Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
na gabatar.
ban tabbatar da abinba saida naganni tsaye a gaban gawar Sarki Sudais shida matarsa Omeshi sai kuma gawar ƙaramin yaro a tsakiya,sosai na shiga wani tashin hankalin sabida a sanina Yarima yana wajena ga kuma wata gawa dana gani.
haka aka buga tambarin masarauta tare da shela cikin abinda baifi awa guda ba,garin bilhas ya ɗauki kuke-kuke mutane jama'a koda ina zuwa ake manyan mutane da kuma Sarakuna da gari daban-daban.
haka akai masu wanka aka kaisu yaron kuma a cikin gida mata sukai masa shida mahaifiyarsa hakan tasa babu wanda ya gansa sai a cikin makara.
a ranar da akai sadakar baƙwai a wannan ranar aka naɗa Mai martaba Khalid a matsayin sarki,Mai martaba Khalid kuma ya kasance wa ga mahaifin Sarki Sudais ma'ana yayane wajan Sufrak wanda suka haɗa uba,uwa kuma kowa da tasa.
sosai nai mamakin yadda akai Mai martaba ya samu kayan ɗanin sarki domin babu wanda yasan inda yake sai Sarki Sudais.
tunda wannan abun ya faro da idanuna banga Mai babban ɗaki ba,ashe itama da wata lukutar qaddararce ta sameta ta makanta.
gaba ɗaya dai na rasa mene yakemin daɗi.
a wannan daren rananne kuma kunnuwana suka jiyemin wata babbar magana wacce ta sanya na gigice cikin gaggawa naje na ɗauki Yarima Maleek na goyashi a cikin darenne kuma nabar masarautar bilhas.
daga nan kuma ban sake sani mene yake faruwa ba,saidai a zuciyata na ɗauki niyar bawa Yarima kulawa da kuma gata haɗi ilimi bayan ya gama samun wananne kuma zam dawo dashi a matsayin garkuwar iyayensa wanda zai ɗaukar masu fansar abinda ya sanya nabar masarautar.
sosai na shiga duniya da Yarima nayi dako nayi zubda shara haka kuma nayi aikatau duk danna kula da Yarima,ina ƙwana banci domin naga na inganta rayuwarsa.
daga nan na sanyashi makaranta islamiya da buko,sosai yake karatu wanda ya bawa kowa mamaki.
shakarunsa goma cif a duniya ya haddace al'kurani cikin farin ciki hukumar makarantar suka bashi kyautar kuɗi masu yawan gaske.
haka na fara juya kuɗin ina business ubangiji kuma ya sanyamin albarka.
shekara na dawowa na zama mai kuɗin gaske a kuma wannan shekarar jama'ar unguwa suka fara zargin Yarima shegena hakan tasa nai mana ticket muka koma Cameroon da zama.
ƙwanci tashi Yarima ya girma ya zama cikakken likita mai zaman gaske ɓangaren Gani wato likitan mata.
sosai ya zama mai kuɗin gaske harya takeni a kuɗi domin har dry yakemin yana ban iya business ba,na kanyi dry domin nasan duk kuɗin hanuna mallakin sane.
Nasan kuna son kuji yaya akai Yarima Maleek yazo masarautar Bilhas a zummar soja? bayan barinmu daga bilhas wajan shekara biyu na dawo a wannan lkcn nayi ɓadda kama na gana da matata wacce ta kasance Jakadiya a wannan lkcn,ita kaɗai na gayawa dukkan abinda yake faruwa kuma na bata number wayata duk yadda tasu na tsaya naga ɗana ƙi nayi.
A wata rana ina zaune a parlour ina duba wasu files naji kiran waya da sauri na ɗaga ciki mamaki dajin muryar matata.
nan ta shaidamin cewa ka sanya a nema maka soja mai kula dakai,sosai nai farin ciki dajin hakan,babu ɓata lkcn naje wajan shugaban sojojin domin na sanshi aiki ya taɓa haɗamu a Cameroon,nan na bai yana masa ƙudirina da ƙyar ya amince,haka na amshi uniform da komai wanda zai nuna shaidar shi cikakken soja ne.
