Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
kuma ya haifeku"
"toke wacce lafiya kike maganane wai muda ba'a gadon asibitin kika ganmu ba"
Miƙewa tayi tace "ina nufin lafiyan da ba zaku iya zama da mace ba,ko mazakutanku bata aiki"
Aida sauri suke miƙe tsaye sabida maganar tazu masu a baza ta,cike da kunya Sufyan yace.
"kekam matar nan bakinki babu linzami sam"
Pillow ta ɗauko zata cillawa Sufyan Tupic yay saurin cafewa kana suka fice daga cikin gidan cike da kunya.
Ita kam faɗi take "Da ubanka Audu kake shine bashi da linzami ba ni ba"
Dry Abba yay jin abinda na neman dawowa kansa,cikin sonya rarrashi mahaiyar fiyar tasa yace.
"ayya Mamu ki daina biye masu fa,kisan yaran yanzu ba kasa fai suke son ana masu maganar aure ba kiyi hqr da halin jokin naki"
Harara ta watsa masa tace.
"kai tafican sakalan wufi banda haka bakai ne zaka zaɓo masu matan auren ba,amma kayi burus da lamarin"ta faɗi hakan tana shigewa ɗakinta bakinta sai kumfa yake.
Shidai hqr kawai yake bata,tana shigewa ɗakinta Abba ya matsu wajan Mom wacce tunda suka fara magana ba tace komai ba,kallonsa tayi kafin tayi magana taji yay sama da ita kamar yarinya dry yay yace.
"en matana ki daina tunani babu,oyyyya muje na samawa little ƙanwa ko ƙani"
Lafewa tayi jikinsa tana shaƙar ƙamshin jikinsa..
A wani yanke na gari Kogi boka Gilmas ne zaune gaban wata tafkekiyar ƙwarya dukkan yadda yasu yaga abinda yake ɓoye a wannan karan kasawa yay.
Cikin tashin hankali ya ƙara watsawa ƙwaryar wani baƙin abu tare dayin wasu surutai mara kan gado.
Madadin yaga fuskokin da yake gani sai wani sihirhintaccen haske ne ya bai yana garesa,cikin fushi da fusata yay wurgi da ƙwaryar tare da miƙewa ya ƙwarara wani mahaukacin ihu mai firgitarwa.
Dauwas dake gabansa yana kallon dukkan abinda yake faruwa yay shuru ba tare da yace komai ba.
Cikin ƙanƙanin lkc wata guguwa mai ƙafin gaske ta cika ɗakin tare da wani irin ihu mai amsa kowwa.
Gaba ɗaya ɗakin ya hargirte da ihuce-ihuce sabida haɗewar muryar boka Gilmas da kuma ta aljanin dake ihu.
Wata girgiza ɗakin yay saiga ƙadon zabgegen ɓaki aljani 👹ya bai yana baki cike da zaƙwa-zaƙwan hqr tare da manyan idanu kamar zasu faɗo waje,sai faka-fakan kunnuwa wanda a ƙalla zasu kai wajan ashirin a jikin aljanin.
Cikin wata murya mara daɗi da kuma cika kunne al'janin yace.
"Tafi ƙarfina wallahi tafi ƙarfi,ina ƙoƙarin shigewa jikinta a koda yaushe,amma burinta bai huce ta ƙonani da manyan addu'oin da suke matsayin gariya gareta,ya shugaban ka yafeni tunda kaga na dawo tabbas abin yafi ƙarfina kuma....."
Bai ƙarasa maganar ba yaji boka Gilmas ya daɓa masa wuƙar tsafi cikin tsakiyan kansa.
Wata ƙarar a zaɓa aljanin yay kafin yay girgiza cikin rashin sa'a bakin ya fara feshin wuta...
Masarautar Bilhas.
Yau ƙwanan Saifu biyar cif cikin ɗakin duhu dukkan wata wahala da kake tunanin mutum mutum zai shashi yasha.
Abinka da mai duhun fata hakan ya taimakawa fatar tasa wajan yin baƙi tare daya mutsewa kaɗan.
