THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   34 / 38

99K to 102K   out of 111.1K words

tsaye tare dayi mata sai da safe kana yay ficewarsa waje.
itama miƙewar tayi ta nufi nata part ɗin gidan yay shuru baka jin komai sai wata sasaanyar iska dake kaɗawa,sai kuma raguwar yayyafin da ake har yanzu.

Mai martaba Khalid ne zaune gaban Fulanin sura yayinda ita kuma take gefensa ta zabga tagumi,sai ajjiyar zuciya take saukewa hakan alamace take nuna taci kuka ta ƙoshi.

"shi daman haka lamarin Ubangiji yake,shiyasa a koda yaushe akeso mutum ya dinga aikata alkairi zuciyarsa ta zama mai kyau kuma tsaftatacciya,yanzu kalli yadda son zuciya yakai ka,ka gode Allah daya jarabceka da samun shege a zuri'arka banda haka baka san inda haƙƙin wannan mutanan zai kaika ba"

sosai jikinsa yay sanyi gefe guda kuma zuciyarsa fal tsanar fulani kilishi rayuwa kenan daman duk wanda yace tukunyar wani bazai ta fasa ba tasa ko zafi ba zatai ba.


*_Kogi_*
Misali 11 na safe jirgin yake sauka a hankali,11:30 parsinger suka fara sakkowa saida mutane wajan 30 suka sakkowa daga cikin jirgin amma babu shi.

"anya yazo kowa gashi kusan rabin mutanan ciki sun fito?"

Tupic ya tambaya yana mai ƙara juya ƙwayar idanunsa akan jirgin,wani murmushi Sufyan yay kana ya kalli jirgin sai kuma ya kalli Tupic ɗin yace.

"babu shakka zaizo domin baya magana biyu na bashi nan da five minutes bari kaga"

Sarki Maleek kowa sauke numfashi tare da lumshe idanunsa sabida yadda yaji bugun zuciyarsa na ƙaruwa fiye da ko wanne lkc,ya tabbatar tana kusansa domin akanta kaɗai yake samun irin wannan yanayin cikin sabon mood daya shigesa,ya sanya hannu blet ɗin daya ɗaure jikinsa da ita.
cikin nutsuwa ya miƙe tsaye tare da fara tafiyar nan tasa mai cike da kuzari.
Fadawansa na ganin haka soma suka mimmiƙe tsaye tare dayi masa ƙawanya.
cikin isa da kuma izza haɗi da kuzari ya fara taka steps ɗin benen.

Tupic da idanunsa ke manne a jikin jirgin yay saurin faɗin "wow! Ubangiji yay halittar baiwar ƙyau ƙwarjini haiba da kuma cikar zati ban taɓa ganin Sarki wanda ya dace da sarauta irinsa ba,komai nasa nada banne,dobi yadda yake tafiya kamar wani ɗawisu,wannan shine THE NEW EMIR da ake magana na bilhas kenan masha Allah amma.."

Afusace Sufyan yay saurin sanya hannu ya tushewa Tupic bakinsa cikin ƙasa da murya yace "haba Tupic mene haka ko yawo baka haɗiya sabida tsaɓar surutu,ni wlh na rasa halinwa ka ɗauko dan Allah ka dingayiwa bakinka linzami ok"

rausayar dakai Tupic yay tare da haɗiye sauran maganar a bakinsa,ƙara gyara tsaiwarsa yay gaba ɗaya ya maida hankali ga Sarki Maleek dake taka steps ɗin cikin kuzari kamar wani zaki.

cikin kuzari da jarumta yaci gaba da taka steps ɗin benen jirgin yayin Fadawa suke bayansa,gefe guda kuma Khamis ne riƙe da jakar kayan Sarki Maleek.
sanya yake da wata hadaɗɗiyar milk ɗin alƙyabba wacce akai mata ratsi da kuran ganye.
sai farin rawanin daya zagaye ƙyaƙƙyawar fuskarsa,sai farin glass daya manna saman idanunsa,yana tafe yana dugara sandar girmansa.

da sassarfa Sufyan ya ƙarasu wajan babban abokin nasa,tsayawa Sarki Maleek yay tare da ware hannayensa,ganin hakan ya sanya Sufyan ya ƙarasa da sauri ya rungome abokin nasa.
ɗan bubbuga bayansa Sarki Maleek yay tare da janye jikinsa.
cikin girmamawa Sufyan ya fara zamewa zuwa ƙasa sai gaidashi.
da sauri Sarki Sufyan ya sanya hannu ya ɗagosa kana ya ɗan dungure masa kai ya saki wani tattausan murmushi.

