Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
da maganar tayi masa.
Kallonsa kawai take dan tunanin ya gama bata wannan Saifun data sani bane,zaifi dacewa ace tana cikin mafarkin data saba ne,a hankali ta zame jikinta.
Saurin riƙota yay tare da ƙwaɓe fuska ya ɗan langwaɓar da kansa gefe guda tamkar maraya cikin wata sabuwar muryasa ce.
"Pls ZARINA kada kice A'a banson jin"wasu zafaffan hawaye ne suka sauko daga cikin idanunta zuwa kan fuskarta,jikinta na rawa ta faɗa jikinsa ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya,shuru yay tare da lumshe idanunsa yana jin yadda ta rungomesa sosai.
Cikin fitar hayyaci tace.
"Wlh bana sonka bana ƙaunarka bana jin zan taɓa sonka,hasalima na tsaneka"
Da sauri ya buɗe idanunsa wanda lokaci guda suka sauya kala zuwa jaa,cikin ɗan ɗaga murya yace.
"Ni!? Nine bakiso wlh ƙarya kike,soyayyata da ita kika rayu,kuma har yanzun tana tare da dake,idan ƙarya nake kalli cikin idanuna ki faɗamin abinda kikace..
Wani murmushi tayi kana ta cillah idanunta cikin nasa kamar saukar ruwan sama haka yace tace.
"I HATE YOU NA TSANEKA BAZAN TAƁA SON BASIƘI MAZINACI BA" ta ƙare maganar tana sakin wani saɓon kukan.
Wata ɗamƙa yakai fata tare da sanya hannu ya sauke mata wasu tagwayen maruka,sai kuma ya jawota cikinsa ya rungometa sosai.
"why"shine kawai abinda ya samu damar faɗa sabida tafasar da zuciyarsa keyi masa.
Sosai marin da yayi mata ya gigita wannan shine karo na farko da aka taɓa marinta,gaba ɗaya jikinta rawa yake ko kuka ta ƙasa sabida a zabar da fuskarta take.
A sanyaye ya sanya hannunsa ya tura cikin sumar kanta,kana ya sanya ɗaya hannun ya tallafo wuyanta,lips ɗinta da take taunewa dan azaba ya tsurawa idanu,a hankali ya ɗura fuskarsa saman fuskarta,idanunsa na fiddan ƙwalla ya ware laɓɓansa yace "ZANYI FAƊA DA KOWA AKANKI INA SONKI" ya faɗin hakan yana sauke laɓɓansa cikin nata,a hankali ya kama lips ɗinta na ƙasa ya soma...
_THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE,ZAKI SAMESHI AKAN 200 NAIRA ONLY,MASU BUƘATAR LITTAFAN DANA RUBUTA NA KUƊI ƳAN VIP ZASU SAMU AKAN 500 NAIRA ONLY ,ACCOUT NO 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK,SHAIDAR BIYA 08119237616_
*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
*41-42*
*_Littafin THE NEW EMIR na kuɗi ne,ban yarda a fiddamin shi waje ba,masu fitarwa kuma Allah yay maku albarka_*
#GOODBYE
Lumshe idanunsa yay tare da fesa mata hucin hancinsa akan fuskarta,mai makon yay kissing lips ɗinta kamar yadda yay niyya sai kawai ya zare laɓɓansa daga cikin nata.
Zarina kam numfashin tane ya kusa ɗaukewa,sabida yadda taji saukar laɓɓansa cikin bakinta ba ƙaramin sauya mata lissafi yay ba.
Sosai take sauraran ɗumin cikin bakinsa dake ratsa cikin ƙaramin bakinta,gaba ɗaya ta sare ta sallama tana jiran taji abinda zai biyo baya,hakan kuma da yay mata ya ƙara tabbatar mata da zargin da take masa na lalata ƴar ƴan mutane,wani ƙunci da baƙin cikine suka cika zuciyarta ladamar saninsa ta ɗarsu cikin zuciyarta,shuru kawai tayi tana sauke ajjiyar zuciya sabida kukan da tayi dalilin marukan daya sauke mata.
