THE NEW EMIR Complete Na Na'ima Suleiman (Sarauta).txt

Author :  Na'ima Suleiman Sarauta Category :  Romance

Chapter   32 / 38

93K to 96K   out of 111.1K words

zakazo gaban mahaifina kana faɗin wannan shirman kuma nayi alƙwarin ɗaukan fansa akan abinda kayi mana zaka ganw cewa shayi ruwa ne idan harni ɗan halak ne wlh sai naga bayanku gaba ɗayanku"

Lil prince ya katse Abbu ta hanyar faɗin hakan,cikin tsawa da kuma ƙarani Abbu yace.

"da kata haka nan kada ka fusatani na faɗi abinda banyi niya ba"

tsaki Lil prince yay tare da ficewa daga fadar gaba ɗaya,shuru ne ya biyo baya a fadar ganin duk maza ne a cikin fadar ya sanya Meyrah fita daga ciki,direct kuma part ɗin Mai babban ɗaki ta nufa.
cikin nutsuwa aka zurawa Yarima Maleek lafiyayyiyar alƙyabbar kana aka ɗura masa wata ƙwatacciyar hula ra zallar azurfa sai sheƙi take,cikin nutsuwa da kuma kamala aka fara naɗata masa wani ƙyaƙƙyawan farin rawani mai zaiba,sosai aka ɓata lkc wajan naɗanin rawanin wanda ya kasance mai kunnuwa biyu irin na sarakuna,baya nan aka ɗauki wata takalmin fata mai ƙyau na aka sanya masa a ƙafarsa,sandan girma na azurfa aka danƙa masa a cikin hannunsa,shidai kawai da idanu yake binsu domin jin abin yake tamkar amafarki yana jin kamar bashi ba.
sarkin fada ne yace "masha Allah zan faɗi abu saika mai-mai ta"
i danunsa a lumshe yake yana sauraron abinda sarikin fadar yake faɗa,ware manyan gajiyayyun idanunsa yayi cikin wata zazzaƙar muryaraa mai fidda wani cool sound voice yace.
"NI SARKI MALEEK SUDAIS SUFRAK BILHAS NA AMINCE KUMA NA YARDA ZAN KULA DA TALAKAWA BISA DUKKAN GASKIYATA DA KUMA AMANA,NAYARDA ZAN KULA DA LAFIYARSU,DUKIYOYINSU,KUMA ZAN GIRMAMA RA'YINSU ZAN ZAMA JAJIRTACCE TAKO WANNE FANNI WANNAN RASUWA DA AL'KURANI MAI GIRMA"
gaba ɗaya wajan aka ɗauki kabbara cikin girmamwa aka fara zubewa gabansa ana ƙwasar gaisuwa da kuma jinjina,dake sarautar a jinin cikinsa yake hakan ya sanya baya iya amsa gaisuwar saidai kawai ya jijjina kai ko kuma ya lumshe idanunsa,sai sarkin kirari dake faɗin "an gaisheku sarkim sarakuna mai adalci na gdy"
"Allhamdulillah" Abbu ya faɗa lkcn da wasu hawaye masu zafi suka sauka daga cikin idanunsa zuwa kan fuskarsa,sosai yake farin ciki da sauke haƙƙin daya ɗurawa kansa.
wajan SARKI MALEEK ya ƙarasu tare da ƙoƙarin zubewa gabansa,da sauri SARKI MALEEK (SAIFU) ya zabu daga kan kujerar mulki ya durƙoshe gaban Abbun nasa tare da ɗura kansa bisa cinyar cikin murya mai raunin gaske yace.
"idan kowa zai zube gabana na hqr banda kai Abbu kai rayuwatace kaine mahaifina gaba da baya dan Allah kada ka sake nine nake da ikon kaisheka bakai ba,idan kace zakai haka babu shakka zan hqr da wannan mulkin"
girgiza kai Abbu yay ba tare da yace komai ba sai bubbuga bayan SARKI MALEEK yake sabisa jin yana sauke ajjiyar zuciya hakan kuma ya nuna masa cewa rauninsa ke son bai yana.
ciki ƙasa da murya yace.
"shikenan my love ban ƙarawa Ubangiji ya tayaka riƙo kuma ya baka ikon sauke haƙƙin al'ummar daya rataya a wuyanka"