Sai biyu ake bashi abinci shima wata ƙaddararriyar indome ake bashi da ƙwai guda ɗaya.
Da farko ƙincin abincin yay sai daga ƙarshe yake karɓa yaci iya ƙwan.
Ganin da gaske yunwa zatai masa illane ya sanya yake cin abincin tare da shan ruwan ƙofi guda.
Daga ƙarshe sai aka ƙwashe wayoyinsa,dukkan yadda damuwa tai masa yawa baya taɓa nunawa ko a haka yaci gaba da kaiwa Allah kukansa.
Sufyanma wajan ƙwanansa uku da zuwa Bilhas yay try numbersa harya gaji,gashi bashi da details ɗinsa bare yasan ina yake zaune.
Wanka yay tare da shiryawa kana ya fito daga cikin Bristol place hotel ya nufi compound na hotel ɗin ya shiga motarsa kasan cewar da ita yazu.
Yana ƙoƙarin fita yaga wasu manyan motoci na gidan sarauta na shigowa leƙo da kansa waje yay sabida gajiya da tsaiwa da yayi,karaf idanunsa ya haɗu dana Lil prince,shi Sufyan abun kusan dry ya bashi ganin yadda Lil prince ya zuba masa idanu.
Shikam Lil prince yana kallon Sufyan ɗinne sabida mugun kama da yay masa da Zarinansa,yana ƙoƙarin fitowa a motar Sufyan na ficewa daga hotel ɗin...
Da sauri ta farka daga baccin da take,kanta taji yay mata suwal babu nauyi,cike da mamaki take kallon ɗakin da take.
Baki ta buɗe tace.
"MOM kina inane?
Shurun da taji ne ya sanya ta miƙe ta nufi waje.
Babu kowa dan haka taci gaba da tafiya zuciyarta fal tsoro tunda take bata taɓa ganin gida mai girmansa ba.
Kuka ta fara ƙasa² still kuma tana ci gaba da tafiya,saida tayi tafiya mai tsayin gaske sannan ta iso wata tafkekiyar ƙofa ita babu kowa da alama suna salla ne.
Kai tsaye waje ta nufa wanda kuma fitar na nufin barinta masarautar bilhas.
Titi ne fetal sai abeban hawa da suketa shigewa,haushin karan data jini ya sanya tayi watsi data kalmanta ta ruga da gudu.
Sosai take gudu saida ta shanye titin tas,hron aketa yi mata kasan cewar tsakiyan titi take,da ƙyar ta ɗago kanta ta kalli motar kafin a hankali idanunta ya rufe ta kifa kan motar.
Cikin ƙaraji da zaucewa haɗi da zallar mamaki Sufyan yace...
_THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE 200 DUBA WANNAN NUMBER TA WASAPP IDAN KANA SO 08119237616_
*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
*59-60*
Yace "little sis"
Yana faɗin hakan yay saurin kashe motar tare da muɗe murfin motar ya fito,masu sauran abun hawa ya bawa hqr kasan cewar a tsakiyan yay parking motar masa,yana zuwa ya sanya duk hannunsa dan har yanzu mai gama tabbatar da abinda idanunsa suka gani ba,ɗaukota yay gaba ɗaya tare da birnitota zuwa ƙirjinsa,wata ajjiyar zuciya ya sauke tare da rungometa jikinsa,tabbas zuwansa bilhas nasara ce kuma rabon yaga tilon ƙanwarsu ce,yana zuwa ya buɗe site ɗin mai zaman banza ya shimfiɗeta kana ya nufi side ɗin drever ya shiga yaywa motar key da gudu ya joya zuwa hotel ɗin.
A hargitse ya farka daga nauyayyen baccin asar ɗin daya ɗaukesa,idanunsa da sukai masa nauyi ya ƙara lumshewa a sanyaye ya miƙa hannunsa ya ɗura bisa saitin zuciyarsa wacce take bugawa da ƙarfin gaske,harshensa ya fiddo kaɗan tare da lasar gefen lips ɗinsa,kana ya sanya jerarrun fararan teeth ɗinsa ya datse jajayen laɓɓanda wanda sukai jaa sabida yawan taunesu da yeke akai-akai.