Yarima yana cikin yiwa wata baiwar Allah aikin domin ciro mata baby na sanya a kiramin shi,saida ya gama aikin yazo yana zuwa na shaida masa buƙatata ba tare da tambaya ko kuma musu ba,ya amshi kayan gari na wayewa ya sanya kayan har airport nai masa rakiya domin zuwa bilhas.
idan kun lura tun zuwansa bai taɓa sanya complt uniform ɗin ba,da yawan lkcn kuma idan kun kira sunansa bai fiya amsawa ba sabida yana jin wani iri kasan cewar sunan ba nasa bane.
Maganar fake face kuma bayan na gama shirya komai na tafiya,na samu Oska na shaida masa komai sannan nace ya bani fuskar robar da zatai dai-dai data Yarima Maleek haka ya kawomin na bashi kuɗinsa.
Tsagaitawa yay da maganar kana yay murmushi yace.
"kun girgiza ko? hatta sanya Yarima Maleek a ɗakin duhu da kukai ina sane dashi duk da cewa shiɗin bai gayamin ba,ba kuyi mamakin yadda yake shiga wajan Mai babban ɗaki kai tsaye ba duk da matakan tsaron da yake sashin,dalilin shine wanda yake gadin wajan shine ɗana kuma a wannan lkcn ya riga ya gama sanin komai akan Maleek ɗin ya kukaji wannan bayanin?aƙwai wanda zai girgizako sai nan gama yanzu dai kamar yadda kukace kujera bata jira saidai a jirata toga Yarima Maleek nan yazu domin hawa kujerarsa ta gado"
gaba ɗaya wajan yay shuru wasu kuma hawaye suke gogewa sabida mutuwar Sarki Sudais ta dawo masu sabuwa.
Sarkin fadane ya numfasa yace.
"Allah ya taimaki Sarki Sarakuna ɗan nagada gaba da baya Allah ya ƙara maka lafita da nisan ƙwana matsu a fara ɗani domin lkc naja"
Yarima Maleek dake durƙoshe dafe da kansa yana sauke ajjiyar zuciya,yana jin abun tamkar a mafarki mai yasa rayuwa take masa haka ne?mai yasa qaddara take juyashi ne har haka?mene laifinsa da wannan mafisun suke bibiyar rayuwar mai mene ya sanya za'a ɗura masa mulkin da baya buƙata,mene ya sanya za'a ɗura masa nauyin jama'ar da mazai iya basu haƙƙinsu ba,tayaya zai san wani yaci ko bai ciba.
shikam bazai iya sam baya so baya kuma muradin wannan kujerar ya hqr da ita.
jajayen idanunsa ya ɗaga ya kalli Abbu cikin wata iriyar murya yace.
"Abbuna banso bana buƙata"
cikin sauri Abbu yace.
"bakai kakeso ba,ita Sarautarce take sonka dan haka ko kanaso ko bakaso dolene ka zama Sarkin garin bilhas"
jin abinda Abbun yace ya sanya ya miƙe tsaye jiki a sanyaye ya fara tafiya zuwa wajan kujerar,wani shu'umin murmushi Mai martaba yayi domin yasan babu yadda za'ai Maleek ya zauna a wannan kujerar ba tare da wani abu ya samesa ba,dan haka sam mai dabu da ɗanin nasa ba,dan yasan cewa Lil prince shine magajin wannan kujerar.
a hankali Maleek ya ƙarasa inda kujerar take haka kawai yaji wata faɗuwar gaba tare da tsoran zama akan kujerar ya ɗarsu cikin ransa.
wajan 5minutes yana tsaye shibai zauna ba haka kuma bai juya ba,numfashi mai ƙarfi ya sauke tare da lumshe idanunsa a kuma dai-dai lkcn ya samu nasarar zama akan kujerar.
runtsa idanunsa yay da ƙarfin sabida abinda yaji,gaba ɗaya jikinsane ya fara rawa gargasar jikinsa ta mimmiƙe jijiyoyin kansa suka fito raɗa-raɗa azabar daya kejine ya sanya yay saurin..