"nayi farin ciki da zuwanka boddyna,ashe da gaske kake zaka halarci taron bikina"

lumshe idanu yay tare waresu a fuskar Sufyan ɗin,kana ya ɗan matse hannun Sufyan ɗin dake cikin nasa,hakan ya tabbatarwa da Sufyan abinda Sarki Maleek yakeson faɗin.

tun kafin so ƙarasu Tupic ya buɗe masa side ɗin baya,suna ƙarasuwa Tupic yay saurin faɗin "Allah ya ƙara maka lafiya sannu da zuwa"
murmushi Sarki Maleek yay tare da miƙawa Tupic hannu sai a lkc laɓɓansa suka samu sa warewa kaɗan cikin ƙasa da murya yace.

"Assalamu Alaika Tupic"

baki Tupic ya saki domin baiyi tunanin yana jin hausa ba bare harya iya furtata,cikin motar suka shiga suma fadawan suka shiga wata.
a hankali kuma cikin nutsuwa motocin suka fara tafiya zuwa unguwar gauters.

tana zaune a parlour hannunta riƙe da glasa cup wanda aka cikashi da zuma da garin magani,yayinda hannunta yasha jan lalle na salatif,yay ƙyau sosai kasan cewarta farar mace,lallan ba ƙaramin haska fatar jikinsa yay ba.
ita kanta abar kallo ce sabida wani sahihin ƙamshi dake fita a jikinta ba ƙaramin gyara akaiwa jikinta ba,komai na jikinta ƙamshi yake.
amma kallo guda zakai mata ka fahimci zallar damuwar dake cikin ranta wacce ta kasa ɓoyiwa.
saurin sakin glass cup ɗin hannunta tayi sabida bugawar da zuciyarta da tayi hakan yay dai-dai da tsayawar motoci a harabar gidan nasu.
da raguwar ƙarfin daya rage mata ta miƙe tsaye tare da nufar window ganin hakan da tayi ya sanya Mom faɗin.

"kalli shigar dake jikinki kuma kinsan manyan baƙine zazo shigo,oyyyya shige bedroom"

goge hawayen fuskarta tayi ba tare data kalli mutanan da suke fiddowa daga cikin motar ba ta juya zuwa bedroom ɗinta.

kai tsaye wani lafiyayya parlour aka kai Sarki Maleek su kuma fadawan aka ajjiyesu a nan ɓangaren masu aikin gidan.

bayan ya shiga cikin part ɗin kai tsaye wani bedroom ya nufa yana zuwa ya fara rage kayan jikinsa,sabida zama da kaya a jiki ba al'adarsa bace.

yana gama cire kayan ga rage daga shi dai wani dugun wando na wani tissue ɗin blue ɗin yadi,sai kuma farar singlet mara nauyi.

zama yay saman wata sofa tare da zubawa ƙofar shiguwa idanu haka nan ya samu kansa da jin wata yunwa harya kasa daurewa.

Cikin rashin kuzari da kuma takaicin aikin da Sufyan ɗin ya sata ta fara shirya breafast ɗin a cikin basket.
saida ta gama shirya komai kana ta ɗauki kayan ta fara nufar part ɗin da Sufyan ɗin ya nuna mata.
can ƙasa zuciyarta kuma wani tsoro haɗi da fargaba ne suka shigeta.
haka kawai ta samu kanta cikin wani hali mara fassaruwa a zuciya.
kanta a sunkuye take tafiya,yadda take tafiyarne ya sanya ma dai-dai cin hips ɗin juyawa a cikin abayar data saka.
yayinda hannunta yake dafe da saitin zuciyarta still kuma idanunsa basu bar zubda hawaye ba.
jin ta daki ƙofa ya sanya tayi saurin yin baya sai a lkcn da kula da cewa tazo inda aka nuna mata ɗin.

