THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   10 / 38

27K to 30K   out of 111.1K words

yadda za'ai ta shiga ciki ba tare da kowa ya ganta ba,numfashi ta sauke kana cikin siririyar muryarta tace "Ya rabbi help me"tana faɗin ta soma ɗaga ƙafanta tun daga nesa daimond ring ɗin hannunta ya fara wani irin haske,babu inda kuma hasken ke tsayawa sai jikin ƙofar,tun kafin ta isa taga ƙofar ta fara buɗe tamkar magic,tana ƙarasuwa wajan ƙofar na buɗewa gaba ɗayanta,a dai² lkc'n hasken zoben ya ɗauke..


IDAN NAGA COMMENTS ANJIMA KUGA UPDATE YANZU AKA FARA WASAN👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️🔥.


*THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE 200 NAIRA ONLY 08119237616*
*27-28*



TRUST#
Never lie for someone who trust to you.




Hannu tasa ta murza zoben tana jinjina girma da hukuncin Ubangiji,yana iya komai a lkcn da yasu wannan kaɗan daga cikin hikima da bowayar lillahi wahidul Qahhar,hannu ta sanya ta share hawayen daya zo bo mata,cikin nutsuwa ta sanya kanta cikin haɗaɗɗan parlour'n wanda yaji kayan alato da kuma mure rayuwa,tasan cewa wannan mamallakin wajan na musammanne kamar yadda sashin yake komai nasa na musamman,ko'ina haske yake fiddawa da kuma ƙyalli sabida amafani da zallar azurfa da akai wajan ƙawata sashin,baka ganin komai sai tambarin sarauta da kuma wasu manyan photos mas yawan gaske,babu photon da yafi ɗaukan hankali na sama da wani yaro zaune yake kan wata kujera ta alfarma,yasha wata morron ɗin Alƙyabba mai ɗigwan milk an naɗa masa rawani mai kunnuwa guda biyu,ƴar ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta tsaya dai² da rawanin da aka naɗa masa,hannun riƙe da wani sandan girma na daimon sai sheƙi yake,hannayensa na zubawa idanu ganinsu ɗauke da rings na Azurfa sai ƙyalli,ƙara maida idanunta tayi kan fuskarsa mai cike da haiba da kuma ƙwarjini,tabbas wannan ya girma ba kowa zai iya haɗa idanu dashi ba,murmushi tayi tare da taɓa beauty points ɗinta wanda taga irinsa a fuskarsa sbd murmushi da yayi wanda ya ƙawata fuskarsa.

"Da dukkan alamu baƙon da nayi yau na musammanne naji zuciyata nason kasan cewa dashi,kasan cewarsa baƙo gareni shine yasa yake ƙarewa parlour na kallo without my permission"ta ƙare maganar tana sakin murshinta wanda baya rabuwa da fuskarta.

Ajjiyar zuciya ta sauke wata matsananciyar kunya ta kamata,sunkuyar da kai ƙasa tayi ta kasa ɗaga idanunta taga mai maganar,amma munyarta kaɗai ya tabbatar mata mai muryar macace mai nagarta nutsuwa hankali da kuma sanin ya kamata,jin bata ƙara magana ba,yasa ta ɗaga idanunta tare da zubawa Mai babban ɗaki idanu,kishin giɗe take kan babbar ladduma tana sanye da wata lafaya fara tas sai wal-wali take,hannunta riƙe da casbawa tana ja,zuba mata idanu tayi cike da so da ƙauna wanda ya shingiɗe lkc guda ya shigeta,sosai take kallon Mai babban ɗaki tana son ta tuna inda tasan mai kama da fuskarta ta kasa,cikin nutsuwa ta ƙarasa wajanta tare da zama kusa da ita,cikin sanyi murya tace.


"Ammi barka da wuta Allah yaja da ƙwanaki masu albarka"

Ajjiye casbaharta tayi kana ta joya inda take jin murya,ɗan murmushi mai sauti tayi tamkar tana ganinta,kana ta jinjina kai alamar amsawa,kasan cewarta mace mai karamci ya sata faɗin.