pouting lips ɗinsa yay tare da zame jikinsa daga na Abbunsa,nan ƴan jarida suka fara ɗaukan sabbin labarai da kuma tare photona tun a cikin masarautar aka fara sakin labarai na naɗin *THE NEW EMIR* da akai.
miƙewa Sarki Maleek yay tare da gyara zaman alƙyabbar jikinsa cikin isa da kuma gadara haɗi zallae izza wacce ta gama ratsa jinin jikinsa ya fara tafiya zuwa waje,ganin haka ya sanya fadawa mara masa tare da rufesa ta gama da kuma baya,tsayawa yay tare da ɗaga masu hannunsu kana kuma ya girgiza kansa alamar baiso,haka suka tsaya shi kuma yaci gaba da tafiya zuwa part ɗin Mai babban ɗaki a hankali ya kewa Abbunsa bayani da kuma mitar shifa an takurasa aka nemi matsa masa za'a nemesa a rasa a garin gaba ɗaya.
shidai Abbu dry kawai yake domin yasan yaron nasa da mifa idan baiso abuba.
a haka suka ƙarasa sashin Mai babban ɗaki da sauri hadimi Kamis kuma mai tsaron ƙofar Mai babban ɗaki ya ƙarasu gaban Abbu yana zuwa ya rungome mahaifinsa wanda ya kasance uba a garesa,cikin farin ciki shima Abbu ya rungomesu.
sosai suka bawa Sariki Maleek tausayi ta dalilinsa wannan soyayyar ta rabo,dalilin kula da rayuwarsa ya banzatar da rayuwar tilon ɗansa,lallai wannan sadaukarwa ba kowa zai iya yinta ba.
ganin kallon da yake masu ne ya sanya Abbu ya raba jikinsa dana ɗan nasa,shima Kamis wajan Sarki Maleek ya ƙarasu zai durƙosa da sauri Maleek ɗin ya riƙe hannunsa kana ya jawoshi jikinsa cikin ƙasa da murya yace.
"you are my bro no nees kayi hakan kaji"
jijjina kai Hadimi Kamis yay kana ya sanya remote ya buɗe masu ƙofar hannunsa Maleek ya riƙe a tare suka shiga cikin parlour.
a zaune suka sami Meyrah da kuma kuyanga Kulsum sai kuma Hadima Kaltume.
ɗan juya idanunsa yay ganin baiga wacce yake son gani ba.
daga bayansa yaji an rungomesa lumshe idanunsa yay sabida wani sanyi da yaji ya saukar masa a zuciyar.
cikin farin ciki tace.
'lale marhabika jikana farin cikina taurarona abin alfaharina,wai duhun dake cikin rayuwar yakau yayinda haske ya maye wanann gurbin"
da mamaki yake kallonta ganin yadda idanunta suke a buɗe tamkar bata taɓa makanta ba.

"ka daina mamaki daman haka tsarin sihirin yake sai lkcn da jininta ya amshi sarauta sannan idanunta zai buɗe"

sosai Sarki Maleek yaji daɗin hakan jikinta ya shige yana Allah tasbihi cikin ransa shi kaɗai yasan farin cikin da yaji da ganin Ammin tasa,ashe yana da rabon ganin jininsa a duniya.
hannunsa ta kama tare sa zaunar dashi akan wata lafiyayyiyar kujera cikin ƙaramin lkc aka cika gabansa da kayan marmari.
bayan sun ɗan gaisane Abbu yaja numfashi kana ya kalli Sarki Maleek yace .

"sai maganar auranka"
kallonsa kawai yayi ba tare da yayi magana ba,can ƙasan ransa yana mamaki abinda ya sanya Abbun yace haka bayan yafi kowa sanin halin da yake ciki da kuma wacce yake so.

abinda ya jine a yanzu ya sanya shi saurin ɗago kansa domin tabbatar daga ina maganar ta fito.
gyara zama Abbu yay yace.

