Author : Na'ima Suleiman Sarauta Category : Romance
a jikin hannunsa,ya sani kowa ya sani ko wacce masarauta kallan zanan tambarinta daban yake,kamar yadda zanan masarautar bilhas yake daban.
indai ka zuba idanu aƙwai zanan masarautar bilhas a jikin gurun,zuciyarsa cike da tulin tambayoyi ya nufi part ɗinsa,yana zuwa ya zare alƙyabbar jikinsa tare da saƙaleta a wardrope side,direct bathroom ya shige yana zuwa ya tsaya gaban shower tare da sakarwa kansa ruwa sanyi.
wani huci ya fesar mai zafin gaske zuwa yanzu babu abinda ya keso yaji sama da jin tarihin wannan gurun,shin daman wani na iya mallakarsa wanda ba jinin sarauta ba? ko kuma ana iya bawa wani ba tare da cewa shiba jinin sarauta bane? ƙwarai da gaske yana son sanin wannan amsoshi.
wani sassanyan murmushi ya saki lkc'n daya tuna yau ɗinfa zai mallaki farin cikinsa hakan yana nuni da cewa Mai martaba ya rasa CIKAR BURINSA? ya tambayi kansa cike da farin cikin da yake ciki.
mararsa da yaji tana halbawa yay saurin kalla sai kuma yay dry wacce shi kaɗai yasan ma'anarta.
a gaggauce ya ƙarasa wankan kana ya fito ɗaure da towel a jikinsa.
Meyrah ya samu zaune gefen bed ɗinsa tana danna waya kallonta yay tare da faɗin.
"kin shigomin ɗaki without my permission,daga yau dai ƙya rage shigomin bansam matana ta fahimci abinda yake tsakaninmu,mare ta sanya zargi cikin zuciyarta,rayuwar aure mai tsafta na keso nayi da ita,da gske nake son ZARINA zan iya komai indai akanta ne,haka kuma zan iya ganin bayan wanda yace zai shiga tsakaninmu da ita i love her with all my heart ina jin zan iya rasa rai dalilinta she is my life for ever,so Meyarh ki tayani killace abinda nakeso kema sai kisamu abinda kikeso gareni"
ya ƙare maganar yana zama saman stool wanda yake gaban dressing mirrow,versiline ya ɗauka ya fara shafawa saman farar fatar jikinsa.
murmushi Meyrah tayi kana ta soma takawa zuwa inda yake zaune tana zuwa ta amshi man ta fara gogawa a hannunta kafin ta ɗura hannunta akan naked body ɗinsa,kiss ta manna masa a wuyansa kafin taci gaba da shafa masa versiline ɗin tace.
"so what about me? i mean mene matsayina idan PRINCE NAJEYB ya samu farin cikinsa bayan wargatsa burin wani da yayi"
"matsayin yana nan indai yake bawai sauyawa yay ba,kinan matsayin Dadirota,idanma matsayin ya sauya sai dai ya koma ƘWARƘWARATA shine kawai"
Lil prince ya faɗa lkcn da yake fesa parfume a jikinsa,miƙewa yay ya nufi wajan wardrope ɗinsa wani yadi ya ɗauka mara nauyi kana ya sanya alƙyabba a saman yadin sosai yay sabida farartarsa data amshi yadin,domin Lil prince shima ba baya bane wajan ƙyau.
yana gamawa ya ƙwashi wayoyinsa da key ɗin motarsa,sai a lkcn ya lura Meyarh bata ɗakin murmushi yay kana ya fita daga part ɗin tare da bawa barorinsa umarnin gyara masa part ɗin.
yana faɗin hakan ya nufi Fada wajan Mai martaba domin zuwa yanzu yasan ba'a kammala ɗaurin auren ba.