Ga mamakinta mai makon ya sumbaci leɓenta na ƙasa daya sanya cikin bakinsa,sai taji ya zare bakinsa gaba ɗaya daga cikin nata.
A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tare da buɗe idanunta da sukai mata nauyi sabida kumburar da sukai,idanunta ta tsura masa kamar yadda ya kafeta da nasa fitannun idanun wanda suka sauya kala zuwa jaa tare da ɗan janyewa sabida ɓacin ran dake ƙwance cikin zuciyarsa.
Juna zuka zubawa idanu yayinda ƙwayar idanunsu ke yawo cikin na ko wannansu,yaya zaiyi da soyayyarta wacce ta shigesa lokaci guda?,mene makomar zuciyarsa data faɗa soyayyar da ƙaramar yarinya wacce ya kewa kallon “ƙwaila?”,meyasa take masa kallo nada ban?,shin ya taɓa aikata mata wani abune wanda ba dai² ba?,ta jefesa da maganganu marasa daɗi wanda suke dai² da tarwa tsewar zuciyarsa.
Taje fesa da abu mafi mune,ta haɗasa ta kallma mai munin gaske,kallamar dako da wasa baison jinta,hasalima ya tsani duk wani mutum mai aikata ta.
Kallamar “Zina”data haɗashi da ita ba ƙaramin ɗaci da muni taiwa zuciyarsa ba,yana jin wani ɗaci da baƙin ciki a ransa,zuciyarsa nayi masa zafi da raɗaɗi fiye da tunanin dukkan mai karatu.
Yana daurewa tare da ƙoƙarin danne damuwarsa bai son taga rauninsa ko kaɗan bai shirya hakan ba.
Cike da kuzari da kuma jarumtar daya arowa kansa ya ƙwantar da kansa bisa kafadarta tare da sanya hannunsa ya rumgeme waist ɗinta dashi.
Numfashi ya sauke mata tsakanin wuyanta,sosai yay hugging ɗinta a jikinsa yana sauraran yadda bugun zuciyarta ke tafiya,Zaiyi fata ace numfashinta da bugun zuciyarta baya tafiya saida tunaninsa,soyayya sam ba tai masa adalci ba data haɗa shi da ƙaramar yarinya wacce sam baiga abin ɗauka a jikinta ba.
Yadda yake sauraran bugun zuciyarta haka itama take sauraran tasa bugun zuciyarsa wacce take gudu very past,tana fata ace bugun zuciyarsa da tunaninsa baya fita saida tsanarta,kamar yadda nata numfashin baya taɓa fita saida tsanarsa,tayi masa tsana mafi muni,tayi masa tsanar da bata taɓa tunanin za taiwa wani ɗan adam shi ba.
Hawayen dake maƙale cikin ƙwayan idanunta suka samu damar silalowa tare da sauka bisa ƙafaɗarsa,taune laɓɓanta tayi tana jin yadda zuciyarta keyi mata zafi da kuma raɗaɗi.
Saukar hawayenta saman kafaɗarsa yay dai² da yadda Zuciyarsa ta ƙara gudu da ƙarfin gaske,a hankali ya zare jikinsa daga nata tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa masu kaifi,a sanyaye ya kama hannunta tare da ɗurashi bisa saitin zuciyarsa.
Runtsa idanunta tayi sabida yadda taji ƙirjinsa na bugu kamar zuciyarsa zata fasu waje.
Pouting lips ɗinsa yay tare da lumshe idanunsa some minutes ya buɗe a hankali tare da saukeso bisa ƙyaƙƙyawar fuskarta,matso da fuskarsa yay dab da tata,can ƙasa maƙoshi yay amfani da muryarsa wacce tayi ƙasa da yawa yace.
“RINA.."shuru yay kafin yaja da numfashi ya ɗora da "kinji yadda zuciyana ke gudu a kanki,ohh wow thank you babyluv kinyi nasarar tafiya da zuciyata,kinsa na shiga halin damuwa da kaɗaici duk akan ke ɗaya,zan iya ninka shekarunki guda uku amma na buɗe baki nace ina sonki.."numfashi ya sauke tare da taune laɓɓansa kana yaci gaba da faɗin "see you kene zaki dubeni da idanunki da kuma bakinga kice baki sona for what reason ma?ohh ya rabbi zuciyana ciwo babu daɗi duk a kanki".
