 1.5m a accout ɗinta tana duba sunan wanda ya turo taga ansa MALEEK BILYAM BILHAS.
kanta a ƙasa tace.

"Wannan kuɗinfa? kuma yay yawa ai"

ƙwaciya yay akan bed ɗin hakan ya sanya ƙafafunaa bai yana,ƙaurinsa ta zubawa idanu gani ko ina gashi ne ƙwance sai sheƙi suke gwanin sha'awa a karo na uku kenan daya ƙara shiga ranta fiye dako wanne lkc,wajan 5minute yana ƙwance yana latsa waya harya manna wayar saman kunansa kana yace.

"kee mene kike kije kiyi using dashi na weeding"

da mamaki rashin ko in kula ɗinsa take kallonsa.
murya na ɗan rawa tace.

"Allah yaja da ranka ya ƙara lafiya ina gdy"

da hannu yay mata alama tace tana takurasa,tana fita yace.

"eyee ango ne kai ashe"

ya faɗa can ƙasan maƙoshi,shuru yay yana sauraran wanda suke maganar sai kuma ya mirgina tsakiyar gadon tare da rungomw pillow yace.

"eyee Abbune ya zaɓa,amma dole zangi attending bikinsa,wace take maka shagwaɓa gefe ko amaryarce?"

haka dai suke wayar wacce Maleek yaji daɗinta sosai kuma ya tabbatarwa da abokin nasa cewa gobe yana tafe tunda jibi bikin nasa,daga nan sukai sallama.

jin ana kiran salla ne ya sanyashi miƙewa tare da ɗaukar alƙyabba ya sanya a jikinsa tare da rawanin wanda yay masifar yi masa ƙyau ya fito a cikakken sarkinsa mai taƙama da iko,kuɗi,mulki,ilimi,uwa uba izza a haka ya ƙarasa babban parlou'n.


Cikin ɓacin rai Mai martaba Khalid ya kalli Lil prince yace.

"ka haukace ne,ni kake tunanin zan baka wannan kuɗaɗan masu yawa,nima wacce take ban kuɗin ta daina sabisa tsafin ya karye"

Kallonsa Lil prince yay cikin mamaki yace.

"Ba zaka banba ko? to shikenan wallahi saina ƙarar da kuɗinka gaba ɗaya"

hannu ya ɗaga sai sauke masa mari yay sauri riƙe hannun nasa tare da faɗin.

"tab nine zaka mara? haba Daddy nifa uhmmm"

"idan na mareka zaka ramane ne,niba matsayin uba nake gareka ba...?"


wani dake shiguwa cikin parlour yay saurin faɗin.

"Eh tabbas bakai ne asalin mahaifin Najeyb ba...
*77-78*




Gaba ɗayansu suka juya domin ganin me maganar a nan sukaci karo da Chiroma,wanda hake shiguwa cikin parlour.
Kallonsa yay ba tare da yace komai ba,shi kuma Chiroma yaci gaba da faɗin.

"Baka taɓa tunanin mene ya sanya a kullum a kuma koda yaushe yake maka biyayya a lkcn daka buƙaci wani abunba?baka taɓa tunanin mene ya sanya fulanin sura bata taɓa haihuwa ba ko?baka taɓa tunanin mene ya sanya kake ciwon ciki na wasu lukuta ba?"

Cikin wani irin hali mara fassaruwa Mai martaba Khalid yake kallon Chiroma,baya son yay wata tambayar da zata tabbatar masa abinda Chiroman yake faɗi gsky ne,baya buƙata yaji wani mummunar labari dan gane da Lil prince ɗin.
yasan ya tafka kurakurai masu yawan gaske amma hakan bazai sanya a jarabcesa da ɗan shege a gidansa ba domin bazai iya jurewa ba.
tun ba'aje ko ina ba ya fara ladamar kasan cewaraa mai son zuciya,zalunci,haɗama,da kuma tauye haƙƙin talakawansa.
yay ladamar hakan kuma a koda yaushe a ko wanne lkcn tunanin yadda zaije ya nemi ya fiyar Sarki Maleek yake,amma kunya ta hanashi hakan gani yake kamar bazai saurareshi ba,gani yake da zarar ya faɗa masa shine silar lalacewar rayuwar to shima zai nemi fansa a hakan,duk da cewa sun riƙa sun ɗauki fansar ta hanyar dabai taɓa zato ba.
bai taɓa tunanin aƙwai ranar da zata zo har wani ya samu damar ƙwace mulkin dake hannunsa.
gaba ɗaya idanun sane sukai jaa sabida tsananin tashin hankali cikin dauriya yace.

