Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
shi mijin ba zai tsira ba,ba shi ba kwanciyar hankali da
natsuwa,yanda zan yi rayuwa cikin baƙin ciki haka shima zai rayu cikin rashin kwanciyar hankali".
"Ai ko in ki kai haka kin kyauta yauwa wai Nurain da sanin ki aka maida shi,can Gidan na ji ma ance ya
koma kenan wai da yiwuwar ma an bar ma Momy Hibba shi",a kiɗime Ummu Nurain ta wai go tare da
cewa,"Me ne an bada kyautar ɗana ba tare da na sani ba,duk ikon da ake nuna min a cikin Gidana bai isa
ba har sai an raba ni da ɗana da na haifa da cikina,ba fa tsinto shi nai ba ni na haife shi da cikina","To
aiko haka muka samu wannan labarin don da Mama da kanta zata zo ta ji ba'asi sai Baba Asabe ta hana
ta ce abun magana zai zama gara ni in zo in ji gaskiyar zance ba sai ta zo ba","Wallahi ba zan iya cigaba
da irin wannan rayuwar ba na rasa wa yake Aurena cikin Mahaifiyar Uncle Jaheed da kuma Momy
Hibba,umarni da hukuncin su ne kawai ke gudana a cikin wannan Gidan ba zan iya ba dole in ma abun
tufkar hanci tunkafin a wayi gari in rasa tudun dadafawa a cikin rayuwata".
"Da kin kyauta inji kin aikata abinda zai haukata mutanen cikin babban gida, in ki kai haka ba Mama ba
hatta da Baba Asabe sai ta ƙara yin alfahari da ke,mudun ki ka aikata abinda ki ka ce","Tabbas ki shaida
ma su haka zata faru,zan fara daga waccan sakarar mai ƙaryar Sarauta,sai na nuna mata ita ba bakin
komi ta ke ba,daganan in samu hanyar da zan yi waje da ita,babban fata na a yanzu in rabu da wannan
cikin da ke jikina duk shine ke hana ni aikata duk abinda ya tare min gaba".
"Sai dake ƴar ƙunar baƙin wake ban ce ki raga ma kowa ba,kar ki manta ko ke wace ce ƴa gurin Mama
Zaliha kuma jika gurin Baba Asabe,tijara ba sai an koya maki ba,kin gada kuma kin iya,bari in tashi in tafi
da wannan".
"A'a Asiya ki tsaya ko ruwan shayi ne in haɗa maki bai kamata ki tafi ba ki ci komi a gidana ba","Wa ni
a'a na ƙoshi kin san Mama bata wasa indai maganar girki ne,sai da na cika cikina kafin in fito","To
Shikenan ba damuwa mu je in raka ki",wani daddauɗan zanin na ta ta ɗauka ta yafa a madadin mayafi
suka nufi harabar Gidan,suna tafe Asiya na ƙara famfata,gami da sake tunzurata,wani irin daskarewa
wuri guda Ummu Nurain ta yi sakamakon abinda ta gani,tafe su ke cikin nishaɗi da kwanciyar hankali
janye da trolys,sai briefcase dinsa sagale akan shoulder ɗin Gimbiya Ayush,ba Zeenat ba hatta da ita
kanta Asiyar ta girgiza,sai da tai ƙarfin zuciya kafin ta iya cewa
"Kan uba Aunty Zeenat mai na ke shirin gani haka,na ga kamar unguwa za su tare",kasa iya cewa komi
Zeenat ta yi sai,zuciyarta ke ta faman bugawa da sauri ta ke,gudun jininta ya ruɓanya da wajen kashi
uku,ta kasa iya hassala komi, su ko da alama ba abinda ya dame su,Imam Jaheed sai faman murmushi
yake akan labarin da Gimbiya Ayush take ba shi,ko nuna alamun sun gansu ba su yi ba, ganin da gaske
tafiyar za su yi Ummu Nurain ta nufi inda suke ta sha gaban su,sai faman huci ta ke kamar wacce ta yi
dambe,ko nauyin cikin da ke jikin ta ba ta yi ji,cike da masifa da bala'i ta fara magana da cewa,"Me ye ya
ke shirin faruwa anan,na ga kun kwaso trolys kamar kuna shirin barin gari a'a kar ka ce min fita za kai
tare da ita,idan ma haka neka sani hakan ba mai yiwuwa ba ne".