Shuru tayi masa tana jin tsanarsa na ƙara nunkuwa cikin zuciyarta,da ace zai iya ganewa babu shakka daya batta taji abinda yake damunta,tabbas da ace zai iya ganin yadda tsanarsa tayiwa zuciyarta ƙawanya daya rabu da ita.
Miƙewa yay tare da sanya hannunsa bisa kafaɗarta ya miƙar da ita tsaye,hannayensa ya sanya ya tallafo haɓarta tare ƙurawa lips ɗinta idanu wanda sukai red sabida tsabar taunesu da take,duk yadda yasu tace masa wani abu ƙi tayi saima haɗe fuska da tayi tare da ɗauke fuskarta zuwa wani wajan.
Matsuwa yay kusanta tare haɗe jikinsu waje guda yana jin ɗumin jikinta na ratsashi,hawayen fuskarta ya sanya hannu ya share mata,bakinsa ya ɗora bisa nata kana ya ware laɓɓansa hakan ya bawa lips ɗinta na ƙasa damar faɗawa cikin bakinsa.
A karo na biyu ya haɗe laɓɓansa waje guda tare da lumshe idanunsa kana yaywa lips ɗinta wani mahaukacin tsotsa.
Wani numfashi suka sauke a tare kana yaɗan ƙara shigewa jikinta sabida yadda jikinta ya fara rawa.
Zare bakinsa yay a hankali tare da ɗorasa bisa tsinin hancinta nanma ya sauke mata sumba,haka idanunta da kuma kuncinta.
Kansa ya ɗora bisa wuyanta tare da sanya bakinsa cikin kunanta ya sakar mata da wani zazzafan huci ta cikin bakinta,da wata murya mai sanyi yay amfani wajan faɗin.
“Just wait for me,i will come back,komai nisa komai daɗewa zan dawo WAIT FOR ME BABYLUV".
Hawayen dake manne cikin idanunsa ne suke ƙoƙarin fallasa kansu ta hanyar sakkowa,murya mara sauti yay saurin faɗin.
“Goodbye”kana ya sakar mata wata lafiyayyiyar sumba tare sanya mata wata envelope a hannunta,da sauri ya juya tare da fice daga sashin gaba ɗaya.
Zubewa tayi akan sofa tare da sakin kuka,sosai take kuka mai taɓa zuciya,ta nayi tana sauke ajjiyar zuciya,wani baƙin ciki da takaicine yay ƙwance cikin zuciyarta,yayinda wutar tsanarsa ke ƙara ruruwa cikin rai da zuciyarta,runtsa idanunta tayi tare dajan pillow ta rungome ta soma sakin ajjiyar zuciya a jajjere.
Lil prince dake baƙin ƙofar shigowa sashin na Mai babban ɗaki,yay saurin sakin wani shu'umin murmushi lokacin daya gama jin abinda Saifu ke faɗawa Zarina,da kuma abinda Zarinan ke faɗa masa,da sassarfa yabar wajan sabida alamun tafiya da yaji anayi za'a fito waje.
A hankali ya fita daga cikin sashin Mai babban ɗaki,yana tafe yana bada ɗan faɗin,cikin da juriya da isa yake tafiya,time to time yakan lumshe idanunsa tare da sakin ajjiyar zuciya shikaɗai yasan me ya keji mene kuma yake damunsa,tabbas soyayyarta halittace a zuciyarsa,bawai a sanin da yay mata na yanzu ya fara jin sonta ba,ya sota a lokacin da baisan mene shikansa so ɗin ba,yay dakon sonta tun baisan zai ganta a nan duniya ba,domin tunaninsa ya gama bashi ita ɗin ba mutum bace sabida yawan mafarkin da yake da ita,a ranar daya sauka Masarautar bilhas a ranar ya san cewa soyayyarta ta riga da tayi masa illah,taune lips ɗinsa yay tare da son kawar da abunda yake ransa,sam bai son rauninsa ya bai yana ta dalilinta bai shirya hakan ba sam.