"Nasan zaka iya faɗin komai a kan ka huce abinda nai maka,amma zanso koda abinda zaka faɗa gsky ne kayi hqr da faɗin domin bazan iya jurewa ba,kada ka faɗin abinda zai tar watsamin zuciyata"

kallonsa Chiroma yay a lkcn da yaji wani tausayinsa ya kamashi,amma yaza mana dole ya faɗa masa gsky har sai yau shene za'a ci gaba da cutarsa ta wannan dalilin?gyara tsaiwarsa yay kana yace.


"dani dakai mu dika munyi babban kuskure a rayuwarmu,amma faɗa maka gsky abinda yake ɓoye shine mafita,tabbas Lil prince ba ɗanka bane,ba kuma kaine ka bada ƙwan halittarsa ba,ba manininka ne yay aiki wajan samuwaraa ba,Najeyb ba ɗanka bane ba kuma kaine ka haifesa ba"

Ba Mai martaba Khalid ba har Lil prince saida ya girgiza dajin wannan magana ta Chiroma,cikin tashin hankali ya saki wayar hannunsa tare da matsuwa kusan Chiroma murya na rawa yace.

"Dan Allah ka gayamin gsky kada ka shegantani bayan kowa yasan cewa Daddy shine mahaifina,kada ka bawa maƙiyana damar da zasu wulaƙantani,kada kace ni shegene dan Allah kada ka aibatani,kaza zafi da raɗaɗin da mutum ya keji aduk lkcn da ake shirin sheganta shi,dan Allah ka gayamin gsky na ruɗe kaina ya kulle please"

ɗauke kai Chiroma yay tare da sauke ajjiyar zuciya cikin son ƙwantar masu da hankali yace.

"aikai baka da maƙiya idanma aƙwai to basu bai yana kansu ba,kaine dai kake nufin wasu da sharri domin har zuwa lkcn da kazo nan baka saduda ba,kuma maƙiyan da kake magana ai sun daɗe da sanin wannan maganar kaga koda basu kawo hujjar da zata sanya a bawa Sarki Maleek kujera ba,da zarar sin faɗin wannan ɓoyayyan sirrin kasan tun daga nan za'a shafe babunka akan magnar mulkar wannan gari na bilhas,tabbas wanda kake tunanin shine mahaifin naka ba shi bane,haka kuma wanda kake wulaƙantawa a gaban kowa ake ci masa ZARAFI shine garkuwanka shine farin cikinka shine kuma jin daɗinka"

gaba ɗaya suka ɗago kai suka kallesa cikin wani sabon tashin hankalin da suka riski kansu suka haɗa baki wajan faɗin.

"Wanene?"

kafinsu rufe baki anyi sallama ta ƙofar parlour kana kuma aka shigo.

a mamagance Mai martaba Khalid yake kallonsa cikin fitar haiyaci da kuma sarewa da jin daɗi yace.

"Waziri!!" ya faɗa cikin ɗaga murya da kuma mamakin abin domim koda akace masa wani bai taɓa kawowa shine ba,Lil prince kam da sauri ya ɗauke idanunsa tare da zubewa wajan ya rushe da kukan tausayin rayuwarsa da kuma kunyar abinda yaywa Mahaifin nasa.

"Mene yasa ka zaɓin hakan?mene yasa ka zaɓi kayi ta rayya da matana,kayi hakan domin ka ruguzamin farin ciki ko kuma mene gayamin?"

Mai martaba ya ƙarasa faɗin hakan idanumsa na zubda ƙwalla.

juyawa Waziri yayi,yayinda shima yake tsiyayar da ruwan hawaye,babu shakka wannan ranar yake tsoro ranar da Magaji zan san wawtar da yake aikatawa garesa,cikin ƙasa da murya yace.

