THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   19 / 38

54K to 57K   out of 111.1K words

tace.
"nana tacce ɗan anaci"tana faɗin hakan ta manna wayar a kunnanta.
Numfashi ya sauke tare da kallon Abbunsa wanda ya shigo yanzu bashi magani.
"Abbuna wai nine ɗan a naci fa"murmushi Abbu ya shafa kansa cikin raɗa yace.
"sorry boy"
Sai yanzu ta ƙara gasgata rashin kunyarsa waya da budurwa a gaban Dad ɗinsa.

Dariya suka saki gaba ɗayansu,domin sunji abinda tace,gyara zamansa yay yana amsar maganin da Abbu ya bashi yace.

"waye budurwan,nine na taɓa cewa ina sonki ne?"ya faɗi maganar mai cike da ɗan gwaranci,domin har yanzu zallan hausa bai gaba zama bakin saba,tun yana 10years suka koma cameroon da zama.

Shuru tayi ba tare data kulasa ba,shima shuru yay yana fakar idanun Abbu kana ya wasa maganin ƙasa bed.
Sam Allah bai haɗa jininsa da magani ba.

"yi addu'a bana baki san aljanin dazai kawo maki ziyara ba,sauƙinta ɗaya a Ramadan muke"

Cike da tsoro ta farayin addu'ar kana ta shafa a jikinta.

"nayi fa"

Numfashi ya sauke a hankali lokacin Abbu tuni ya fita da yaga yasha maganin,wata murya mai sanyi da kuma daɗin sauraro yace.

"I luv you Rina"

Idanu ta runtse da ƙarfi da ace tana da iƙon son sanya zuciyarta ta soshi babu shakka da tayi hakan,amma a kullum tsarsa take fiye da ko wanne lokaci.
Shuru kawai tayi masa domin idan tace zatai magana babu shakka baza ta faɗi mai daɗi ba.

Dai² ta bakinsa yay a speaker'n wayar kana ya sakar mata wani gigitaccen kiss wanda ya banda sautin.


"mu'ahhhh 💋"yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da cilli da ita gefe,sabida wani irin raɗaɗi daya keji cikin zuciyarsa.
Lumshe idanun yay tare taune laɓɓansa tamkar ya rabasu gida biyi sabida turirin azabar daya kejin cikin ransa.

Wayar tabi da idanun sabida wani sabon yanayi daya saukar mata,kanta ta cura cikin pillow tare dakin wani wahalallan kuka mara sauti.
Ita ɗaya tasan abinda yake damunta,ita kaɗai tasan abinda zuciyarta keso,ita kaɗai tasan abinda gangar jikinta ke muradi,ita kaɗai tasan kewan abinda kunnuwanta sukai.
Cikin shassheƙar kuka bacci yay gaba da ita.

Abbu na fita ya miƙawa Alhaji Abdallah bandir ɗin 1k kusan bandir biyu,haka ya Alhji Abdallah ya amsa badan ransa yasu ba,sabida matsan tawar Alhaji Bilyamin.

Saifu kowa bacci ɓaro da bai san lkc'n daya saceshi ba,ya hadda masa katsewar tunanin da yake.
A haka yay bacci zuciyarsa cike da ɓacin rai.

Washe gari
Ta tashi jiki babu kuzari haka dai tayi wunin rana ko surutun da take yiwa Mai babban ɗaki bata samu damar yi ba.
Hadima Kaltume da kuyanga Kulsum ne kaɗai ke shirya abinda za'ai buɗe baki.
Sabida Zarina ba azumin take ba,ga kuma wani ciwon mara daya sanyata gaba kamar zai kata lahira,da aduk wata wannan abin take fargaba sabida ciwon cikin da take.

Yana ƙwance saman carpert sa juyi take gaba ɗaya jikinta rawa yake,ga wani a zababban zazzaɓi dake shirin saukar mata.
Zufa ce kawai ke karyo mata duk da sanyin A.c'n dake kaɗawa da kuma yalwatacciyar iskar dake kaɗawa a hankali tana ratsa jikin ɗan adam.
Amma baisa ta daina jin zufar da ƙwaranyo mata ba.
Mai babban ɗaki dake kishin giɗe bisa tattausan cosin ta numfasa tare da faɗin.