NOT FREE IS FOR SALE 08119237616
*9/4/2021*
*Friday*
*7:44*
*NIMCYLUV*
*73-74*
Faɗin "Ya salam"
sai kuma ya ƙara runtsa idanunsa da ƙarfi fiye dana baya,yayinda ya kejin wani sanyi na ratsa saman fatar jikinsa zuwa cikin namansa jikinsa,baki yatsa ya datse teeths ɗinsa da suka ɗan soma ƙara suna bada wani ƙaramin sauti.
wani irin girma yaji kansa yay masa tare dajin laɓɓansa sun masa nauyi fiye da ko wanne lkc,a hankali yaji nutsuwa na ratsa cikin zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,wata izza da gadarace yaji ta saukar masa lkc guda har yana jin sam bazai iya buɗe idanunsa bare da buɗe bakinsa harya samu damar faɗin wani abu.
dukkan yadda ya kejin kansa a wannan lkcn ya huce tunanin dukkan wanda yake wajan,sosai yake jin kansa yay masa girman gaske tamkar wanda aka ɗurawa dutsen dala.
tabbas a wannan lkcn babu abinda yake tunani cikin ransa sai iyayensa,lallai ya tabbatar kuma ya amince Ubangijine kaɗai zai iya tsare bawansa a ko wanne hali,shine kaɗai zai bashi kulawa da kuma kariya,koda wasa kuma ko amafarki mai taɓa tunanin ya haɗa jinin da wata aba sarauta ba,bare harya saka ran zai sama sarki.
Allah buwayi gagara misali kenan,maiyin komai a kuma lkcn dayaso,komai na rayuwa yana da iyaka kuma yana da ƙarshe kamar yadda ƙaddara take da nata lkc'n.
qaddara ta juya rayuwar zuwa baƙin ciki,damuwa,takaici ta kuma sanyashi a halin daya san babu wani ɗan adam daya isa ya fiddashi sai Ubangijin daya nufa abin zai sameshi.
rayuwa kenan kana taka Allah yana tashi kuma ta sane gsky,yasu ace koda sau ɗaya yaga fuskar iyayen nasa,yasu ace ya rayu dasu irin rayuwa ta har abada ɗinnan amma babu yadda zaiyi,zaita ƙoƙarin ganin ya nema masu gafarar Ubangiji.
numfashi yaja a hankali kana kuma ya taune jajayen red lips ɗinsa.
wacce hanya mahaifinsa yabi ya gudanar da mulkinsa har jama'a suke sonsa?tayaya ya iya sauke haƙƙin al'umar da suke kansa?shi sam bayajin zai iya wannan abun kula da al'umma wanda baka isa kasan adadinsu ba ƙaramar masifa bace.
a zahirance sun haifeshi ne kawai amma a yanzu bashi da wani mahaifi kuma jigonsa sama da Abbunsa,shine komai masa haka kuma shine jin daɗinsa da kuma farin cikinsa a koda yaushe.
a hankali kuma cikin nutsuwa ya fara ɗaga lashes ɗin da suke ƙwance samar idanunsa harya samu nasarar ware manyan idanunsa wanda sukai jaa har wani ruwa-ruwa suke sabida damuwar da yake ciki.
kallonsa ya sauke zuwa ga Abbu,inda shima Abbun shi yake kallo aka samu sa'a suka haɗa idanun cikin son ƙarfafa masa quiwa ya jinjjina masa hannu tare dayi masa murmushi.