"babu ruwana daka shirya ko baka shirya ba aldy na zaɓa maka Meyrah matsayin mata saika shirya zama ango nan da ƙwana uku...




*_(Yadaa mutum ya keso ba hakan ke kasan cewa ba,kamar yadda qaddara bata shawara damu yayin shiga rayuwarmu,naso na ida labarinan kafin ramadan amma ubangiji bai nufa ba,sai dai duk da hakan yaci gaba da posting a ramadan tunda raguwar pages ya rage mana masu comment ina gdy marasa comment dan Allah ko babu yawa kunayi hakan yana faranta raina,kullum ina ƙwashe 3hours zaune ina typing a hakanma idan ban tashi ba,gaba ɗaya comment ɗin baiyi 5minutes ba,wlh nayi busy fiye da tunaninku a kullum sai dare nake samun damar typing banda wajan aiki da nake zuwa ga wajan yarana na NGO so abun duk sai hqr🙌🏼🤝🏻)_*



*NIMCYLUV*
*75_76*




```BARKANMU DA SHIGUWA WATA MAI FALALA DA KUMA TARIN ALKAIRAI,INA MAFATA ZAMU MASU AIKTA MANYAN IBADO DOMIN ƘYAUTATA RAYUWARMU,ALLAH KASA MUNA CIKIN BAYINKA ƳAN TATTU INA MAKU BARKA DA SHAN RUWA DAY 1🌙🌚```




Saukar maganar yaji tamkar ruwan sama wanda ba'a shirya saukarsa ba,kallon Abbun yay kawai ba tare daya samu nasarar faɗa masa wani abunba,tabbas bazai taɓa ja da maganar wansa yake ganin bashi da kamarsa ba,domin hakan kamar butulcine washi ɗin.
ya kula dashi tun yana ƙarami ya basa ci da kuma sha,tayaya zai iya bijirewa buƙatarsa ta son ya auri wata muradin zuciyarsa ba,tabbas bazai iya jure rashinta kusa dashi ba,yana jinta tamkar jinin dake guduna a cikin jijiyoyinsa.
hakan na nufin tasa ƙaddarar soyayyarce tazu masa a haka ba tare daya sani ba.
ƙwarai da gaske bazai taɓa iya sauke nauyinta garesa ba,hakan kuma kamar ya cutar da itane musamman idan akai duba da yadda abun yazo masa ba tare daya shirya ba,babban abun kuma rashin soyayyarta da babu cikin zuciyarsa.
numfashi yaja mai ƙarfi tare da sauke ajjiyar zuciya hannu yasa ya gyara zama alƙyabbar jikinsa,cikin wata ƙasaitacciyar murya mai sauti da kuma daɗin sauraro yace.

"Auran Meyrah matsayin mata gareni na nufin buɗewar wasu sabbin qaddarori a cikin rayuwata,zanzo ace Abbu ka fahimci yadda zuciya a koda yaushe take bugawa a dalilin soyayarta,zanso ka fahimci ƙunci da kuma raɗaɗin da zuciyata take a dalilin rashin mahaɗinta,Abbu ina son ka fahimci sauyawar ruhi da kuma ganggar jiki da suke dalilin rashin abokiyarsu,ina sonta inaji kuma bazan iya zama da wata ƴar mace ba saɓaninta,Abbu ka fahimci zuƙatan zuciyoyi guda biyu kada ka rabasu ta hanyar tirsasani na auri wata ba Rinaaa ba,wlh bazan iya sauke dukkan nauyinta dake wuyana ba,kuma dalilin hakan haƙƙinta zan ɗauka domin itama macace kuma tasan menene aure Abbu dan Allah ka fahimceni ka janye maganar wannan auran banso"

shafa hannunsa Mai babban ɗaki ta kama tare da riƙesu gam cikin nata hannun,wata soyayyar jikan natane ta soma ratsa dukkan wata gaɓa da kuma sassan jikinta haɗi da kuma zuciyarta,tana jinsa tamkar ɗan data haifa a cikinta wato Sudais.