"Ke kinci baki son magani an taɓa ciwo babu magani,kai wannan abuba da zamani mu ina mukasan wani ciwon ciki,gaki da shegen son zaƙi kamar jikar shazomamu ba dole ciki yay ciwo ba"

Kuka Zarina ta sanya sabida azabar daya isheta zuwa yanzu kam ko kuzari babu jikinta sabida tsananin ciwo,a hankali ta soma birgima tare ƙara sautin kukanta.

Wayar Mai babban ɗaki dake bisa kujera ta fara ringing a hankali tace.

"kulsum pic the call"

Hannu Kulsum ta sanya tare da ɗaukan wayar,screen ɗin wayar tabi da kallo tace.

"Vedio call ne Ammi"cewar kulsum sabida itama bakinta yabi na Zarina na faɗin Ammi.

"ɗauki man"Mai babban ɗaki ta ƙarasa faɗa tana maida kanta saman pillow.
Da mamaki tabi wayar da kallo ganin number babu suna.
Cikin far nutsuta ta sanya wannan tare da connectiny na vedio.
Ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta bai yana mai ciki da haiba da kuma hasken muslunci
Da hanzari Kulsum ta sunkuyar da kanta sabida wani ƙwarjini da yay mata.
Zubewa tayi har ƙasa tace.

"barka da yammaci ya azumin?"

Lumshe idanunsa yay ba tare daya amsata ba yace.

"wake kuka kuma?"

Da saurin ta jingine wayar saman sofa inda zai iya ganin Zarina dake ƙwance ƙasan carpet tana rera kuka.
Lumshe idanunsa yay tare da fesar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa,a taushashe yace.

"cikinne halan?"
Da sauri Kulsum tace "eh"gaba ɗaya haibarsa sun cikata.
Jinjina kai yay yace "Uhmm Kulsum zamu ruwan zafi a bowl da ƙarfin towel"
Da sauri ta ƙara miƙewa ta nufi kitchen domin samo ruwan zafi kana ta huce bathroom ta ɗauki ƙaramin beby towel mara nauyi.

Numfashi Saifu ya sauke yana kallo yadda ta ɗura hannunta bisa cikinta sai kuka take gaba ɗaya fuskarta ya haɗe da majina da hawaye haɗi da yawo.
A hankali ya gyara zama murya can ƙasa yace.

"sorry Rina sorry pls"
Ina sam Zarina bata san mene yake faɗi ba,sabida ciwo ya riga dayaci ƙarfinta.
Bowl ta towel ta ajjiya kusa da Zarina duk abinda suke yana kallonsu.
"maza ɗaya rigarta kiɗan jaaa siket ɗin ƙasa kaɗan maranta ya bai yana"ya faɗi hakan yana haɗe rai tamau sabida kallon mamakin da kulsum tayi masa.
Yadda ya faɗa haka tayi tana gamayin hakan yace.

"ohyaa sanya towel ɗin cikin ruwan zafi saiki ɗan fara murza mata saman cikinta zuwa mararta"

Da "to"ta amsa masa kana ta farayin abinda yace.
Wata ajjiyar zuciya Zarina ta sauke sabida yadda taji daɗin saukar ruwan zafin saman mararta.
Ajjiyar zuciya ta fara saukewa jikinta yay laƙwas ta tsaya da kuka sai shassheƙa kamar ta haɗiyi zuciya.

Bayan ta gama yace.

"ɗauki wayar ki ɗura bisa kunnanta"duk yadda yace haka tayi a hankali ya gyara zama cikin zazzaƙar muryarsa yace.

" Bisimillah"
Saida ya faɗa sau uku kana ya fara yi mata addu'ar samun sauƙi wajan ubangiji.
Saukar numfashinta yaji sosai tana yi tana sauke ajjiyar zuciya alamun bacci ya ɗauketa.

Numfashi ya sauke sabida soya da maƙoshinsa ke masa,a sanyaye yace.
"ɗauke wayar idan ta farka ki haɗa mata tea mai zafi da kauri ki mata"yana faɗin haka ya disconnecting na kira.
Cike da mamaki Kulsum take kallon Zarina inda tayi luff saman carpet tana sauke numfashi.
Miƙewa ta ajjiye wayar kana taci gaba da aikinta.