ƙwaɓe fuska yay tare da langwaɓar dakai,tunawa da yay basu kaɗaine a wajan ba yay saurin dai-dai ta nutsuwarsa tare da haɗe ransa a dole bai son abinda ake ƙoƙarin ɗura masa nauyinsa.
hakan ya ƙara masa kyau sabida wasu bai yanar manyan beauty points ɗinsa,a hankali ya sanya hannunsa ya shafi ƙwantaccen baƙin beard ɗin da yaywa ƙyaƙƙyawar fuskar ƙawanya.
daimond ring ɗinsa ya zuba idanu ganin yana haske pouting lips ɗinsa yay sabida jin zuciyarsa ta buga da ƙarfi wanda yay dai-dai da buɗewar baƙinsa cikin ƙasa da murya yace.
"My Rinaaa whare are you,i was looking for you but i can't found you"
ya faɗa yana mai ƙara taune laɓɓansa wanda ya kejin sun ɗan jige sabida yawon bakinsa daya sauka kan lips ɗin.
Sarkin fada,da sarkin sakar gida ne suka ƙarasu inda yake zaune suna zuwa suka fara ƙoƙarin sanya masa wata lafiyayyiyar alƙyabba.
Mai martana Khalid mai murabus ne yace.
"kafin ai ƙoƙarin ɗurashi bisa wannan kujerar yana da ƙyau shima ya kawo shaidun da zasu sanya ai masa wannan naɗin,kamar yadda aka buƙaci sauran suyi"
"mene kakeci na baka na zuba yanzu nake ƙoƙarin kawo kayan sai kuma kayi saurin tarar numfashina"
cewar Abbu wanda ya faɗa yana ɗan tafa hannayensa guda biyu nan take wasu mutane guda biyu suka shigo ɗaya mace ɗaya namiji,cikin sauri da kuma ɗaga murya haɗi da gigicewa Lil prince yace.
"Meyrah!!"
wani shu'umin murmushi tayi masa haɗe da juya ƙwayan idanunta akan fuskarsa,sosai yay farin cikin ganinta da sauri ya ƙarasu inda take tsaye yace.
"Meyrah bani wannan ring ɗin ko mene kikeso zan maki amma ki bani wannan zoben shine farin cikina da kuma jin daɗina gsky am happy to see kin dawo akan lkcn kafin komai ya ƙaremin"
far tayi da idanunta kana ta sanya hannu ta zaro zoben daga jikin hannunta kamar zata miƙa masa zoben sai kuma tayi saurin baya da hannunta.
da mamaki ya kalleta tare da faɗin.
"bani mana saiki faɗi kuɗin da kikeso na maki matsayin bansar zoben"
dariya tayi kaɗan tace.
"what the think ahaa kana tunanin na dawo ne sabida na baka zoben ai dana baka gwamma nayar a bola"
baki ya saki yace.
"amma mene ya saka hakan bayan kinsan wanene ni da kuma tarayyar dake tsakaninmu"
tako ɗaya biyu tayi zuwa gabansa kana tace.
"ba kayi tunanin yadda na shigo rayuwarka lkc guda ba,shin ba kayi tunanin yadda nasan komai a kanka ba?bakai tunanin yadda ina zuwa nace ina son wannan zoben ba? lallai ƙaramar ƙwaƙwalwa gareka da kuma ƙarancin tunani,nai mamaki yadda koda wasa baka taɓa tuhuma ta da wani abunba,sannan bakai tunanin tunda muke ban taɓa yadda ka kusancan ba? na baka dama a wannan karan ka tambayi dalili"
gaba ɗaya launin idanun sane suka sauya kala wani sabon tashin hankali ya ƙara shigarsa ga kuma baƙin cikin rashin kujerar daya daɗe yana muradi da kuma son mallakarta.
tun yana ƙarami aka sanya masa son mulki cikin zuciyarsa.
cikin wata iriyar murya wacce take nuna zallar damuwar da yake ciki yace.
"why mene ya sanya kika aikata hakan wacece ke?"