gefe guda wani tausayinsa ta keji domin tasan ba zata iya sama masa abinda ya keso ba,komai hqr da kuma juriyar mutum indai yana ɗauke da zazzafar soyayya a cikin zuciyarsa za kuga komai nasa nada banne yana yinsa tamkar ba sauran mutane ba,zai zamana juriya da kuzarinsa nayin ƙasa yayinda zai kasance vry weak.
numfashi ta sauke tare da murza tafin hannunsa cikin ƙasa da murya kasan cewar tasan bai son haniya da kuma surutu ya sata faɗin.

"Hausawa sunce abarwa rai abinda ya keso sai komai yazo da sauƙi,amma anayin hakanne idan aka tabbatar da cewa wannan rai ɗin tabbas zai samu abinta yake muradi da ƙauna,shin tayayane za'a iya zuba ruwa a cikin rariya harya zauna?tayaya mutum zai rayu babu iskar shaƙa?tayaya zuciya zatai aiki bayan numfashi da take amfani dashi a yanzu babu?..."shuru tayi na ɗan wani lkc sai kuma ta ɗura da faɗin.
"tayane MALEEK zaici gaba da takon son abinda yasan bazai sameshi ba?,wacece ita? ina take? ina zaka sameta duk baka sani ba?to kana tunanin zamu barka cikin ƙunci da kuma haɗi da kaɗaicinta,ka sani kakai matakin da zaka ajjiye iyali kamar kowa kuma wannan yarinyar da kake magana koda ka sameta zai wahala su amince su baka aureta domin tayi ƙanƙant...."

ka tseta yayi ta hanyar ware narkakkun idanunsa a saman fuskar Abbu kana kuma ya juya ƙwayar idanunsa zuwa ga Mai babban ɗaki,pouting lips ɗinsa yay yana jin zuciyarsa na breating kamar zata fiddo waje cikin wani cool sound yace.

"Rainonta zanyi"

gaba ɗaya suka zuba masa idanu musamman Abbu da yafi kowa sanin wanene Maleek da kuma abinda yake so,kuma da lalurar dake tare dashi.
shi kansa zaiso ace ya samu wacce ya keso,amma yasan hakan ba mai yiwowa bane domin a yadda Mai babban ɗaki ke magana ya tabbatar ba zata iya ɗauke buƙatar gwarzon namiji maiji da ishasshiyar lafiya kamar Maleek ba,ya tabbatar dukkan wacce Maleek zai amshi virgin nata ba ƙaramar wahala ake sha ba,ga yarinya mai ƙaranci shekaru irinta ai sai yayyon fitsari ya kamata ta dalilin hakan.
numfashi ya sauke wannan shine karan farko da bazai iya samu ya bawa Maleek ɗin abinda ya keso ba,yana jin hakan kuma a matsayin babban lamari ya san cewa a yadda Maleek ya ɗaukeshi ko Mai babban ɗaki bazai iya sharing damuwarsa da ita sai shi ɗin daya zame masa GARKUWA.


Danne abinda yake ransa yay kana kuma ya gyara zama yace.

"Eh zaka iya ranonta kowa ya san da hakan,amma shinkai baka tunanin kanka da kuma abinda kakeso?kana buƙatar samu lafiya mai inganci kuma wannan yarinyar ba zata iya sama maka ita,kuma muna buƙatar ganin yaranka kamae yadda muke ganinka a gabanmu,ka ɗauka mun amince tayaya zaka sameta? shine abin tunanin alfarma guda zan iya yi maka Maleek zaka auri Meyrah idan yaso kaci gaba da nemanta ita yarinyar idanka sameta mun amince kayi aure da ita a karo na biyu"

tunda Abbun ya fara magana idanunsa a lumshe yake har kawo yanzu daya gama,ware laɓɓansa yay ba kuma tare daya ce wani abu.
a sanyaye kuma a kasalance ya miƙe ya nufi part ɗin da Mai babban ɗaki ta kaisa ƙwanaki.
cikin nutsuwa da kuma kamala yake tafiya harya kusa zuwa part ɗin sai kuma ya tsaya cak kamar wanda yaga wani abu,mai makon ya amsa masu waccan maganar sai yace.