Wajan Saifu shima ficewa yay daga parlour ya samu Abbunsa shi ɗaya yana kallon tafsir,key ɗin Abbu ya amsa kana yay waje domin zaga gari.

A hankali yake dreving cike da nutsuwa da kamala,yana tafe yana sauraran daddaɗar ƙira'ar dake tashi a cikin mutarsa cikin suratul Ahzaaab,a hankali laɓɓansa ke motsawa alamin bin karatun yake tym to tym yana lumshe idanunsa sabida daɗin ƙaratun da yake,can ƙasar zuciyarsa kuma fal yake da tausayin Zarina,sosai yake jin ciwonta a jikinsa domin yafi kowa sanin zafi da raɗaɗin ciwon ciki.
Taune laɓɓansa yay kana ya sanya hannu yaja ma dai² cin gemun dake manne bisa haɓarsa.
A haka yake dreving cike da nitsuwa harya isa wani babban gida wanda kana ganinsa kasan yaji kayan mure rayuwa ko ina matakan tsaro ne a wajan.
Wanda sukaiwa kadangar gidan ƙawanya.
Ɗan kansa yay saman gidan inda aka rubuta *Disable and Opanage house* lumshe idanunsa yay tare da murza kan motar ya ɗan danna horn a hankali.
Tun kafin ya ƙarasu get ɗin getman ya hangame masa ƙofar get ɗin,cikin ƙwarewa y cilla hancin motar cikin harsbar gidan nakasassun da marayun.
Yana fitowa wani mutum ya ƙarasu wajan tare faɗin.

"sir how can i helf you?"

Murmushi Saifu yay kana yace.

"daman shiga zanyi wajan manager'n wajan,but tunda kaga fine"hannunsa ya saka cikin aljihu kana ya zaro bank Tyler tare da ɗauko pen ya cike masu komai hadda sa hanunsa kana ya saka sauran tyler cikin aljihunsa ya miƙawa mutum takaddar hannunsa.
Cike da mamaki mutum ya zaro idanu tare da faɗin.

"what sir 2million na mene?"

Mota Saifu ya faɗa tare dayi mata key kana ya zuro kansa ta ƙofar motar yace.

"aci gaba da kula da marayu da nakasassun fisabilillah"

Cikin farin cikin mutumin yace "sir sunanka address naka pls".

Murmushi kawai Saifu yay tare dajan motar da gudu ya fice daga cikin gidan.
Da kallo mutumin yabisa tare da mamaki irinna Saifu yay sadaka but baison asan shine yay.
Hannunsa ya ɗaga sama yace.

"Allah kada fawa wannan mutumin Ubangiji yay masa albarka fiye da tubansa,ya jiƙansa fiye da tunaninsa,Ubangiji ya sanya haske cikin rayuwarsa,Allah ka bashi abinda ya keso duniya da lahira"yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi office ɗin manager yana shiga yay masa bayanin komai.
Cike da farin ciki shima yay masa addu'a domin daman kuɗinsu yay ƙasa suna buƙatar abubuwa da yawa musamman yadda salla yazu.

Kai tsaye Saifu gidan da yake zaune ya nufa yana shiga ana kiran sallar magrib.
Lumshe gajiyayyun idanunsa yay tare da furta.

"Allahamdulillah"

Yana fitowa daga cikin motar su Abbu na fitowa daga cikin gida zasu masallaci.
A hankali ya rufe motar tare da murza key,bayansu yabi da ɗan sassarfa ya shige masallacin lkc'n har anta da kabbara.
Bayan sun idar sunyi azkar kana suka fito tare da nufar cikin gida.
Gaba ɗaya danning area suka nufa suna zuwa kowa yaja kujera tare da zama.
A hankali Saifu yaja kujera ya zauna shima kana ya ɗan siyayi coffee a glass cup ya manna bisa bakinsa.
Lumshe idaninsa yay yaci gaba da shan tea ɗin.
Bayan ya gama yaja fruit gabansa tare da ɗaukan dabino ya sanya cikin bakinsa.
Daɗi da zagin dabinon haɗi da garɗinsa suka ratsa cikin kunnuwansa,wanda suka haddasa masa rufewar idanunsa.
Sosai dabinon yay masa daɗi cikin bakinsa.
Saida yaci guda baƙwai kana ya ɓalli inibi bayan ya shanye,yana gamawa ya ɗauki Apple ya saka cikin bakinsa.
Yana gama shan apple ɗin yaja ƙujerar baya tare dayin ƙyasa a hankali ya ware laɓɓansa yace.