Wani zazzafan numfashi ya fesar,ya rasa mai yawa yake yawan mafarki da ita a ƴan wannan lukutan,shinko tana cikin matsala ne? Sannan waye ya ɗauketa ya fita da ita daga masarautar,ƙara matse saitin zuciyarsa yay tare da mirginawa yay flat a ƴar ƙaramar tabarmar kabar da yake kai a ƙwance.
Ƙwarai babu koko ƙwanta ko kuma wasi-wasi soyayyarta tayi masa mugun kamo,wanda shi kansa bai san da hakan ba,rana rayuwa da zallar soyayyarta wacce tayi ƙwance saman zuciyarsa,mai san yaya akai baya iya jure dukkan abinda ya shafeta ba,ta zama jinin jikinsa wanda idan babu shi tabbas dai² yake da ɗaukewar numfashinsa,hakan na nufin duk sanda ya rasa Zarina rayuwarsa tana cikin matsala?.
A hankali ya ɗaga eye lashes ɗin idanunsa hakan ya bawa ƙyawawan fararan ƙwayar idanunsa damar bai yana wanda suke janye kaɗan sakamakon baccin daya samu nasarar ɗauketa.
Laɓɓansa ya motsa kaɗan tare da lumshe idanunsa ya saki wani zazzafan numfashi cikin ƙasa da murya mara sauti yace.
"uhmm jini na zama a inda ake samun ishasshen numfashi,haka nan mutum na rayuwa akan taimakon abubuwa biyi,ruwa da iska,babbu shakka zuciyar Saifudeen na bugawa ne dalilin bugawar taki zuciyar...."
Shuru yay ba tare daya ƙarasa magnar ba,wahala lallan nunfashi ya sauke sabida tsayin da maganar tayi masa,ɗan runtsa idanunsa yay kana ya ɗura hannunsa saman mararsa wacce ya kejinta a ɗan kumbure,ya rasa dalilin daya sanya ta tsawaita yi masa ciwo a ɗan lukutan nan..
Lamo yay yana sauke numfashi a hankali yana mai son ƙara tabbatar da kansa abinda ya keji game da ita,babu shakka shi ɗin yana da rauni,raunin da baya tashi sai a kanta,ta zama silar bai yanar rauninsa wa mutane,haka nan tayi nasarar samunsa matsayin masoyi wanda yake hope sunan ya tashi daga masoyi zuwa miji,da yawan lukutana yana zama yay tunanin mene yasa zuciyarsa ba tasu wasu daban ba kuma manya ƴan mata,sai zuciyarsa ta yaudaresa ta haɗashi da soyayyar ƙaramar yarinya mai ƙaranci shekaru,yasu yadda yake da yawan shekaru ya samu mace dai² shi wacce yake da tabbad a kanta na ɗaukewar dukkan buƙatunsa da kuma nauyinsa, amma ya ƙara gasgata maganar nan ta *AGE IS JUST A NUMBER* ita ɗin bai san kalan nata baiwar ba.
A lokaci na farko ta shayar dashi mamaki haka kuma ta ɗauke masa abinda yake damunsa na ɗan wani lkc yana da tabbas wata rana akanta zai rabo da ciwon da yake damunsa.
Kiran sallar asar ne ya dagatar dashi daga dugun tunanin da yake,miƙewa yay tare da ɗaukan raguwar ruwan daya ajjiye,kana ya ƙarasa can gefe da inda yake ya zare wandonsa zuwa ƙasa yay fitsari tare dayin tsarki,wasu tagwayen hawaye ne suka sauko daga cikin idanunsa sosai yake baƙin cikin zamansa a cikin ɗakin duhun,duk da idan da sabo yaci ace ya saba da hurun irin wannan,amma hurun daya yake ciki a yanzu ya shallake nako wanne lkc.
Yana ibada cikin najasa wannan babbar damuwansa,amma Allah ya sani bashi da laifi ko wajan mahaliccinsa wanda suka sashi a nan sune masu wannan lefin.