"Banine na zaɓi ta rayya da matanka ba,itace ta zaɓi yin hakan dani,domin ni bana nufin kowa da sharri,a lkcn data fahimci kaine baka haihuwa ba itaba,shiya sanya hankalinta ta dashi domin burinta bai huce taga ta samu ɗa ba,wanda zai mulki garin bilhas yay mulki dakai kanka bakai irinsa ba,ganin bata da wata mafita shiya sanya wata rana ta zubamin ƙwaya a cikin lemo bayan ta kirani,nidai daga nan bansan komai ba sai farkawa nayi na ganta ƙwance a gado kusa dani,sosai nai kuka da kuma baƙin cikin abinda ta sanya nayi haka kuma na fara neman yafiyar ubangiji.
babu jimawa naji ance fulani ta samu ciki na shiga tashin hankali ba kaɗan ba,hakan ta sanya naje na sameta babu musu tacemin ƙwarai cikinane,amma a zahiri zai tashi cikinka,ganin bana da wata hujja zanyi musu da ita na amince mata,haka taci gaba rainon ciki a lkcn nima matana tana da ciki,kusan a lkcn guda suka haihu yayinda Maleek ya basu tazarar wajan shekara guda.
abu na gama a lkcn da Waziri na zamanin Sarki Sudaid ya ɗauki Maleek zuwa sashin a lkcn nima na ɗauki ɗana Imran nakai wannan sashen,domin na riga nasan mugun ƙulli da aka shirya a kansu,nasan kuma da zarar an fahimci Maleek na raye za'a farar neman yadda za'ai a rabashi da ransa,shiya saka na zaɓi taimakonsa ta hanyar dasaukar da ran tilon ɗana Imran,inaji ina gani aka kaishe rami ba tare da naje nagansa ba.
washe gari ranar da yamma shine nace ɗana Imran ya ɓata wanna hanyar ta sanya babu wanda ya tambayi ina yarona yake,kuma mene ya sanya ba'a gawar Maleek ba.
Kai Lil prince da yawan lkcn kana ganina tare mahaifiyarka kuma babu abinda yake haɗamu sai faɗa da nake mata akan tana bari ana kassara rayuwarka haka kawai,ta mareka a gaban idanuna wanda dalilin ka ƙara jin haushina,nan ita kuma hukuntaka tayi bisa rashin kunya da kayiwa Mahaifinka.
komai naka na sani ina sane dashi haka kuma bana guyan bayan ka mulki wannan garin sabida ba zaka taɓa a dalci ba,kana da tari zunubai a kanka,kana da gidan giya wato Night club wanda shi kansa Mai martabar bai san dashi ba,wanda a yanzu munyi magana da Sarki Maleek yace a rugujesa"


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine kawai abinda Chiroma yake faɗa domin shi da yawa bai san haka abin yake ba.

Lil prince kuma kecewa yay da kuka tare da rarrafuwa ya riƙe ƙafar Waziri haɗi da kifa kansa a ƙafar sai rusar kuka yake tamkar zai rasa ransa.

sunkuyawa Waziri ya miƙar dashi tsaye tare da rungomesa jikinaa yana jin soyayyarsa na ratsa zuciyarsa,sosai yake so da ƙaunar yaron nasa.
bayan ya fara bubbugawa tare da faɗin.

"baka da wani laifi Najeyb soyayyace ta kuma tarin ƙauna haɗi da sangarta da akai maka shiyasa rayuwanka ya lalace haka,ina fata ka zama kamili kuma shiryayye kamar ɗan uwanka Maleek,bashi da nufin cutar dakai haka kuma kullum cikin ƙaunarka yake saɓanin kai daka tsanesa,kayi shuru haka nan kuma ka nemi gafarar ubangiji domin shiɗin mai gafara ne ga dukkan bayinsa,kaje ka nemi yafiya ga dukkan matan daka zalunta zaika zauna da kowa lafiya kaji zuciyar tayi sauƙi ka samu lisimana a cikin ranka maza sharw hawayenka kuma ka maida kayannan part ɗinka domin babu batun wata tafiya da zakai zuwa istanbul kaji ko"

cikin kuka Lil prince ya ƙara rungome mahaifin nasa tare da faɗin.