"ZAAHBAZZAM'U WATALATUL URUUF WASABBATIL AJJIRAA INNSHA ALLAH"

murmushi Alhji Bilya yay tare da zubawa ɗan nasa idanu,sosai ya kejin soyayarsa a zuciyarsa,tunane² kala a ransa,yana son faɗa masa abinda ke ransa amma yana tsoro dan haka kawai yake shareshi domin yafi son yay komai cikin sirri,yasan har abada bazai taɓa kuka akan abinda yay masa komai daɗewa komai jimawa aƙwai randa zai masa godiya akan hakan.

"Abinci fa naga duk tar kacan ruwa kasha"

Shuru Saifu yay kana kuma ya buɗe idanunsa tare da zubasu bisa fuskar Mom wacce take sanya cips cikin bakinta,ganin tana ƙoƙarin ɗago kai yay saurin janye idanunsa.
Kana ya kalli Abbu yace.

"Abbu zuma nakeso ko dakakkiyar fura"ya faɗa yana pouting lips

Gaba ɗaya suka ɗago kai suka kallesa,Mom,Mamu,Abba ankai azumi kowa yana son sanya abu mai ɗan nauyi cikinsa shi kuma yana neman wani abu ikon Allah.
Shikam Abbu baiyi wani mamaki ba domin yasan hakan zai iya kasancewa wajan Saifu neman Abinda ya zama halayyarsa wanda yabi jini da tsokar jikinsa.

"ok anjima za'a kawo maka"cewa mom jinjina kai yay tare da faɗin.

"uhmmm nagode"yana faɗin hakan ya shige part ɗinsu tare da faɗawa bathroom yay wanka.

Haka dai ya ƙarasa sauran sallolin kana yay shirin bacci bayan yasha furar da aka kawo masa.

Number Mai babban ɗaki ya kira amma swcith up haka ya ƙwanta zuciyarsa fal tunaninta sabida yasan bata da lafiya.


_Dubai_
Hankali ƙwance lil prince ke aiwatar da rayuwarsa ba tare data kura ba.
Azumi ne idan yay guda biyar sai yasha guda 1 acewarsa wai bazai iya zama babu mace ba.
A haka ya haɗu da wata yarinya mai suna Meera,haɗaɗɗiyace ajin farko,tun ganin farko da yay mata yaji mararsa ta halba da sauri kana cikin dauriya yace.

"heyy"
Juyowa tayi tare daci gaba da tuna cimgom ɗin bakinta kana tace.

"ohh hello"

Murmushi yay kana yace.
"basai nayi maki maganar abinda ke raina ba,domin ganinki hakan ya tabbatarmin ke ƴar hannu ce,so ina buƙatar haɗin kanki"

Wani shu'umin murmushi tayi kana ta ciro wani card a wayarta ta miƙa masa cike da yauƙi.
Ganin accout number ta da sunanta da kuma bank name ɗinta yasan abinda take nufi.

"wow smart gal"yan faɗin hakan ya ciro wayarsa yay mata transfer ɗin dubu ɗari biyar cif.
Gyara zama tayi haɗin da ɗan banƙaru ƙirjinta kana ta zare glass ɗin idanunta tace.

"Lil prince cikikakken sunan kuma NAJEEB KHALIS BILHAS ɗaga sarkin bilhas maici a yanzu,kana da aboki Yazeed shine best friend ɗinka ya kasance kuma lecture a N.S University,kana da gidan giya a ɓoye wanda ko mahaifinka bai san dashi ba,well kana ɗauke da zoɓen da idan babu shi babu wanda ya isa ya gaji sarauta,kana son Kuyangarka mai suna Zarina yayinda take maka kallon nagari bata san kaiɗin kumurcin macijine sara zai kaiga duniya,ka sadu da ƴan mata da yawa wanda ƙarfin tsafi da shirin jikinka yake sanyawa su mutu,yarinyar daka kashe ta ƙarshe Haseenatu ana kiranta da suna Seenat,number wayanka itane 0903333777 ba wannan ba aƙwai ɓoyayyan abu game dakai wanda ake ɓoye maka wanda dana su zan iya gaya maka"

Saurin miƙewa yay tsaya zuciyarsa cike da mamaki haɗi da tsoro yake kallonta tare da faɗin.