Agogon dake manne a tsintsiyar hannunsa ya kalla ganin har shaɗaya ta kusa.
Da ɗan sassafar ya ƙarasa sashin Mai martaba kamar yadda ya umarci shi akan ya sameshi a tirakarsa.
Yana zuwa bakin ƙofar ya ɗan tsaya haka nan ya samu kansa da samun faɗuwar gaba,addu'ar neman tsari yay kana ya sanya kansa cikin tirakar tare dayin sallama cikin muryarsa mara fita.
Daga can cikin tirakar Mai martaba yay gyaran murya tare da bawa Saifu damar shigowa daga ciki.
A hankali ya sanya kasan bakinsa ɗauke da wata addu'ar,kana ya ƙarasa shiga cikin ƙawataccen parlour'n na Mai martaba wanda yaji kayan mure rayuwa.
Zaune ya samesa bisa wani cosin mai ƙyau da kuma laushi,gabansa ciki yake da kayan marmari kala²,danginsu pineapple,mango,orange,inibi,apple,gauva,fasadabir.
Gefe guda kuma al'kakine,dubulan,makilawa,sai kilishi wanda yaji kayan haɗi.
Zama yay tare da langwashe ƙafafunsa ya fuskanci mai Mai martaba,kamar zaice wani abu sai kuma ya share kawai ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da zubawa wani zobe dake hannun Mai martaba idanu.
Tun shiguwarsa Mai martaba ya zuba masa idanu yana mai gasgata zancen Ciroma da sukai ɗazu,shi sam bai kula da hakan ba sai yanzu,wani murmushin gefen baki yay cike da izzah yace.
"A'a kace harka fito yau sai ganin Abbunka daya ƙwace mana kai"
Kallonsa Saifu yay na wani lkc kana ya ware laɓɓansa yace.
"Eh! Nayi missed nashi ne fa"
"ok ka gaishesa,amma yana da kyau ka dawo kafin sallah,sabida aƙwai shagalin ƙaramar sallah da ake bisa tsari kuma a al'adance,hakan tasa dole muke neman tsaro mai kyau bisa taimakonka kuma"ya ƙare maganar yana ciro bandir ɗin ƴan 1k sabbi fil kusan bandir goma ya ajjiye gaban Saifu sannan yace "ga wannan aiwa mutun gida abin buɗe baki"
Girgiza kai Saifu yay cike da kuzari da izzah yace "No! Thank you gwamnati na biyana,ban amsar naka"
"nikam Saifu zanzo insan wanene kai,idan na kalleka sai kayimin kama da Fulanin daji masu kiwo da manyan shanu"
"uhmm idan wannane tunaninka to basshi a hakan"yana faɗin hakan ya miƙe tare da nufar hanyar da zata sadashi da waje,yana gaf da fice yaji Mai martaba yace.
"ka rage wannan izzar taka,kabar wanda suka gajeta suyi ta ƙama da ita ba talakawan ƙasa irinku ba"
Tsayawa Saifu yay cak,tare da sauke wani numfashi ɗan cizon leɓensa yay kana ya juya ya kalli Mai martaba,a hankali yace.
"wasu izza a jininsu take wacce ta zame masu halayya,wasu kuma mulki ke saso,idan kuma kana ta ƙama da mulkin kane babu shakka munga FIR'AUNA yana ina yanzu?babu wani mulki dake tabbata idan bana ALLAH ba,dan haka izza a jini da tsokar SAIFUDEEN take na barka lafiya"
Yana faɗin hakan ya sakai ya fice daga sashin gaba ɗaya,da idanu Mai martaba ya bisa yana ƙara mai-mai ta maganganun da Saifu'n ya faɗa masa,wani murmushi ya ƙarayi mai cike da ma'anoni,wayarsa ya ɗauka tare da kiran wata number,yana kira akai picking.
Daga can ɓan garen akace.
"Allah ya ƙarawa Mai martaba lafiya,Allah ya taimaki sarkin sarakuna barka sa shan ruwa"
Ba tare daya amsa maganar da yay masa ba,cike da ƙasaita yace.