Da sauri ya ɗago kansa daga cikin ruwan jakuzzie ɗim,tare da sauke wani wahalallan numfashi,ƙwarai ya saba da shiga ruwa komai yawansa amma yay mamakin yadda ruwa kaɗan ya keson tafiya da numfashinsa ba tare daya kula da hakan ba.
a hankali kuma a sanyaye haɗi da raguwan ƙarfin daya rage masa a jiki ya zuro da ƙafafunsa daga cikin jakuzzie'n kana ya miƙe tsaye daga ciki tare da fita gaba ɗaya daga cikin jakuzzie'n,idanunsa da sukai jaa sabida ruwan daya shigesu ya buɗe a hankali tare da mannasu a mirrow'n dake banne a cikin bathroom ɗin,cikin kasala ya ƙarasa gaban shower tare da sakarwa kansa shower'n,a karo na biyu ya ƙara sakin numfashin tare da gyara tsaiwarsa a tsakiyan shower'n ya sanya duka hannunsa ya dafe jikin bangon ruwan ya fara dukan fresh chocolate skin ɗinsa.
wanka yay sosai har saida yaji skin ɗinsa nayi masa zafi sannan ya hqr ya koma wajan sink yay brush tare dayin al'walar asar.
meddium towel ya ɗauka ya ɗaura bisa waist ɗinsa,kana ya juna handrayer ya soma busar da gashin kansa wanda yay ƙwance sai zuba sheƙi da ƙamshi yake sabida mayukan da yaji na gyara,sosai ya gyara gashin kansa yay lub lub saman wuyansa sai walwali yake.
kashe handrayer'n yay tare da ajjiyeta gefe guda,sannan ya mayar da man wanke baki ma calgate ma zauninsa,pouting lips ɗinsa yay yana jin yadda cikinsa keyi masa kukan yunwa,wajanwa zashi yace abinci ya keso? wane yake dashi mai kula dashi?wa zai faɗawa damuwarsa a wannan lkc'n?.
wannan duk haƙƙin uwane amma shi tayi masa nisa,nisan da baza ta taɓa dawowa garesa ba,tabbas shi ɗin yana da rauni,rauni mai yawan gaske.
da ace zai samu madadin uwa babu shakka zai zauna ya fito da sirrin zuciyarsa gareta ko hakan zai sanya yaji daɗin a ransa,zugi da raɗaɗin da zuciyarsa yake masa ya daina.
a nutse ya fito daga cikin bathroon ɗin,wajan dressing mirrow yaje ya ɗauki lotion mai sauƙin zafi ya fara shafawa sai daya kammala ya ɗauki body spray ya fesa saman fararsa,yana gamawa ya nufi wajan wardrope ya ɗauki wani long dark blue crazy ya sanya tare da wata amy ɗin colour ɗin riga irinta sojoji,wacce ta kamasa sosai ta zauna a jikinsa tare da amsar duhun fatarsa.
sosai six part body ɗinsa suka bai yana tare da faffaɗan ƙirjinsa,ƙara lumshe idanunsa yay a hankali ya ɗura hannunsa saman beard ɗinsa wanda ya ƙara yawa a fuskarsa.
wajan dressing mirrow ya nufa ya ɗauki uhudmood ya fesa a jikinsa.
datse tongue ɗinsa yay kana ya nufi wajan frigde ya buɗe,wani banana yogourt ya ɗauka tare da wani fresh milk haɗi da gurar ruwan sanyi,yana ɗauka ya nufi parlour ajjiyewa yay a kan senter table ya nufi kitchen ya ɗauko wani glass cup.
dawowa yay ya zauna bisa kan sofa tare da ɓalle murfin fresh milk ɗin ya tsiyaya a glass cup ɗin.
komawa yay jikin sofar tarr da nutsewa a jikinta,a hankali ya manna glass cup ɗin saman laɓɓansa,sanyi da gargaɗin daya jine ya sanya shi lumshe idanunsa ba tare daya shirya hakan ba.
cikin nutsuwa yaci gaba da shan fresh milk ɗin,yana yi yana ƙarawa a glass cup ɗin harya shanye fresh milk ɗin.
wayarsa dake kan table ɗince ta fara ƙara idanunsa dake lumshe ya buɗe tare da mannasu a saman screen ɗin taune lips ɗinsa yay ya ƙara manna gorar ruwan a bakinsa,saida ya shanye tas sanna ya ɗauki wayarsa yay dailing number da aka kirasa da ita.
jinjina kai yay a hankali ya ware laɓɓansa murta can ƙasa yace.