"wacece ke?mene kike nema dani?yaya akai kika san da abinda ko Mai martaba bai sani ba"

Miƙewa Meera tayi kana tayi sama kallon sama da ƙasa tace.

"bana buƙatar komai wajan sai ƙuruciyarka duk ta riga ta watse wajan wasu matan,amma hakan bai daman ba,kai infact ma dankai nazu Dubai kuma tun a kafin kazu nan na sanya ayimin bincike a kanka kuma na samu,ka sameni a gida kana duk ranar da zaka koma bilhas tare zamu tafi kada ka damu bazan takuraka ba,zanje matsayin baiwa duk sanda kake buƙatar ne ɗauke maka kewa ina maraba da kai"

Tana faɗin hakan tasanya kai ta fice da cikin gidan tana kaɗa masa manyan bom bom ɗinta.

Bai wani tunanin komai a kanta,burinsa kawai ya jisa cikin jikinta dan haka ya shirya zuwa after 10:30.
Tun daga wannan ranar suka ɗinke shida Meera kullum suna tare,yayinda basa haɗuwa sai bayan ansha ruwa.
Sun yanke shawarar ranar sallah zasu dawo bilhad inda Meera zata shiga matsayin Kuyanga..


**** *****
Kamar yaune ake faɗin saura ƙwana ashirin Ramadan yau gashi ankai azumi na shirin da tara.
Kuma a yau ake sanya ganin watan zul ƙiida.
Sosai fuskar Alhaji bilya ta cika sa farin ciki har bata iya rufe bakinsa.
Sa ɗan sauri ya shigo part ɗinsa tare da faɗin.

"My boy..my boy kana ta inane oyyaaa fito maza"yana faɗin hakan ya zauna bisa duguwar sofa.
Saifu kam yana cikin ɗakinsa suna waya da best friend ɗinsa yana tsoka narsa akan zama jeni da suke.
Haka dai sukai shirarsu cike da farin ciki inda yace shima Biyar ga sallah zai dawo.
Yana tsaka da wayar yace Sufy..sai kuma yay shuru kana yace "i will call u lrt".
Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da nufar parlour inda Abbun nasa yake yana zuwa ya gansa zaune bisa sofa.
Ƙarasawa yay tare da zama kusan Abbu yace.

"Ayya Abbu ka bani tsora fa what is going on?ya ƙara maganar yana kallon Abbun wanda har yanzu fuskarsa take ɗauke da farin ciki mara misaltuwa..
Rungome Saifu yay tare da shafa ƙwantacciyar sumar kansa yace.

"Allah yay maka albarka yau ranace mafi muhimmanci cikin sauran ranakunsa,sai kuma wanda zasu riskeka nan gaba"

Da mamaki Saifu ya kalli Abbu cike da son jin abinda ya faru yace.

"uhmm menene wai har haka?"

Murmushi Abbu yay yace
"kada ka damu aƙwai lkc'n da zaka san komai,gobe zan huci Cameroon kaima ka shirya komawa wajan aikinka,tunda kayi nasarar hanani zuwa Umara amma nayi farin ciki ma da hakan domin wannan abin farin cikin dana tafi da tuni bai sameka ba"

Zamewa yay tare da ƙwantar da kansa bisa cinyar Abbu yace.

"Abbu ina tsoro bansan yaya zan fuskanceta harta gane abinda yake gaskiya akaina,duk lkc'n dana kansa ina loosing brain ɗina hakan tasa nake nesa da ita,ina kasa control kaina a kanta"

Shafa kansa Abbu yay yace.
"wai wacece wannan ban taɓa jin sunanta ba kullum labarinta na keji"

Ajjiyar numfashi Saifu ya sauke kana yace.

"Sunanta Za...."bai ƙarasa maganar ba Alhaji Abdallah ya shigo cikin parlour'n hakan tasa yay shuru sai kuma daga baya ya gaisar dashi kana ya miƙe ya shige cikin bedroom ɗinsa.