"Madallah da yarinyar arziƙi wacece ke,yaya akai kika shigo sashina da wannan safiyar?"ta cilla mata tambayar tana sakin murmushi alamar jin daɗi.


Shuru Zarina tayi tana tunanin abinda zata faɗawa Mai babban ɗaki domin ta yarda da ita,ba tason ta nuna wani abu wanda zai sanya ayi alamar tambaya a kanta,ba tason ƙarya dan haka yanzuma ba zata iya yinta ba,ƙara fuskantar Mai babban ɗaki tayi kana ta buɗe baki cikin ƙasa da murya tace.


"Ammi na daɗe ina son zuwa nan sashin,duk sanda naga flat ɗinnan inajin sanyi a zuciyata,shiyasa yau nace bari nazu na kawo maki breakfast,ina zuwa wajan ƙofar sai zoben hannuna ya fara haske abun ya ƙara bani mamaki ganin ƙofar ta bude,ina sonki Ammi inajinki tamkar Mamuna wacce ta haifi Abbana,dan Allah ki amince min na dinga zuwa wajanki shira zaki ɗebe min kewan iyayena"ta ƙare mgnar tana ɗura kanta bisa cinyar Mai babban ɗaki ta shiga rera kuka.

Ɗan jim Mai babban ɗaki tayi tana tunanin abunda Zarina ke faɗa mata,ta kasa amincewa da kowa tun lkcn da aka saka mata poison a abinci,shiyasa har yanzun ta kasa amincewa da kowa sai Hadimarta Kaltume,ta kasa yarda da kowa bare ta bashi aminci,amma tun shigowar Zarina taji zuciyar tayi wasai tamkar an cire mata wani abu,taji a ranta ta yarda da ita ɗari bisa ɗari,ɗan numfasawa tayi kafin tasa hannu ta shafi kan Zarina tace.


"tunda zuciyata ta yarda dake babu shakka keɗin alkairice wani,na aminta dake ƙwarai,ohh ya bani breakfast ɗin"ta ƙare maganar tana ɗaga Zarina daga jikinta,farin cikine ya kama Zarin wanda ya sanya ta kasa dannesa,cikin farin ciki ta shige jikin Mai babban ɗaki tare da faɗin.


"Thank you soo much Ammi Allah yaja da ƙwana ya ƙara maki lafiya da ƙwanciyar hankali,Allah yasa ki samu lafiyar da zakina bani Bakilawa da hannunki masu albarka"ta faɗa tana zarw jikinta daga na Mai babban ɗaki.


Zuciyar Mai babban ɗaki ce ta ɗan buga kaɗan wanda ya haddasa mata saurin sanya hannu ta zafe saitin zuciyarta,maganar Zarina ta ƙarshe ta sanya ta tuna abubuwa da yawa,cikin sanyin murya tace.


"Allah sarki MALEEK Allah ya jiƙanka yayi maka rahama,lallai nayi kewanka kewa mai yawan gaske,kewan da baki bai isa ya faɗeta ba,kewan da saidai ka jishi a cikin rai da gangar jikinka,Rabbi rahamhuma kama rabbayani sa'ira,Ubangijin sammai da ƙassai ya bani hqr da juri ka ƙaramin ƙarfin imanin yarda da ƙaddara mai ƙyau ko akasin hakan"ta ƙare maganar tana lumshe idanunta hakan ya bawa hawayen dake ƙwayar idanunta damar sakkowa.

Kuka Zarina ta fara cike da tausayin Mai babban ɗakin,shuru tayi mata domin tasan kukan da zatai shine zaisa taji sauƙin data keji a ranta,saida ta tsagaita sannan ta tsiyaya mata kunun gyaɗan da tayi,kana ta miƙa mata amsa tayi ta soma sha saida tasha fiye da rabi kana ta ajjiye gefen tana ɗaukan tissue ta goge bakinta,murmushi tayi mai sauti wanda yake nuni da jin daɗi kana cikin harshen larabci tace.


"Jazakillah Rabbi yashi albarka,ɗiyata kin iya girki"dryan jin daɗi Zarina tayi kana tace.

"Ammi abincin da saura ai ga farfesun kayan ciki"girgiza kai Mai babban ɗaki tayi jikin jin daɗi tace.