Waige-waige Jaheed ya fara yana son ya tabbatar da shi ta ke ko-ko da wani daban take,"Wai da wa ta
ke,wace ce ita ,nan a wurin dai banga wani ƙaramin yaro da zai dai-dai da ɗan ta ko sa'an ɗan ta ba balle
in yi tunani shi take bama wannan umarnin",ya kai zancen yana mai zagaye ta ya buɗe but ya shigar da
kayan da suka fito da su,"Kar ka nemi ka raina min hankali Yayah ,Ni ɗin ce ba ka gane ba,ko dai ka fara
samun matsala a cikin tunanin ka ne,ka samu juyewar ƙwaƙwalwa ne kome ?".
Da fushi ya saki murfin but ya fuskance ta da cewa,"A'a ban samu juyewar tunani ko ta hankali
ba,kamar yanda ke ki ka samu,kuma da gaske ban san ki ba,domin ni ban Auro mahaukaciya mara tunani
kamar ki ba,ban aje ballagaza kuma mara tunanin irin ki ba,da kuma ki ke tambayar ina zamu ko tafiya za
mu yi?, Eh tafiya zamu yi domin ba zan bar maki ita ki kashe ko ki naƙasa min ita ba,ita ɗin mata ta ce,ina
samun natsuwar hankali da kwanciyar hankali a tare da ita fiye da ke,ki sani a duk randa ki ka shirya
zama mace ta gari ki ka koyi ɗaukar nauye-nauyen da su ke a kan ki ,to daga ranar ni kuma zan cigaba da
kallon ki a matsayin Mata ta,amma ba a yanzu da ki ke rayuwar da ko dabbobi ba sa irin ta ba".
Cikin rawar baki Ummu Nurain ta tari numfashin sa da cewa,",Me waɗannan munanan kalaman na ka
su ke nufi,shin kana nufin na zama sakakkiya,to ka sani wallahi ba ka isa ka maida ni bazawara ba, ina so
ka sani ba wata mace da ta isa ta zo har cikin Gidana ta ci ni da yaƙi ta fidda ni daga cikin sa,Aurena da
kai mutu ka raba,babu wata da ta isa ta shiga tsakanin mu,ba a haife ta ba,daga kai har ita ku rubuta
wannan a cikin ran ku,ba zan yafema cutar da ku ke min ba, sannan ke kuma".ta mai da kallonta kan
Gimbiya Ayush,"Kar ki yi farin ciki ko murna domin zato da tsammanin da ki ke karen ki ya kama kura to
ba kura ya kama ba damisa ya kama,Ni da kaina zan kawo ƙarshen zaman ki a cikin Gidannan",tun kafin
ta gama fadar abinda ta ke cewa Jaheed ya shigar da Gimbiya Ayush cikin Mota ya barta sai ɓaɓatu ta
ke,ganin da gaske tada Motar zai yi su tafi ya sa ta shiga gaban Motar ta tsaya ta babbake ko ina gami da
ɗaga muryar tare da cewa,"Wallahi in ka ga ka fita da Motarnan to ba na raye,sai dai in gawata za ka
taka ka bi ka wuce,amma babu inda za ni inanan",kan shi ya leƙo ta wurin glass yana mai cewa da ita"Au
haukan na ki har ya kai haka,to ki tsaya zan nuna mi ki naki lissafin gajere ne,in ya so in ki ka je can
lahirar sai ki samu wanda za ki nunama wannan kalar hauka da baƙin kishin na ki", gadan-gadan ya taka
mota gami da nufo ta, Gimbiya Ayush runtse idanunta tayi gami da kama shi ta cukwuikuye sai faman
salati ta ke gami da ba shi haƙuri akan ya daka ta kar ya bi takanta ,in badan wani tsalle da Asiya tai ta
janye ta gefe da yanzu ba wannan labarin ake ba,kai tsaye yai ficewar shi ba tare da ya ko waigo ya ga
halin da ta ke a ciki ba.