"abi bayansa yanzu har zuwa inda zashi"yana faɗin hakan ya kashe wayar,tare da miƙewa ya nufi ɗakin da shigarsa ya zame masa kamar al'ada a watan azumin da kowa yake neman rabauta da rahamar ubangiji.
Lil Prince cike da farin ciki ya shige sashinsa,yana mai jinjina abinda zai aikata akan tafiyar Saifu'n,tabbas zai dawo ya samu mummunan labari,domin zai dawo yaga Zarinan dake neman zaucewa a kanta ta zama mallakinsa ta zama matarsa ƙarƙashin inuwarsa,zai mallaketa kamar yadda suka mallaki masarautar bilhas gaba ɗayanta.
Zarina kam kanta ne ya shiga sarawa tare dayi mata wani mahaukacin ciwo,a hankali kuma wani zazzafan zazzaɓi ya fara ratsa cikin gaɓoɓinta,hakan ya haddasa mata jin wani tsayi na musamman na shigarta,curewa waje guda tayi dan ba tajin zata iya miƙewa tsaye bare harta nufi ɗaki ta ƙwanta,zafin zazzaɓinne ya tsananta a jikinta cikin fitar numfashi da wahala ta soma sauke wata sabuwar ajiyar zuciya,yadda jikinta ke tsumane ya haddasa gazawar numfashi wanda ya fara fisga kamar wacce ake shirin zarewa rai.
Wasu tawagwan hawaye ne masu zafi suka soma sauka bisa kuncinta,duk yadda kake tunanin zaka fassara halinda take ciki yafi ƙarfin hakan.
Kuka ta fashe dashi jin ciwon nata ya sake tsananta ga babu wani kusa mai taimakonta,a haka tai ta zama tana rera kuka har bacci yay nasarar ɗauketa.
A hankali saifu yake taka steps ɗin jet wanda ya daɗe da sauka a babbar harabar masarautar bilhas,sai da yaje steps ɗin ƙarshe ya tsaya tare da juyawa ya zaubawa masarautar idanu,zuwa wasu minutes ya ɗauke idanunsa tare da ƙarasa shigewa cikin jet ɗin.
Wata lafiyayyiyar kujera ya nema ya zauna akai,kana ya kashe wayoyyinsa ya ajjiyesu bisa side ɗinsa,lumshe idanunsa yay yana sauraran gudun zuciyarsa wacce take fita da ƙarfin gaske.
"ya rabbi ka karesu na danƙa amanarsu bisa hannunka"
Yana faɗin hakan ya ƙara lumshe idanunsa,yana jin yadda jet ɗin ya fara kewaya masarautar a hankali kuma ya luula zuwa sama.
_The new emir zaku samesa akan farashi mai sauƙi 200 kacal,masu buƙatar vip kuma 500 zasu samu duka littafan dana rubuta na kuɗi, yadda zaka turo kuɗin da a sosu na, 0116886423 Sulaiman Na'ima S union bank, shedar biya 08119237616_
*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
*43-44*
_Littafin THE NEW EMIR na kuɗi ne akan 200 for nrml grp,500 vip,domin samun bayani yadda zakai payment duba ƙasan shafi_
*HELLO AFTERNOON POST*
A hankali jet ɗin ke luulawa saman gajimare harya ɓacewa ganin Ciroma.
Numfashi Ciroma ya sauke tare da ɗauko waya ya kira number Mai martaba,wajan ringing uku ya ɗaga,Ciroma najin ya ɗaga wayan yace.
"Allah ya ƙara maka lpa yaron nan ya shammace mu,har Masatautar bilhas jet ɗinsa ya sauka yanzu haka sun jima kaɗan da barin wajan".
Daga can ɓarin Mai martaba yace.
"Ohh zai san da Sarki Khalid Bilhas yake magana,jeka abinka kawai"yana faɗin hakan ya ƙatse wayar tare da wurgi da ita,saman bed ya faɗa ya cukokuye jikinsa,bai jima bacci yay gaba dashi.