ƙara juya ƙwayar idanunsa yay akan ƙofar tare da gyara zamansa,dukkan abinda yake na dauriya ne domin ji yake zuciyarsa kamar zatai tsalle ta faso waje.

ajjiyar zuciya ta sauke a karo na biyu,cikin wata murya mai raunin gaske tace "Ya Allah helf me wannan tsoran na mene?" ta tambayi kanta a lkcn da take murɗa handle ɗin ƙofar tana tura kanta ciki taji ance...
*79-80*


*_Rinamaleek or Rinayusuf???_*




"Little sis bani basket ɗin nan" da sauri da juya wajan Sufyan dake bayan yana magana,hannu na rawa ta miƙa masa basket ɗin ta juya ta fara tafiya domin shigewa cikin part ɗinta.

Gajiyayyun idanunsa ya ƙara saukewa a jikin ƙofar ganin kamar mutum ne zai shigo,lumshe idanunsa yay lkcn da yaga wata ƙyaƙƙyawar ƙafa ta bai yana a gefen ƙofad wacce tasha jan lalle na salatif,ƙara runtse idanunsa yay sabida jin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi,ɗan siriri tsaki ya saka mara sauti sakamakon jin Sufyan nayi mata maganar ta koma.
haka kawai yaji yana son ganin yarinyar da take ƙoƙari shiguwa,ganin bashi da wani abu mai muhimmanci da zaice haka ya sanya yay shuru tare da lafewa a jikin sofar da yake kai.

Da sallama Sufyan ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi ya ajjiye basket ɗin a gaban Sarki Maleek tare da jawo wani ɗan ƙaramin danning table.
cikin farin cikin daya kasa ɓoyiwa yace.
"Am sorry boddy na barka da yunwa,wacce yarinyar dana sanya ta kawo maka abincin itace lazy gril"
ware idanunsa yay wanda suke a lumshe kana ya ɗauki bottle water mai sanyi tare ɓalle murfinsa bottle ɗin ya kafa a bakinsa.
sai daya sha fiye da rabin bottle ɗin kana ya sauke wani zazzafa numfashi wanda yake nuni da duniyar tunanin daya tafi a wannan lkcn.
a zahiri idan ka ganshi zaka ɗauka duk yaji maganganun da Sufyan ɗin yake faɗe,amma ina sam abin ba haka yake ba,domin ya daɗe da tafiya tunanin sahibar tasa da kuma yadda zai ya sameta.
yana da ƙarfin quiwa amma a kanta kuma a dalilinta yana so ya maida kansa wani sakare,domin da gaske komai nasa neman ƙwancewa yake,yana so ya zama zautacce a dalilin zazzafar soyayyarta wacce tayi masa muguwar kamo.
ko kowa zai yarda cewa ita ba mutum bace shi har abada bazai taɓa yadda ba,sai lkcn data bai yanar masa a siffarta ta aljanu.
idan ya tuna da ita ƙara sonta yake.
idan akai maganarta ƙara sonta yake.
idan ya ganta ƙara sonta yake.
dukkan wani motsi nata baya tafiya saida soyayyarta.
ƙara lumshe idanunsa yay haɗi da taune laɓɓansa,yayinda ya ƙara shigewa cikin luntsumammiyar kujerar.
a kuma lkcnne wani sabon yanayi mara fassaruwa ya fara bai yana garesa,cikin dakiƙo kaɗan tsigar jikinsa ta fara tashi yayinda wani sihirhirtaccen sanyi ya fara ratsa shi.
haka ya faru ne sabida soft pink lips ɗinta da suka bai yana garesa.
a kuma lkcn ya fara tuna mood ɗinsu na ranar kilisa koda wasa ko a mafarki mai taɓa tunanin zai kissed wata rayinya wacce ba muharramarsa ba sai ita,tasa ya ƙarya dukkan wani tanadinsa a kan mace,zazzafar ƙaunarta daya keji ya sanya yay hakan ba tare daya sani ba.
duk wannan girman soyayyar amma Abbunsa bai gani ba yake ƙoƙari haɗashi da wata ɗiya mace ba ita ba.
tayaya zai iya rayuwar aure da ita? tayaya zai bata dukkan wata kulawa daya dace ko wanne namiji ya bawa matarsa.
ina sam bazai iya ba,koda ace bazai taba kasan cewa da Rinaarsa ba..