"bana iya zama a part ɗin da wasu ƙazama suka gudanar da mulkinsu,itama fadar dan babu yadda na iyane,ina son nan da gobe a gyara part ɗin..."fesar da numfashi ta hanci mahaifinsa zaice amma yana jin kunyar idan Abbu kana kuma baison da wanne suna zai kira shi mahaifin nasa dashi ba.
gyara tsaiwa yay tare da covering jikinsa da alƙyabbar yace.
"part ɗin Daddy sannan fadar a sauya mata tsari ta hanyar zuba sabbin abu a sanarwa da sarkin fada haka,bro kuma daga yau yabar tsaron ƙofa shima ai ɗan uwane mai ƴanci"

yana faɗin hakan ya shige cikim part ɗin ba tare daya jira abinda zasu faɗa ba.
wani ƙayataccen murmushi Mai babban ɗaki ta sauke yau jinta take wani fresh kamar babu abinda yake damunta.

"Abbun Maleek sai a fara shirye-shiryen bikin nan da 3days ko,za'a haɗa da bikin naɗinsa idan babu takura"

kaiya jinjina mata ta hanyar girmamawa kana ya miƙe tsaye yace.

"Allah ya ƙara maki lafiya yanzu kam domin dama shirye-shirye sunyi nisa da kuma irin event da kuma al'adun da za'ai a bikin domin dole duniya tasan da zaman bikin tun a safiyar yau na buga invitation tare da manyan photonansa wanda na tura yanzu da akai masa na naɗi,na tabbatar zuwa yanzu labarin bikin SARKI MALEEK SUDAID SUFRAK BILHAS,ita kuma yarinyar yau za'a mai data gidansu saidai tazo matsayin fulanin bilhas"

murmushi jin daɗi Mai babban ɗaki tayi kana tai masa gdy shi kuma yay waje domin samun Sarkin fada da kuma Drever ya maida Meyrah gida..


Fulani kilishi ce tsaye a tsakiyan tirakarta sai kaiwa da kawowa take tare da haɗe hannayenta tana bugasu a jikin na juna.
bata taɓa tunanin irin wannan ranar zata riskesu ba,ta gama yarda da kuma yaƙinin cewa zuwa yanzu tilon ɗan nata wato Lil prince ya gama zama Sarki.
sai kuma abin yazo mata a ba zata domin yadda take tunanin abin ba haka yazo mata ba,bata taɓa kawowa ranta cewa Maleek ɗin yana raye ba.
bare kuma harya nemi dawowa kujerar mahaifin nasa.
lallai basu da wata dabara domin duk yadda sukai da haɗa wani mugun saiya wargatse.

"Uhmm yanzu dole muyi hqr mu riƙi abinda yazo mana dashi,sai dai dole nayi abu guda yana da kyau kaje wajan mahaifinka kace kana buƙatar kuɗi kimanin 20m domin barin ƙasar kai ba zaka iya zama kana ganin baƙin ciki ba,kaga kana amsa saika sanya wasu su katse Sarki Maleek kai kuma kabi jirgi kamar gari dole ba za'a taɓa cewa kai bane idan aka ɗauki watanni saika dawo a naɗaka sarki a karo na biyu"

shuru yay yana auna maganganunta daka bisani kuma ya miƙe tsaye tare da soma tafiya yace.

"idan har jinin mahaifina ke gudana a jikina babu shakka sai naga bayan Sarki Maleek tabbaa nina zan kawo ƙarshe mulkin zan nuna masa cewa tawa ZARRAH gaba take da tasa,babu shakka zan nuna masa kalan nawa ƙarfin iko lallai daga yanzu zai fara irga raguwar awannin da suka rage masa a duniya"

yana faɗin hakan ya saka kai ya fice daga cikin part ɗin nata baki.

direct part ɗinsa ya nufa yana zuwa ya fara gyara kayansa cikin aƙwati sai daya gama komai sannan ya miƙe ya nufi tirakar tsuhun sarki mai murabu wato Khalid.


