Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
ban ta`ba tsanmanin haka daga gare shi ba,Dan haka ki yi hak`uri,komi da
ki ka ga ya faru it's about destiny,kafin in zo nan mun yi magana da Daddy na yace in baki hak`uri zai
zauna da Dadyn Samuel sannan ya na son ki had`a shi da Broth Daniel d`in zai yi mashi wa'azi ko da za a
samu ya dawo cikin hankalin da natsuwarsa".
" Kai..kai ...Gloria I'm so happy Na ji dad`in wannan magana taki ,thank you ban dan da wanne irin
baki zan gode maki ba".
"Kar ki damu Cecelia wannan ai duk yi ma kai ne,kin san fa irin yanda na ke son Broth Daniel, Na
kwallafa raina akan shi,ba na jin zan iya rayuwa ba tare da shi ba,zan yi iya yina na ga mun dawo da shi
kan haya madaidaiciya".Nam fa Gloria ta cigaba da lallashin ta har ta samu ta ci wani abu cikin abincin da
ta zo da shi.
Shi kuwa Abbakar sai wajen Magaribha ya iso Jos sai da ya tsaya ya sauke sallolin da su ke akan shi
sannan yai sai duk abinda ya ke ganin zasu buk`ace shi sannan ya Isa hospital d`in da ya ke tunanin ko
tabbacin can Cecelia zata kai Grandma, san da ya Isa bai sha wahala ba a ka kai shi d`akin da a ka
kwantar da su,Cecelia ya iske ta d`ora kanta kan gadon da Grandma take, barci ya kwashe ta a haka
hannunta d`aya na rik`e da da hannu Grandma,kamar mai jin tsoran wani zai kwace mata ita,sosai ta ba
shi tausayi ,gefe guda ya samu ya zauna ba tare da ya yi wani motsin da zai tashe su ba,ganin da gaske
barcin ta ke ita kuma Grandma an sama mata drift yasa ya shigar da duk abinda ya zo da shi ya nufi office
d`in Doctorn Dan yasan me yake damun Grandma d`in da har ta shiga cikin wannan halin.
Sosai ya samu kwanciyar hankali bayan ya samu gamsasshen bayani daga bakin Doctor d`in ,"Kar ka
damu stress ne ya jefa ta a cikin irin wannan halin amma za ta samu lafiya da izinin Allah,zamu sake
dubata zuwa gobe daganan sai mu ba ku sakamakon na k`arshe ",wannan shine batun da Doctor yai
masa na ƙarshe.
Bai sake komawa Room d`in ba har sai da ya gabatar da Sallahr magariba, lokacin Cecelia ta farka daga
nannauyan barcin da ya sace ta,sosai ta rink`a mamaki kayan da ta gani an shigo da su,ganin Abbakar ya
shigo cikin d`akina yasa ta d`aure fuskarta gami da kauda kanta gefe alamun bata ma son ganin shi.
" Me ya sake dawowa da kai ,ko ka zo ne k`arasata kamar yanda ka d`auko hanya ne ?".
"Shut up Cecelia na gaji bana son wad`annan k`ananun zancen , ki bar komi ya wuce,I have my own
right to do any religion that I want,don haka ki bar ni,Na zo nan ne domin Grandma ta samu lafiya Dan
haka bana buk`atar wani sabon tashin hankalin".
Ganin da gaske yake yasa ta ja bakin ta tai shiru,suka cigabada da zaman kurame,shi ya cigaba da yi
ma Grandma duk abinda akace ayi mata,duk bayan wani lokaci zasu rik`a motsa mata hannu da
k`afafunta don gudun paralysis ya same ta.
" Ki tashi ki tafi Gidan su Gloria ki kwana ni zan kwana da ita anan",shine abinda Abbakar ya ce da ita,
ta so tayi ma sa musu amma ganin ba fuska ya sa dole ta hak`ura,ta d`ebi kayan abincin da Glorian ta zo
da su ta tafi da su.
Lokacin da ta Isa Gidan su Gloria ta sanar da ita zuwan Daniel ba k`arami Murnar da mamaki ta yi ba,
har Allah Allah take Gari ya waye su je hospital d`in ta gan shi,ta sanya shi a idonta ko ta samu sauk`in
daga irin nauyin da Zuciyarta ta ke yi mata akan son shi.