"ayya ɗiya dama ƙwaɗon zogala ne saina ci,wannan kam na gode"


Sosai taɓa hira a nan Zarina tayi sallan zuhur da asar,sannan ta taimakawa Mai babban ɗaki tayi tana gamawa tayi mata sai gobe,domin hankalinta yayi wajan Saifu tana tunanin yaci abincin ko baici ba,da wannan tunanin ta fice daga ɗakin,ananma zobenta ne ya taimaka mata wajan ficewa,tana fita daga Bafade Kamal zaune hannunsa riƙe da wani ƙwano yana juya abincin,yana kallon yayi mata banza,itama taji daɗin hakan cikin saurin ta fice daga sashin ta nufi ɓangaren Saifu.



Cikin nutsuwa take tafiya,kanda a ƙasa gaba ɗaya jikinta rawa yake tamkar tarwaɗa musamman mai dai² cin hips ɗinta,tana jin zuciyar wasai ka sancewa da Mai babban ɗaki da tayi yau,ta fahimci abubuwa da dama akanta,babu abinda ya tsaya mata daga cikin maganganunta kamar yawan kiran sunan “Maleek” da take kuma yadda take abu zai tabbatar maka da wannan mutanan ba mutuwar Allah da Annabi sukai ba,kenan yaron data photonsa shine “MALEEK” ɗin?lallai idan shine Ubangiji yayi baiwar ƙyau,tana cikin tafiya yaji an jata zuwa wani lungo baki ta buɗe zatai ihu yayi saurin rufe mata baki da hannunsa,kasa buɗe idanunta tayi sabida yadda zuciyarta take tafasa sabida tsoro,cikin yanayi na shauƙi da kuma so yace.


"ban na isa na kiraki kizo ba ko?"wata ajjiyar zuciya ta sauke tare da buɗe idanunta ta manna akansa,sanye yake cikin wata ash ɗin Alƙyabba yayi shar dashi,sai a lkcn daga ƙyansa tabbas Prince bashi da makusa ko kaɗan a tsarin halittarsa,fari ne shi tas komai na jikinsa yayi ƙyau,kasa amsa shi tayi sabida wani kallo da yake mata,kanda ta sunkuyar ƙasa,ɗan matsawa yayi kusa da ita tare da zuba mata idanu cike da tuhuma yace.

"daga ina kike mene yasa bakizo jiya ba bayan kinsa ina jiranki?"ya jefa mata tambayar idanunsa a kan lips ɗinta da take taunewa,yana jin tamkar ya jawota jikinsa yayita kissing lips ɗinta,sosai wutar sha'awarta ke neman tarwatsa masa mara,yana jin wani zafi da raɗaɗi a kanta,duk lokacin da yayi kusa da ita yana jin yanayinsa na sauyawa sosai ya kejin wani a zababben sonta da ƙaunarta a ransa,kullum da marmarin jin ɗumin jikinta yake ƙwana yake tashi,a ɗan zaman da yayi da ita sai yaji mata da yawa sun fice a ransa,amma hakan ba shike nuna ya dayya ta rayya da mata ba,kullum cikin romantic yake da mata,ba koda yaushe yake ta rayya dasu ba,sbd bai son ya rasa ransu sosai suke ɗebe masa kewa,dukkan wacce ya ƙwanta da ita tace tana sonsa ne,sai yayi amfani da wannan damar ya amshe budurcinsu hankali ƙwance.
Jin tayi shuru babu magana yasa yayi saurin riƙe hannunta,cikin sauri ta ɗaga kanta ta kallesa tare da zame hannunta,cikin muryarsa daya soma sauya yawa sabida a zabban feelings ɗinta da yake yace.

"Ni zaki maida ɗan iska kome ina tambayarki kinyi shuru"girgiza kanta tayi a hankali kafinta cije leɓenta na ƙasa tace.