"I'm Senat's sister!!"
da sauri yay baya tare da sanya hannu ya dafe kansa sabida da sara masa da yaji yayi lkc guda.
cikin ruɗewa da kuma tashin hankali yace.
"mene yasa kikaimin haka me yasa kika rabi da abinda zai zamemin garkuwa a rayuwata?"
dariya tayi masa.
"tabbas na shigo rayuwarka da niyar ɗaukan fansa,idan nace fansa ina nufin fansar ran ƴar uwata,bana da ƙarfi ko kuma ikon da zan kaika court hakan tasa na hqr bawai dan abin baya damuna ba,aa kuma ina ƙwana ina kuma tashi da tunanin yaya zanyi na ɗauki fansar ran ƴar uwata,haka na tattara komai a gefe harna samu nasarar zuwa Cameroon da niyar karatu,satina guda kenan na ziyarci super market a nan na haɗu da da wannan mutumin.."
ta nuna Abbu kana taci gaba da faɗin.
"nan naji yana waya kuma a ciki naji yana faɗin masarautar bilhas,sosai mai mamaki banyi ƙasa a quiwa ba naje na tambayesa ko yasan wani a masarautar anace masa Lil prince,da mamaki ya kallan yace meme haɗinki dashi,nan na gaya masa komai sabida a ranar da Senat tabar gida ta ajjiye wasiƙa kuma ta rubuta inda zata hakan tasa koda maga gawarta babu wanda nai tunani sai Lil prince,nai yagamin komai na masarautar bayan na gaya masa qudirina,nan shima ya bani labari Yarima Maleek sosai naji tausayinsa hakan tasa na ɗauki niyar taimakonsa,dan haka da niyar abu guda biyu nazo wannan masarautar,wata rana idan baka manta ba kaje kasha giya kazo kana bani labarin irin tsanar da kaiwa Saifu wanda baka san cewa shine Maleek ba,kuma tun kafin nan daman nasa matsayin zobe hannunka domin a sanda naga zoben nasan akwai babban abu a tattare dashi hakan tasa na nemi kabani kai tsaye,yawwa yadda akai nasan inda kake a wannan lkcn shime wannan mutuminne ya faɗamin"
tsayawa tayi da maganar tana ƙara wani murmushi wanda yake ɗauke da mugunta tace.
"nasan zakasu kasan tayaya akai Yarima Maleek ya tsallake tarkon daka kafa masa?,a wannan daren naji komai da kake faɗa sabida a make kake,sosai na shiga tashin hankali bayan bacci ya ɗauke na tashi da sauri na nufi part ɗinsa cikin tsoro sabida babu kowa a lkcn sai masu tsaron ƙofa,a haka harna samu ma ƙarasa part ɗin cikin tashin hankali na shiga parlour'n sabida ganin ƙofar a buɗe tunanina sun riga da sun aikata abinda ka turosu,saidai ina zuwa na same zaune akan dadduma da alama salla ya idar,nan na shaida masa abinda yake faruwa kuma na roƙi alfarmar kada ya ƙwanta a ɗakin,kasan cewar bai son yawan surutu da hayaniya ya sanya ya jinjjina min kansa tare da nunamin hanyar fita daga nan bansa yaya akai ya tseratar da kansa ba".
lumshe idanu Maleek yay lkcn da Meyrah ta gama bada labarin,kana ya waresu akan fuskarta haɗe ta taɓe baki can cikin ransa yace.
"parrot"
a zahiri kuma gyara zama yay tare daya mutsa fuska domin ya fara gajiya da zamansa a kan kujerar,ware red lips ɗinsa yay yace.