Sai dai kash tun kafin su tashi a barci Mahaifiyarta ta yi masu knocking akan su tashi.
" Lafiya Mom za ki tashe mu tun yanzu ?", Gloria ta tambaya da alamar barci akan fuskarta,"Surprise
Dadyn ki ya shirya maki".
Sai da Gloria ta `bata fuska kafin ta ce,"Surprise kuma wanne irin surprise ? ",.
My daughter ya Na ga fuskar ki haka kamar ba ki farin ciki da abinda ma fad`a maki ba ?".
" Ba haka bane ba Mom kawai da akwai inda na ke son zuwa early in the morning d`innan that's why ".
" Ayyah my dear hakan ba zai yiwu ba domin yanzu haka Mota na waje na jiran mu,go back and fack
your thing zamu bar Garin Jos yanzu"...."What!....za mu bar gari mu je ina,yaushe aka yanke wannan
hukuncin?".
"Oh ki kwantar da hankalin ki,domin Mahaifinki ne ta samu matsayin Pastorn a wani Babban Church
d`in da suka gama Ginawa yanzu haka yau za a gudanar da bikin bud`e Church d`in shi yasa ya aiko da
Mota a d`auke mu a kai mu Airport domin mu samu Isa Lagos d`in don mu samu halarta bikin".
"A'a Mom.. No ....hakan ba mai yiwuwa bane ba,ni babu inda zanje,ina da wanda nake son gani a yau
ba zan biki ba"....
"Kema kin san baki isaba babu inda za ni ba tare da ke ba,koma meye ki bar shi sai wani lokacin ,idan
kuma kin musa,min a haka da sleeping dresse d`in zamu tafi da ke".
Hankalin Gloria ya yi matuk`ar tashi yai ba, ba shiri ta nufi inda Cecelia take zaune ta rabka uban
tagumi ta ce da ita," I'm so sorry, Na so ace tare da ni zamu yi fighting d`in wannan battle d`in da ya tun
karo ki sai dai kash hakan ba mai yiwuwa bane ba, ina mai baki hak`uri akan haka,tafiyar gaggawa da ta
kamani zuwa Lagos mun koma can da zama gabad`aya da family na,sai dai ki sani a ko ina nake ina tare
da ke,zan baki goyon baya hundred percent akan mu dawo da Broth Daniel kan hanyar da ta kamata,zan
tafi ba dan na so ba".
Haka suka tashi jiki kowa a cikin su a sanyaye ,Cecelia ba ta tafi hospital ba har sai da taga tashin su
Gloria kana ta juya ta tafi tana mai share hawayen kewar k`awa ta Gari da tai yi,k`asa hak`uri Gloria tayi
har sun fara tafiya ta dakatar da driver d`in da gudunta ta dawo baya tana mai kwalama Cecelia kira,cike
da mamaki ta juya tana mai tambayarta.
"Lafiya Gloria na ga kin dawo?",Gloria na mai da hakin gudun da ta yi ta bata amsa da cewa," Komi
lafiya ina son in baki sak`o wajen Broth Daniel ki fad`a masa har yau har gobe ina son shi,ina jin shi a
cikin raina, Zuciyata ba zata samu salama ba har sai na ganni a matsayin Matar shi,ba zan huta ba har sai
na ga hakan ta kasance,I promise I will be back soon zan dawo saboda Soyayyar shi,shi shi kad`ai ki gaya
mashi hakan".tana kai wa nan a zancenta ta juya da d`an gudun ta ta koma motar su ka tafi Mahaifiyarta
ma ta yi mata mitar tsaida sun da tayi amma ita ko a jikinta.
Ba k`aramin mutuwa jikin Cecelia yai ba sakamakon jin abinda Gloria tace,wannan wacce irin Soyayya
ce,da har za ta bari ta makantar da ita har haka shin ko ta manta yanzu ba addinin su d`aya da Broth
Daniel ba ne ba ko me?",abubuwa da dama suka cigaba da kai kawo a cikin rai da Zuciyarta kafin daga
bisa ni ta watsar da su ta cigaba da tafiyata zuwa hospital d`in da Grandma take kwance.