"Na muzantaka,nayi maka rashi ɗa'a kana kuma na wulaƙan taka bisa rashi sanin abinda yake a duhu ka gafarceni"


"babu komai ban taɓa riƙonka ba,sai dai inajin baƙij cikin yadda kake rayuwar kamar dabba,babu ladabi bare biyayya,kuma babu addini haka kake faɗawa dukkan wata ƴar macen da tayi maka,na yafe maka ina fata zaka sauya?"

kaiya jijjina kana kuma ya miƙe tsaye ya nufi hanyar fita harya tsaya sai kuma yay ficewarsa kai tsaye part ɗin Mahaifitarsa Fulani kilishi ya nufa.
yana zuwa ya sameta zaune akan sallaya a gabanta ya zauna,ya labarta mata dukkan abinda ya faru kana kuma yace ta ruguza masa rayuwa akan son zuciyarta,dukkan wata uwa ta gari baza tai haka ga ɗan data haifa ba.
yana faɗin haka nan yay ficewar kuka ta fara sabida sosai tai ladamar abinda ta akaita ga babu kuɗin babu mulki gata tuzarta a cikin masarauta.

Cikin nutsuwa Sarki Maleek yake tafiya shida Abbunsa yayinda wasu fadawa basu yawa suka rufesu,a wanan karan baice masu komai ba sabida tafasar da zuciyarsa keyi masa.
cikin isa da izza da kuma sallar sarauta haɗi da kuzari yake taka ƙafafunsa yana tafe yana ɗan rufe jikinsa da lafityayyiyar alƙyabbar dake jikinsa,sosai iska take kaɗawa garin yay duhu hakan ta tabbatar da hadirin dake ƙwance ne yake ƙoƙarin tashi.
lumshe idanunsa yay sabida ƙamshin ƙasar daya daki hancinsa,ɗan taune jajayen laɓɓansa yay tare da ware idanunsa sabida saukar ɗigon ruwan da yani a kan hancinsa,hakan ya tabbatar masa da cewa yayyafi aka fara.
suna shige sashin Mai babban ɗakin ruwan na kecewa da saurin fadawan suka koma gefe da gefen ƴar rumfar dake sashin.
a nan parlour suka tarar da Mai babban ɗaki tare da Khamis da kuma Kuyanga Kulsum da Hadima Kaltume suna jera abinci a saman danning table.
akan wata luntsummiyar ladduma mai taushin gaske ya zauna tare da tanƙwashe ƙafafunsa.
hakan kuma da yayne ya nuna masu cewa baya ra'ayin zaman danning ɗin,nan Mai babban ɗaki ta bada umarnin gaba ɗaya su ƙwasu abincin zuwa wajansa.
lkc kaɗan suka cika gabansa da kaya abincin kala-kala haɗi kuma da kayan itatuwa masu gina jiki.
zama sukayi tare da fara cin abincin ganin yaƙi sanya komai cikinsa ya sanya Mai babban ɗaki faɗin.

"mene kakeso naga kamar babu abinda yay maka a nan"

ɗan ya mutsa fuska yay haɗi da ware idanunsa ya saukesu a fuskar Abbu,murmushi kawai Abbu yay ba tare da yace komai ba.
jinjina kai Mai babban ɗaki tayi tana mamaki halin irinna Maleek ɗin babu inda yabar mahaifinsa komai nasu iri ɗaya ne (idan kuna buƙatar kuji rayuwar da Mahaifin Maleek yay a masarautar bilhas ku nemi littafin *IZZAR SO*)

Saida Abbu ya gama cin amincinsa kana ya jawo wata ƙwarya da aka dama dakakkiyar fura wacce taji ciƙwi da zuma a hankali ya sanya ludayin ya fara juya furar sabida ta fara daskarewa sabida sanyin da yay mata yawa.
ɗebowa yay hakan ya sanya Maleek ɗin buɗe bakinsa ya amshi furar,daɗi da kuma garɗin haɗi da sanyin da yajine ya sanyasa lumshe idanunsa tare da fiddo da tongue ɗinsa ya lashe gefen lips ɗinsa inda furar ta maƙale.
sosai yasha furar tare da cin ƙwaɗom zugalan da yaji tumatir da lemon tsami,kana ya shanye bottle ɗin ruwa mai sanyin gaske.
lumshe idanu yay lkcn da yaji sanyin ruwan na ratsa dukkan wata jijiya ta jikinsa,sosai sanyin ruwan yay masa daɗi cikin maƙoshinsa.
gefe guda kuma yana sauraran ruwan saman da ake kamar da baki ƙwarya,tsaɓar ruwan ko gudunsa ba'a ji sai dai shuuuuu kamar ana zuba wani abu.
miƙewa tsaye yay tare da kallon Abbun nasa cikin wata kasalalliyar murya yace.