Da haka ya ƙarasa al'walar kana ya data salla.
Bayan ya idar yaji an buɗe ƙofar baiko motsa ba,bare wanda ya shigo yay tunanin zai juyo ya kallesa.
Wani ƙwanon aka ajjiye a gabansa ƙwanon duk tsatsa,wainar shinkafa ce guda ɗaya sai cinyar kaza ɗaya,sai kuma gorar ruwa mai sangin gaske.
Ganin ya sunkuyar da kansa ƙasa bai musa ba,mai tsaron ƙofar yace.
"tausayinka dana keji ya sanya yau ban iya cin abinci na ba,sai da na raba biyu na kawo maka rabi,hatta ruwan dukkansa na baka banko sha ba,amma a kullum kana nuna zaman da kake cikin a yanzu bai dameka ba,bayan ga zallar wahala nan ya bai yana saman fatarka da kuma fuskarka,sam wannan rayuwan ba irin taka bace,nace ka bani wani abun na fiddaka daga wajan nan kaƙi"
Ya ƙare maganar yana ficewa daga ɗakin sabida wani tiririn zafi daya gallabesa.
Saifu kam ko tari baiba banda lazimi cikin ransa babu abinda yake,ya ɗauki wajan 30minutes zauna kafin ya miƙa hannu ya ɗauki gorar ruwan da mutumin ya ajjiye masa,murfin gorar ya ɓalle kana ya kafa a bakinsa,saida yasha fiye da rabi sannan ya ajjiye gorar a gefensa,hannu yasa ya murza cikinsa sabida ƙugin da yake masa sakamakon yawan ruwan da yake ɗirkawa cikinsa,kallon masar da naman kazar yay kana ya janye idanunsa kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa take bacci ya ɗaukesa sabida baya samun bacci da daddare.
A tsaye take tsakiyan bedroom ɗin da aka sanyata,sai juya ƙwayan idanunta take tamkar wacce take neman wani abu,ƙarar buɗe ƙofa data jine ya sanyata juyowa da sauri tare da ƙanƙame jikinta waje guda,kuyangun da suke shigo tabi da kallo tana kallonsa tamkar baƙin fuska wanda bata saba ganinsu ba,kayan hannunsu suka ajjiye da alamu abinci ne nau'i daban-daban,ɗaya daga cikin kuyangunce ta matsu kusanta tace.
"Fulani mai zuwa ranki ya daɗe ya ƙara maki lafiya ga abinci nan saƙo daga Mai martaba yace kuma anjima yana nan tafe"
Ɗan rolling eye balls ɗinta tayi tare daja baya ta soma girgiza masu kanta,can gefe guda ta cure jikinta waje guda ta fara rera kukanta wanda take tun ɗazo,da mamaki gaba ɗaya suke kallonta wakan 5minutes ɗaya daga cikinsu mai suna Kuyanga Falmata tace.
"Fulani mai zuwa kuka ba naki bane,tun jiya baki sawa cikinki abinci ba,dan Allah ki daina kuka kada kisa Mai martaba ya ɗauka wani abu akai maki"
Ta ƙare maganar tana ƙarasuwa wajan tare dasa hannu ta riƙe,kallonta kawai Zarina take ba tare da tace komai ba,sai idanunta kawai dake tsiyayar da ruwan hawaye,lumshe idanunta tayi sai kuma tai saurin buɗewa sabida mutumin da ako da yaushe take mafarki dashi,a wannan karan mafarkin na musamman ji take tamkar tayi rayuwa dashi a zahiri bawai iya mafarkin data saba ba,taune lips ɗinta tayi tare da ƙara lumshe idanunta tabbas su take ta ƙara ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa mai cike da haiba da kuma ƙwarjini,uwa uba cikar zatti da fasalin halittar jikinsa wacce a kullum take ƙara zautar da tunaninta,soyayyarsa ta zama jigon komai nata,numfashinta,cinta,shanta,tunaninta dukkan wani abu da take saida tunaninsa,shin ina zata gansa? Anya shiɗin ba aljani bane tunda ya kasa bai yana gareta,haka za taci gaba da zama da sonshi cikin zuciyarta,shin idan da gaske shiɗin aljanine mene makoman nata rayuwar? A yadda take jikinsa a dukkan wani bugun zuciyarta bata jin ko aljanine zata iya rayuwa idan ba dashi ba,ta shirya zama dashi a duk halin da yake,ƙwarai idan ya kasance mafalkin da take dashi gaibune babu shi tsakanin jinsin mutum da aljan babu shakka ko tantama babu sonsa shine ALJALINTA,magnar kuyanga Falmata ce ta dawo da ita daga dugun tunanin da take.