Sanda ta Isa duk wani abu da ya kamata ayi ma Grandma anyi mata hatta da wanka yasa Nurse d`in
asibitin sun yi mata,nan haka suka cigaba da jinyar Grandma har na tsawon kwana biyar tun Cecelia Na
jin haushin shi har ta fara ragewa,domin ba abinda ya rage daga kulawar da yake ba su sai ma abinda ya
k`aru,kuma zaman shi a tare da su bai sa ya daina ko rage na shi Addinin ba,har mamakin k`arfin halin shi
take,tsakanin shi da Hibba kuwa sai dai waya tuni an kawo mata Muhammad Jaheed shi ke taya ta hira.
Ranar da suka cika one weak ranar Grandma ta farka,ita kanta ta yi mamakin ganin shi tsaye akan duk
lamarin ta ,duk wani abu da ake so ko za a buk`ata shi ake tambaya, ba musu kuwa zai je ya kawo shi,da
kallon mamaki kawai ta ke bin shi da shi har daga k`arshe ta ce da shi,"Daniel ina cikin mamaki na sha
canja Addini da kai zai sa ka guje mu ka wofintar da dukkan lamarin mu ashe ba haka bane ba, kawai
Zuciya da tunanina ne su ke ba ni hakan".Grandma ta fad`a cikin muryarta ta marasa lafiya.
"Haba Grandma ta ya za ai in aikata hakan ba fa ni da wasu ahali da ya wuce ku, me zai sa in guje
ku,ina son ku ba zan iya barin ku ba ,kamar yarda na ke son Addini na ba zan iya barin sa ba".
"Shikenan Daniel indai haka ne na yarda ka cigaba da bin Addinin da,kake so amma Na rok`e ka kar ka
barmu,kar ka sauya mu a matsayin ahalin ka.
"In Sha Allah ba zan aikata hakan ba,ni ban k`i ba ma ku shirya mu koma can Kanon da ku,mu yi
rayuwar mu a tare a can"...
Ta katse shi da da cewa," A'a ni babu inda zani nafi son in k`arasa `yar sauran rayuwata a cikin wannan
Garin tare da `yan sauran k`awayena da suke Raye,muna daga nan zan dunga yi maka addu'a da ga kai
har Matar ta ka".
"Dan Allah Grandma ki daina fad`ar mutuwar nan ba yanzu ba ina son har `ya`yana da na Cecelia sai
kin gani".
" Kayya dai d`annan a haka ma ai mun sha miya,sai dai mu jira mutuwa kawai yanzu,damuwata d`aya
a yanzu shine bazan ta`ba iya kama hannun d`anka in tafi Church tare da shi ba,ba za ka ta`ba iya
haihuwar `ya`ya kasa sunan mamarka,ni ko babanka ka ba shine kawai damuwata.
Cecelia ce tai saurin amshe batun da cewa,"Kar ki damu Grandma ni inna haifi yarana zan sa sunan ki
har da ma sunan su Dad".
"Kai na ji dad`in haka my dear Allah yasa in ga `ya`yan naku gabad`aya".
''Yauwa Grandma ki K`ara kwantar da hankalin ki hatta da Maganar bikin Cecelia zan yi k`ok`ari in ga
na dai-daita ta kafin intafi,kin ga Doctor ya ce ba zai sallame mu ba har sai ya ga kin samu lafiya sosai da
sosai".
"Kar ka damu Yarona indai don wannan ne komi zai koma normal",haka Abbakar ya cigaba da jinyar
Grandma sai da yai kwana goma kafin ya koma Kano, gaba d`aya ya raba hankalin shi Gida biyu yau ba
shi Kano gobe ba shi Jos,sosai ya fita cikin hayyacinsa har Rama sai da ya fara ,bayanda za ai ya bar ma
Cecelia jinyar Grandma ita kad`ai hakan ya sa dole yake go and come d`in ,ya kan yi aikin shi a system ko
da yana can Jos d`in ,Grandma tafi wata kwance a asibitin hakan ya sa ya maida Hibba Gida ganin Month
d`in Edd ta ya kusa shi kuma ba mazauni ne ba, sosai jikin Grandma d`in take samun sauk`i hatta fara
tafiya amma da taimakon k`arafa hakan ya fara sa hankalin su ya kwanta ita kanta Grandma d`in har
tausa Abbakar d`in take gani irin fad`i tashin da yake duk akan su.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1
PAGE 10 ❤
FREE PAGE
"Yauwa Yarona d`an Albarka Na gode sosai, in sha Allah za kai albarka".