"Aunty Zeenat wannsn wanne irin abu ne haka ta ya za ki sa rayuwar ki da ta abinda ke cikin ki cikin
hatsari ko ba ki dubi kan ki ba ai kya yi duba da shi ai ","Asiya ki bar ni.....Asiya me yasa ma ki ka janye ni
da kan hanyar da kin bari ya bi ta kaina in ya so sai haddin kisa ya hau kan shi, wallahi Jaheed ka cuce ni
kuma Allah ya isa ban yafe maka ba,innan ina jiran ka za ka dawo sai ka yi mamakin bala'in da za ka zo ka
iske a cikin Gidannan,ke kin ga wuce mu tafi Gida domin ban ga abinda cigaba da zama cikin Gidansa zai
amfanin ba",takai zancen tana mai kama hannun Asiya ta fara ja,su ka nufi hanyar barin Gidan,ko ta kan
Gate Man dake ta faman ba su haƙuri ba su bi ba.
"Wai lafiya duk kun bi kun ishe mu, wannan sai faman kuka ta ke, wannan kuma sai faman cika ta ke
ta na batsewa sai ka ce wacce ake yi ma fanfo",cewar Baba Asabe bayan shigowar su wacce ta ke daga
zaune.
"Hmmmmm Baba Asabe akwai matsala wai yau Yayah Jaheed ne ke shirin bi takan Aunty Zeenat da
Motar don kawai ta ce ba ta yarda ya fita da wancan shashashar matar ta sa ba".
"Kamar ya ban gane ba,shi Jaheed ɗin ya fara shaye-shaye ne,ko-ko ya ci kan kare ne ?",Cewar
Mama,"Wallahi lafiyar shi lau,babu abinda ya same shi,kawai tsabar balaja'un ɗa Namiji ce",nan fa su ka
kwashe ƙarya da gaskiya su ka gaya ma su.
"Abun Mamaki wai Jaheed ɗin ne ya aikata duk wannan abun anya kuwa",Mama ta faɗa cike da
mamaki,"Yo ban da abunki Zaliha ai fiye da haka ma zai aikata jika ne fa wurin Hadiza,wanne irin baƙin
hali ne ba zai gada da ga gare ta ba,saboda tsabar munafunci da iya ƙulla makirci sai da ta raba ni da
ɗan'uwana ciki ɗaya,ki bar mutum in ya kasance ya na gadon mugun tsatso,sai da ta ga na baro Gidan
sannan hankalin ta ya kwanta"....."Kai Baba Asabe wannan da kamar kin yi ihu ne kin daɓama kan ki
wuƙa,ko kin manta nan Gidan ma da ki ke zaune Gidan ɗantane ",Cewar Nabila Yayar Asiya.
"A'a meye haɗin fura da kashi,don me ki ke ƙoƙarin danganta koko da giya,ai shi kwata-kwata ba irin
halin su ya biyo ba shi wannan sak ɗan'uwana ne Malam Ibrahim Mai sai da fata hafizin Malami,hanya
natsuwar sa ce ta a na bashi Auren Uwarku gatanan a zaune,kuma ni dalilin ta na ke zaune anan ba dan
wani ba,ato dan ki ji, yo ni Allah na tuba in badan haka ba me zai sa in zo in zauna anan ai da daki".
"Ta na kasa ta na dabo,ko kin mata shima Abbanmu shima ita ce ta haife shi,ba fa zai ji daɗi in yaji
kuna aibata masa uwa ba".....Asiya ta katse ta da cewa, "Ke dalla ki rufa mana baki waya ce aibata ta ake
ba halin ta ba ne ba,ai dole a faɗa ni na rasa wacce irin Zuciya ce da ke Nabilah duk irin cin mutuncin
ƴar'uwarki da akayi ba ki gani sai ƙoƙarin kare wasu a banza a wofi da ki ke,mutanen da ba su san ma
kina yi ba,in kin ji ba za ki iya goya mata baya ta rama abinda aka yi mata ba ki ja baki ki yi wa mutane
shiru "..."Ke Asiya ki yi min shiru domin ba dake na ke ba",....."Ke ce dai za ki yi ma mutane shiru
sakaryar banza mara zuciya kawai wacce ba ta san ta taya ƴar'uwarta kare martaba,ƙima da mutuncin ta
ba", Ummu Nurain ta katse ta cike da tsiwa muryarta dauke da sheshshekar kuka.
Sallallami Baba Asabe ta saka gami da ɗorawa da cewa,"Ni na rasa ina wannan talasurar yarinyar ta
samo wannan soloɓiyo ɗin wannan zuciya ta ta ba, kwata-kwata ba ki taya ƴan'uwanki jimamin halin da
su ke a ciki","Baba banni da ita da kusa da ni ta ke da tuni na kai ma ta duka a baki wata ƙila daganan sai
ta gane ta yi kuskure".Kamar ta ce ta na zaune bakin murhu.