_Masarautar Bilhas_
Tun asuba kowa ya miƙe cike da farin ciki da murnar zagayowar watan ƙaramar sallah.
Kowa na masarautar wankan tafiya sallar idi yay kana kuma kowa bakinsa ɗauke da kabbara.
"ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR LA'ILAHAILLAHU ALLAHU AKBAR WALILAHIL HAMM"

Haka masallacim Marautar bilhas cike da Mutane yara da manya maza da mata kowa yaci sabbin kayan sallah.
Sahun farko Mai martaba ne sai,Hakimin bilhas,Chiroma,Waziri,Sarin fada,Tiraki,Sarkin dawakai,Sarkin cikin gida,baya kuma fadawa ne da sauran ƴan Masarautar kana kuma al'ummar gari.
Salla kai raka'a biyu aka sallamewa aka shiga gaishe².
Cikin girmamawa Fadawa suka baza rigunansu aka lulluɓe sarki.
Yana zuwa ya shiga wata ƙaramar mota wacce yake amfani da ita a cikin gidan sarautar.

Bangaren Fulanin sura tasha sabuwar alƙyabbar irinta mata mai ƙyan gaske.
Cikin nutsuwa kuyangunta da barorinta suka take mata baya har zuwa sashin Mai babban ɗaki.

Zaune ta sameta kan wata sabuwar ladduma mai ɗan tudu irinta masu sarauta.
Tasha ado cikin wata dakakkiyar lafaya orange sai green flowers masu ƙyau.
Kana ta sanya farar alƙyabba sosai ƙyanta ya baiyana a fili,gabanta cike da girke-girken da akai na sallah.
Cikin ladabi tace.
"Barka da buɗe baki Mai babban ɗaki fatan anyi sallah lafiya"

Murmushi mai Babban ɗaki tayi cike da jin daɗin ganin Fulanin sura tace.

"lafiya Allahamdulillah baƙo yazu ya tafi daman komai lkcne"

"hakane fa,Allah yasa munyi karɓaɓɓe"

"Ameen ina Khalid ɗin?"
Shuru Fulanin sura tayi sai kuma tace"bai dawo daga sallar idi ba"idanu ta zubawa wata ƙofa ganin wata ƙyaƙƙyawar yarinya mai ƙarancin shekaru ta fito.
Sanya take da lace sky blue wanda yaji stone masu ƙyau sai sheƙi suke.
Anyi mata ɗikin buba wanda ya zauna faffaɗan jikinta mai tsari.
Ta sai light blue na vail ta yane sumar kanta dashi.
Gashinta ya sauka har ƙasan vail ɗin sai sheƙi yake.
Kamar sanya cikin wani flat shoe wanda yake da blue ɗin igiya.
Sai zamga ƙamshi take fuskarta aya mutse sabida ciwon da cikinta yake.
Daman farko da ƙarshen period sai tayi ciwon ciki,yanzu ma duk da tayi wankan tsarki amma bai hana cikinta ciwo ba.
Sosai Fulanin sura ke ƙare mata kallo far gabarta ɗaya idan ya kasance ita lil prince ya keso.
Domin yarinyar tayi mata musamman nutsuwarta.
Ita kam Zarina sam bata kula da Fulanin sura ba sabida idanunta a lumshe yake.
Tana zuwa ta zauna kusa da Mai babban ɗaki tare da shigewa jikinta tace.

"Ammi ciwon ya dawo pls ayimin irin wancan"
Shafa kanta Mai babban ɗakin tayi kana tace.

"Ɗiyata ciwonne dai,wacce tayi maki bata kusa,amma zan kirashi Saifu'n naji yaya ake"

Kaita jinjina mata kana ta ƙwantar dakan bisa cinyarta.
Da idanu kawai Fulanin sura take kallonsu ita dai harga Allah yarinyar ta birgeta,Hadima batul kam sai ware idanu take tana ɗaukan rahotu.
Sallah Fulani tayiwa Mai babban ɗakin tare fice ta nufi sashin Fulani kilishi domin sauke haƙƙin Allah.

Jin ciwon na tsanata ya sanya Zarina miƙewa tare da faɗin.
"bari kawai na duba Kulsum ciwon ya

19 / 38