Sai da ya washe bakin sa alamun yaji dad`in Addu'ar da tai mai kafin ya ce da ita," Momynah na
k`agara in ga kin haihu,na ga d`an k`anina da za ki haifi min mai kama da ni".ya kai zancen ya na mai
cigaba da matsa mata k`afafunta.
Sai da Hibba ta zaro idanunta waje kafin ta ce,"Kai Muhammad Jaheed Namiji kuma ka ke son in
haifa,ina laifin ka ce in haifa maka yar Mace,wacce za ka rik`a kama hannunta ku je makaranta, wacce za
ka rik`a tayawa Home work, wacce kuma za ka tsaya kai da fata wajen ganin tayi ilimin Addini da na
zamani,ka zama bango kuma gatanta,ka cike mata sauran gurbin Ahali da ta rasa",ta kai k`arshen zancen
muryarta a raunane.
Duk da k`arancin shekaru na Jaheed sai da maganganun Hibba kuma Momynsa suka sa jikinsa yai
sanyi,"Shikenan Momynah da ga yau zan rik`a Addu'a Allah ya sa ki haifo mana Baby girl,zan kama
hannunta mu tafi ko ina,duk inda zani tare da ita zani,ba zan bari wani Namiji ya shiga cikin rayuwar ta
ba balle har yasa ta Kuka,zan kasance mai aikata komi dumin ita,kuma ni zan za`ba mata suna",ya d`an yi
shiru kafin ya cigaba da cewa,"Amma fa dole ta rik`a ce min Yayah ko tunda na girme ta ko?".ya kai
k`arshen batun cikin sigar yarinta.
Sai da Hibba tai dariya kafin ta bashi amsa,"Ba dolenta ba Jaheed, ai dole ta Kira ka da Yayanta,kasan
akwai tazara ta wajen shekara Goma a tsakanin ku,ka kenan dole ta girmama ka".
"Yehhhhhh Na ji dad`i tunda nima na kusa zama Babba".
" Yau to bar k`afar haka naji ta yi min sauk`i yanzu taho mu ci abincin da ka kawo min","A'a ki ci naki
ne ni na ci nawa,kuma ni bana jin yuwa"....."Shhhhhh rufa min baki,sai ka ci shi,ki baka ga abincin da
yawa bane ba ai nasan irin Cin abincin naka dan haka ha bud`e bakin ka".
Sai da Jaheed ya saki murmushi kafin ya bud`e baki ta fara sanya mashi abincin a baki,a cikin Zuciya da
Idanunsa kuma ta na k`ara samun k`ima da matsayin mai girma ya rasa wanne irin so,k`auna da kulawa
ta ke ba shi,a lokacin da tai Aure ba sa tare ba k`aramin kewa da rashin ta yai ba,ta kan ba shi
muhimmanci fiye da dukkan wani abu ko kuma ita kanta,takan `bata lokaci mai tarin yawa don ganin
kawai ya yi farin ciki ko nishad`i,ta fi kowa sanin shi da kuma fahimtar halayen shi,ko wannan abincin
yasan za ta iya cinye shi har ma ta nemi k`ari amma saboda yana tare da ita ba zata iya cin shi ita kad`ai
ba,dole sai sun ci tare,haka ta koma yanzu bunu-bunu ta nemi abinci,ba su wani d`au lokaci wurin cin
abincin ba ya mik`e ya ce mata ya k`oshi.
"A'a ba ka isaba dawo zauna sai mun cinye shi tare".
" A'a ni kam ba zan dawo ba na k`oshi,wannan abinci ai sai dai ke ni yafi k`arfina in ba so kike nan gaba
kad`an a kasa banbance ni da ke in zama Orobo kamar ke".