"okey"
miƙewa yayi tare da ƙwasar key ɗin part ɗin haɗi da wayoyinsa ya nufi hanyar fita a gidan,sai daya rufe part ɗin sannan ya fara tafiya cike da nutsuwa da kuzari haɗi da zallar izza yake taka ƙafafunsa.
duk inda ya keta barori da kuyangu ne suke gai dashi tare dayi masa barkar fitowa,da idanu kawai yake binsu,yadda juya manyan ƙwayar idanunsa shi kaɗai zai nuna masu cewa yana amsa gaisuwar tasu,harya ƙarasa part ɗin mai babban ɗaki.
a gadarance ya shiga cikin Fadar tare da ƙarasawa gaban Mai martaba ya zauna,mutanan Fadar ya gani ƴan tsirari,wani killer smile yay sabida yasan inda suke.
kansa ya sunkuyar ƙasa sai kuma ya ɗago ya kalli mahaifin nasa yace.
"Allah ya ƙarawa Mai martaba lafiya da nisan ƙwana,wani abune yake ɗauremin kai harya saka bazan iya shuru da baki ma ba,ina son ƙarin bayani akan GURUN wannan masarautar!"
Murmushi Mai martaba yay kana ya gyara zaman alƙyabbar jikinsa,numfashi ya sauke tare da gyara murya,cikin nuna shiɗin Sarki ne mai cikakken iko da kuma izza yace.
"Shi GURUN da kake magana akai ya samu asaline tun iyaye da kakanninmu wanda sukai mulki a wannan masarautar,haka kuma dukkan wanda ka gani da wannan Gurun babu ko tantama wata rana zai iya gadar kujerar wannan garin na bilhas,shi kansa Gurun anyi sane da tambarin masarautar kuma tun mutum yana ƙarami kakansa wanda yake Mulki a lkc'n yake sanya masa,wannan shine a taƙaice"
wani gumine ya shiga karyo masa a fuska,cikin tashin hankali ya sanya hannu ya goge gumin tare da faɗin.
"aƙwai matsala idan hakane aƙwai tashin hankalin da yake shirin tun karomu ba tare da mun shirya masa ba"
cikin rashin fahimtar Mai martaba yace.
"man gane ba,what are you try to tell me wacce irin tashin hankali kuma,harmu wani tashin hankali zai ɗagawa hankali kai bai zai taɓa yiwuwa ba muna da ƙarfin ikon da zamu hana faruwar hakan kuma..."
"A'a Mai martaba yadda kake tunanin abun ba a haka yazu ba,tabbas lukutar matsala na shirin zuwar mana,idan nace lukutar matsala ina nufin tafi ƙarfinmi mulkinmu bazai iya yi mana maganinta ba,abinda na keso na tambayeka shin aƙwai wani ɗa da kake dashi ne bayan ni?"
lil prince ya katse Mai martaba ta hanyar faɗin hakan.
rikitattun idanunsa ya zubawa Prince,yana gudun ace sirrin da yake ɓoyewa na tsahun shekaru masu yawa su bai yana a yanzu,baya jin tsoron abu amma a yanzu ƙwarai yana jin tsoron amsar tambayar NAYJEB ɗin,bashi amsar wannan tambayar yana nufin abubuwa masu yawan gaske,babu yadda zai dole zai faɗi wanan sirrin koda hakan na nufin Prince zai ɗaukesa matsayin mugun uba,numfashi yaja tare da buɗe baki zai magana su Chiroma suka shigo cikin fadar cikin wani sabon tashin hankali.
kallonsu yay,Prince kam saurin miƙewa yay tare da ƙarasawa wajan Chiroma haka kawai yake ganin girman mutumin ya kejinsa tamkar Mai martaba baya iya tsallake umarninsa.
"baba Chiroma am ɗaura? ina matata? tana ina naje gareta?"
ɗauke idanunsa Chiroma yay daga kallom Lil prince sannan ya kalli Mai martaba yace.