Hawayen da yaci gaba da tsiyaya daga idanunta tasa hannu ta goge,a raunane kuma cikin muryar kasala wacce kuka yaci ƙarfinta tace.
"su wayeku? Mene zan maku kuka kawo ni nan? Inane nan ɗin? Ina Mom ɗinta da Abba da Mamu da Yaya Sufyan da Yaya Tupic,dan Allah ku kaini wajan ahlina ni duk ban sanku ba"
Ta faɗa cikin wani sabon kukan da yake ƙwace mata,gaba ɗaya baki suka saki sabida tsananin mamaki da kuma Al'AJABI tsahun watanni kusan tara tana gidan sarautar nan amma bata san da zamanta ciki ba,Kuyanga Falmata murmushi tayi domin zuwa yanzu ta gane asirin dake jikin Zarina ya ɓalle wanda akai amfani dashi wajan mantar da ita abubuwan baya aka ɗura akan na yanzu wanda take tunanin shine dai²,kuma ta ɗauka nan ɗin shine danginta kuma gashi anyi rashin sa'a asirin ya karye ko mene zai faru nan gaba?....
"ƙwantar da hankalinki muɗin ƴan uwanki ne,yanzu kici abincin sai nakai ki gida kinji?
Cike da zallar ƙuruciya da wawta Zarin ta giɗa kanta alamar "to" a hankali ta kalli Falmata cikin siririyar murya wacce take nuni da mamallakiyan mai muryan bata fiya magana ba tace.
"Ayya teddy nafa?,dan Allah aƙwai dawakai a gidan nanne,nayi mafarkinsu jiya"
Murmushi Falmata tayi kana ta kalli Zarina cikin son ƙwantar mata da hankali tace.
"teddy'nki nan,dawakai kuma gsky ne bawai mafarki ba,wajan ƙwana sati guda dayin kilisa tsakanin Saifudeen da Lil prince"
Da sauri Zarina ta miƙe tsaye tare da murza daimond ring ɗinta,ji take kamar tasan wannan haka kuma kamar tasan mai sunan,tana kallo suka fice daga ɗakin ba tare data samu damar tambayarsu wani abu ba.
Kukan da cikin yake na alamun jin yunwa yasa bisa dole ta zauna gaban manyan wamers ɗin kana ta fara buɗewa,wamer ɗin farko farfesun kayan cikine na babbar dabba,wanda suka ji kayan ƙamshi sai turiri suke,rufewa tayi ta buɗe wata taga white rice and chicken pepper soup sai haɗin cosilo,nan ma rufewa tayi ta buɗe wata taga zallar cipis tare fruits salad shi ta ɗauka ta faraci ba taci mai yawa ba ta ture,sai fruits salad ɗin data sha sosai bayan ta gama ta shiga bathroom ta wanke bakinta da da hannunta kana ta dawo jikin window wurga idanunta ta farayi can ta hangi wani waje wanda bashi da yawan mutane da alamu waje ne na musamman,sabida yawan masu tsaro data gani a ƙofar ɗan ɗakin take wajan.
Zoben hannunta ta kalla gannin yana ta sheƙi da ga wani haske dake fita ta jikinta,lumshe idanunta tayi sabi zuciyarta da taji tana gudu vry past.
A sanyaye kuma a kasalance ta juya ta koma kan bed ɗin tana jiran dawowarsu domin kaita wajan Mom ɗinta.