Miƙewa tsaye tai gami da cewa da su,"Allah ya ba ku haƙuri amma duk da haka ba zan daina faɗa ba
ku bi duniya a hankali, Gimbiya Ayush dai matar shi ce,tafiya kuma ya tafi da ita ba yanda za ku yi sai dai
ku ɗauki haƙuri da dangana"......tun kafin ta ƙarasa ta zura da gudu ganin yanda Zeenat ta biyo ta,Baba
Asabe ce ta riƙota ta na mai cewa,"A'a kyale ta banni da ita Ni da kaina zan yi maganin,ko kin manta
halin da ki ke a ciki ne","Baba dan Allah ki bar ni in je in huce haushina akan wannan yariyar, Allah da sai
ta yi dana sanin sani na","Na ce ki kyale ta ki bar ni da ita na wallahi wani lokacin in na kalleta ita da
Alƙasim sai in yi tunanin ko musayarsu akayi min ba ni na haife su ba".
"Dawo zauna ƴarnan ai yanzu ba ita yakamata ki sa a gaba ba zo mu san yanda za mu yi da wannan
babban lamarin da ya tunkaro mu".cewar Baba Asabe.
"Yauwa Baba Asabe don wallahi har yanzu ina jin maganganunsa suna min yawo a cikin kai,karma
maganganun sa da suke nuni da kamar ya sake ni","Haba shi ɗin banza ya isa ya ce ya ya sake ki,ke ko
kuskuren sakin ki yai sai dai ki koma zama ɗakin Mahaifiyarsa,Uban shi fa ƙanin Mahaifin ki ne, sannan
da kakanshi Namiji da kakar ki ni ki Mace tsatson su guda,kin ga kuwa kusan ta yi kusan da bai isa ya iya
sakin ki ba,shi ɗin banza,waye shi".
Wata irin dariya suka saki su duka har Asiya na cewa,"Ina yin ki ƴar tsohuwa,hakan ya sa na ke ƙara ji
da ke Allah yakaro nisan kwana mu ƙara yin degree a wurin ki,na tabbatar da ke ce za ki yi mana
maganinsu",nan fa ta miƙa mata hannu su ka tafa kafin kuma su cigaba da tsara faruwar duk abinda su
je so.
Page 31
"Ina mai ƙara baki haƙuri akan dukkanin ƙalubalen da ki ke fuskanta ta dalilin Aurena da ki kai ,na kasa
baki farin cikin da kowacce mace ke expecting samu a wurin Mijinta,ki yafe ni",sai da Gimbiya Ayush ta
nisa kafin ta ce da shi cikin sanyi,"Na tsorata sosai ban taɓa ganin mace irin Ummu Nurain ba,sosai na
tsorata,ina jin kamar Shikenan za mu mutu ne tare da ita,na rasa me nai mata,ko dai Auren ka da na yi
shine mafi girman kuskuren dana aikata a rayuwata"......ya dakatar da ita da cewa,"A'a kar ki ce haka, sai
in ji kamar na gaza a wani fanni mai girma daga cikin rayuwar ki","Ba ina nufin haka ne ba,sai dai ina jin
wani iri idan naga kana biye mata sai inga kamar duka laifin ko nauyin faruwar haka ya na kaina",sai da
ya kama duka hannayenta ya riƙe kafin ya ƙara tausasa murya da lafazin shi,"Zeenat ba ta cikin hankalin
ta na rasa wa ya canja min ita,ta riga ta zama zuma sai da wuta,idan na cigaba da yi mata sanyi-sanyi
lamarin ta zai fi haka,hakan ya sa na fiddo hanyar da zan hukunta ta mafi kyawun hanya wanda da kanta
za ta fuskanci kuskuren da ta aikata har ta yi nadama,da izinin Allah wata rana za ta shiryu za ta bar duk
abinda ta ke mara kyau,ada na san ba haka halin ta ya ke ba,hakan ya sa na ke da sa ran wata rana za ta
gane gaskiya,ta koma asalin Zeenat ɗin da na sani",wani gajeren murmushi ta saki kafin kuma ta ɗora da
cewa,",To Ameen Allah ya amince ,yanzu ko dai fasa shiga cikin Masarautarnan zan yi in bika mu tafi