"kina fita nima na miƙe kai tsaye bedroom ɗin na nufa na kera manyan pillow kana na lulluba masu barko,ina cikin haka naji ana taɓa ƙofar cikin sauri na shige cikin toilet tare da rufewa na sanya key,a haka naji tafiyarsu har cikin bedroom ɗin nan na leƙa kaina domin har yanzu ban wani tabbatar da abinda kika faɗa,cikin mamaki kam naga wasu manyan mutane gaba ɗaya sun rufe fuskarsa,ina nan tsaye ina leƙesunta ta cc tv camera har suka fiddo da wannan injection ɗin,a tunaninsu sun ɗauka nine hakan ta sanya suka caka allurar kai tsaye suna gamawa sukai waje ba tare da tunanin duba wanda yake ƙwance ba,dana tabbatar sun tafo saina fito a nan naga sirinjin allura cikin sauri na ɗauka kasan cewata babba likita mai zaman kansa ban wani sha wahala gane wacce allura bace,sunsu haukatani irin haukan da wahala mutum ya dawo hayyacinsa,nan na ɗauki sirinjin na adana cikin box ɗita sabida ta zama evedance gareni,washe gari da sassafe ko salla banyi ba nayi wanka tare da al'wala na fice daga cikin masarautar gaba ɗaya,direct Bristol place hotel na shige na kama ɗaki a nan nayi salla,bayan na idar nayi wanka na sauya kayana zuwa dark blue ɗin gezna sabida sanya ƙananun kaya baya tsarina,ina kammalawa naji wayata na ringing nan naga number Abbu a nan ya shaidamin alrdy ya sauka a bilhaa bayan yabi ta Kogi,nan na faɗa masa inda nake harnan hotel ɗin ya saman,yana zuwa shine wannan tazo"
wata ajjiyar zuciya mai ƙarfin gaske sabida jin numfashinsa na fisga dalilin dugun maganar da yayi,kana kuma ya lumshe idanunsa har yanzu itace a ransa yana nanne kawai amma zuciyarsa tana gareta.
baya jin zai iya jure rashinta kusa dashi a koda yaushe a kuma ko wanne lkc yana jin kansa kamar bashi ba,kewarta sa kuma rashin inda zai sameta ya addabi zuciyarsa da kuma gaggar jikinsa.
shuru Lil prince yay saima sunkuyar da kansa yay yayinda yaji wata matsananciyar kunya ta kamashi.
Mai martaba kam mamakine ya kamashi ganin har yanzu babu abinsa ya sami Yarima Maleek duk daya shafe wajan 30minutes zaune akai.
mutumin daya shigo tare da Meyrah ne ya yaye abinda ya rufe fuskarsa dashi,da sauri Mai martaba ya zare idanunsa cikin ɗaga murya yace.
"Dauwas!!"
murmushi Dauwas yay yace "kana mamaki da ganina ko,a zahiri ni yaron bokanka Gilmas ne,amma a baɗini Wannan mutumin na kewa aiki.."ya nuna Abbu kana kuma yace"ka kawo wata yarinyar masarautar nan,kuma ka buƙaci Gilmas ya juyar maka da tunaninta ta yadda zata manta wacece ita,nayi amfani da wannan damarne nima nayi aiki da abinda na koya wajan Gilmas na tura wani aljani jikinta wanda zai bata kariya,a wannan lkcn'ne kuma aljanin ya fara aiki ta hanyar ƙwashe takobi da kuma hular masarautar dukkan abinda take ina ganinta ta cikin allon tsafina,kuna hatta faɗuwar da Yarima Maleek yay a hawan kilishi Gilmas shine sanadi,kuma rashin sanin an bawa Yarima Maleek dokin da mahaifinsa Sudais yafi ƙyauna sama da sauran,muna zuwa bilhas yanzu haka babu inda na tsaya sai lambun da kayan suke barima kaga shaida"yana faɗin hakan ya fita waje babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke sa tsuhuwar aƙwatin..
girgiza kai kawai Abbu yay yace "toya kaji wannan tarkon? bana jaa da mutum idan nasan ban shirya ba,kamar yadda ka hana idanuna bacci na ɗauki alƙwarin nima saina hanaka farin ciki da muradin rai da zuciyarka kuma.."
"dakata malam baka da hurumin da