Da idanu kawai Sufyan ke binsa dashi can ƙasan ransa kuma yana mamakin zurfin ciki irinna abokin nasa,tun a airport ya lura aƙwai abinda yake ci masa zuciya,yay tambayar amma a banza,ko tankashi bai yiba.
hakan tasa yanzu ma bai kulasa ba domin yasan bazai taɓa gaya masa sirrinsa ba.
numfashi ya sauke yace.
"boddy abinci fa?"

Saukar maganar ta Sufyan ya sanya shi dawowa cikin haiya cinsa,a kasalance ya buɗe fitanannun idanunsa wanda sukai jaa kaɗan sabida tsaɓar hurt feelings ɗinsa da damunsa.
numfashi ya sauke a hankali tare da pouting lips ɗinsa.
a hankali ya zamo daga kan sofar ya zauna a ƙasan carpert cikin nutsuwa ya fara buɗe food flast ɗin dake gabansa.
da white rice with carrot ya fara cin karo,sai kuma onion soap,sai kuma farfesun kaji wanda yasha kayan ƙamshi,gefe guda kuma fruit salt ne,da kuma haɗin cousilo,wani ƙaramin flast ya gani,ji babu ƙauri ya buɗe flast ɗin ƙamshi daya daki hancin sane ya sanya yay saurin lumshe idanunsa few minutes ya ƙara saukesu akan flast ɗin.
dambun shinkafa ne wanda yaji carbet da kuma bushasshan kifi haɗi manyan gyaɗa da kuma carrpot sai albasa.
sai ƙamshi yake.
ganin kamar yafi son dambun ne ya sanga Sufyan ɗaukan plat ya zuba masa kusan ciki,kana ya tura masa gabansa.
lemon ginger wanda Zarina tayi ta tsiyaya masa a glass cup.
cikin nutsuwa ya ɗura hannunsa akan spoon ɗin tare da ɗebo dambun yana da sauri ya lumshe idanunsa sabida wani daɗi da kuma garɗin gyaɗar daya ratsa bakinsa,musamman ɗanɗanon kayan ƙamshi.
cikin nutsuwa yake tauna dambun a bakinsa har yaci kusan rabi.
turewa yay daga gabansa kana ya ɗauki lemon ginger'n ya kafa a bakinsa wani ɗanɗano yaji wanda bazai taɓa manta lkcn daya fara shan lemo irinsa ba.
tabbas yasan wannan kalan abun amma a ina? wani murmushi ya saki lkcn daya tuna zamansu da ita a bilhas a watan ramadan kuma biyu ga wata a wannan ranar ta haɗa masa wannan lemon.
jin babu banbanci da wata tayi ne ya sashi saurin shanyewa tare da juyawa ya kalli Sufyan tabbas so yake ya tambayesa wacece tai wannan lemon amma ya garara koda ware lips ɗin sane bare ya samu damar faɗin wani abun.

Ganin kallon da yake masa ne,ya sashi jawo jug ɗin lemon a tunaninsa ƙari yake nema.
hakan tasa ya cika masa glass cup ɗin dashi,jinjina kai kawai yay ga mamakin Sufyan yaga ya ƙara shanye lemon a taƙaice saida ya shanye kusan cikin jug ɗin.
yana gamawa ya ƙara shanye raguwar ruwan sanyi dake cikin bottle ɗin kana yay ƙyasa cikin wata ƙawatacciyar murya mai amo yace.