"kaina ke ciwo bayan nasha magani bacci ya ɗaukeni,yanzu kuma wajan Kulsum naje amsar kaya akace..."kasa ƙarasa maganar tayi sabida hangosa da tayi ya fito dafa fada yana tafiya cikin nutsuwa da izza haɗi da gadara tamkar ɗawisu,yana dafe yana lumshe idanunsa,sanye yake cikin dugun wandonsa na kakakin sojoji sai farar t.shirt wacce ta fito da murɗaɗan surar jikinsa mai ƙyau da tsari,sai picap daya sanya irinta wandonsa,picap ɗin ta rufe fuskarsa babu abinda ake gani saman fuskarsa sai jajayen laɓɓansa da kuma sumar kansa wacce ta sauka har wuyansa,ta gabansu yazu ya huci.

Wajan da take kallo shi yabi da kallo,tare da sakin wani shu'umin murmushi shi kaɗai yasan abinda zai shirya masa,idanunsa ya ɗauke yace.

"inajinki mene kike cewa?" lumshe idanunta tayi tana jin wani irin abu a zuciyarta me kama da kewa,wasu hawaye ne suka cika idanunta tayi saurin mai dasu sbd bata son ya fahimci rauninta,tabbas tasan cewa Saifudeen shine rauninta,ƙara taune laɓɓanta tayi tuna irin wulaƙancin da yayi mata jiya a gaban mutane,cikin dauriya ta kuma jarumta tace.

"Ancemin ka sanya Kulsum cikin ɗakin duhu dan Allah ka saketa ba danni ba"waro idanunsa yayi sai kuma ya saki dariya yace.


"taɓ nina manta da ita banda yanzu to Allah yasa ta tsira da ranta zanyi magana a saketa tunda kince"

Ɗaga ƙanta tayi alamar ta yarda,shurun da yayi mata yasa tace "zan huce magrib yazu"


"still baki sona ko?"ya watsa mata tambayar yana zubawa ƙirjinta idanu,girgiza kai tayi a hankali alamar "A'a"

Dariya yayi kana ya haɗe rai yace "idanma zaki koyi sona saiki koya dan wallahi Sai na aureki nine mijinki ba kowa ba"yana faɗin hakan yabarta tsaye.


Bayansa tabi da kallo cike da ɓacin rai, hawayen da take ɓoyewa ne suka sabi damar sakkowa daga cikin idanunta,cikin sanyin murya tace "ya rabb save me" tana faɗin hakan ta huce zuwa sashinsa.

Zaune ta sameshi a kan ladduma da alama Sallah yayi,kayan fruit kala² a gabansa gefe guda kuma system ce yake latsawa cike da ƙwarewa,ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta zubawa idanu musamman ƙwantaccen sajen daya zagaye fuskan tasa,lumshe idanunta tayi tare da sauke wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi.

Yadda zuciyansa ke beating vry past ga kuma yadda yaji tsigar jikinsa na tashi,ta babatar tana kusa dashi,ajjiyar zuciyarta ya ƙara gasgata cewa ita ce,ta gefen idanunsa ya zubawa ƙyaƙƙyawar farar ƙafarta idanu musamman yatsun ƙafarta wanda suke zara² abin sha'awa.

Durƙosawa tayi cikin rawan murya da kuma tsoransa daya kamata,wanda za'a iya cewa tsananin ƙwarjinsa ne da haibarsa yasa take ɗan tsorata dashi,ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tayi tace.

"what the you want?"

Sarai yaji me tace yayi banza da ita tamkar bai ji ba,a ƙaro na biyu ta ƙara mai² abinda tace,hannunsa ta ɗaga daga jikin system ɗin,a hankali ya joy da fuskasa tare da manna idanunsa akan tata fuskarta,lumshe idanunsa yayi kana ya ɗauke kansa tamkar bazai magana ba sai kuma yace.

"bana buƙata"ya bata amsa a taƙaice,kallonsa tayi sai kuma ta sadda kanta ƙasa lokacin hawaye ya gaba wanke mata fuska,cikin rawar murya tace.


"amma ba kaci komai ba"tsaki yaja sbd ta fara takurasa cikin gajiyawa yace.

"ina kikaje?"ya samu kansa dayi mata wannan tambayar,kasa yi masa ƙarya tayi dan haka tace.

"naje wajan Mai babban ɗaki ne"

Saurin ɗago kai yayi tare da sauke ajjiyar zuciya,kana yayi pouting lips ɗinsa tare da shafa sajen fuskarsa haɗi da jan ƙaramin gemunsa,cikin daddaɗar murya mai amo yace.
“FARIN CIKINA"..