Kuyagun kam tunda suka fita basu dawowa ba,sabida rashin amsar da zasu bata,ɗaya daga cikinsu ce ta sulale ta nufi Fada (kusan gidan sarauta badai gulma ba😅😂).
Tana zuwa ta nemi iso wajan tsarkin fada babu jimawa aka bata izinin shiga,a gaban Mai martaba ta zube tare dayi masa kirari kana ta numfasa tace.
"kaine mai takama da ƙarfin mulkinsa,an gaisheka sarki mai tausayin talakawansa,aƙwai matsala Yarinyar daga bamu ajjiya dai ya dawo cikin hayyacinta,kuma ta fara kiran ahlinta,shine nace bari nazo na faɗa akan lkc"
Kallonta Mai martaba yay cike da tashin hankali da ɗimuwa,tambayar kansa yake yaya akai asirin harya fice daga jikinta cikin ƙanƙanin lkc,shida yasu har ƙarshen rayuwarta ya kasance brain ɗinta a juye yake,tabbas aƙwai matsala ya zama dole ya gana da boka Gilmas,gyaran murya yayi yace.
"kada nowa ya koma sashin da take,daga yanzu Chiroma zai dinga kai mata"
Jinjina kai tayi sannan tayi gdy tare da miƙewa tayi waje,a wajan su kaci karo da Kulsum da Falmata sai Batul,damurcewa tayi gaba ɗaya kana ganinta kasan babu gsky a tare da ita,wani murmushin takaici Falmata tayi tace.
"kinje kin faɗa masa Zarina ta dawo haiya cinta shine yasa mike sunkuyar dakai alamun rashin gasky ko?"
Falmata ta faɗa cike da ɓacin ran abinda Zuwaira tayi,da sauri Kulsum ta kalli Falmata tace.
"daman kuna tare da Zarina? Kina nufin kice da bata san wace ita ba sai yanzu"
Jinjina kai Falmata tayi kana ta labartawa Kulsum komai,Batul kam shuru tayi tana ɗaukan rahutun taje ta faɗawa Fulani kilishi.
Watsewa sukai kowa ya koma part ɗin daya kewa aiki,Kulsum na zuwa ta shaidawa Mai babban ɗaki abinda yake faruwa,Murmushi kawai tayi tace.
"Allah ya ƙyauta"
Tana faɗin hakan tai shuru ita kaɗai tasan abinda yake damunta, sosai zuciyanta yay kewan Saifudeen a duk lkc'n data tuna shi tana jin kamar ta saka kuka.
3 and months and 29 days ago
Haka ƙwanaki suka dinga mirginawa suna Komawa satintika daga nan su juye zuwa watanni,haka rayuwar Saifu da Zarina taci gaba a masarautar bilhas.
A kuma gobe ne ake saka ran fito da Saifu sabida a gobenne yake wata huɗu cif a ɗakin duhun.
Haka kuma yay dai² da shekara ɗaya da wata biyu da zuwansu cikin masarautar dukkan inda wahala da matsatsi yake Saifu ya shigesa idanunsa sun faɗa ga wata rama data bai yana a wuyansa har ƙashin wuya saida ya fito masa.
Amma hakan baisa ya karaya ba yana nan da hqr da juriyarsa haɗi da tsantsar kuzarinsa kullum cikin ambatan Allah yake.
Tana zaune sai kuka take banda kiran sunan Mom babu abinda Zarina take,ƙofar taji an buɗe da sauri ta ɗago kanta Falmata ta gani fuskarta cike da farin ciki kafin tayi magana tace.
"inane garinku insha Allah yau zaki bar wannan masarautar"
Da sauri Zarina ta goge hawayen idanunta cikin farin ciki tace.
"A Kogi nake"
Hannunta Falmata ta kama kana ta sanya mata hijab mai liƙab tace.
"Maza yanzu Mai martaba ya fita zuwa dare zai dawo kafin nan kinyi nisa"
Ta faɗi hakan tana kuntu kuɗi masu yawa a gefen zaninta ta bawa Zarina