A hankali Sarki Maleek ya zare alƙyabbar jikinsa tare da saƙaleta a gefen bedside,kana kuma ya sanya hannu ya zare rawanin da aka naɗa masa a kansa,wanda ya kejin yay masa nauyi gaske komai yake dauriya yake badan yana so ba.
shi kaɗai yasan abinda yake damun zuciyarsa amma ya fahimci ba kowa zan gane zafi da kuma raɗaɗin daya keji akan rashinta ba.
ta zame masa rayuwarsa yana jin komai nata a tattare da ita babu shakka saya sameta dan bai taɓa kakowa ransa cewa a wannan karan zai zama mara nasara ba.

hannunsa dake manne a jikin handle ya mura nan take ƙofar bathroom ɗin ta buɗe cikin nutsuwa ya tura duka gangar jikinsa zuwa bathroom ɗin.
a gaban makeken madubin dake manne a jikin bangon bathroom ɗin ya tsaya.
idanunsa ya ɗan lumshe kana kuma ya ƙara buɗesu a jikin mirrow'n ƙwantacciyar sumar dake ƙwance a ƙirjinsa ya tsorawa idanu ganin yadda ta ƙara yawa tare da baƙi sai sheƙi take.
taune lips ɗinsa yay dai-dai lkcn da yaji mararsa ta harba da ƙarfi har saida ya saki ƴar ƙaramar ƙara,tare da sanya hannu ya dafe saman marar tasa wanda yaji yana dripping haka nan.
sosai yay mamakin hakan cikin son kawar da hakan ya sanya hannu ya zame wandon shadar dake jikinsa ya saƙale a hanger.
a kasalance ya ƙarasa gaban shower'n tare da sakarwa kansa ruwa.
duka hannayensa ya sanya ya dafe jikin bangon kana ya ɗaga fuskarsa sama.
ruwan shower'n ya fara dukan saman beauty face ɗinsa wacce ta ƙawatu da zagayayyiyar saje da kuma gemu.
jin ruwan na shirin yi masa illa ya sanya yay saurin ɗauke kansa tare da gyara tsaiwarsa.
sosai ruwan ke dukan jikinsa saida yay wanka ya gyara jikinsa tare dayin brush ya ɗaura al'wala ganin dab da magrib ake.
wani long blue black ɗin towel ya ɗauka ya ɗaura saman waist ɗinsa.
kana ya fito daga cikin bathroom ɗin jin garin na ɗan kaɗawa alamar yanayin damuwa ya soma bai yana ya sanyashi lumshe idanunsa tare da ƙara sawa gaban window'n dake bedroom ɗin ya ɗan buɗe kaɗan.
ƙyaƙyawar ƙoramar dake gudana ya zobawa idanu inda gefe da gefenta ya kasance da wasu kurayen jiyayi masu ƙyau da kuma tsari.
banda kukan tsuntsaye babu abinda ke tashi a wajan.
saurin lumshe idanu yay tare da harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa sabida wani ƙamshin furannin daya kawowa hancinsa ziyara.

wata daddaɗar iska mai ratsa jikin mutane ce ta fara kaɗawa hakan ya bawa sumar kansa damar kaɗawa yana sauka a saman idanunsa.
a wannan lkcn shi kaɗai yasan abin yake tunani,lallai wanda ya ja da ikon Allah shine sa taɓewa,kamar yadda bai taɓa tunanin ko amafarki zai zama sarki ba,haka kuma bai cire ransa da samun abinda zuciyarsa keso ba.
a wannan zaibi abinda zuciyarsa keso ne,zai kuma tabbatar da kasan cewarsu tare *ABADAN DA'IMA* wannan shine buri da kuma fatansa,bayan ya tsallake *TUGGU BIYU* da maƙiyansa suka ƙulla masa.
da zarar kuma ya samu abinda yake ƙauna zai bar masu garin zaije ya zauna da ita tamkar *TAGWAYEN ASALI* wannan shine kawai muradinsa.

sakin labulan window'n yay kana ya juya zuwa gaban dressing mirrow bisa dole ya

32 / 38