Lagos ɗin tare ?","Da na so hakan domin na tabbatar zan kasance ɗan gata kuma ɗan lele,da zaran na
dawo na yi ido huɗu da kyawawan idanunan naki zan ji na rabu da duk wata gajiya da na ɗebo,zan samu
kulawa da soyayya wadda har za ta iya sawa zuwa gobe da safe in makara zuwa gurin taron",Cikin aji
Gimbiya Ayush ta saki wata dariya gami da cewa,"A wayance ka sallame ni gami da nuna min ba zaka je
da ni ba","Wane ni ,waye Imam Muh'd Jaheed da har zai ce ba zai yi tafi tare da Gimbiya Ayush ɗin shi
ba,ai ban isa ba,domin ina jin tsoran hukuncin da ka iya biyo baya,domin nasan kujerar ta mai adalci ce
ba lalle ta yi duba da mi a matsayin Mijinta ba,tuba na ke","zaka fara ko,to bari in zo in tafi tun kafin
abun yai nisa",...."Tuba na ke bana kuma ba",ya faɗa yana mai riƙo mayafin ta,"Yaushe za ka dawo?",ta
tambaye shi ba tare da ta mai da hankali kan wancan batun ba,"Am inantunanin ba zan wuce four days
ba da izinin Allah ","To Shikenan Allah ya tsare,ya kuma bada sa'ah a abinda aka je don shi,ya sanya
sauƙin da ake son a isar ya isa ga waɗanda zasu amfana da shi,zan cigaba da yi maka addu'a har ya zuwa
san da za ka dawo","Ina alfahari da ke,zan kasance mai yawan tunawa da daɗaɗan kalaman ki har zuwa
sanda zan dawo,ki kula min da kan ki,bari in zo in tafi na sanar da Hameed ya same ni a Airport zai dawo
maki da motar ko za ki buƙaci yin amfani da ita".
"A'a ba sai an dawo da ita ba,ko ka manta akwai wadatar motoci a cikin wannan Masarautar,zan
samu Motar da zan yi amfani da ita".
"A'a Ni ma ban manta ba,amma a gani na kamar zai fi kyau kiyi amfani da Motar Mijinki,kamar hakan
sai ya fi girma ko?","As you said my beloved husband, yanda ka ce haka za ai,zan jira",Nan fa sukai
sallama tafito Bayi Mata guda biyu da suke dakon fitowar ta suka ɗauki kayan da ta zo da su,bai bar
wurin ba har sai da ya ga tafiyarta, sannan ya isa Airport ɗin kafin terminal ɗin su ya tashi su nufi garin
Lagos.
"Gimbiya Ayush irin wannan soyayya haka kamar ba za a mutu ba ,tun ɗazu ina hango isowar ku ina
daga Upstairs da na yi tunanin ba za ki fito ba har sai anzo an fitar da ku saboda tsabar nunama juna
soyayya bakwa ji ba kwa gani",cewar Gimbiya Fadeela da ke tsane gashin kanta alamun ta fito wanka.
"Oh ki ce ido ki ka sama na bamu sani ba,yaushe ki ka fara sana'ar sa ido ban sani ba",cewar Gimbiya
Ayush,"Ba wani sa ido kawai gaskiya ce na faɗa,na gan ki harda ƙaramin troly ince dai
lafiya","Hmmmmm aikin Yah Imam ne,sai da na ce masa ba zan ɗauko komi ba amma ya matsa sai na
taho da su,na faɗa masa duk abinda zan amfani da shi akwai a cikin Masarautarnan in babu ma in nazo
za a nemo min shi,amma ya ƙi yarda","Ni fa har yanzu ban gane abinda ki ke son faɗa ba,wanne dalili ne
yasa ki ka baro Gidan ki ki ka dawo nan ince dai ba wata matsala ko?","Ba wata matsala tafiya ce takama
shi zuwa Lagos shine fa na ta sa shi a gaba kan ya bar ni,in zo Gida kafin ya dawo,amma fa da ƙyar na
samu ya amince".
"Ki ce min kin zo hutu ne, a'a wallahi takawar ki lafiya Gimbiya Ayush amarya a Gidan Imam
Jaheed"...."Ke ni duk ba wannan ba,akwai