"an nemi Kuyanga Zarina babban tashin hankali shine babu ita a masarautar bilhas,dukkan inda ake tunanin ganinta babu she alrdy left"
ya faɗa yana sauke numfashi,da sauri Mai martaba ya miƙe tsaye cikin ransa yace.
"hakan na nufin asirin dake jikinta ta warware,ohhh wow sai yanzu na fahimci dalilin daya sanya Zaitun dana tsaface ta daina bani kuɗi"
a zahirance kuma kallonsu yay yace.
"zata dawo da kanta kada ko damu da hakan"
prince kam durƙoshewa yay wajan yana jin zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske,gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya ya rasa mene ya sanya yaji tsoro da fargaba barinta masarautar,cikin tashi hankali ya miƙe ya kalli Mai martaba yace.
"tashin hankali biyu lkc guda,ka manta da ɓatan Zarina kayi tunanin GURUN dake Manne jikin Captain Saifudeen domin wannan gurun da nake magana akai shine yake manne jikin hannunsa"
yana faɗin hakan ya fice daga cikin fadar cike da tashin hankali.
Saifu.
a hankali ya durƙoshe gaban Mai babban ɗaki bayan ya kuri Kuyanga Kulsum da Hadima Kaltume.
rikitattun idanunsa ya zubawa Mai babban ɗakin,soft hand ɗinsa ya sanya ya riƙe hannun Mai babban ɗaki yace.
"zuciyata ciwo Ammi meyasa zata tafi ta barnin a cikin halin dana shiga,shin daman ba sona take ba,Ammina bazan iya jurewa ba soyayyarta ta gama ratsa jini da tsokar jina,itace rayuwata bazan jure rashinta ba Ammi yaya zanyi da zuciyata wacce ta mace akan son ƙaramar yarinya,yaya zanyi Ammi?"
ya faɗa yana sauke wani numfashi da ƙarafi sosai maganar tayi masa tsayin gaske,amma babu yadda zaiyi dole ya furta koya samu sauƙi cikin ransa.
so wannan dalilin ya sanya kullum ya kejin faɗuwar gaba na shigarsa,wannan dalilin yasa a koda yaushe baya da wani tunani sai nata,wannan dalilin ya saka kenan kullum yake mafarki da ita,shin yaya zaiyi? mene matsayin zuciyarsa?.
wannan dalilin ya saka bai taɓa sanya wannan cikin ransa ba,bare harya tun kareta matsayin yana sonta ba.
yafi yadda a kullum ya zauna da heart dream ɗinsa,yafi samun farin ciki idan yay tuzali da ƙyaƙƙyawar surar Aljanarsa,wacce ta gama sace masa zuciya cikin baccinsa.
sai gashi ta bai yana matsayin mutum kuma sun haɗu wajan da bai taɓa tunanin hakan ba.
shin kodai daman Aljanace da gaske?
shikam a yadda ya kejin zallar soyayyarta da kuma ƙaunarsa ya saka bazai iya rayuwa babu ita ba,ya shirya rayuwa da ita koda ita ɗin aljanace ba jinsin saba.
rayuwa babu ita tabbas hakan na nufin tsaiwar numfashinsa,idan yace haka kuma ya nufin bugawar da zuciyarsa zatai ta dalilin rashin samun mahaɗinta.
yana jin sonta sosai kuma zaiyi ƙoƙarin ganin ya samu MURADIN ZUCIYA,zai nemota kuma tabbas SAI NA AURETA!!.
ya faɗa da ƙarfi cikin zuciyarsa,zai ƙoƙarin samun mafaɗin rayuwarsa komai wahala kamae yadda ANWAR yay a ƘADDARAR MACE.
zai zama cikakken namiji mai tsayawa a kan ra'ayinsa kamar CAPTAIN YISHAM, zai jure dukkan wata wahala kamar yadda MUKKATAR TIJJANI M.T ya jure.
zaiyi faɗa da kowa a kanta kamar yadda FAHAD yay.
haka kuma zai toshe kunnuwansa daga jin surutan jama'a like IRFAN,zai zama marajin magana zai zama ɗan iskan kanshi a kanta kamar yadda *_MUHAMMAD KABEER MUHMMAD_* YAY A KAN HIBBA ta jure dukkan wani iskancinsa domin tana tunanin mijinta ne ashe......🏃🏻♀️ all in *_UNCLE NE.!!_*
ƙwantar da kansa yay saman cinyar Mai babban ɗaki ya shiga sauke ajjiyar zuciya,lumshe sexcy and beauty eyes ɗinsa yayi yana sauraran zuciyarsa dake beating kamar zata fito.