"Allahamdulillah"

Dariya Sufyan yay yace "yanzu duk faɗin kana jin yunwa iya ɗan abinda za kaci kenan,gsky boddy matarka zatai kallo" harara Sarki Maleek ya watsawa Sufyan tare faɗin "tunda na zama tom da jerry dole ai a kallan mumu kawai"
"a'a maid wuƙar gobe idan akayi ɗauri a lkcn kaima zaka tafi kosai washe gari?"
miƙewa Sarki Maleek yay tare daya tsuna fuska kamar bazai tanka Sufyan ba sai kuma yace "ji iskanci ubane zan zauna nai maka?"miƙewa shima Sufyan yay kana yace
"au na manta ashe kaima ango ne,uhm soo sorry matan Sarki Maleek amma zaki haɗo da zakin zakuna,ina tausaya maki"
tsaki Sarki Maleek yaja tare da shige part ɗinsa a ransa yana faɗin "abune mai wahala idan bata suma ba..."


ɓangaran Zarina a sanyaye ta faɗa kan bed ɗinsa,a kullum tana ƙara samun kanta da sabuwar soyayyarsa,amma a yau a inda ta keji game dashi nada banne,babu shakka shiɗin namijin daya kai a soshine,a kullum kuma a koda yaushe ƙara yi mata ƙyau yake a cikin baccinta.
mirginawa bed ɗinta tayi tare dasa hannu ta dafe saitin zuciyarta dake bugawa tamkar zai tsage ya rabe gida biyu haka ta keji.
tana nan zaune taji an turo ƙofar tare lumshe idanunta tayi domin tasan Mom ce,ga mamakinta sai taji muryar Mamu a kanta na faɗi "maza tashi ki shanye wannan zumar da nonon da nake fama dake,haka za'a kaiki gidan mijin babu gyara kijimin da yarinyar,yanzu zamani ya sauya da anshiga ciki za kiga yarinyar da ciki kamar wacce tasha a ruwan al'wala maza tashi"

turo baki tai gaba tare da kallon Mamun cikin muryar kuka tace "haba Mamu ku tausayamin mana,kusan auren nan basu nake ba,amma kuzo kuyita takurani haba dan Allah,ku barni naji da abinda yake damuna zuciya ciwo ji nake kamar zata fito waje"
ta faɗa yayinda wasu hawaye ke ambaliya a cikin idanunta.

"kee shafamin lafiya banson zancan banza,idan bakiso shi yana so,kuma sannu a hankali zaki soshi,banda zamani ba mu lokacinmu ina muka san wata soyayya basai dai kiga mijin da aka aura maki ba a ɗakinki ko zance bayi muke ba,maza shanye ƙirji duk yay sama amma kice baki son aure sabida sakalci"

ita dai Zarina bata ƙara cewa komai ba ta miƙe ta nufi inda wayarta take tana ringing ganin wata number babu suna yasa taja tsaki hakan kuma ya tabbatar mata da cewa Yusuf ne,wajan bed ɗin ta dawo tare da karɓar glass cup ɗin ta kafa abakinta jin zaƙine yasa ta shanye tass kan ta bawa Mamu cup ɗin.
wani sabon kirane ya shigo watar ganin hakan yasa babu tace 'ko ki ɗaga kirannan ko kuma yanzu naje na kira ubanki Audu tunda ni ba tsorona kike ji ba"

Raurau tayi da idanu kafin ta sanya hannu tai picking call ɗin,daga can ɓangaran ya saki wata ajjiyar zuciya tare da faɗin.
"beautyna na kasa jure rashinki gani nake gobe tayimin nisa"
ya mutsa fuska tayi ganin Mamu a samanta ya sata faɗin "Allah sarki"
murmushi yay tare da faɗin "beautyna mene kike tana dar mana gobe a gidana wallahi da gaske ina sonki har bansan yayane zanyi ba"