*KUYI MAGANE PLS👏🏻*

*THE NEW EMIR IS NOT FREE IS FOR SALE 08119237616*
*29-30*




“Farin cikina”ya ƙara mai-mai tawa cikin zuciyarsa amma yanayin yadda laɓɓansa suke juyawa zai tabbatar maka da abinda yake faɗi,lumshe idanunsa yayi tare da pouting lips ɗinsa,a dukkan lokacin daya tun Abbunsa da kuma soyayyar da yake masa sai yaji wani farin ciki na musamman a ransa,dalilin hakan yake kiransa da suna “FARIN CIKINA”.
Zuba masa idanunta tayi tana mai ƙara gasgata baiwa da tsarin halittarsa,yadda zuciyarta ke kaɗaituwa da son ganin fuskarsa ya sanya ts ƙasa ɗauke idanunta daga garesa sabida nutsuwar da take samu a dukkan lokacin da tayi kusa dashi,mai yasa a koda yaushe zuciyarta ke muradin ganinsa? Mene yesa bata iya jure ganin ƙwayar idanunsa?,Mene yasa ta kejin faɗuwar gaba idan tana kusa dashi?,Mene yasa zuciyarta ke buga indai ta gansa",Mene yasa ta kejin wani irin yanayin na shauƙi mai kama da feelings idan ta tunashi?,wannan tambayar a koda yaushe ta kewa kanta amma ta gagara samun amsarsu.

Sosai ya kejin idanunta a kansa ya shareta ne domin yasan hakan shine abinda take buƙata,yadda take sauke ajjiyar zuciya kaɗai zai tabbatar masa da abinda yake cikin rai da zuciyarta,a karon farko ya saki tattausan murmushi wanda ya bayyanar da fararan jerarrun teeths ɗinsa.

Wata ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfin gaske,ta ƙara bajewa kan carpet ɗin,sosai murmushinsa ya kusa zautar da tunaninta,wani irin mood ta fara shiga mai wuyar fassaruwa a zuciya,a hankali ta janye idanunta daga garesa tare da kullesu,ita kaɗai tasan mene ta keji a zuciyarta dama gangar jikinta gaba ɗaya,hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa ne ya samu nasarar sauka daga cikin idanunta,taune laɓɓanta tayi cikin ranta tace.

"this is no time for love there's something big dake gabana".

"coffee"shine abinda daji yace a taƙaice,jiki babu ƙwari ta miƙe ta nufi kicthen tana zuwa ta haɗa masa coffee tare da haɗa masa fruit salad mai ƙyau,tana kammalawa ta jera saman saman tray,cikin nutsuwa ta ƙarasu inda yake,zuwa yanzu ya kammala abinda yake ya cire rigar jikinsa,hakan ya bawa faffaɗan ƙirjinsa nasarar bayyana,sumar ƙirjinsa tayi luff sai ƙyalli take,ya lumshe idanunsa tare da cusa hannunsa cikin sumar kansa,saurin ɗauke idanunta tayi daga garesa.

Durƙusawa tayi gabansa tare da ɗaukan wani cup glass ta zuba masa coffee ɗin a jiki,cikin rawar murya tace..

"take ur coffee"sai a lokacin ya ware idanusa tare da saukesu a kanta,amsa yayi ya soma sha ba tare daya ɗauke idanunsa daga gareta ba,sai da ya shanye tas sannan ya miƙe tsaye.

"amma fruit ɗinfa?"ta samu kanta dayi masa wannan tambayar ganin baiko kalli fruit ɗin ba,ɗan tsayawa yayi tare juyowa ya kalleta kana ya ɗauke kansa yace.

"am ok,uhm yawwa kidaina saka wannan kayan sai kace likkafani,kaya duk sunyi datti amma a haka kikeson yin girki naci,ohhh ya Allah Abbuna kana can ana azabtar makani akan yunwa"ya ƙare maganar yana rausayar da kansa gefe.