ƙara sauke numfashi yay dalilin saukar hannun Mai babban ɗaki da yaji saman sumar kansa.
a hankali taci gaba da hargitsa masa ƙwantaccen gashin kansa tare da bubbugawa bayansa cikin son ƙwantar masa da hankali ta fara rera masa waƙa cikin yaran kanuri na Igbora koto.
"Tawo tawo ɗan yaro ƙyaƙƙyawa in maka tawai,gaka fari fari wuya sam baka shaba"
haka ta dingayi masa waƙar cikin zazzaƙar raguwar muryarta wacce tsufa ya fara kamawa,still kuma tana bubbuga gadon bayansa.
ƙara lafewa yayi jikinta yana sauke numfashi kafin daga baya ya ɗan sakar mata nauyinsa tare da ƙwanciya a kan sofar ya ɗura kansa a jikinta ya zagayeta da hannunsa ya fara sakin wani sabon ajjiyar zuciyar.
saukar numfashinsa mai zafi ya saka ta gane cewa bacci yay gaba dashi,a hankali ta shafi kansa tare dakai baki ta sumbaci goshinsa..
kogi
farin cikin daya cika zuciyar Tupic ne ya sanya ya shiga tsula gudu saman ƙwalta,babu jimawa suka ƙarasu unguwar Gauters horn yay cikin sauri mai gadi ya buɗe masa get ɗinsa,da sauri ya sako hancin motar cikin compound ɗin gidan.
a gaggauce ya ƙarasa parking ya fito daga motar lkc'n Zarina itama ta fito zagayawa yay wajanta ya riƙe hannunta suka nufi cikin gida.
tun a ƙofar babban parlour ya fara ƙwararawa mutum gidan kira ɗaya bayan ɗaya.
mom dake zaune tana haɗawa Sufyan Coffee wanda ya cika yay fam sabida matsifar da Mamu take maza naya shirya suje asibiti a duba mata lafiyarsa daya sanya bazai yi aure yanzu ba,gashi har Tupic ya nemu mata.
murmushi Mom tayi tace.
"naga lkcn da tawayen samarin gwarazon yarana zasu girma,kai ka sanyani gaba kana mita,shi kuma jibi yadda yake ƙwalan kira kamar bai san inda zai sameni ba,kai nidai naga banu nikam ku shafamin lafiya,ai wallahi Mamu itane maganinku oyyyaa amshi kaban waje"
Sufyan kam muryar wacce yaji ya sanya bazai iya bawa Mom amsa ba,baki kawai ya saka yana son gasgata abinda ya gani.
Zarina wacce ta biyo bayan Tupic da gudu tayi wajan Sufyan tana zuwa ta faɗa jikinsa ta rungomesa tare da sakin kuka.
shima rungometa yay sosai jikinsa danya kasa cewa komai.
Mom kam farin cikine yay mata yawa ya sanya ta durƙoshe wajan tayi Sujudul shukkuri,tayi Allah gdy,kana ta shiga kiran Mamu da Abba.
kusan a tare Abba da Mamu suka fito suna zuwa Mamu tayi wajan Zarina dake jikin Mom.
"kai Ubangiji abin gdy masha Allah yadda na ganki Allah ya sanya naga aurenku gaba ɗaya"
sosai gidan sukai farin ciki da ganin autar gidan Zarina,koya faɗi yake mene ta keso me za'a kawo mata,Abba kam kasa magana yay sai juyawa da yayi zuwa cikin part ɗinsa.
Mamu ce ta gyara zama tace.