"Insha Allah gobe zanbi jirgin safe zuwa taron ɗaurin aure kasamin albarka Abbu"

ya faɗa yana ɗan murza saitin zuciyar dake gudu tamkar zata faso ƙirjinsa.
shuru Abbu yay shima yana jin babu daɗi a ransa,da ace yana da iko da kuma damar da zai gano yarinyar da Maleek yake so babu shakka da ayau za'a ɗaura masa aure da ita.
sosai yake jin matsanancin tausayinsa a cikin zuciyarsa,ganin yadda soyayya take fatali da zuciyarsa duk ya rame amma duk da hakan yaƙi bari rauninsa ya bai yana.
hakan kuma ba ƙaramin illa zai masa,kasan cewarsa mutum mai zurfin cikin da rashin son a damesa ya sanya Abbun bai iya ce masa komai sai numfashi da yaja yace.

"Amma kasan cewa kaima a jibin za'a ɗaura maka naka auren,mene mutane zasu ce idan su kaga baka wajan,sannan idan aka kawo amaryar me zamu ce mata Maleek?"

Ware hannayensa yay tare da kamo gefe da gefen alƙyabbar dake jikinsa,a hankali ya sauke ajjiyar zuciya tare da ɗan murza daimond ring ɗin dake manne a saman yatsansa.
cikin san kawar da damuwar dake ransa,ya juya ya kalli Abbun nasa sai kuma ya kau da kansa gefe cikin murya mai sanyin gaske yace.

"zuwa wajan bikinsa yana da muhimmanci a gareni,kuma na ɗauki alƙwari tun kafin zuwan rana,shi ɗaurin auren ai basai ina nan,ita kuma wacce kake magana a kanta a zan dawo gidanne kafin nan a gyara part ɗin da zan zauna"

yana faɗin hakan ya juya abinsa kai tsaye part ɗin daya shiga ɗazu nan ya nufa,yana zuwa yasa key ya rufe ƙofar,alƙybbar jikinsa ya zare ya ɗura a saman wardrope,kana ya zare jallabiyar itama ya ajjiya ya rage daga shi sai boxer.

cikin nutsuwa ya ƙwanta saman makeken royal bed ɗin dake bedroom ɗin,a hankali ya mirgina yay rufda ciki tare da rungome pillow'n dake hannunsa.

runtsa idanunsa yay sosai tare da sanya hannu ya dafe saman mararsa dake murɗa masa alamar zatai ciwo.
ƙara manne marar yay da hannunsa tare da sakin ƴar siririyar ƙara,a hankali ya lumshe idanunsa kozai samu bacci ya ɗaukesa amma ciwo da mararsa take masa ya sanya idanunsa suka ƙeƙashe.
miƙewa yay kana ya nufi hanyar da zata sadashi da bathroom.

a can parlour kam da idanu sukabi bayansa,saida ya shige part ɗin sannan Mai babban ɗaki ta sauke ajjiyar zuciya tare da kallon Abbu tace.

"anya ba za'a fasa wannan auren ba?yaro duk yabi ya lalace akan soyayya?jibi yadda ya rame akan rashin wacce bashi da tabbacin tana raye wai yaya za'a ɓulluwa wannan lamarin ne?"

numfashi Abbu ya sauke kana ya gyara zama yace "bamu da wata mafita face mu bisa da addu'a,amma wannan aurenne kaɗai zai saka ya manta da batun waccen yarinyar,ki barshi ko yana nan ko baya nan babu shakka za'a ɗaura masa aure da Meyrah"

yana faɗin hakan ya miƙe

33 / 38