Cike da farin ciki Ciroma ya nufi sashin dan shima burinsa bai huce ya cimma tasa buƙatar ta zama Sarkin Masarautar Bilhas na 5.
Yana ƙoƙarin shigewa sashin domin wunin yau curr baiga iyalinsa ba,yaji muryar Waziri a bayansa.
"Mene kukeson aikatawa wa Saifudeen,mene yasa duk wani bakirci da za'a haɗa a wannan masarautar sai ansami hannunka ciki,Mulki fa ba hauka bane,wanda ubangiji ya ƙaddara zai zama Sarki bayan Mai martaba yay burabus dole ne ayi masa biyayya,amma ka zauna kana cin ƙafar wanda ya amince maka,koda yake sam bana ganin laifinka wlh,sabida Shima Mai martaba ba'a bisa ƙa'ida yake aiwatar da mulkin saba,nida fatana Ubanji ya kawo *Saɓon sarkin* dazai wakilcemu bisa gsky da kuma amana"ya ƙare yana kallon Ciroma.
"Daka tamin nan Waziri waikai wanne irin mutum ne mai sa idon masifa,ina sane da cewa kaima fa mulkin nan kakeso,kuma nasan komai akan ɓoyayyen sirrin da kake ɓoyewa shekara da shekaru,da nasu da tuni nayi hanyar da zata saka a kulleka a ɗakin duhu na iya tsawon shekarunka,kayi gaggawar ɗauke idanunka daga kaina na faɗa maka"
Kafin Waziri yay magana lil prince ya ƙarasu wajan,domin hanyarsa ce ta zuwa lambu,kallonsu yay gaba ɗaya kana ya buɗe baki yace.
"mene Wazirin ke ɓoyewa tsawon wasu shekarun maza faɗamin?"
Da sauri Ciroma yace.
"Allah ya taimaki magaji mai jiran gado,ba wani abu bane kawai na faɗane don rantsa ya ɓaci,haka nan yazu yake gayamin magana ciki wannan daren a kuma wata mai falala"Ciroma ya ƙare maganar yana matso ƙwalla daga cikin idanunsa.
Lil prince ne ya kalli waziri yace "Kai baka taɓa tunani magana kafin ka faɗeta,mai yasa baka da tunani ne,ni sam banga abinda yasa Mai martaba yake zaune dakai ba,tunda Mahaifiyar ta sheƙa kasan dai mulki ba samunsa zakai ba,dan haka ka yayeni"yana faɗin hakan ya shige cikin lambun.
Da idanu Waziri yabi Prince Najeeb dashi,ganin hawaye dake ɓoyewa na neman bayyana kansu yay saurin barin wajan tare da shigewa ɓangarensa,daman tunda matansa ya mutu bai kuma wani auren ba.
"daga kai har Mai martaba ɗin dai² nake da ƙugunku,bare wani Magaji"Ciroma na faɗin hakan ya shige sashinsa.
Lil prince,
Da sauri ya shige cikin lambun tare da soma kewayesa yana son ya laluɓo inda Mai martaba yace masa aƙwai wata tsuhuwar aƙwati amma ya kasa gane inda take.
Haka yay duba shuru harya huce inda Zarina ta haƙa ta cilla aƙwatin ciki.
Apple guda biyu ya tsinka kana ya fice daga cikin lambun.
*_Washe gari_*
Ya kama uku ga azumi,sosai jama'ar masarauta dama ƴan unguwa su kaji babu daɗi da tafiyar SAIFU wacce tazu masu a bazata.
Misalin 5 na yamma,Sarkin sakar gida ya fito da sauri sabida gaba ɗaya ya manta ance yaje ya fito da Kulsum daga ɗakin duhu.
Da sauri yake ratsawa cikin gidan sarautar sabida yana da girman gaske,saida yaje ƙarshe kana ya tsaya a wani ƙaramin ɗaki mai ginin bilan ƙasa,yana zuwa ya sanya masu tsaron ƙofa sauri buɗewa tare da bashi waje
Girgiza gansa yay tare da faɗin.
"fito da ita"
Ya faɗa a taƙaice,juyawa Mai tsaron ƙofar yay tare shigewa