"Uhmm"shine amsar data bashi a taƙaice,ganin ya zage yana surutu wanda ita harga jinsa take tamkar yana dukan brain ɗinta ne ya sanya cikin sauri ta tari numfashinsa tace.
"zanyi aiki sai an jima"
kafin yay magana ta kashe wayar miƙewa tayi ta nufi wajan dressing mirrow'n wani mugun ƙyau taga tayi jikinta sai shaining yake,komai yaji fresh skin ɗinta ya koma tamkar bayan ƙwai sabida santsi da kuma sheƙi.
tsaki taja tunawa da duk wannan ƙyan ba wanda ta keso ne zai gani ba.
vail ɗin a bayarta ta ɗauka tare da ɗaukan hand bag ɗinta ta zura wani flat shoe mai ƙyau kana tai waje.
ganin babu kowa a parlour yasa kai tsaye ta nufi compound na gidan tana gaba taji alamun ana tafiya a bayanta,ganin bazai huce Tupic bane ya saka ko juyawa batai ba.

Cikin nutsuwa yake kallon tsarin halittar bayanta musamman ma dai-dai cin hips ɗinta dake juya a cikin duguwar riga,a hankali ya ɗaga idanunsa zuwa ga dugan baƙin gashinta wanda ya bai yana ta ƙasan vail ɗinsa.
da sauri ya dafe saitin zuciyarsa sabida bugawar da tayi masa,sosai yake son ganin fuskar wannan ƙaramar yarinyar hakan tasa ya ɗan ƙara sauri wajan tafiyarsa,shima Sufyan saurin ya ƙara amma duk saurinau kafinsu iso ta shige cikin motar,tana shiga ta lumshe idanunta.
tsaki yaja kaɗan sabida rashin ganinta da baiyi dalilin baƙin glass ɗin dake banne a jikin motar yana kallo drever yaja suka bar harabar gidan
Sufyan kam tunaninsa sauri yake zuwa masjid sabida tada iqama da akai,cikin nutsuwa suke tafiya da sauri fadawansa suka mara masa baya,tare da rufesa da manyan rigunansu,a haka suka shiga cikin masjid ɗin dake wajan gidansu Zarina..


Kasan cewar ansan da labarin zuwan sarin bilhas ɗin wato Sarki Maleek ya sanya masallacin ya cika domin kowa burinsa bai huce yaga Sarkin idanu biyu ba,mutane da yawa hamdala suka dingayi tare da faɗin "Allahu akbar"ba kaɗai suka razana da ganin ƙyansa da kuma ƙwarjinsa haɗi da cikar zatinsa.
duk inda ya ratsa zubewa ake ana gaidashi,haka ya dinga ɗaga masu hannu idan mutun nada girma har ƙasa yake gaidashi,a dole yake biye basu sabida a tunanin bai dace suyi hakan ba,sabida cikin masallaci suke,amma ina su farin cikin ganinsa ya hana su gane abinda yake ganewa.
har sahun gaba ya tsaya shida Sufyan sai Tupic da kuma abokin Tupic ɗin.
cikin nutsuwa sukai sallah nanma saida Sarki Maleek yay wa'azi mai ratsa jiki wasu hadda kuka sunaji dama shine sarkin garinsu.
bayan sun kammala ne suka nufi gida a babban parlour suka haɗu da Mom da kuma Mamu,cikin farin ciki Mom ta tarbesa shikam ko a jikinsa haka yaje ya rungometa yana jin soyayyarta a ransa,haka Mamu ya gaidata,cikin jin daɗi Mom tace.

"hala Sufyan ya tsareka da shegiyar maganarnan tasu da babu aya shiyasa bamu ganka ba"

murmushi yay domin yasan gsky ta faɗa indai surutu ne masha Allah, haɗe rai Sufyan yay tare da faɗin.

"Haba Mom nike da magana ai wannan aikin Tupic ne..."

"Me Tupic yay ake kiran sunansa sabida anga baya nan ko?"

Tupic dake shiguwa yay saurin tarar numfashin Sufyan ta hanyar faɗin hakan.

Mom itama dry tayi tace "toya isa haka nan yanzu zaku fara mitar taku kamar a kanku aka fara Tagwaye"

34 / 38