Baki ta saki ganin yadda yayi mata wani mugun ƙyau ga yadda shagwaɓa ta zauna a jikinsa tamkar yaron baya,samunta tayi da faɗin.

"bana da wasu kayan ai"ta faɗa tana zubawa bayansa idanu.

"baki damu dasu bane amma kaya sun daɗe a bedroom ɗinki"yana faɗin hakan ya sakai ya fice daga parlour ya shige bedroom ɗinsa.

Miƙewa tayi itama ta shiga bedroom ɗin da take tunanin shine wanda yake magana,tana shiga taga kayan da sukai shopping shekaran jiya,da sauri ta buɗe taga Abaya ne kala² da hijab masu yawa sai fakistan,sai kuma kayan shafa lotion powder,lipstic,parfume,da sauransu.

Wanka tayi tare dayin alwala tana fitowa ta saka wata pech ɗin abaya mai ƙyau wanda hannunta yake abuɗe,tamkar an gwada da jikinta haka abayar ta zauna a jikinta,hijab ta saka tayi sallah kana ta fesa wani parfume daɗin ƙamshi ga sanyi,parlour'n ta koma ta ɗauki fruit ɗin daya ƙi sha ta shanye sannan ta maida kayan kithen,parlour ta koma ta ɗan ƙwanta saman kujera lokaci kaɗan bacci yayi gaba da ita.


Misalin 2 na dare ya fito cikin shigar kayan baccinsa farare tas masu ƙyau da tsari,yana ƙoƙarin shigewa kicthen ɗin ya ganta ƙwance akan parlour ta cure waje guda da alama sanyi ta keji.

Zoba mata idanunta yayi kana ya taɓe baki haɗi da cije lips ɗinsa,cikin nutsuwa ya ƙarasu inda take tare da sanya hannu ya ɗagota zuwa jikinsa baki ɗaya,dicret bedroom ɗinta ya nufa,ƙamshin daya daki hancinta ga yadda fresh skin ɗinsa ta haɗu da tata yasa ta ƙara shige jikinsa ta tura fuskarta cikin ƙirjinsa,dukkan abinda take yana jinta amma ko ajikinsa,yana ƙarasawa ya shimfiɗeta akan bed ɗin tare da rufe mata jiki da duvet.

Juyawa yayi zai fita yaji tayi saurin kama hannunsa tare da tura yatsanta cikin bakinta ta soma tsotsa tamkar sweet,ɗan waro idanunsa yayi tare da saurin lumshe idanunsa jin yadda tsigar jikinsa ke miƙewa ga wani shock daya kamasa tamkar wutar nefa,saurin zare hannunsa yayi tare da fice a bedroom ɗin,yana zuwa parlour ya faɗa saman sofa tare da lumshe idanunsa ya shiga sauke numfashi,ya daɗe kafin ya samu bacci yayi gaba dashi.



*_Washe gari_*
A hankali ta shiga buɗe manyan gajiyayyun idanunta wanda sukai mata nauyi,sabida daɗewa da tayi tana bacci,cikin kasala ta miƙa hannu tare da kashe alarm ɗin da ruri a bedside,miƙa tayi kana ta zura da santala-santalan ƙafafunta zuwa ƙasa,sai a lkcn ta fahimci a bedroom take amma yaya akai ta shigo nan bayan a parlour ta ƙwanta? Fuska ta yamutsa tare dayin magana a zuciyanta.

"nikam da mantuwa nake may be a bedroom ɗin bacci ya ɗaukeni"ta ƙare maganar tana tattare sumar kanta tare da ɗaureta da ribbon,kayan jikinta ta cire tare da zobasu wajan datti clothes,a ɗan zurace ta juya sai kuma ta saki ajjiyar ganin ƙofar ɗakin a rufe sbd naked take kuma ALLAH ya zoba mata kunya,a gaggauce ta faɗa toilet tare da sakarwa kanta shower,sosai ruwan ke dukan fatar jikinta,bayan ta kammala tayi brush kana ta ɗaura alwala,wani light blue ɗin towel ta ɗauka tare da ɗaura a jikinta,sannan ta juna handrayer bayan ta kammala busar da kanta ta fito daga toilet,cikin sauri ta fara shafawa naked fresh

10 / 38