Yanayin yanda ya ga ta zaro idanu waje ne yasa ya fara dariya gami da k`ok`arin barin wajen da
gudu,"Au guduwa za kai to wallahi Inanan ina jiranka za ka dawo ka same ni ba dai ni kake kira da Orobo
ba,zamu had`u ai,inna kama ka za ka basu labari".ta na zancen da fara'a kwance akan saman fuskarta.
"Ah aha,su Hibba ne zaune anan Ana hutawa?", Cewar Baba Asabe cikin yanayin izgili da k`arasowarta
wurin kenan.
Murmushin yak`e Hibba ta saki kafin ta bata amsa da uhm.
Bayan ta samu wuri ta zauna ne ta ce da ita," Ananan Ana ta zuba ma ciki lodi ko,ni na rasa wanne irin
Aure ne wannan ki ka yi, kin tafi kamar ba ki tafi ba kullum kina cikin Gidannan, wai me ye matsayin da
ma'anar wannan Auren,shin mijin na ki gajiya yai da ke ne ya maido ki Gidan ku ko ko sakin ki yayi,ko dai
ya kasa d`aukar nauyin d`awainiyar ki ne da ta ke abinda ya ke cikin ki,domin na ga alama shi kan shi da
za a bashi dama da cikin Gidannan zai dawo ya tare,shin ahalin su ba su da Zuciya ne komi?"...
Kamar an jeho Ummie Maryam haka ta shigo cikin Parlourn tana mai fuskantar ta da cewa,"Haba
Baba Asabe wannan wacce irin magana ce,ta ya za ki zo gabanta ki titsitsiye ta da irin wannan zafafan
tambayoyin,ai hakan bai dace ba kuma bai kamata ba".
"A kamarya bai dace ba,a tunanin ku Dan ku kun Gaza gaya mata gaskiya sai muma mu taru mu zuba
mata ido,dole ne mu gaya mata gaskiya, taya mace da Gidan Mijin ta zata dawo zama Gidan
iyayenta,gabad`aya ci da shanta har ma dana Wanda ta ke ikirarin Mijin ta ne yana cikin Gidannan,me
hakan yake nufi shin ta zama sakakkiya ne ko kuma ya nuna gazawarsa akan ta ne a fili,kullum tana
zaune k`ark`ashin bishiya bata aikin fari balle na `baki daga ta ci sai tai kashi,ko da yake duk wanda ya k`i
cin biri ya ci dila,haka kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho,ayi dai mu gani domin tafi-tafi takardar
sakinta za ku ga ta biyo baya ,ko kuma wata rana ku wayi gari ya gudu ya barta"....
''Wa ya gaya ma ki haka zata kasance da ita,ko angaya maki kowa ke da bak`ar k`addara irin ta ki
Asabe", Cewar Mama Hadiza da fitowar kenan daga sashen ta hannunta d`auke da jik`on maganin da
take baiwa Hibba Dan samun sauk`in nak`uda.
A kid`ime Baba Asabe ta waigo jikin ta har yana rawa," Hadiza me kike nufi da wannan kalaman naki a
gare ni ?''.
"Oh baki gane ba,to bari in yi maki dallah-dallah yanda zaki gane shin kin manta nan Gidan ba Gidan
Mijinki ba ne ba Kema Gidan iyayenki ne,Gidan da ki ke zaune tsawon shekaru Ashirin da wani abu tun
`yar ki da kuma d`an ki na da `yan shekaru,shin ko kin manta da hakan ne,ke yara biyu ki ka zo da su ,Na
rasa me ma tsare mi ki a cikin Gidannan Asabe, shin nayi maki wani abu ne wanda na can-canci wannan
cin kashin da ki ke min,ba ki da wani abu sai dai son ki ka ga kin bak`anta min da ni da `ya`yana me na
tsare miki dan Allah ?".
Hawaye Baba Asabe ta sharce muryarta Na fidda sautin kuka ," Yanzu daga na zo fad`a ma `yarki
gaskiya sai ki bi bayana da sharri da kuma gori"....
"A'a Asabe k`aryar kike ba gaskiya ki ka zo faɗa