"Zarina kema na baki mako guda cif ki fito da mijin aure wannan girman naki tsoro yake ban,har yanzu baki rufa 18 haba"
zaro idanu Zarina tayi tare da turo baki ta shagwaɓe fuska tace.
"kema Mamu matsalata dake takura,ina laifin kimin maganar karatu gaba ɗaya nawa nake haba aure fa"
baki Mamu ta riƙe lkcn kam so Sufyan tuni sunbar waja sabida gudun kada faɗan ya dawo kansu tace.
"Ubanki Audu shine mai takurar bani ba,yarinya nono duk ya gama cika ƙirji kicemin wai aure,tun kina shekara 15 kika fara al'ada kuma hakan na nufin kin isa aure kin isa ɗaukar buƙatun namiji"
da sauri Mom ta miƙe tsaye cike da mamakin abinda Mamun ta faɗa,da sassarfa ta ƙara part ɗinta dan tasan yanzu faɗan zai dawo kanta.
haka Mamu ta ƙaraci faɗanta ba tare da Zarina ta ƙara cewa komai ba,zuwa yanzu ita hankalinta ya tafi ga aljaninta na cikin dare.
washe gari a bilhas.
a hankali ya sauke idanunsa daga screen ɗin wayarsa bayan ya gama ƙarewa ƙyaƙƙyawar fuskarta kallo.
lumshe idanunsa yay tare da taune laɓɓansa ya jin yadda zuciyarsa keyi masa zafi da kuma raɗaɗin rashin abokiyarta.
ware idanunsa yay tare da saukesu a fuskar Mai babban ɗaki wacce take zaune a kan wata ladduma mai laushin gaske.
a hankali ya murza daimond ring ɗin hannunsa kana ya sanya hannu ya shafi sajen fuskarsa zuwa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa,sosai yake cikin damuwa ta dalilin rashin ganin gimbiyarsa.
ture ƙwaɗon zugalan da Hadima Kaltume tayi masa yay,tare da miƙewa tsaye ya sauke numfashi,yana ƙoƙarin fita yaji wayarsa ta fara ringing a hankali ya sanya hannu ya ɗauki wayar a cikin aljihunsa kana yay rejecting kiran,2minutes yay dailing number ringing biyu tayi aka ɗauka.
can a ƙasar Cameroon kam Alhaji Bilyaminne ya gyara zamansa yace.
"Suger na inaka shigane har haka,tun jiya ina kira shuru?"
lumshe idanu Saifu yay yana jin sanyi na ratsa jikinsa,sosai yaji daɗin jin muryar Abbun nasa a cikin kunnansa.
ɗanya mutsa fuska yay tare da langwaɓar dakai gefe guda,cikin cool and sweet voice ɗinsa yace.
"Abbuna..!!"
kafin ya ƙara magana yaji kirarin Fadawa alamun Mai martaba ne zai shigo,taɓe baki yay tare da ƙara manna wayar a saman kunnansa ya neman wajan zama yaji muryar Mai martaba a kansa yana faɗin...
_so sorry sweetheart double sorry afuwan afuwan🏃🏻♀️😂😂😂_
THE NEW EMIR IS FOR SALE 08119237616
*NIMCYLUV🤏🏼🔥*
*65_66*
Da kata a nan Captain Saifudeen.
Mai martaba ya faɗa cikin isa da kuma iko yay maganar ne bisa bada umarni,hakan na nuni da dukkan wanda akaiwa ita dole ne yabi maganar ko yaƙi ko yasu.
Tsayawa Saifu yay ba tare da yay magana ko kuma ya juyo ba,daga can ɓan garan cike da mamaki Abbu ya ɗan miƙe tsaye tare da sakin numfashi yace.
"Saifudeen kaida waye haka?"
da yake indai magana mai muhimmanci ce Abbu bai fiye ɓoyewa Saifu sunansa ba.
tsaiwarsa ya gyara tare da lumshe gajiyayyun idanunsa wanda suke cike da bacci,kana ya sanya hannu ya shafi ɗan lafaffan cikinsa,daimond ring ɗin hannunsa ya zubawa idanu ganin yadda yake ta haske.
"Are you with me? Yarona meke faruwa ne?" kayi